Chapter Eighteen
"Hasbunallahu Wani'imal Wakeel." Ta dinga maimaitawa acikin zuciyarta. Hakan ya saka a hankali ta ya fara dawowa cikin hayyacinta. Sannu a hankali, nutsuwarta ta daidaita.
A hankali ta ɗago da fuskarta, saboda sauƙin hayaniyar mutanen da taji.
Karaf! Suka haɗa ido da Ammey, ta sakar mata wani lallausan murmushi, cike da kunya Radiya ta sake sunkuyar da kanta tana ci gaba da mamakin wannan al'amarin da yake wakana kamar a mafarki.
A cike da nutsuwa Ammey ta taso ta nufo in da take, ta kama hannunta, ta nufi wata ƙofa wadda ta sadata da ainahin ɓangarenta. Bata zame ko'ina da ita ba, sai bedroom ɗin ta.
A nutse ta zaunar da ita a gefen gado, sannan ta saka hannunta ta gyara mata mayafin lifayar, fuskarta ta bayyana sosai.
"Radheeya!"
A sanyaye ta ɗago ta kalle ta, saboda yadda ta faɗi sunan nata. Sannan kuma ga fargabar da take ciki. Saboda tunda ta kama hannunta, ƙirjinta yake ta faman dukan uku-uku. Amma haka ta daure ta amsa cikin sanyayyiyar muryar.
Sannan ta sake kallon ta tace:
"Kin tabbata kina son Sultan, ba dole suka yi miki ba da wannan shiriritar tasu ta neman haihuwa?"
Sunkuyar da kanta tayi tana nazarin kalaman Ammey, bakinta yana motsi ta rasa me za ta ce da ita.
Shigowar Sauban ce ta katse mata tunaninta, ta hanyar ɗagowa ta kalli hanyar shigowa.
Cikin hanzari Ammey ta mayar da hankalinta kansa, tare da faɗin:
"Sai da nace karka biyo mu, amma baka yarda ba ko?"
Sosa ƙeyarsa yayi, sannan ya shagwaɓe fuskarsa yace:
"Ammey sauri fa muke yi mu kaita gidanta, Sultan yana hanya kuma kin tsare ta da tambaya."
A hankali ta juya sosai ta ƙare masa kallo, sannan tace:
"Kana tsoron tambayoyin da zan yi mata ne?"
"A'a Ammey, ke da ƴar ki, ni ai ban isa ba, kawai dai ki hanzarta."
Ya faɗa yana kallon idon Radiya cike da wani rikitaccen kallo da yake isar da saƙo.
Murmushin takaici tayi, saboda har yanzu bata gamsu da abinda ya faɗa mata ba. Amma sai ta yafito shi da hannu tare da faɗin:
"Zo ka zauna."
A sanyaye ya ƙaraso ya zauna kusa da ita. Ya saka hannayensa guda biyu ya rungume ta ta baya, yana yi mata magana a sigar shagwaɓa, duk saboda ta bar zancen.
Saboda tsoronsa Allah, sannan tsoronsa Radiya kar ta fadi wata magana da zai saka Ammey ta fuskanci cewar, Radiya itace genetic match ɗin Sultan wadda a baya suka ce mata tana da aure.
Duk da hakan Ammey bata fasa abinda tayi niyya ba. A hankali ta ture Sauban daga jikinta, tare da faɗin:
"Kirawo min shi a waya, sannan ka saka hands free."
Bai yi musu ba, ya ɗakko wayarsa ya fara ƙoƙarin kiran layin Sultan.
Bugu ɗaya ya ɗauka tare da faɗin:
"Me kuke jira har yanzu baku kai min matata ba?"
Murmushi Sauban yayi, sannan yace:
"Yanzu muke shirin kai ta..."
Yayi shuru, a daidai lokacin da Ammey take masa nuni da kar ya nuna tana kusa dashi wajen.
"Ku hanzarta saboda ni kaina nasan yau zanyi kwanan farin ciki..."
Abinda Sultan ya furta kenan wanda hakan ya saka Sauban yayi saurin kashe wayar. Saboda kar ya ɓaro wani zancen. Sannan ya kalli Ammey yace:
"Shikkenan?"
Jinjina kanta tayi, sannan ta mayar da hankalinta kan Radiya tace:
"Na ɗauka shiriritar taku ce, amma yanzu na fahimta, tunda har Sultan ya nuna yana son ki, to tabbas da gaske ne. Saboda hakan ina yi muku fatan alkhairi. Allah ya baku zaman lafiya Radheeya."
"Ameen."Sauban ya amsa.
Ita kuwa Radiya tayi shuru tana sauraron su. Ba tare da tace komai ba, kuma wannan karon, abun sam bai dame ta ba. Saboda ta riga ta tsinke da al'amarin su Sauban.
Babu abinda ba zasu iya aikatawa ba. Hakan ya saka, tayi tunanin, wannan wayar da suka yi da Sultan, itama shiri ce.
