Yah Mu'allim
***
Another exclusive piece from the passionate writer of AYSAM, INTENSE LOVE, EHSAAS and SCARRED.
Chapter 9
Yah Mu'allim
Yau aƙofar gida Malam garba ya sauke su, daga Imsal har Natasha sunyi ligif a gajiye suke musamman Imsal da tun bayan break suke lab.
kwankwasa gate Natasha ta shigayi da ƙarfi, da sauri Malam Haruna ya ƙaraso yana musu sannu da zuwa,
Imsal ce ta amsa da
"yauwa"
tana gaishe shi,
"Ina wuni baba,"
yace
"lafiya lau yan makaranta andawo kenan?" jinjina mishi kai tayi ta bi bayan Natasha da already tayi gaba don yunwa take ji, aƙofar entrance ta sameta cikin nasiha take cemata
"wai sau nawa zan ringa ce miki ki ringa gaida bawan Allah nan Nats bakya ganin Babba ne kuma...."
"Please"
ta dakatar da ita a gajiye take faɗin
"Just let him do his job,
ba'a biya shi don ya ringa buɗe kofa muna gaida shi kullum ba,"
"Natasha shima badon yana so yake mana gadi ba Allah..."
Haɗa hannu biyu tai alamar roko take cewa "dan Allah kibari inci abinci seki ɗaura daga inda kika tsaya Malama Imsal"
tafaɗa tana shigewa cikin gidan.
Imsal tsayawa tai ta bita da kallo tanajin har cikin ranta babu daɗi ace babba kamar Malam Haruna kanwarta Natasha bata gaida shi duk sanda ta shigo gidan setaga dama.
Sanin inta matsa faɗa zasu ƙare dayi yasa kawai tabi bayanta tana sallama,
ƙamshin turaren da taji ne yasa tai sak don irin sane ya cika ajinsu ranar da ya fara zuwa kuma irinnsane ya makale a school clinic ɗin da aka kwantar da ita jiya,
Sannan irinsane acikin motarsa da duk inda ma ya zauna, idonta sauka yayi akansa yana zaune saman couch yana scrolling through MacBook ɗin sa shishi kaɗaine a falon.
Natasha har tayi ɗakinta, ji take kamar ta zama invisible ta wuce ba tareda ta gaidashi ko ta mai magana ba, ahankali ta zagaya ganin kamar baya kallonta cikin sanɗa take tafiya donma kar yaji takunta seda takama karfen stairs zata hau taji yace
"Sannu da dawowa"
Rintse idonta tayi tana ƙamewa awurin don bata taɓa ɗauka ya ganta ba idonsa na kan MacBook ɗinshi, juyowa tai taga har lokacin idonsa na kai ahankali ta tako ta ƙaraso gurinsa,
nesa dashi ta ɗan risina tana faɗin
"Ina wuni Yah mu'allim,"
Se alokacin ya ɗago yana rufe MacBook ɗin yayi crossing legs ɗinshi yana kallonta she looks so cute cikin school uniform ɗin,
Ɗan gyara necktie ɗin suit nashi yayi yana faɗin
"Sanɗar me kikeyi ɗazun?"
Rintse ido tai kafin ta shiga girgiza kai trying to deny ba sanɗa takeyi ba,
Amman kasancewar bata iya karya ba nan da nan body ɗinta yayi betraying ɗinta tai tsuru tsuru,
Yace
"na takura miki koh?
inata zuwa gidanku,
you don't wanna see me,"
Da sauri taɗago tana girgiza kai tamai rau rau da ido kamar zatai kuka,
Murmushi ne ya kufce mishi daga baki yana kallon yadda take ƙoƙarin kare kanta,
Yace
"words I'm not a recko,
da kike ta girgiza min kai kina jinjina kai,"
"Yah mu'allim ba haka bane naga kana aiki ne,I don't wanna distract you,"
tafaɗa tana wasa da yatsunta,
Ahankali yace
"should I tell you a secret?"
jinjina mishi kai tai jin yayi shiru yasa tai saurin cewa
"eh"
don ta tina yanzun yace mata bayason body language,
Hannunshi ya haɗe wuri guda yana faɗin
"The MacBook,"
Se kuma yayi shiru yana kallonta ƙasa ƙasa
"Is the one distracting from looking at you fully don shi ya kawo ni,"
batasan sanda wani tari ya sarƙeta ba jin abinda ya faɗa ɗin kuma kamar ba daga bakinsa ya fito ba.
Ruwan da aka ajje mishi saman center table ya ɗauka yana buɗe mata ya miƙa mata directly from the bottle ta amsa tana kaiwa baki,
Sha tashiga yi ba ƙaƙƙautawa har seda yace mata
"I think that will do"
yana mika mata hannunsa alamar ta bashi bottle ɗin, ba musu ta miƙa mishi instead of ya maida cap ɗin se taga ya ɗaga yaɗaura abakinsa shima ya shiga sha ahankali, wata irin kunyace ta mamaye ta ji take kamar ta nitse awurin, kaɗan yasha ya maida cap ɗin ya ajje asanyaye yake cemata
"where's your phone?"
