TALES OF THE WAZEERIS

the alliance sealed

by @surayyahms

*10.* zamkora's..


ummu salma ta jima tana safa da marwa a tsakar uwar dakinta dan ita mace ce me zafin kai da rauni she carries alot of trauma nd pain in her heart da jimawa najin cewa ita din babbace agidan wazeeris amma har yau jininta bai da wani iko da daraja me girma..

tanaso kota yaya ne yau dinnan ta samo wann daraja ma jikarta leelah ta hanyar kulla alkwarin auren nan sa yarima shamsan, dan tun da suka dawo yau daga masarautar kano Da kyar da fitina take iya danne wnn restlesness da intense anxiety datakeji da kuma damuwarta dan ta zubawa sarautar Allah ido, tana dai jira taga uban meye Nana A zata aikata yau a fadar iko idan magann auren yarima shamsan ya taso agaban kowa.

after few moments Gidan ya sake dauka wa da wani irin shiru sai can wajajen daf za'a doshi azhar kafin nan kofar golden gate na farko ya buga da alamr isowar sabbin baqi, nan masu tsaron kofa suka bude musu gate

manyan jefafai GMG yukon farare kall da jan tuta ajikinsu suhudu kacal suka shigo cikin wazeeris mansion ajere suna tafiya ahnkli kmr baza su tafi ba.

sarki murad ne da wasu shegun kayan sarauta ajikinsa a mota na biyun sai matarsa da yarsa Arisha ana ukun kuma da securities ne da yan rakiyarsu da basu wani wuce mutane uku uku ba

tsabar kiyayya da gaban dake tsakaninsu da ahalin wazeeris shi baima taɓa taƙa kafar sa yaxo cikin wannan gidan ba sbd duk wani tubalin tsana da rashin adalci da aka kafta ma kakansa imamu yan uwansa maza guda goma da suka mutu duk daga nan gidan yafara tashi.

har motocinsu suka iso cikin golden gates na karshe kuwa babu wanda ya tarbe su da murmushi ko kalmar maraba…

kusan komai a tsaye yake ga wani irin shiru mai nauyi da ke nuna musu tun daga kofa cewa sun shigo inda ba a kaunar jininsu koda na minti daya

daga shi har izuwa kan matarsa gimbiya amani noorain data rufe jikinta da wani alkyabba mai daraja basuda nitsuwa aransu saidai yarsu Arisha dake gefe tana zaune a nitse ta riga tay nisa acikin wani duniya nadaban ganin irin gidan iko da mulkin da ko a mafarkinta bata taɓa kawosa ba

dan kuwa tharim vale da ultra huge mansion din wazeeris sun wuce yadda ake fadinsu a tarihi, koina da komi datake kallo tacikin windon motar yanayi mata ne kamar mafarki dan bata taɓa ganin inda iko da dukiya yake nuna kansa a fili kamar nan wajen ba dan tama kasa gane ko nan din gida ne ko wani dniyar duba da tsarinsa da girmansa ta wuce ka ce masa gida.



koda motocinsu suka kai ga wajen tsayawa saida suka ci akalla minti 5 kafin nan duka suka sauko kasa securities dinsu na zagaye dasu

a matsayinsa na sarki kamata yayi ace wani babba ne agidan zai fito waje danya tarbesu amma kuma inaa suna saukowa kasa bada jimawa wani dan dattijo daga cikin servants na gidan sanye da uniform dinsa shine kawai ya tunkaraso wanda kafin ma su hadiyi yawu kai tsaye cikin ladabi yace nine zan isar da ku fadar iko...

tun daga nan ran sarki murad yakara baci amma baice uffan ba servants din yana wucewa gaba kmr da minti goma snn suka fara binshi abaya


suna takawa ahankli idanuwan Arisha ya gama sauyawa tanaji kamar kanta na juyawa dan bata taɓa tsammn cewa haka girma da darajar tharim vale yake a zahiri ba.

this is even more than what she craves for dan babu hadi da gidan ubanta..

komi na mansion din wazeeris ya gama tafiya da zuciyarta da imaninta sai kalle kalle takeyi tana dan lumshe idanunta ahnkli tare da imagining kanta acikin nan gidan a matsayin jinin su, inama ace anan gidan ta taso with all this luxuries nd servants suna bauta mata tako ta ina hala da bazata taɓa tunanin jin bukatar samun wani matsayi a duniyar nan ba.