Zainab ce ta katse musu shurun, a daidai lokacin da ta shigo ɗakin Fawaz yana bin bayanta. Ganin yadda Sauban ya sake rungume Ammey ya saka ta kalli Fawaz tace:
"Kaga Daddy abinda yake yi ko? amma idan kana rigima ya dinga yi maka faɗa."
Dariya suka yi gabaɗayansu. Sannan ta sake kallon su tace:
"Zamu shirya amarya ku ɗan bamu waje."
Miƙewa Sauban yayi ya nufi hanyar fita hannunsa riƙe dana Fawaz.
A hankali ta ƙaraso ta zauna kusa da Radiya. Ta kamo hannunta, sannan ta kalle ta cike da murmushi tace:
"Sannu amaryarmu."
Murmushin ƙarfin hali Radiya tayi.
Sannan daga bisani Ammey ta kalle su tayi musu nasiha sosai mai ratsa zuciya wadda har kuka Radiya tayi. Sannan taja hankalin Zainab sosai akan ta kula da ita, kasancewar gidajensu suna kusa da na juna.
Har ga Allah Radiya taji wannan nasihar, duk da zuciyarta ta shiga wani nau'i na tantama, ta rasa meyasa al'amuran suke tafiya a haka kamar gaske.
To bayan nan Ammey ta fita. Zainab ta miƙe tare da raka Radiya banɗaki.
Ta sake yin wanka bayan ta fito ta iske an ajiye mata wata lifayar mai tsananin tsada, da wata doguwar riga wadda za'a saka aciki.
Radiya sai bin yadin rigar take yi da kallo, saboda tsananin ɗaukar idon da yake yi. Sannan tana mamakin irin yadin da aka yi ɗinkin rigar dashi. Saboda ko kusa, bata taɓa ganin irinsa ba.
Sannan ga wani ni'imtaccen ƙamshi da kayan suke yi mai sanyaya zuciya. Sannan babban abinda ya bata mamaki shine, saitin yari da sarƙa, awarwaro zobuna, da kambun hannu da suke ta sheƙi a gefe.
Cikin zuciyarta tace: "Kar dai ace wannan duka na gold ne?"
To haka amarya ta shirya tsaf! Zainab ta fito da ita babban parlour. Daga nan wata mata da suke kama da Ammey, ta kama hannunta suka nufi waje.
Nan ma guri ya sake kaurewa da guɗa da shewa har suka nufi in da aka jera wasu motoci na alfarma, ba waɗanda suka ɗakko ta ba. Sannan daga bisani, kowa ya shiga motocin, suka nufi gidan Sultan.
Tun da suka doso tagwayen gidajen gabanta yake faɗuwa, saboda ba ƙaramin kyau da ɗaukar hankali sukayi ba. Saboda tsantsar dukiyar da aka kashe ta wuce misali. Saboda gini ne na yayi, wanda yake tafiya da zamani.
Kamar a mafarki taga an nufi ɗaya daga cikin gidajen, take aka wangale katafaren gate ɗin shiga. Motocinsu suka shiga, tare da ƙoƙarin parking a katafaren filin da aka tanada domin ajiye motoci.
To tun daga nan, Radiya ta zama tamkar gunkin tsaye wanda ake sarrafa shi. Saboda gabaɗaya tunaninta ya gaza saituwa, ta kasa fahimtar cewa, wannan a gaske yake faruwa da ita ba a mafarki ba.
Saboda ita tun da take a rayuwarta bata taɓa tunanin akwai wata sila da zata saka ta wuce ta gaban irin waɗannan gidajen ba. Ballanta ace zata shiga, kuma ta ɗauki tsawon lokaci acikin sa.
A hankali aka kama hannunta, aka fara kutsawa da ita cikin katafaren gidan. Sauke kanta kawai tayi ƙasa ko da ƙwaƙwalwarta zata samu ta huta.
A hakan aka dinga ratsa gurare da ita, ƙarshe har aka iso wani katafaren parlour, sannan aka kama wata matattakala a tsakiyarsa, suka nufi wani haɗaɗɗen bedroom da ita.
Masu guɗa suna yi, masu addu'a suna yi ta samun zaman lafiya da zuri'a ɗayyiba.
Ba'a zame ko ina da ita ba, sai a gefen gadonta. Duk da ta lumshe idonta, amma hakan bai hana ƙwaƙwalwarta hasaso mata a in da take ba, saboda ita kanta katifar da taji ta zauna akanta, ta tabbatar mata da cewar, ruwa ba sa'an kwando bane.
A wannan lokacin ne ƴan uwa da abokan arziki na Ammey kowa ya baje basirarsa ya fito da kyaututtuka na amarya aka fara jere mata su a gabanta.