Jakarta ta zamo daga kafaɗarta tana zugewa ta ciro mishi wayar da tunda safe rabonta da danna ta, don batada ɗabi'ar danna waya amakaranta.
miƙa mishi tai tana faɗin
"gashi,"
ɗan kallonta yayi ya kalli wayar ganin babu wani insecurity ko tsoro ko tashin hankali saman fuskarta yasa yace
"hold it,"
Wani kwalin waya dake gefen sa ya ɗauka sabuwar waya ce dal aciki ya miƙa mata yana faɗin
"hold it for me,"
amsa tai ta ɗaurashi kan wayarta.
Gently cikin mata bayani yake faɗin
"earlier na kira ki your on another call da safe,
I get jealous easily Imsal, I'm sorry to say but in ina kiran ki ina jinki on another calls raina zaina iya ɓaci wasu lokutan, and you have family da friends dake kiran ki ko yaushe that is why I decide to bring you a new phone wanda number nane kaɗai ze kasance aciki, I'll be the only person dazan ringa kiran layin kan wayar,"
Shiru tai tana kasa gane inda maganar sa ta dosa, don kawai ya kirata yaji tana waya shine ze siyo sabuwar waya ya kawo mata,
"Are you listening?"
ya tambaya jin kamar hankalinta ba a gurin yake ba jinjina mishi kai tayi kafin ta ajje masa wayarsa agefe tana faɗin
"zan faɗawa yaya first,"
ɗan murmushi yayi kafin yace
"Bin Umar?"
Jinjina kai tayi
Yace
"ɗauki phone ɗinnan Imsal,
he already knew"
da ɗan mamaki take kallonsa,
Ya jinjina mata kai.
Kafin yace
"yana sama be jima da hawa ba and I was here with him earlier mun tattauna akan treatment naki all the stuffs are with him ze miki bayani later kinji,"
Jinjina mishi kai tayi, kallon agogo yayi yana faɗin
"get ready for islamiyya, I'll drop you nima gida zan koma,"
Jinjina mishi kai kawai tayi ta miƙe ta ɗauki wayar ta nufi ɗakin Hajiya
da sallama ta shiga
Hajiya na kashingiɗe saman gadon ta tana jan charbi ta amsa mata ta ƙaraso tana faɗin
"Hajiya ina wuni mundawo,"
Murmushi Hajiya tayi tana faɗin
"Toh sannu da zuwa maza ai wanka aci abinci atafi islamiyya,"
jinjina mata kai tayi tana nuna mata sabuwar wayar daya bata tana faɗin
"kinga,"
ɗagowa Hajiya tai tana kallon wayar tace "kamar sabuwar waya ko,"
Jinjina mata kai Imsal tayi alamar eh, ɗan kallonta tayi kafin tace
"waya baki sabuwar waya Imsal?
ko Rayyanu?"
ɗan girgiza kai tai idonta aƙasa tace
"ba shi bane..uhmmm...yah mu'allim nefa dama yace....yace....wai,"
miƙewa zaune Hajiya tayi da kyau tana kallonta tace
"ki buɗe baki kiyi magana kin tsaya kina inda inda Imsal, "
Imsal kasa haɗa ido tai da ita kawai tace "bani yayi yace ze ringa kira cikinsa,"
tamiƙe tana barma hajiya wayar agabanta zata gudu, Hajiya tace
"Imsal dawo nan shi Abdullahinne ya baki waya yace zaku ringa magana?"
seda ta kai bakin ƙofa ta jinjina mata kai, murmushin Hajiya tayi irin nasu na manya kafin tace
"toh keme kika ce masa?"
ahankali Imsal tana wasa da jikin ƙofa kamar wata yar shekara goma ba tareda ta kalli Hajiya ba take faɗin
"cemishi nai sena tambayi yaya,
kinsan ya hanamu amshi abu agurin kowa inbe saniba, shine yace ya sani kuma yama yarda in ɗauka kawai,"
Hajiya jinjina kai tayi kafin tace
"bayannan meyace miki,"
Shiru Imsal tayi,
Hajiya jin haka tasan kunya take ji tace
"yace yana sonkine?
ko wani abu?"
dasauri Imsal ta gwalo ido tana girgiza kai kamar wacca aka faɗama wani babban zunubi.
Hajiya ganin yadda take neman tserewa yasa tace
"zoki ɗau wayarki nidai zan gamu dashine," "ki ajjemin Hajiya bari nadawo daga islamiyya"
tafaɗa tana saurin ficewa a ɗakin, koda tazo hawa bene bata ganshi ba ganin MacBook ɗinsa na nan yasa ta gane ƙila suna ɗakin Rayyan da sauri ta wuce zuwa nata ɗakin ta shiga tai wanka ta ɗaura alwala sallah ta farayi seda ta idar tukunna ta soma laluben hijab ɗin da zata saka.
Natasha ce ta turo ɗakin tana faɗin
"yah Imsal gashi"
tana wullo mata wata leda da kaya aciki mamaki tai ganin Natasha sanye da uniform ɗin bin Suhail yaushe aka basu, tashiga tambayar kanta, Natasha kamar tasan me take tunani tashiga cewa
"seda nagama zaɓa"
tana dariya
"sannan na kawo miki, ina shigowa yaya mu'allim ya bani su,"
Ɗaukar ledar Imsal tayi tana ciro kayan sababbi dasu fil amman da alamar har goge su anyi,
Ta kalli Natasha tana faɗin
"indai hijab ɗin dakika ɗauka yafi girma garama kidawo dashi kinsan na fiki tsayi ba,"
dariya Natasha tayi tana faɗin
"da inch ɗayan,"
Imsal tace
"ko rabin incine kinsan banason saka hijab ɗin dabe kaimin idon sahuba koh,"
Natasha tace
"kwantar da hankalinki kai ɗayane aina gwada kayanne kawai aka banbanta"
karɓa tayi ta shiga toilet ta saka tafito.