majestic tall greek inspired buildings ta dinga kalla har aka bude musu golden gate na uku suka iso sashen uwarjini bata ma lura ba saida taji masu gadin kofa sun dakatar dasu atsaye kafin wanda zai kaisu ciki ya fito.

lokcin sarki murad ya gama hatsala da irin tarban kaskanci daya ga anfara musu sunci wani minti 10 again a tsaye kafin nan wani servant din kuma ya fito ya sake musu iyo cikin sashen uwarjinin kai tsaye.

yana lura har iyanxu babu koda bawa agidan daya musu gaisuwa ko ya musu kallo na biyu...

suna shiga can ciki tun a falo na biyu security suka dakatar da yan rakiyansu da securitie din su anan.

sarki murad zamkora ya taka kai tsaye cikin fadar iko da cikakken daure fuska da girman kai, matarsa amani da yarsa suna biye dashi idanuwansa kai tsaye na kallon gaba

matarsa ce kawai  tadan shimfida wata nutsuwa a fuskarta duk dama zuciyarta na bugawa sosai tana jin yanayin wurin kamar sun shigo wani irin duniya ne nadaban dan wannan ba irin fadar da suka saba gani ko shiga bane.

fararen idanuwan arisha na yawo cikin fadar da nutsuwa mai sanyi komi da komi take karewa kallo kmar tana haddacewa

 tsaro ne takota ina a kewaye dasu amma duk wannan shigowar tasu da alaman bata girgiza uban kowa ba dan anan fadar tharim vale duk wanda yazo  will just look ordinary nd less powerful in the environmnt.

babban kofa me tsayi aka bude musu suka shiga ciki suka tsaya cak atsakiya ganin kowa yana xaune yana abunda yake gabansa

tamkar wanda ba'a wani expecting dinsu dan babu wanda ya daga kai ya kallesu sosai bare a nuna cewa akwai wani muhimmin bako a fadar

ganin shigowarsu wajen bai canza komai ba yasaka cikin zucyr gmbya amani ya kare tsinkewa.

Arisha ta zuba ido tanata kallon jerin iko da ya cika wajen kanta na juyawa da sauri

shugaba imran ne zaune da nutsuwarsan nan mai nauyi, fuskarsa a tsare yke kullm kmar dutse, anan gefensa ummu salma wanda daraja da kamun kai suka lullubeta kwayar idanuwanta na kallon can kasa tanamai ayyana lissafi da tunanin meye zai zamo makomarta dana jikarta leelah.

daga daya bangaren zafar wazeeri sai nana A suna zaune cikin cikakkiyar nutsuwa da alama tagama shirya komi kwayar idanunta ta dago ta xuba akan sarki murad ba tare da taboye masa tsabar tsana dake tsakaninsu ba.

wasu tsofaffin dattijai biyu ne agefenta irin tsofin magadan jini da tsafi wanda dole sai dasu atsakiya ake kulla yarjejniyar jini..

ubangida salis abdqadir dattijo mai tsawon shekaru da dan uwansa sheikh haroun zubair wanda muryarsa kadai na iya sanya daki ya dauki shiru.

tsofin nan sune zasu tabbatar da wann doka ta yarjejiniyar hadin aure da zai wakana tsakanin ahalin nan guda biyu snn su ne baqin ikon da baya bukatar hujja anan gaba.


duk jarumta da daure fuskar da sarki murad ya shigo musu dashi bai isa ya sa ace musu su zauna ba hakanan dai akabarsu a a tsaye da fuska a daure.

idanuwan sarki murad daya sauya kala yay jaajur na zagaye su daya bayan daya yanaji kmr ya juya yabar wajen amma ina hakanan ya tsaya cak atsakiya tare da danne wani abu me tsananin nauyi azcyrsa


gimbiya amani noorain na tsaye a bayansa cikin natsuwa duk dama zuciyarta tana bugawa bana kadan ba dan bata taba jin kanta a kaskance har haka ba 

yarsu arisha kuwa tuni
ta riga ta nutsu cikin kallon mutanen dake gabanta wanda komi nasu ya gama tafiya da ita.

wann ne irin daraja, iko, dumbin dukiya, karfin mulki, kima, tsaro da zazzafr izza da kuma girman kan datake so taga ta rayu aciki.

gaba daya sai tanaji aranta kamr ahalin wazeeris shine asalin suka dace da yarinya kamar ta. this is where she meant to be ba can fadar ubanta me tattare da tarihi da jinin bayi ba.

