KISHIYAR WAJE

Chapter 10

by @sadiyagarbayakasai

KISHIYAR WAJE
SADIYA GARBA YAKASAI 
10
Masud ya yi niyyar zuwa gun Samha suyi ta su gama ko da kuwa ba ta so,yau zai mai da ta matsayin da ya ba ta dole kuma ta yi biyayya a gun sa ko da kuwa ba ta so hakan sai ta faru.Ya ja numfashi gami da gama cin abincin da Maryam ta kawo masa.Tuwon shinkafa ne miyar ganye ta sha nama da kifi sosai ya ji daɗin abincin ya kora da lemon abarba da aka haɗa da niƙaƙƙiyar kankana ta dau sanyi sosai ya ji daɗin komai ya yi hamdala,yadda ya ci abincin ya ba ta nishaɗi kuwa,duk fushi da wani kumburi da zargi duk ta ajiye a gefe tai masa fara'a fatan za ka ɗore da haka cin abinci ai sunna ne Yallaɓai ta faɗa tana gyara masa kwalar rigar sa tace "Sai ina?"
Ya samu kan sa da jin kunyar ƙaryar da zai mata yace "Wata unguwa za mu da Salmanu neman bayani a kan wannan case ɗin  da nayi miki magana ya dame ni kike ganin kaman wasa ne to shi ne dai nake neman addu'ar ki na dace."
Ta dan rangaɗa kai kaɗan tace "Ka ji ka dai kawai dai ba na so ai min kan tawaye ina zamana lafiya da mijina wata can ta zo ta ɗauke minn kai.
"Ya ɗan taɓa kumatun ta sannan yace "Ke ma kin san daga ke ba kari."
Wani irin murmushi ta saki sannan tace "Allah Ya sa."Raka shi gun motarsa. Sai da ya tada ta ya leko yace da ita "ki shiryan dafaffen dankali da miyar hanta."
Tace "An gama Allah Ya ba da sa'ar abinda aka je nema."
Ya amsa yana murmushi yace "Amin Merry ta."
Ya na fita ya ja ja numfashi sannan ya   gode wa Allah da kwaɓar sa ba ta masa ruwa ba.Yau ya kamata su kawo karshen diramar  da suke yi,tun da dai sun san suna son juna kuma ya san za ta karɓe shi da hannu biyu-biyu.Don shi kawai ta sani, kuma shi ne ya ke ɗauke mata nauyin ta na sayayya ko rufin asiri,abun da ta yi masa kuwa fushi ne ya sa ta yi masa hakan. Kuma sai shi ya taɓota, za su daidaita junan su.Duk waɗannan maganganun yana yin su a fili. 
 Siyayya suka yi sosai a kasuwa,Samha na yi ta na duba lokaci har dai Sima ta siƙe ta ce da ita  "Ki na wa Allah ki bar agogon nan ya huta haba.
"To ce na yi miki saboda shi nake duba wa?"
"To gayan saboda waye?"
Ta murguɗa mata baki tace "Saboda Kai na kin san ba na son rana.
"Eh kwarai na sani amma dai yau da gayya ki ke komai shi ya sa na harbo ki."
Samha tace  "To uwar iya." Ta faɗa cike da tsokana.Kaitsaye gida suka nufa don yin abinda ya dace kafin zuwan Junaid.
*
Faka motarsa ya yi a ƙofar gidan.Ya  soma hangawa ko zai ga wanda zai aika kiran Samha tun da mai gidan ta yi masa gargaɗin kar ya shiga gidan ta ba izini,duk da ya san suna da mai aiki to iya ma an shiga tsakanin su kuma sulhu ya zo nema ba sai ya yi musu katsalandan a sha'anin aikin ta ba.Ya na zaune ya yi shiru ga rana bata sauka ba da ma,kawai sai ya kunna mota ya saki a.c yau dai ba inda zai je sai ya yi tozali da ita komai rashin son da zata nuna masa iya ka dai ta tuttura masa magana zai iya dauka. Kaman an ce dago Ido kawai sai yayi arba da motar Simah ta faka a ƙofar gidan ya ɗago daga zaman kwanciyar da yayi akan kujerar.Hango madam ɗin ta sa ya yi duk da babu alamun ado tare da ita amma ta yi kyau abin ta wato ita ba abun da ya dame ta da rashin sa . Ta manta da shi.Cikin ransa ko cewa ya yi "Ikon Allah."Shi yana nan yana ta faman wahala na rashin ta,amma ita  ya kula ma kiɓa ta yi abin ta.
kaya ya ga  suna fitowa da su daga mota alamar  sun yo siyayya ne.Fitowa ya yi daga  cikin motar cike da  takun isa da kasaita ya nufi inda suke.Mutum ne wanda ya iya ado.Kowa ya san da hakan.Basu lura da shi ba sai gyaran muryar sa suka ji,sannan ya yi musu sallama "Assalamu alaikum" 
Da Samha da Sima a tare suka ɗago kai suka kalle shi tamkar mage ta ga bera.Cikin ɗaure rai Samha ta amsa masa sallamar "Wa'alaikum Salam" ita ma don dole ne amsawar ba don haka ba ma ba za ta ko kalli inuwarsa ba.Gwanar  iya shariya ce da ma in har ta fita rayuwar mutum to uban kuturu ma yayi kaɗan. Sima ce ma ta ɗan rangwanta masa ta yi masa fara'a.