Natasha kallon yadda milk colour uniform ɗin yayi mata kyau take tana murmushi ita kaɗai kafin tace
"let's take a selfie"
tana ƙarasowa gabanta, tace
"bari nafara saka hijab nasan halin ki se kije kisaka mutane ba sutturar kirki aduniya" murmushi tayi tana barin ta ta saka hijabi itama nata dake hannunta ta zira tana faɗin "smile,"
murmushi Imsal tai ta ɗaukar musu hoton da yayi mugun kyau, dukda basa kama amman kana kallonsu ta yanayin idanunsu zaka gane sun haɗa jini don idon daddy ne.
Tare suka sakko ƙasa har lokacin bayanan, Natasha ce ta zuba abinci tana kallon Imsal tace
"wai bazaki ci abinci ba?"
"Ɗazun naci snacks da juice"
tabata amsa tana zama kan kujera da jakar islamiyyar ta arungume akirjinta gefenta kuma kayan Mubeena ne da Mama Zuhra ta ɗauka da safen ita bama ta sani ba tana makaranta ta wanke ta goge data dawo ne take ganinsu cikin press ɗinta.
Jin takun sakkowar mutane yasa takalli benen sau ɗaya taga shida Rayyan ne suka jero kamar wasu yan biyu don yanayin tsayinsu da kaurin jikinsu iri ɗaya ne sak, hatta da haɗuwa da kyau da kwarjinin dayake kan fuskokinsu na fisge sedai Abdullah ya fishi cikar beard da hasken fata.
"Inyeeeee yan makaranta har an shirya" Rayyan ya faɗa yana ƙarasowa gefen Imsal, murmushi tai mishi sanin idon Abdullah na kanta yasa ta jinjina mishi kai, yace "daganan se ina Unique nah?"
Ahankali tace mishi
"Islamiyya"
"Toh ayi karatu dakyau"
ya faɗa yana kallon wristwatch ɗinsa,
Yace
"Unique zan wuce can karkasa site,
daddy yasa na duba mishi wani aiki,"
Jinjina mishi kai tayi tana faɗin
"adawo lfy yaya, Allah ya tsare hanya,"
Yace
"Ameen Unique"
yana kallon Abdullah,
Yace
"Bin Suhail mu wuce ko?"
Girgiza kai yayi yana ce mishi
"I need to pick up something at home so zan fara biyawa ta can kawuce kawai zan biyo ka abaya,"
murmushi kawai Rayyan yayi sanin ba wani abinda ya manta yanason spending time da Imsal ne kawai yace masa
"Laters buddy"
yana ɗan bubbuga kafaɗarsa jinjina mishi kai yayi yana faɗin
"laters,"
Rayyan ya wuce yayi gaba.
kallon Imsal Abdullah yayi yana faɗin
"ready,"
jinjina mishi kai tayi, kafin tace
"Natasha bata gama cin abinci ba,"
Natasha da spoon din ta na karshe take kaiwa da sauri ta tura,
tana miƙewa ta ƙaraso falon tana faɗin
"I'm done"
da roban ruwan ta a hannunta, ɗan kallonta yayi kafin yace
"sit down and drink the water properly,"
bata musa ba sanin ba:a mishi gardama ta zauna ta shiga shan ruwanta.
Tanajin ya isheta ta rufe ta ajje,
ganin haka yasa yayi gaba Natasha ta mike tana kallon Imsal har yayi bakin ƙofa bata tashiba ganin kamar ya fita yasa Natasha juyawa da sauri cikin ƙorafi take faɗin
"wai badai shine ze kaimu ba innalillahi wa inna ilaihirraji'un wai shine ze kaimu?
Tasake tambaya
"na shigesu"
taƙarasa tana ɗaura hannunta saman kanta,
"Imsal kinsan tari kwakkwara ba'a yi a gefen sa zece ana irritating nasa,"
Dariya Imsal tafarayi ita kanta batasan sanda tace mata
"na gafa kamar yayi sauƙi ya dena saurin faɗa kamar dacan,"
irin kallon kinsan ma me kike faɗa Natasha tai, bata bata damar magana ba tace
"muje karmu sashi wani jiran muyi laifin dagaske"
hannunsu cikin na juna suka fito daidai motar Rayyan tana barin gidan suna kallon Abdullah nawa Malam Garba magana da alama faɗa mishi yake ya hutashshe dashi shi zekaisu, Malam garba se murmushi yakeyi.
