JANNAH YAR GIDAN ANDERSON

The golden cage _kagon zinare

by @zahrabmrs02

page 1 


iskar daren garin Kano tana busawa da sanyi, amma a cikin babban penthouse ɗin Jannah Anderson da ke unguwar Lamido Crescent , shiru ne kawai yake tashi, sai ƙaran agogon ɗaki da ke bugawa cikin nutsuwa.

Jannah tana tsaye a bakin katafaren gilashin ɗakin, hannunta riƙe da ƙofin shayi mai zafi wanda ƙamshinsa ya gauraye da ƙamshin turaren wuta na Oud. Daga inda take tsaye, tana kallon fitilun birnin kano da suke sheƙi kamar lu'u-lu'u. Tana sanye da wata doguwar rigar sanyi kalar burgundy, gashinta a naɗe cikin wani tsadadden silk scarf.

Duk da dukiya da mulkin da take da shi, idanunta suna ɗauke da wani irin sirri da babu wanda ya taɓa iya karantawa.

"Shekaru biyar," ta raɗa wa kanta, muryarta na rawa kaɗan. "Shekaru biyar da kowa yake kallo na a matsayin makashiya."

Ta tuna ranar da Mr. & Mrs. Anderson suka rasu. Ta tuna yadda dangi da abokan arziki suka juya mata baya, suna nuna ta da yatsa cewa ita ce ta shirya haɗarin don ta mallaki miliyoyin dalolin da suka bari. Ba su san cewa ita ɗin ma tana cikin raɗadin rashin su ba.

Arewacin Najeriya ya ɗauki zafi akanta. "Mace tana zaune ita ƙaɗai tana shekara 33 ba aure?" "Miyagu ne kawai suke rayuwa haka," in ji mutane. Amma Jannah ba ta damu ba. Katangar da ta gina a kusa da zuciyarta ta fi ƙarfin maganar mutane.

A wani gida madaidaici a cikin garin Kano, unguwar Hotoro, Aliyu (Tareeq) yana zaune a gaban iyayensa. Fuskarsa tana sanye da wani irin kwarjini, natsuwa, da ladabi.

"Tareeq, yanzu duk aikin garin nan ka rasa inda zaka samu sai a ofishin Jannah? Yarinyar da tayi ƙaurin suna a rashin tarbiyya?" Abba ya faɗa cikin ɓacin rai.

Malam Yusuf Sada (Abba) kowa yasan abba ya  tsani Jannah Anderson  saboda irin badakalar da ake yaɗawa akanta. Ganin fadan abba yaki kare wa mahaifiyar Aliyu  Laila Al-Yemeni, wacce  kowa Ummi yake kiran ta ,tasa baki ,Ummi asalin ƴar ƙasar Yemen ce, mace ce mai kyan gaske wacce kallo ɗaya za ka yi mata ka ga asalin kyan Larabawan Yemen—fatar nan tata mai haske da santsi, duk ba a cikin kudi suke ba  .manyan idanuwa masu natsuwa. A gurin Ummi ne Aliyu ya gado wannan kyan tasa; fuskarsa saƙ take da ta mahaifiyarsa, musamman hasken fatarsa da hancinsa mai tsawo.

"Haba habibi kayi haƙuri ka barshi. Kaga Tareeq ya daɗe yana neman aikin nan. Ina ruwansa da wata Jannah? Ba lallai ma ya dinga haɗuwa da ita ba," in ji Ummi cikin sanyin muryarta. Ganin yadda Ummi take lallashi, Abba ya amince amma tare da gargaɗi mai tsanani.ya kuma ce masa yaji tsoron Allah ya kula da mutuncin sa da addinin sa 

MONDAY

A cikin babban ofishin kamfanin Anderson Global, sanyin AC ɗin da ke kaɗawa bai isa ya kawar da fargabar da ke zukatan ma'aikatan da ke waje ba. Jannah tana zaune a kan kujerarta, ƙafa ɗaya kan ɗaya. Tana sanye da wani tsadadden suit kalar duhu wanda ya zauna daram a jikinta, kanta kuma sanye da turban kalar zinare. Ba tare da ta ɗago kai ba, ta ce: "Next!"

