Namiji Ƙanin Ajali (Book 01)

Chapter --- O8

by @amdeeytejjdunique587

Bismillahir Rahmanir Raheem.

       ***Namiji Ƙanin Ajali***

                             By

              

         Amdeey Tejj (d'Unique)

Page 08.

"Wai ni Alti zata nunawa Audu ɗan uwanta ne,har tana gaya min a yau idan taso zata sa ya sake ni, to wallahi yau....." Sai kuma naji tayi shiru,ban san me ya sata yin shirun ba,ban kai ƙarshen tunanin nawa ba naji ta kurma uban ihu,sai naji Hassana da Lantana na bata haƙuri, muryar Baba Audu najiyo yana faɗin "lafiya me ya faru,ko mutuwa akayi",sai yanzu na gano dalilin shirun nata.

Taja sheshsheƙa sannan cikin muryar kuka tace"nidai Allah ya gani bani da niyyar raba tsakanin ƴan uwa amma abin da Alti take min a cikin gidan nan yana damuna, ko ba komai ni matar yayanta ne,ai ance  guga na tsiran igiya,naci albarkacinka da ƴaƴan dake tsakanin mu, amma ni na rasa sai kace wata kishiyarta"tayi maganar cikin kukan kissa tana jan hanci

Hassana tace"wallahi kuwa Baba in gaya maka irin cin mutuncin da Alti tayi mata yau  a gidannan kare ba zai ci ba abin sai wanda ya gani".

Mamakin rashin tsoron Allah irin Hassana ya kamani har da rantsuwa,na duba naga ita kanta har yanzu bata asalin abinda ya faru ba,ko da yake ba abin mamaki bane a halayen Hassana,faɗowar da Layla tayi a jikina nane ya ankarar dani dawowanta,na ɗago da ita ina faɗin"kun taso wa ya dawo dake",dan ina zaune bansan lokacin tashinsu yayi ba.

"Sakina  nace muka dawo tare"ta faɗi cikin maganar ta da har yanzu bata gama iyawa ba,dan bata fiye magana sosai ba, tashi nayi nace "muje in cire miki kayan makaranta  kici abinci sai ki koya min karatun da aka koya muku yau"

Tace"to,yau ma malamar mu tace muce a siya ma kowa baji ko a kori inba haka ba zata kore mu"

Nayi murmushi nace"to ai ke kina dashi baki gani bane gashi a nan"nayi maganar ina nuna mata gaban hijabinta da na cire mata da kuma rigarta da ban riga na cire ba.

Tayi dariya sannan tace"laaa nawa guda haka"ta nuna ƴan yatsunta guda uku dan ta kasa tanƙwara  na kusa da ɗan ƙaramin da zai nuna biyu, nayi murmushi akaro na biyu, nace"zo incire miki kaya ki ci abinci"ta matso na cire mata uniform ɗin nasaka mata gajeren wando na ɗakko mata zoɓonta dan bata fiye cin abinci sosai ba sai zoɓo ko garin madara idan nasa mata madara a shayi bata saboda bata son magani tana ganin maganine,na ɗauko shinkafa mai da yajin da Baba Lami  ɗazu ta kawo min,na ɗiba mata kaɗan dan ba cin kirki zatayi ba, motsin Husna naji alamar ta tashi daga bacci,na juya na kalleta nace "Yayan  Mama antashi?,tashi kizo"tashi ta ƙaraso,na kamata muka fita na na wanke ma mata baki,har lokacin akan mai da yanda akayi, sannan muka dawo,na ɗiba mata shinkafar na ɗakko garin ƙuli-ƙulin da bana rabuwa dashi saboda ita na barbaɗa mata akai,dan bata abinci da miya sai ƙuli-ƙuli ko kisa mata ruwa da siga, sai da suka gama sannan na fito dasu na juye ruwan Flask nayi musu wanka,sama-sama na shafa musu mai na sa musu ƙananun  kaya saboda zafi da akeyi sannan suka fita filin gida,da zasu fita nace "Layla kada ku ɓata kayan ku kunga yanzu nasa muku".

"To"suka ce sannan suka fice,ni kuma na tura ƙofana na shigar da takalmana ciki bayan na shinfiɗa tsumma kafin na ɗora su akai,na janyo drawer da nake ajiye littattafai na duba bani da sabon littafi,dama kuma na kwana biyu ban siya ba dan ni bana yin renting,kwana biyu damuwan gabana ma ya ishe bata littafi nakeyi ba,dan sai da nutsuwa kake gane me kake karantawa ma, duk da yakan ɗebe min kewa wani lokaci ya kuma hanani tunanin da aka hanani yi a asibiti,dan samun sauƙin ciwona da har yanzu ba wanda yasan ina daahi,haka na duba na ciro wani,na kwanta na soma karantawa,daga nan bansan yadda su Ladiyo suka ƙarasa ba,dan tun ina jinsu har na daina jiyo tashin sautinsu, sai dai bansan ko anje ƙofar Alti bane, kasancewar ƙofa na yana daga ƙurya ne a shashinmu,kuma akwai ɗan loko duk da ba a matse nake ba, ohoooo dai su suka sani.