"seema ya garin kwana biyu?"
Smah tace "Mu a su wa kwaɗo a ruwan zafi.
"ku din nan manya masu abin mamaki."
Tuni Samha ta sai kai ta shige cike suna can suna magana har ta kai bakin kofa. Cike da fuskar tausayi Mas'ud ya kalli Simah yace "Ki taimaka min na ga kawar ki don Allah."
Seema tace "Ƙarya da ciwo ,a dai yau gaskiya abu  ne mai wahala ka samu kan Samha. Abu ma fi sauƙi shi ne don Allah kar mu wahalar da junan ka je , yanzu ta gaji dama kuma ba wai hucewa ta yi ba, amma na yi ma ka alƙawarin ka dawo da daddare zan shawo kanta."
Ya so ya turza amma abun da ta gaya masa haka ne tilas ya amince da maganar ta. Ba don ya so ba ya yi mata sallama ya koma wurin motarsa ya buɗe ya shiga ciki.kallon ƙofar gidan ya sake yi kamar zai gan ta a gun sai da ya ja wank gauron numfashi sannan ya ja motar ya bar wurin ba don yana so ba ya tafi."
Samha tana fito da kayan da za su yi amfani da su, su Simah ta shigo tana kallon ta . Sai da ya harare ta sannan tace "Wallahi yarinyar nan ba ki da kirki meye na barin mu a gun." 
cike da rashin kulawa tace "Ke kika ga za ki iya.Ina nawa a ciki,ai kin san dama ba zan tsaya da wannan tujararren ba Wallahi kin ma ji na rantse miki,ke yanzu na san ciwon kaina aure zan yi na samar wa kaina ladan da zai kai ni aljanna na kuma roke Kaina a matsayin marainiya mara uwa da uba da dangi,kowa nawa babu sakamakon rashin tsari an kashe min su."Tana maganar hawaye na zuba a kan fuskarta.Ita kanta Seema shiru tayi,jikinta ya yi sanyi,ita da iyayen ma amma ta bar su tabbas ta yi kuskure amman zata gyara.Samha ta yi gyaran murya ta dalilin ta ne ta daina kule-kulen maza,ta daina bin kowanne namiji,dalilin ta ta san ciwon Kan ta ko Alhajin da ya bushe mata ido,shi ma ta taka masa burki ta gaya masa in dai yana son ta da gaske ya aure ta.Anan dai simah ta ba wa Samha ƙwarin guiwar abun da ta yanke tayi amma ta yi haƙuri ta saurare shi yau da daddare ta fito masa a mutum ta gaya masa gaskiya ta samu mijin da zata aura,da ƙyar Samha ta amince din ba zata iya dagawa Siman Ido ba saboda kawa ce ta arziƙi yar'ruwa kuma ba abun da zata nema ta kasa yi mata,ta karbe ta san da take neman mafita ta riƙe ta da daraja, babu tsangwama ko gori ɗin haka zata mata wannan alfarmar ita ma.Sun gama haɗa abun da za su tari Yallabai Junaid sai suka yi wanka suka yi ado daidai misali sabuwar atamfa ta saka wata ja mai ratsin kalar ɗorawa ɗinkin ya kamata kaɗan ya yi mata kyau matuƙa da yake Allah ya bata jiki murjajje sai ta fito kamar wata yar babyn roba.Hatta Seema sai da ta tanka da "Masha Allah kin yi kyau tabbas Junaid ya yi dacen mace , Allah Ya mallaka miki Yallaɓai Junaid kun dace Wallahi da Junaid."
Samha tayi dariya tace "Hum! ke kuma fa ba ki ga yadda ki ka yi ba ne,fulanin jama'are akwai na su kayan."Dariya suka yi kowa na yabawa kowa.
Junaid ya ci kwalliya cikin wata dakakkiyar shadda,kai ka ce sabon saurayi ne komai ya yi masa tsam shi a iya kan sa ya san ya yi yadda ake so har yanzu dai ruwa na maganin dauɗa sai godiyar Allah.Duk yadda Ramla ta yi don ta ɓoye damuwar ta hakan ya gagara. Hakan nan yau ta ji tana kishin mijin ta fiye da yadda ta ji lokacin auren sa da Salma,ta kuma ji tamkar wannan adon gun wata za shi,gaban ta ya ci gaba da faɗuwa, ta shiga salati har dai ta kasa juriya tace "Amma ɗaurin aure za ka ko?" Ya ɗaga manyan idanun sa ya  ajiye mata cike da kulawa ya ce "A'a gaskiya da inda zani babu ɓoye-ɓoye tsakanin mu unguwa za ni mai mahimmaci.Amma me kika ga ni?"