ganin ya juyo ya nufi motar yasa suma suka nufi motar wannan karon Imsal ce take cema Natasha
"kece zaki zauna agaba,"
wani kallo Natasha tai nata tana faɗin "wallahi bazan zauna ba yadda kika saba zaman gaba motar Rayyan da Daddy shima zaman gaban zaki anan haka kawai nai misbehave ya kauɗe ni,"
Sanin tunda ta rantse ba zatai ba yasa kawai ta hakura suka ƙarasa gaban motar, mamaki ne ya kashe Natasha ganin ya zagayo ya buɗe kofar gaba yana wa Imsal wani shegen kallo da direct ta alaƙanta shi dana love yana cemata
"get in my lady,"
"My lady"
ta sake maimaita kalmar abakinta, Imsal bata musa mishi ba ta shiga Natasha kam dakanta ta buɗe baya ta shiga jin wani kamshi ya ziryarceta da sanyin Ac daya kunna take ƙoƙarin mamaye motar taji hatta da hankalinta ya soma kwanciya ta gyara zama tana leƙa yadda Imsal ta wani takure agaba.
zatai magana taji ya buɗe side ɗinsa ya shigo, shiru tayi tana kamewa itama don batason tayi rawar kai ta kwafsa.
Karatun ƙur'ani ya kunna yana tuƙi cikin nutsuwa suke tafiya har suka ƙara so Bin Suhail, har cikin harabar makarantar ya shigar da motar sa, ganin sun tsaya yasa Natasha buɗe ƙofar tayo tana faɗin
"yaya angode adawo lafiya,"
jinjina mata kai kawai yayi,
Imsal ma ta buɗe side ɗinta zata fice ahankali yace
"bakiji ba,"
Yana komawa ya kwanta saman steering wheel din lazily,
Juyowa tayi suka haɗa ido da sauri ta sauke gaze ɗinta,
yace
"Your niƙab"
se alokacin ta tina manta bata sauke niƙab ɗinta data ɗaura saman kanta ba,
hannu tasaka ta sauke shi ya sauke wata ajiyar zuciya yana murmushi yace
"good girl, keep it up,"
Jinjina mishi kai kawai tai ta fice acikin motar ta barshi, tana ƙarasa corridor na ajujuwa Natasha ta riƙota ashe bata shiga ajiba laɓewa tai,
"Me hakan ke nufi yah Imsal?
Naga yana miki wani kallo kallo kamar ba yaya mu'allim masifaffe ba,
Nidai Imsal Allah bana supporting ɗinsa karma yace yana sonki don wallahi ni nafison ki auri mutum faran-faran me sakin fuska wanda innaje gidanku duk wani rashin mutunci na zanyi ba tareda ɗarɗar ba gaskiya,"
"Nats"
Imsal tafaɗa tana ƙoƙarin rufema Natasha baki don da ɗan karfi take magana,
Jin tayi shiru ta cire hannunta tana faɗin "shi yaushe yace miki haka and even if he does did I?
banason haka don't ever do that to me again,"
ganin yadda Imsal tai kicin kicin yasa Natasha yin shiru har suka ƙarasa aji batace komai ba don harga Allah ita batason Imsal ta wani yi soyayya da ustaz ita datake son ta samu wanda ze wayar mata da yar uwa taɗan shigo gari amman Abdullah ai sedai ya ƙara mata ƙaimi gun ustazanci.
Su yan kadanne yau a ajin kasancewar rabinsu anbasu suspension, hakan yasa Natasha na zuwa aka fara bata labari se alokacin take jin full abinda ya faru in detail don Imsal summary ta mata kuma yanzunne ta gane irin rashin mutuncin dasu Latifa suka aikata ta tsine musu yakai cikin carbi.
yau se gata da zuwa gurinsu Imsal da la'asar tanaji Mubeena taimata tass bata tanka taba dai har aka idar suka dawo aji,
Imsal gani tai yau duk inda tayi da malamai da ɗalibai se anmata magana har wanda ma bata sani ba kuma da niƙab ɗinta amman ganeta sukeyi tsaf, masu yimata sannu nayi, harda masu tambayarta alaƙarta da director din.
se ƙarfe biyar da rabi suka tashi as usual abakin wata hauwa Natasha ke jin cewar iyayen wasu yaran sun dawo dasu sosai yau sun bada haƙuri sunce azane yaran Principal yaƙi karbarsu yace se sunyi satinnan farilla inji director haka ba yadda sukai suka mayar da yaran gida.
Ahanyar dawowa Natasha take bama Imsal labari tana faɗin
"wallahi ya min daidai for the first time strictness ɗinsa ya burgeni,"
"Allah ya kyauta"
kawai Imsal tace.
Suna ƙarasawa gida ta shige ɗakinta, zamanta kenan taji wayarta na ringing, ƙarasawa inda ta barta tai saman side drower ta ɗauka ganin Mummy ce tai picking tana murmushi don tayi kewarta sosai,
"Assalamu alaikum"
tafaɗa cike da kewa da ƙaunar da take ma mahaifiyar tata,
"Shut up"
taji Mummy tafaɗa cikin faɗa faɗa.
sak tai tana sulalewa agurin ta zauna, bata bata damar magana ba ta shiga faɗa
"Imsal ni zaki wulakanta na bawa yaro number ya kira ki kinsan schedule ɗinsa kuwa,
kinsan kalar commitment ɗin da yake kansa kuwa kinsan millions ɗin da wasu suke kashewa just to get his time and contact shine ke kinsamu abanza zaki wulakanta koh?
mene kika ma farouq eh?