Ina nan akwance nan ina karatu dan bani da aiki  bansan ko zuwa azahar a kawo ba,bacci yana shirin ɗauka na na jiyo hayaniya ta bayan ɗaki na,kuma kamar kukan Layla nake ji,miƙewa nayi na ɗauko takalmina na saka na fito,ina zagayawa Nasamu Aisha jikar sabuwa wata matar lungun namu tana dukan Layla, abin takaicin shine kakarta tana zaune tana kallo da yake ba nata ake zalunta ba tana kallo ko a jikinta, raina ya ɓaci da alama bata lura da zuwana ba, kafin in ƙarasa Layla takai hanu ta kai mata duka sai ya sameta a fuska,ta fasa wani uban ihu kai kace wuya ta fille mata,nan sabuwa ta miƙe ki fawa Layla wani uban mari kai kace fuskar kishiyarta ta sama har sai da Layla ta faɗi ƙasa, ta saki wani marayan kuka raina ya ƙara ɓaci na kawo har wuya zuciya ɗebeni da sauri na ƙarasa wurin banyi wata-wata ba na ƙalle fuskar Aishan da wani gigitaccen marin da saida ta kasa ihu,sannan na ƙarasa wajen da Layla dake ƙasa tana kuka na ɗagota.

A har gitse sabuwa tayo kaina cike da bala'i ta fara magana kamar zata kaimin hannu"wani irin iskanci da rainin wayo wannan zaki wani zo ki wanke yarinya da mari kamar wata sa'arki, kinsan meya faru ne da zaki zo ba tambaya ki wani zartar da hukunci to wallahi ki kiyayeni dan zamuyi ba daɗi ni dake"tsabar bala'i kamar zata tsinke harshe ni sai naga kamar har wani kunfa-kumfa bakinta yakeyi

Tsabar takaici rasa me zance, saboda idan nace magana zanyi,to ashar zan ƙunduma mata sai dai kuma ina ƙoƙarin naga banyi hakan ba, ko bakomai ta girme min dan zata kai sa'ar yaya Asma'u marigayi ya maman su Fareesa, sam ba halina bane faɗa akan yara dan nasan idan kayi ma yanzu, anjima zaka gansu tare kuma su yara ba a rabasu da faɗace-faɗace idan suna faɗa sai dai in raba su ko in zane su idan sunƙi bari, sai in basu sweet ɗin da nake siya saboda su Husna saboda bana basu kuɗi,daga nan shikenan an gama faɗan.

Cike da ɓacin rai a murya da fuskata nace"Eh dole tunda ita ba naƙuda akayi akayi haifota ai dole,ke da kike kallo ake dukar min yarinya dake ba naki ake zalunta ba, kinsan ai a lokacin makancewa kikayi,sai da ta rama kafin kika warke makanta ko,ke a matsayin ki na wacca kika fini shekaru, kuma kika san ya kamata da kika tashi kinsan ai kin bi ba'asi kafin kika yanke hukunci ko,da ni nazo zanyi nawa shine ya zama sai na tambayeki,na nemi izninki kafin in yanke hukunci ko?,tunda gaki uwata ta farar gada mai jan(red) mazaunai,in Banda rashin tsoron Allah irin naki ina Layla me shekara uku da rabi ina A'isha me shekara shida,kema da bake kika haifa kikayi haka,balle ni, to wallahi ina jin kunyar ki,kada ki bari in taka girman wlh,dan kunga bana magana,to ba tsoro bane,ba wai kuma bana son ƴaƴan nawa bane,dan nasan kaf anguwar nan ba wanda bai sanni ba,bana neman faɗa amma idan aka nemeni za'a sameni, idan kin manta ki tambayi Ladiyo,ko kije tarihi na a anguwarmu"daga nan naja hannun yara na muka yi gaba na barta a wajen dan dama ni bana dogon magana idan na faɗa maka abin da yake raina zanyi gabane in barka da ɓaɓatu a wajen.

Ina jiyo tana faɗin"idan Ladiyo tana tsoro na ita bata tsoro na kuma idan taƙamata rashin kunya to tana da wanda suka fini, kuma zata kai tokaciya wun umma na, kuma mijina zai dawo"dama dai maganganu makamantansu,nidai iskar da ya ɗebo maganarta ma ban sake bi ta kanshi ba balle ita.

Muna zuwa ƙofana na cire musu kayan dan ya ɓaci da ƙasa,na shiga na ɗakko ɗayan flask ɗin,na juye ruwan ciki na sirka na musu wani wankan muka shige dan na canza musu kaya....

Sai mun haɗu a page na gaba na gode da bani aron lokacinku....

Mu huta lfy

   

Amdy ne 👋