suna tsaye har na tsawo mintuna amma shiru har abun ya fara zama abin raini

daidai lkcin da srki murad yaji kamr bazai iya daurewa ba har zai hatsala ya juya dan ya fita caraf sai yanayin dakin kuma tuni ya canza batare da anyi magana ko an sanar ba nan kofar bangaren uwar jini ya bude a hankali ta shigo cikin tafiyarta mai nauyi da iko bata sauri amma sautin sarkan kafarta ya riga ya sanar da isowarta

numfashin sarki murad atake ya tsaya cak jikinsa ya fara rawa rawa ta ciki dan tsabar irin qiyayya da tsanar dayake ma wannan matar

nan kowa ya mike tsaye atare ba tare da an ce kala ba

jikin sarki murad xamkora ya dauki wani irin zafin da bai shirya masa ba dan da wani irin tafiya me tattare da zurfin iko uwarjini ta wucesa da shi lokcin yanaji kamar jinin jikinsa ake tsiyaye tsabar zafi..

wannan yanayin shi ne abin da ya fi bashi haushi a duk duniya

cikin iko uwarjini ta wuce gaba batare da ta kallesu ba har ta zauna a kujerarta dake a gefen dama da danta shugaba imran layin da dattijan nan biyu suke har saida ta zauna kafin nan ta dan daga hannu sama kadan

kowa ya nemi waje ya zauna anitswa har sai a lokacin ne snn nana A ta nuna musu sarki murad kujerar xama


sarki murad da jikinsa yake wani irin tafasa taciki da kyar ya zauna badan son ransa ba kmr wanda aka tilasta masa.


shiru ne ya sake mamaye wajen after like 2 mints ubangida salis abd-qadir ne yamike tsaye anitse yafara magana muryansa na fita a hankali amma tana kaiwa kunnuwan kowa atsanake.

babu wani bata lkci kai tsaye yace masarautr zamkora ya jima yana bijirewa kiran fadar iko
kuma duk lokacin da aka bijire kasa tana amsawa da nata kalar hukuncin

nan kwayar idanunsa suka tsaya kan sarki murad yace "kai yaro, da ace ka amsa kiran da aka maka tun farko da abubuwa da yawa da suka samu babanka salim zamkora da basu faru ba amma abunda ya faru ya riga ya faru


nan sheikh haroun zubair ya mike tsaye cikin karasa mgnr acikin sanyi yanamai cewa baxamu koma baya ba

cikin katseshi da iko da taurin kai sarki murad yace "wann ne dalilin gayyatar da aka min?

kai tsaye sheikh haroun ya daga kai ya kalle kwayar idonsa yace "don kwantar da wannan yanayi na qiyayya, tsana, domin tsaftace abin da aka tabo na mutuwa akan ahalinmu gabaki daya ruhi me tsarki ya nemi hadin jini.

sarki murad bai wani fahimce inda maganr ya dosa ba sai baice komi ba ya xuba masa ido..

anitse tsohon yace daya daga ‘ya’yanka mata za ta shiga cikin ahalin wazeeri.

dedenan numfashin gimbiya amani noorain ya dan tsaya cak ta dago kanta da sauri kuma a raxane ayayin da idanuwan Arisha suka haskaka da wani irin tsnnin mamaki mai tattare da wani irin tsananin farin ciki aranta ganin burinta na kasncewa agidan nan zai samu cika acikin sauki


sheikh haroun ya cigaba da cewa idan lokaci yayi da yayanka mata duka suka isa aure zamu zo da yarima daga jininmu zai zabi daya acikinsu za'a kulla wann alaqa ta auren jini da zata kare ahalinmu duka.

sarki murad dayajima da shiga shock ya saki wata karamarr dariya data kufce masa abazata gabobin jikinsa har na rawa kar kar yamike tsaye da tsananin fusata a yanayin sa yana kallonsu duka da karfi yace

“Hakan Bazai taɓa yuwa ba baxan taɓa mika yaya na ga wann zuriar taku ta zalunci ba..idan ku kun mata baya to mu bamu mantashi ba
..na rantse da...

kafin ya karasa dire rnsuwar shugaba imran ya katseshi ba tare da daga murya ba yace"..Enough. ba tambayar ixininka akeyi anan ba..doka ce...idan lokaci ya yi jinin wazeeri zai dauki daya daga cikin  ‘ya’yanka mata dan haka kaje ka shirya kana da lokci mai tsayo dazaka fahimtar dasu iya abunda ake bukata daga garesu tun kafin lkaci ya kure.