Mekika mishi?
ita gaba ɗaya ma ta manta da wani farouq arayuwarta cikeda tausashshiyar murya take faɗin
"Mummy meyace namai?
nifa ban wulakanta kowa ba,"
Mummy shiru tai kafin tace
"nasan wulakanci ba halinki bane Imsal meyasa zaki fara uhmmm,
yaronnan bakisan yadda ya ɗaukake ki cikin zuciyarsa da rayuwar sa ba,
yau wuni yayi beci abinci ba yana ta rigima da ɗacin rai nan matar ubanshi ta kirani tana gaggayamin maganganu duk akanki Imsal ko so kike na rasa aikina ne eh after everything I went through nai working hard na kawo stage ɗinnan duk don na inganta rayuwar mu gaba ɗaya,"
shiru Imsal tai don ba gane maganganun Mummy ɗin take ba,
Tace
"daga yau idan ya kiraki yace kiyi mishi wani abu indai be saɓawa addini ba kiyi mai straight ba'a mishi gaddama, he hates no,"
"But Mummy school fa zanje yace wai in fasa inyi hira dashi kinsan kuma SSCE zamu fara,"
ɗan shiru Mummy tayi kafin tace
"kin tabbatar abinda ya faru kenan,"
jinjina kai tai kamar tana gabanta tace
"yes Mummy,"
tace
"toh da kika dawo meyasa baki kirashi ba?" shiru tai don batasan kalar ansar da zata bata ta kirashi tace mai mewai ta sanshi ne,.
"Alright zanyi ma tufkar hanci Imsal,"
"I'll talk to you later,"
bata kashe wayar ba Imsal na jiyota wata a background ɗin tana tambayarta
"ya akai?"
tashiga labarta mata Imsal ce ta kashe wayar tanajin koma waye wannan Farouq da yake nema ya shiga tsakaninta da mahaifiyar ta bata yinsa.
Seda akai sallar maghrib ta sakko ƙasa, Natasha ta tarar tana kallo ta wuce kitchen ta zubo abincinta ta dawo saman dining tana ci, Hajiya ce ta fito tana zama tace ma Natasha
"ke kaimin wa'azin Abdullahi ni banason kallon fina finan nan na masu jajayen kunne,"
Natasha cikeda ƙorafi take faɗin
"Hajiya aiba kullum akesa wa'azin nashiba Please kibari in angama zankai miki," juyawa tai tana faɗin
"Imsal bazaki je ki ɗau wayar ki da kika yasar ɗakina ba kin wulakanta kamar bada kuɗi akasa aka siya ba"
ita se alokacin ma tatina da wayar batace komai ba Natasha ta juya tana kallon Hajiya tace
"baga wayarta anan ba"
ta nuna saman center table.
Girgiza kai Hajiya tayi tana faɗin
"ba wannan ba sabuwa ce dal baki ganta ba Abdullahi ya kawo mata ɗazunnan" cikeda mamaki Natasha tace
"yah Imsal wai haka,"
Hajiya ce ta katse mata hanzari tana faɗin "aidama ni makaryaciyace,"
Murmushi Natasha ta shiga yi tana faɗin "yah Imsal muganta?
wace kala ce?"
tana ƙarasawa kusa da ita abincinta takeci ahankali tace mata tana ɗakin Hajiya,
da sauri ta wuce tanaji Hajiya nace mata karta sake ta har gitsa mata ɗaki tana cikin a dakarta.
Ko minti ɗaya Natasha batai ba ta dawo riƙe da kwalin dalleliyar wayar tana faɗin
Wow!
Wow!
ta ƙaraso falon cikeda excitement yadda kikasan ta taka rawa take faɗin
"Imsal this is an upgrade kinsan wai wace wayace wannan,"
Imsal da ko a jikinta batama san wayoyin ba balle tasan wace kalace tace
"wallahi sixteen pro ce,"
waro ido Hajiya tayi tana faɗin
"ko kicemin irin wayar da babarku ta siya take ta ɗagama mutane hanci, da sunan po ɗin nagane"
jinjina mata kai Natasha tai tana faɗin "project ba to ba Hajiya itace"
Hajiya riƙe baki tai tana faɗin
"Abdullahi tare albashin nasa yayi ya siya miki waya,
nifa banason almubazzaranci zezo ya sameni ne zanji inda yasamo wannan kuɗin ina likita ina ɓarin kuɗi haka?"
Natasha wara ido tai tana faɗin
"kai Hajiya da Allah karkice mai komai salan ma kisa ya dena siya mata abubuwa masu tsada da kyau, abeg meye sixteen pro bakiga yayar tawa bace ba,"
ƙarasawa tai tafara unboxing wayar, Hajiya tace
"ke wai takice naga se wani rawar jiki kike yi karfa kije ki ɓata mata"
bata kula taba har seda ta ciro wayar sabuwa gal fara, ta shiga jujjuyata tana faɗin
"bari nasa miki charge,"
gefen kwalin taga wani sim tace
"laaa Imsal harda sim card yasa miki, maganata ta tabbata"
ganin Hajiya nata mata gorin rawar kai yasa kawai tasa charge ta barta, seda taga Hajiya ta shige ɗaura alwalar isha'i ta dawo gefen Imsal data gama cin abinci tana faɗin
"nace sonki yake kince a'ah?
toh meyasa ya baki waya eh?
bakina da waya ba meye ma'anar hakan inba soyayya ba?"