Ƙofar ta buɗe, Aliyu Yusuf Sada ya shigo. Takunsa na nuna natsuwa. Sanye yake da farar shadda danyar gaske, kansa sanye da Zanna Bukar. Aliyu ba kowa ba ne face jami'in tsaro na sirri (Special Intelligence Agent) a ƙarkashin hukumar DSS. An turo shi ne don ya bankado asirin kisan iyayen Jannah. Yana ƙarkashin matsin lamba na hukuma; dole ne ya kawo datti akan Jannah ko kuma aikin sa ya fuskanci barazana.

Jannah ta ɗago kai, ta kura masa ido na tsawon daƙiƙa goma.

Introduce your self muryar jannah ta fito in a very professional way 

Sunana Aliyu Yusuf Sada ,also known as tareeq 

"Aliyu Yusuf... CV ɗinka ya nuna ka fi kowa ƙwarewa. Amma ina son ka sani, wannan ofishin nawa ne, ba masallaci bane  ko gidan biki."

Ta nuna shi da yatsa tun daga kansa har ƙasa. "Wannan shaddar da kake takama da ita, ita ce ta ƙarshe da zan gani a jikinka. Daga gobe, ina son ganinka sanye da 'Corporate Suit'. In ba haka ba, karka kuskura ka taka kofar kamfanin nan."

Aliyu ya ji haushi, amma ya dake. "An gama, Ma'am," ya amsa.

Jannah ta matso daf da shi, tana jin ƙamshin turarensa. "Sun ce kai ne ƙwararre. To ka nuna min ƙwarewar taka, Mr. Yusuf. Domin idan na gano kana min wasa, zan nuna maka dalilin da ya sa duniya take tsoron sunan Jannah Anderson."

Aliyu ya murmusa a ransa. "Zaki ga fiye da yadda kike zato, Miss Anderson," ya faɗa yana kallon cikin idanunta.


Tareeq ya ji wani irin haushi ya daki zuciyarsa, amma ya dake. Ya san Jannah tana da takama, amma bai zata "Bossy" dinta ya kai haka ba.

"

Jannah ta tura masa wani file. "Wadannan sune 'rules' dina. Rule number one: Idan na yi magana, ba a tambaya ta 'me ya sa'. Rule number two: Lokacin barci na duk mahimancin meeting kar a tashe ni ko a kira ni , duk inda zan sa kafa, kai ne zaka kula da su. Kuma kuskure daya zai iya zama ajalinka a wannan kamfanin."

Ta kara mikewa tsaye, ta matso daf da shi. Koda yake tana da tsawo, sai da ta dago kai don ta kalli idanunsa saboda tsawon da yake da shi. "

Be warned Mr Yusuf "

Tareeq ya murmusa a ransa. Wutar da yake gani a idanun Jannah ta tabbatar masa da cewa wannan "mission" din ba zai yi sauki ba. Tana da kyan gaske, amma kyan nata yana cike da hadari kamar wutar daji.

"Zaki ga fiye da yadda kike zato, Miss Anderson," tareeq  ya kara fada yana kallon cikin idanunta.

"Maza fita. I have a meeting in five minutes," ta fada tana juya masa baya, tana nuna masa cewa magana ta kare.and one last thing nan ba primary bane ,bana son Jin tareeq a office dina ,CV Dinka Aliyu Yusuf Sada ne ,Anderson global ba Wajan wasa da kiran mutum da pet name bane 

Tareeq ya juya ya fice, zuciyarsa tana tunanin yadda zai fara hako sirrin  wannan macen da ta gina katanga da izza da mulki a kusa da ita. Bai sani ba, ashe duk wannan Bossy din nata, akwai wani rauni da yake boye wanda ba Wanda ya San dashi .