sarki murad dake ɓari kar kar da tsananin bacin rai xai magana nan kenan yaga take security sun zagaye shi da bakin bindiga technology ce irin wanda bai taɓa gani aruyuwarsa ba..

gimbiya amani noorain tay sauri ta miƙe tsaye taje kurkusa dashi ta rike gefen rigarsa da alaman sassaita shi kafin nan Arisha ta taso itama ta tsaya agefensu tay shiruuu

uwarjini data gama karewa arishan kallo daga sama har kasa ba ta kara magana ba sbd ko kadan yarinyar bata mata tsari da kyaun da ma zata iya haɗata jininta da su ba.

tasan yaran murad guda biyu ne and she wonders why d oda girl was not brought here..

koda shike kmr ance mata sun turata qasar waje karatu...koma miye ne bataga alamr wann ahalin suna da kwarjini da kyaun da zasu hada kafada da yarima shamsan

dan haka koda anyi auren duk wacce shamsan zai aura saidai ta tsaya musu a matsayin baiwa kuma bazata bari ya haihu da wann kaskantacen ahali masu snyin jini ba.

adeden nan taron ya kare babu wani dogon salama tsakaninsu nan dattijn nan suka saka hannu atakarda aka manna hatimi.

sarki murad ya doshi kofa fuskarsa a mugun daure...

zafi da kunci na balain tafarfasa a ransa jin wai zaa dauki daya daga yaransa mata gashi babu abin da zai iyayi anan duba da yafi kowa snin cewa ahalin waxeeris basuda imani zasu iya sakawa aje  akashesa agidansa yau yau snn abar matarsa da yayansa su rayu kuma azo yi auren babu shi, kai  koda zai fada ko musu dasu ba a wannan wajen ba dole ne saiyaje yay tunani dan wallh bazai amince data daga yaransa daya haifa su kare a matsayin bayi da sunan aure ba.

kamar yadda suka shigo haka suka fice..


daga Cikin fadar iko kuwa Ummu salma ce ta fara kawo kananan magana akan yanayin Areesha, tareda nuna wa a fili cewa sarki murad baida yara mata da suka dace da auren shamsan. tabbas wnn dokar hadin aure na ruhi ya kaskantar dasu

atake mutane dayawa suka bi bayanta, uwar jini ce kawai dai batace komi awajen ba sbd itama sosai ta karewa arishan kallo amma bataga wani cikakken royal energy ko wani muhibba ajikinta ba.


wann maganar ne ya jawo Nana A, ta shigo da siyasarta, na cewa daga zarar anyi wnn hadin auren yakamata abawa shamsan wata matar auren daga cikn jininsa da yar uwarsa leelah wazeeri dansu gyara masa irinsa da jinin xuriarsa.

snn ta kawo shawarar cewa yakamata ma akara karfafa auren zumunta acikin gidan domin kawo cigaban ahali.

uwarjini bata wani amshi batun sosai ba amma kuma shugaba imran da zafar sun nuna hakan yay musu sosai sai batace komi ba...

yau din wani irin farin ciki ne ya mamaye zuciyar ummu salma dan har aka tashi a fadar iko tanaji kamar zata xuba ruwa kasa tasha dan dadi.


Bayan kwana uku da faruwar haka angama kulla yarjejniyar aure snn sarki abdallah yana can kano da matarsa hajarat sakeena suna mulkar masarauta dayankin dala gabaki daya

saida kusan komi ya lafa snn uwarjini ta sake zuwa jeji dan takai ma ruhi me tsarki ziyara snn ta sanr da shi duk wani hukunci data yanke game da bukatansu


ganin ta jima da ficewa agidan yasaka Nana A ta tako taho sashen ummu salma dan su tattauna muhimmiyr shiri data tsara musu dazai kaisu ga cin nasara.

a hadadden garden din ummu salman suka keɓe da yamma an kawata gabansu da madara da dabino da kuma zuma da kofin shayi dayaji kayan qamshi masu dadi..

suma zaune bisa kan lallausar dadduma fuskr ummu salma na cike da annuri cos all  she can think abt shine jikarta leelah ynx ta samu wata mafaka a rayuwar shamsan tunda har uwarjini bata kushe zancen agaban kowa ba.

yau da nana A tazo mata da wata magana gameda shirun da uwarjini tay sai abun ya dan dameta, gashi batason ta tunkareta kai tsaye, batason wani abu na rashin fahimta ya gifta tsakaninsu barema har uwarjini tace bazata bari yarima shamsan ya hada jini da ita ba duba da jininta da zuriarta basu taba haihuwar ɗa namiji ba.