Shiru Imsal tayi kafin tace
"nidai bece yana sona ba haka kawai yace in ɗauka kuma shishi kaɗai zan ringa waya dashi da wayar bayaso ya ringa kirana yaji line busy,"
Natasha buɗe ido tai ta kalleta tasake kallonta kafin ta rufe tana faɗin
"wai yah mu'allim ɗinne yace miki haka," turo baki Imsal tayi tana faɗin
"zanyi mishi karyane,"
Wani irin cakawa Natasha tai tana faɗin "kuma shine har yanzun baki gane me yake nufiba Imsal rainamin hankali kawai kike, koɗan shekara biyar yaji statement ɗinnan ai yasan mugun kishinki yake shiyasa ya faɗi haka, kuma ba'a so saida kishi,"
Toshe kunnanta tayi alamar bama tason taji maganar tata,
Natasha tai jim se kuma tace
"Imsal amman fa masifaffe ne zaki iya rayuwa dashi ahaka ga shegiyar sa ido da takura kin tuna..."
"Nats Please"
Imsal taƙarasa tana dakatar da ita
"Is not what your thinking"
taƙarasa faɗa tana ɗaukar wayarta ta haye sama binta da kallo tayi kafin tai murmushi tana faɗin
"har anfara bakiso nafaɗi aibunsa koh, toh wallahi sena faɗa sedai ki tsireni."
Se wurin tara Imsal ta ƙara sakkowa ganin Rayyan har lokacin be dawo ba, ta saka number sa ta fara kira ringing biyu ya ɗaga yana fadin
"Unique ya?"
Cikin tausashshiyar murya tace
"kana ina?"
Yace
"ina nan ina bawa fure na ruwa,"
Bata gane me yake cewa ba tace
"meye kuma fure?"
Be bata amsa ba yana murmushi yace
"naki malamin be fara ɗaura miki darasi bane kikeso ki takuramin ni ina nawa karatun,"
Tace
"yaya kayi magana straight kawai bana gane wannan yaran naka, is late fa yaushe zaka dawo"
Yace
"toh hira nazo ina nan tal'udu gurin kawarki" tace
"kaiiiii yaya wai da gaske"
yace
"a'ah da wasa,"
daga ɗaya bangaren ya miƙama Mubeena wayar karba tayi tana faɗin
"Imsal baki barci ba,"
Dariya ma ta bata yadda take wani lanqwasa murya kamar ba talkative Mubeena ba wai tana gaban saurayi, tace "barci kuma karfe taran, wai dagaske yana wurinki?"
Tanajin murmushin ta amman bata bata amsa ba.
"Abin yar zagaye akai min kenan shikenan zakiyi bayani gobe,"
dariya Mubeena ta shigayi tana faɗin "bazaki gane bane Imsal I'll explain tomorrow in sha Allah,"
tace
"Allah ya kaimu"
karɓar wayar Rayyan yayi yana faɗin "Unique kije ki kwanta don ba yanzun zan dawo ba seda safe ya ƙarasa yana kashe wayar"
bin wayar tai da kallo tana murmushi ta jinjina kai kawai tana hasaso yayan nata da Mubeena.
*Abdullah*
Wurin ƙarfe tara da rabi ya shiga juyi yana sake trying number ta amman har lokacin akashe bata shiga alamar bata kunna wayar ba har lokacin, gyara kwanciyar sa yayi yanajin duniyar tana mai ba daɗi duka kafin ya miƙe zaune yana fitowa,
daga corridor yana jiyo dariyar Mubeena da ƙus-ƙus din magana kamar har lokacin da mutane a falon kallon agogo yayi kafin ya wuce falon hannunsa cikin pocket ɗin pants ɗinsa ya tsaya yana kallonsu.
Daga shi har ita sun lulu basusan ma da wanzuwarsa ba da alama don magana yake mata tanata dariya, shi kuma yana murmushi,
"Excuse me"
yafaɗa yana kallon both of them, da sauri Mubeena ta matsa daga gefen rayyan don akujera ɗaya suke zaune amman da ta zara a tsakanin su.
"I think firan ya isa haka Muby seda safe gobe akwai School"
ya faɗa strictly ba musu ta miƙe tama kasa haɗa ido dashi don ta manta gaba ɗaya a sashensa suke tace ma Rayyan yaya seda safe ka gaishe dasu Imsal ta ɗau wayarta tana zira takalmanta ta fice daga ɓangaren nasa baki ɗaya.