Kan Radiya yana kasa tana jin duk abubuwan da suke faruwa, amma sam bata fahimtar komai, saboda tunanin ta tuni yayi tsuntsuwa ya bar jikinta.
Sai da komai ya lafa kowa ya tafi, saura ita da Zainab kawai.
Sannan Zainab ta ƙaraso in da take ta zauna kusa da ita, tare da kama hannunta. Sanyaye Radiya ta ɗago ta ƙarewa bedroom ɗin kallo cike da mamakin girmansa. A cikin zuciyarta tace: "Wannan ɗakin ai yafi gidana na ɗorayi girma."
Sannan a hankali ta mayar da hankalinta kan tilin kwalayen da suke zube birjik a gabanta kamar bola. Cike da mamaki ta mayarda hankalinta kan Zainab.
Murmushi kawai Zainab tayi, sannan tace:
"Wannan duk naki ne amarya."
Sannan ta fara buɗe mata komai dalla-dalla.
Wato mai karatu kar kace na zuba ƙarya.
Wannan harkace ta arziki wanda sai wane da wane. Saitin gwalgwalai ne na gani na faɗa wanda siyansa sai jinin arziki jinin dukiya. Wannan yana wane waccan.
Sannan kuma da kayan sakawa na gani na faɗa, musamman lifaya masu tsadar gaske. Wanda dangin miji suka baje basirarsu domin su gwangwaje amarya.
Da mamakin Radiya ta kalli Zainab tace:
"Kuma waɗannan duk gold ne?"
Murmushi Zainab tayi tare da gyaɗa mata kai alamar "Eh." Sannan daga bisani ta jawo wata ƙaramar jakar siyayya kusa da ita ta fara zaro nata gudunmawar ta miƙawa Radiya.
"Ga nawa."
Cike da mamaki ta kalli Zainab.
Murmushi ta sake yi mata. Sannan tace:
"Ki kwantar da hankalinki Radiya, haka al'adarmu take wannan ba wani abu bane."
Sunkuyar da kanta kawai tayi saboda jin kalamanta. Can cikin zuciyarta kuma, tantama da tsoron mai zai je ya dawo suka fara yawo.
Sannan ta fara tambayar kanta: "Shin idan na gama wannan aikin za'a barni na tafi dasu kokuwa?"
Saboda a iya kintacen da tayi, ko ba'a biya ta kuɗin aikinta ba, wannan kawai ya ishe ta tayi rayuwa.
Saboda haka, hankalinta ya fara kasuwa kashi-kashi.
"Taso na nuna miki cikin gidan naki kafin angon naki su ƙaraso ko?"
Murmushin yaƙe tayi, sannan ta miƙe tabi bayan Zainab.
Ciki da wajen gidan babu inda basu zagaya ba. Ita kam Radiya da abun ya ishe ta, da suka dawo sai ta wayance da shiga banɗaki.
Haka ta shiga ta nemi waje ta zauna, ta ja numfashi mai nauyi ta sauke, sannan ta ƙarewa banɗakin kallo tare da nufar jikin madubi ta kalli kanta tace:
"Radiya wannan zama ne na ɗan lokaci ba don ki rayu har abada ba. Ki kama kanki, ki daina mamaki, saboda damace da ta same ki da zaki gina taki rayuwar.
Idan Allah ya ƙaddara kika tsaya da ƙafarki, kuma kikayi aiki tuƙuru kika juya kuɗinki to zaki samu wanda yafi wannan.
Saboda haka ki daina mamakin duk abinda kika gani ba naki bane na aro ne."
Da wannan nasihohin da tayiwa kanta ta samu nutsuwa sosai, sannan tayi alwala ta fito. Kafin ta tayar da Sallar masu aikin gidan sun jere mata kayan abinci a bedroom ɗin, wannan umarnin Zainab ne.
Sannan daga bisani ta umarce su da su kwashe duk waɗannan kyaututtukan su adana a in da ya dace.
Sai da Radiya tayi sallolinta sannan sukayi sallama da Zainab ta tafi.
Tana zaune a gefen gadon tana ta ƙarewa bedroom ɗin kallo taji an ƙwanƙwasa ƙofa.
"Bismillah" Kawai ta furta sannan masu hidimar gidan mata uku suka shigo suka gabatar mata da kansu da yaren turanci tun da gabaɗayansu ba Hausawa bane.
Haka ta amsa musu ba yabo ba fallasa. Sannan daga bisani suka sanar mata da cewar, Sauban yana son ya ganta.
Ba tare da tace komai ba, ta miƙe tabi bayan su.
A zaune ta iske shi a babban parlour kasa. Yana ganin ta yayi sauri ya miƙe tsaye, fuskarsa babu yabo babu fallasa. Sannan yayi mata nuni da ta zauna, sannan shima ya zauna.
Shuru ne ya biyo baya, saboda dukkannin su sun lula kogin tunani. Sannan ya ɗago ya kalle ta yace:
"Radiya, muna godiya matu