Bayan tareeq ya fice, ofishin ya koma shiru tamkar ba mutum a ciki. Jannah ta dade a tsaye tana kallon kofar da ya bi ya fita, sannan ta saki wani boyayyen numfashi wanda ta dade tana rike da shi.

Ta koma ta zauna a kan kujerarta, ta jawo file din  Aliyu Yusuf Sada ta kara budewa. Hotonsa da ke manne a jikin CV din ya kalle ta da wadancan idanuwan nasa masu natsuwa amma kuma cike da wani boyayyen siri.

‘Aliyu Yusuf ...’ ta fada a zuciyarta.

Gaskiya daya  tareeq  kyakkyawan namiji ne na buga mujalla. Yanayin tsayinsa, fadin kafadunsa, da kuma yadda yake magana cikin natsuwa yana nuna cewa shi din ba bawan kowa bane. Ko da yake ta wulakanta shaddar da ya saka, amma a ranta ta sani cewa shaddar ta zauna masa daram kamar an dinka ta ne don jikinsa kadai.

Jannah ta yi murmushi mai ciwo, ta taba wuyan turban dinta. "Wace irin duniya ce muke ciki? Namiji kamar wannan, me ya sa zai yarda ya zama mataimaki na? CV dinsa ya nuna ya fi karfin aikin nan sau dubu."

Ta lura da shekarunsa a takardar. Shekararsa ashirin da tara (29). Jannah ta girme shi da shekaru hudu, domin ita tana da talatin da uku (33). A al’adar Arewa, namiji irinsa ya riga ya zama maigida, watakila ma yana da ‘ya’ya biyu ko uku. Amma kwarjinin da yake dauke da shi ya fi na wanda yake shekararsa.

"Akwai abin da kake boyewa, Aliyu," ta fada tana zare glass din idonta. "Ina jin kamshinka ba na mutumin da yake neman albashi bane. Kuma idan har Alhaji Bashir ko nadiya ce suka  turo ka kamar yadda nake zata, to ka fada tarkon da ba ka sani ba. Domin Jannah Anderson ba ta taba barin maciyi ya sha ba."

Ta mike ta nufi bangon gilashin ofishin nata, tana kallon yadda motoci ke zirga-zirga a titunan A kano Ta saba da ganin kyakkyawan maza , ta saba da maza masu dukiya da mulki suna neman kofar shiga wurinta, amma tareeq ya banbanta. Akwai wani sanyi a tare da shi wanda yake barazana ga katangar da ta dade tana ginawa a kusa da zuciyarta.

Ta danna intercom din dakin sakatariyarta. "Maimuna, ki tabbatar dukkan na'urorin sauraro (bugs) da nake da su a ofis dinsa suna aiki yadda ya kamata. Kuma duk inda ya sanya kafa daga gobe, ina son rahoto."

Jannah ba ta yarda da kowa ba. Ba ta yarda da Turawa yan uwan mahaifanta ba ,bare kuma namiji dan Arewa sanye da shadda da Zanna Bukar wanda ya shigo rayuwarta a lokacin da makiya suke kokarin bankado asirinta.

"Shekaru hudu na girme ka, A

ta rada, tana kallon inuwar fuskarta a jikin gilashin. "Kuma a wadannan shekarun, na koyi cewa kyakkyawar fuska tana iya boye mafi munin zuciya. Zan ga ko kwarewarka ta kai ga jure wutar da zan kunna maka."

Ta jawo bututun shishar dake gefe, ta kunna ta tana fito da hayaki. Zuciyarta tana gaya mata cewa Aliyu  ba zai zama kamar mataimakan da suka shigo suka gudu ba. Akwai wani abu a tare da shi... kuma wannan abun ne take tsoro.