Rayyan riƙe baki yayi yana kallon Abdullah kafin yace
"I was planning to leave by ten,"
Yace
"me kuke cewa harna awa biyu inba ƙarya zaka zauna kaita karan tama yarinya ba, Please daga yau karku ƙara wuce ƙarfe tara idan ba haka ba,
ka koma zuwa da rana kawai,"
jinjina mishi kai Rayyan yayi ba tareda yamai musu ba don shima yasan lokaci na nan zuwa ze rama.
yace
"afwan babban yaya banzo da wuri bane kasan eight nashigo"
yace
"yes zuwa nine ai yaci ace kungama zaman meye kuke har ten saura,"
miƙewa Rayyan yayi ya ɗau wayarsa da key ɗinsa yana faɗin
"nima bari na wuce Unique nata kewana tanata kirana awaya,
She miss me,"
yaƙarasa faɗa yana kallon Abdullah daya bishi da ido jin abinda yace
"so that means batai barci ba idonta biyu kuma she do miss people shi ka ɗaine bata missing,"
Tsabar haushi be cema Rayyan komai ba har ya fice daga sashen nasa baki ɗaya, jingina yayi da gefen kujera yana lumshe ido yanajin kamar ya kira main line ɗinta amman kishin sa baze bari ba yana tsoro ya kira yaji line busy yayi hurting kansa, yasan Imsal nada tarbiyya yasan tanada hankali amman kullum yakalli irin kyan da Allah yayi mata zuciyarsa seta motsa saboda yasan yadda takemai acikin idonsa in yakalleta Allah ne kaɗai yasa dubbannin mutaben da take musu irin wannan kyan suma, da zuciyarsa tayi shawara dashi kafin tafara jinta tun tana ƙarama tabbas dabe bata iznin zurfafa gurin ƙaunarta ba,
Kullum jiyake kamar yana cikin hadarin rasa ta.
*Imsal*
Imsal na gama waya da Rayyan ta ƙarasa ta ciro sabuwar wayar data gama charge ta wuce da ita zuwa ɗakin Natasha bata tai tace mata ta saita mata komai kafin gobe da safe don ita bata wani iyaba tace mata toh shikenan seda safen ta wuce ɗakinta.
idonta biyu lokacin da Rayyan ya dawo,
don tanajin sanda ya buɗe ɗakinta ya dubata sannan ya fice batace mishi komai ba don tunanin sa tayi barci,
se can sannan ɓarawon barci yayi gaba da ita kamar yadda tasa ba karfe huɗu ta farka tayi na filfilin data saba,
tafara zikri har zuwa sanda aka kira sallar asubah, seda tai asubah ta fara karatun ƙur'ani acikin zuciyarta har zuwa gari yafara sha ta kammala tai addu'o'in.
ta tawuce ta faɗa toilet wanka tayi ta shiga shiryawa cikin uniform ɗin ta.
Turo Kofar ɗakinta akayi tana saka safa Natasha ce ta shigo lazily da alama tashinta abarci kenan don sleeping dress ce ajikinta tai dumping mata sabuwar wayarta saman bed tana faɗin
"tun ɗazun yake ta kira ya hanani barcin kirki ga wayarki nan na samiki komai tun jiyan,"
Tana ƙarasa faɗar hakan ta fice tana mita tana ƙunƙuni,
zuwa tayi ta ɗauka tana kallon screen ɗin, ganin 4 misscalls yasa tai dialing ahankali ba tareda tayi shawara da ƙwaƙwalwar ta ba zuciyarta ne kawai ya raya mata tayi hakan,
Se da ta kusa katsewa ya ɗaga yana
Sallama cike da nutsuwa ta amsa, shiru sukai dukkaninsu shikam sauke numfashi yayi don jiya da kyar ya samu barcin two hours tinanin tane ya gama addabar zuciyarsa baki ɗaya.
Jin ba zatace komai ba yace
"ina kwana,"
kunyace ta rufe ta jin shine ya fara gaisheta asanyaye tace
"Ina kwana Yah Mu'allim,"
Shiru yayi kafin yace
"we need to change that,"
dan jim tayi don batasan me yake magana akaiba,
Jitai yace
"Ko nima nafara kiranki da Ya Mu'allimati Imsal,"
Yadda yayi maganar cikin nitsuwa da muryarsa mai sanyi yasa ta nemi wuri ta zauna tana rufe fuska kamar tana gabanshi,
ahankali tace
"aini ɗaliba ce ba malama ba,"
Yace
"nima ɗalibi ne ba malami ba don haka adena cemin yah mu'allim ɗin nan,"
Batasan sanda ta tambaya cikin sanyi ba "toh me zance maka yaya?"
ahankali kamar me raɗa yace
"malak qalbik,"
Yadda maganar ta shiga cikin kunnen Imsal direct zuwa zuciyarta ta nufa tanaji kamar ta nitse awurin,
Jin tayi shiru ya ɗora da,
"Urīdu qalbaki lī waḥdī, lā urīdu shay’an siwāh,"
(inason zuciyarki ne kaɗai, banason wani abu bayan ta)
Ji tai maganganun Mu'allim ɗin nata na ƙoƙarin fin ƙarfin kunnuwanta kamar ya manta da ita yake magana,
Jin bata ce komai ba yayi murmushi ahankali yana tambaya
"Hal anti khajūla?"
(Kina jin kunya ne?)
Jinjina kai tai kamar tana gabansa muryarta na ɗan rawa saboda yadda ta daɗe batai practicing Arabic dinta ba gudun kada tai mistake tace mishi,
"Shwayya bas...,"
(yar kaɗan...)
Murmushi yayi yana juya harshe zuwa turanci dama so yake yayi testing har yanzun bata manta larabci ba kuma yaji bata mantaba ɗin, don mahaifinsa ke koyama yaran tunkan ya rasu, yace
"You don't need to be shy kinji,
we are going to be one bari nabarki kiyi shirin school koh,"
Jinjina mishi kai tayi, yace
"one sec yaushe zanzo nagan ki?"
shiru tai nanma no answer yace
"inzaɓa time da kaina?"