wann kalman ya sake daga mata hankali sosai dan tariga tasan hakan kawo mata wani irin baraza anan gaba

batada tabbacin leelah ma zata iya haifar wa shamsan ɗa namiji koda anmusu aure.

atake murnan ummu salma ya koma ciki, farin cikinta ya rikide ya dawo sabuwar damuwa da tashin hankli

wann fargabn ne ya jawo har nana A ta gaya mata wani sirri,..

ta fito mata da wani madubin sihiri tare da nuna mata cewa wani malami ya mata bayani cewa nan gaba kanwar shamsan wato rihanna zata haifi ɗa namiji ne a haihuwarta na farko idan tay aure, dan haka dolene ta jawota jikinta snn ta hadata aure da kanin mijinta farees salman, ya zamo ajininsa aka samo da namiji, tunda farees salman yana da alaqar jini da tsohon mijin yarta marigayi suhaila waxeeri, babu tantama hakan zai kore zargin cewa leela bazata haifi namiji wa shamsan ba a zcyar uwarjini.

idan sukaci nasarar haɗa auren farees salman da rihanna kuma aka haifi da namiji dolene agane cewa leelah ma zata iya gado jinin ubanta bana uwarta ba tunda ita da farees kusan  cousins ne ta fannin uba.

sai yanxu ummu salma ta asalin fahimce dalilin dayasaka nana A tace akawo farees salman gidan snn tafara cusa shi acikin rayuwar rihanna waziri dan su kulla wata abota.

wannnan shawara da nana A ta kawo mata bakaramin zama a zuciyarta yay ba dan kuwa shine musu kawai mafita dolene ma ta hada auren nan.


hira me tsayi kuma me cike da sirri tskanunsu har yamma ya rufa snn suka rabo, nan ummu salma ta koma cikin chambrta da tunanin yadda abubuwa zasu kasance. dole ta bi shawarar nana A, snn dole ta gamsar da zuciyar jikarta leelah dan tasan cewa shamsan wazeeri shine kawai ta zaba mata amatsayin mijin da zata aura itama anan gaba.


dayan bangaren kuwa komawar sarki murad zamkora saida yay kusan kwana uku yana cikin baqin ciki baya kuma magana da kowa dan duk sadda ta tuna cewa tharim vale zasu taho nan gaba dan dauki daya daga cikin yayansa su aura sai yaji kamar yakashe kansa atake kawai ya huta da dumbin baqin cikin duniyar nan

dan yariga yasan wnn fa ba auren daraja ko mutunci bane, auren bauta da kaskanci ne yafi kowa sanin cewa muddin uwarjini tana raye koda zai mutu ne bazata kaunace jinin baiwa acikin zuriarta ba.

bai kuwa dauki lokaci ba abubuwan suka fara dakule masa

manyan takardu daga masarautar dala sun fara taruwa a kan teburinsa da hatimin dokoki dala ajiki

umarnin sauya tsari da
umarnin dakatar da wasu manyan shirye shiryensa da kuma shirin mayar da mafi karfin rundunarsa na tsaro zuwa karkashin iko na tsakiya da gaggawa ba tare da jinkiri ba.

wann takardun nasu sosai ta fara daga masa hankali duba da baiga jin sassauci a zuciyarsa nasanin cewa wai yau sarki abdallah wazeeri shine shugaban dala ba.

wanda ya gimesa da kusan shekara biyu wai yau shine yake mulkansa tsabar an raina masa wayo..

tunda sarki murad yau  ya shigo cikin fadarsa ya tsaya atsaye yana kallon takardun dokokin dake hannunsa jikinsa yana rawa rawa ta ciki zuciyarsa na tafasa sosai bana kadan ba

dan wani lokaci da ya wuce shine yake bada manyan rinduunonin sojojinsa umarni amma yanzu kuma wai makiyinsa ne zaina saka masa dokoki akan komi.

akarona farko da sarki murad ya ji wani irin rauni  wanda bai taɓa ji a duniayr nan ba amma dake yana da taurin kai sai ya bar abun aransa yana kona shi a hankali..

ME KUKE GANIN ZAI FARU???

SHARE UR OPINIONS..

AS EDEY GET MORE ND MORE INTRESTING



 idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata 

*AREWABOOKS*
*@SURAYYAHMS*

*WATTAPAD @SURAYYAHMS*


*WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER *** TO BE ADDED*


#SURAYYAHMS
#COMEBACK SERIES
2024/2025