"uhmmm"
tace mishi kawai, tana rintse idonta don sosai take jin kunyarsa yace
"Toh ni yanzun ma zan iya zuwa I'm desperate,"
Batasan lokacin datai chuckling ba tana girgiza kai,
Tace mishi
"se anjima yaya,"
yace
"again ko,"
da sauri ta rufe bakinta alamar tayi kuskure yace
Khallī bālik ʿalā nafsik ʿashānī (ki kulamin da kanki)
Bata ce komaiba ta katse wayar tana lumshe ido.
ta dafe saitin zuciyarta yadda yake bugawa kamar ze fito kafin ta saki wani murmushi tana saka tafin hannunta tana rufe fuskarta kamar wata taɓaɓɓiya ita kaɗai.
kasa fitowa tai da wuri gani takeyi duk wanda ya kalleta ze gane maganganun da Abdullah ya faɗa mata awaya da har yanzun suke mata yawo acikin kunnuwa da Arabic accent ɗinsa me mugun daɗi.
Natasha jin shiru har ta shirya ta kammala breakfast Imsal bata sakko ba yasa ta ƙarasa ɗakin tana faɗin
"wai badai har yanzun wayar kike ba?"
ganin ba waya akunnen ta yasa tace
"kizo kiyi breakfast mutafi,"
miƙewa tayi ta fito tana kasa yarda su haɗa ido da Natasha, Natasha binta da tai da kallo kafin tazo ta jera da ita tana faɗin
"ya Imsal me yace miki uhm?
badai bossing ɗinki yake around ba?"
"His not like that"
Imsal tafada asanyaye tana ƙarasawa saman dining, Natasha dariya tayi tana faɗin
"Imsal kareshi kikeyi, kaddai ki nuna mishi kema kina sonshi haka nasan ke farin shiga ce a soyayya amman ba'a zaƙewa ki kula,"
wani irin ɗagowa Imsal tai tana kallonta cikin denial take faɗin
"when did I say I like him, kamarfa yaya yake, kuma ba kareshi nake yiba kawai gaskiya ce"
Tace
"koba yayaba,
is all over your face look at how your cheeks sukai turning red, admit it you like him, wai ya iya soyayya ne har haka?"
Ta tambaya tana dariya don kwata kwata zuciyar ta ta kasa aminta da cewar Abdullah me daure-dauren fuska ze wani iya tsayawa ya bawa mace lokaci da kulawar me kyau ba.
"Yah Imsal Please tell me now?
I'm your only sister inbaki gisting dani ba da waye zakiyi kedai ba ƙawaye ne dake ba kawarki ɗaya Mubeena Suhail zakije kice mata yayanta yace miki kaza yace miki kaza ne just tell me,"
Ahankali tace
"kawai cewa yayi yaushe zezo yaganni fa' tana kora ruwan tea ɗinta mai ɗumi, Natasha tace
"se kika cemishi me?"
Imsal kamar batason magana tace
"ni ba abinda nace,
shine yace ze zabi time dakansa,"
Natasha kaɗa kai take alamar tana saurara jin imsal bata ce komai ba, kasa haƙuri Natasha tayi tace
"se yace me?"
ɓata rai Imsal tayi tana faɗin
"your not my mother bazan faɗa ba da kike sani agaba"
dariya ta farayi tana faɗin
"Imsal nifa koya miki soyayyar nan zanyi karkije ki ringa mai blunder gashi mafaɗaci...."
"Baya faɗa"
tai saurin faɗa ba tare tasan kareshi take ƙoƙarin yi a idon Natasha ba,
Natasha tace
"faɗawa wanda besan shiba damacan yafi raga miki akan kowa ashe shi kamu yakeyi tun muna tal'udu takura mikin dayake ashe duk kansa yake ma tanadi"
Miƙewa Imsal tai daga saman dining din tana faɗin
"nina ƙoshi"
Dasauri Natasha tariƙe hannunta tana faɗin
"Sorry Allah nagi shiru, bazan sake cewa komai akansa ba dawo kici abinci ki"
ta ƙarasa tana dariya ƙasa ƙasa zama Imsal tayi, tana wasa da fork ɗin hannunta kawai.
Its fatoumspassion IMSAL
Don't forget to
Share
Like
Comment
Vote
SPECIAL ANNOUNCEMENT
Ina farin cikin sanar muku cewa zan fara posting sabon novel dina IMSAAL a ArewaPen da Wattpad 🤍
But don’t worry… WhatsApp readers are still my priority 🫶🏽
Nothing is changing here, this is still home ❤️
To celebrate this, I have something special for my real supporters
🎁 The FIRST 20 PEOPLE to:
✔ Follow me on ArewaPen
✔ Follow me on Wattpad
Will get FREE entry into my paid WhatsApp group 💫
🎁 HOW TO QUALIFY 🎁
After following me,
📌 Take a screenshot showing you’re following me on BOTH platforms
Then send it to me on WhatsApp 👇
📩 ***
⚠️ Include your username
⚠️ Only the first 20 valid people will be accepted
⚠️ No screenshot = no entry 👀
ArewaPen @fatoumspassion
Wattpad @fatoumspassion
Hurry… once the 20 slots are gone, that’s all 🔥