 Ta ɗan saki numfashi sannan a hankali tace "Babu komai, Allah kwalliyar ka tafi karfin ace harkokin ka zaka sai dai ko neman aure."
ya ɗan ji dam amma gudun kar ta gane ya yi dariya sannan a wayance yace "Mata ho shikenan namiji bai da damar yayi wani abu sai ai masa fassarar aure haba tauraruwata ko da ma auren ne me zai dame ki?"
 Ta ɗan haɗe rai tace "Ai ni ma mutum ce kuma Mai kishin mijin ta wanda ka mun da Salma na ji ciwo amma daga baya ya wuce ga mu dai tare da daɗi ba daɗi mun saba,Amma wannan kam jikina yana ba ni tafi karfin kowa a gun ka,shi yasa ka ga na damuwa kwarai." Ya ji tausayin ta tabbas yanzu soyayyar Samha shi Kan sa ta fi ƙarfin sa,so yake mata ba da wasa ba,ya rasa daidaita zuciya sa jarabawar ce ta Allah,tabbas Samha jarabawar sa ce ya Kuma san ba fita sai ya same ta zai huta. Ya matsa kusa da ita ya riƙo hannayen ta  ya sanya idanun sa cikin na ta yace "Hajiya ta ki kwantar da hankalin ki ki sa ranki a inuwa, unguwa ce za ni da Usman mai muhimmaci ba zance za ni ba." Ya samu kansa ta gaya mata ƙarya yau farko da ya gaza gaya mata gaskiyar inda za shi baya son ya ɓata mata ko ya bar ta da kallon bai da adalci. Ta ɗan yi murmushi tace "Na yarda Allah ya tsare hanya." "Amin matas." Ya amsa yana dariya ya fita daga shashin ta.Sashin Salma ya nufa.Tun kan ya shiga yaron yace mai "Daddy Mum ba ta nan fa."
Junaid ya ɗan yi shiru ya kalli daddy nasa  yace "Ina ta je?"
yaron ya  maƙale kafaɗar sa yace "Ban sani ba na ga ta fita tana kuka."
Hannunsa ya sa ya shafa kan yaron don kore masa shakku yace "Tafi wajen wasan ka." Ya ce "To."Ya fita yana jinjina wautar Salma da ta kasa girma,kuma faɗan ba gaira balle dalili.Tilas ya koma shashin uwar gida tana kiciniyar kunna tashar larabawa kawai don kallon girke_girkin su. juyawa tayi ta kalle shi tace "Yallabai lafiya ka dawo?" 
"Ina son ki sa Ido sosai kan su Daddyna Salma bata nan ta fita ba izini na." Yana kai wa nan ya juya rai ɓace ya fice. Ta yi shiru tana jinjina wautar abokiyar zamanta na rashin haƙuri "Ko ma ina taje zata dawo."  Ramla ta faɗa a fili tana taɓe bakin ta.
A hankali yake mai da numfashi tabbas in ka biyewa mace zata iya sa maka hawan jini over ma kuwa,ba ya so yaje ma Samha cikin fushi farin cikin ta yake son gani kawai. kafin zuwan sa,ya samu kansa da kunna karatun al'ƙur'ani yana bi, a hankali nutsuwa ta same shi ya manta da wata Salma da kayan haushin ta,daidai kofar gidan Seemah ya faka motar sa ya zaro wayar sa ya danna mata kira tana zaune ƙasan kafet,  tana wasa da wayar ta kiran sa ya shigo,ta ɗaga da sauri cikin taushin murya da lafazi ta gaishe  shi. Ya ji daɗin yadda tai masa ladabi tamkar yana gurin. abun da ya ke Jan hankalin sa gun kaunar ta kenan. "Ina waje." Ya faɗa .
Da sauri tace "To bismillah ka shigo mana ka tsaya a waje."
"To ai ba na shigo ba babu izinin masu gidan ko?"
" Haka ne to mun baka izini." Ta faɗa.
Ya zare  wayar daga kunnen sa ya fito cike da jin isa kamar wani saurayi ya ƙwanƙwasa ƙofar.
Da kanta ta buɗe masa ƙofar. Ƙamshin ta ya cika masa hanci ,cikin kyakkyawar sura da kwalliya ta fito.Ba ƙaramin kyau tayi masa ba kamar yar tsanar roba ko wani fure mai kyau da ban sha'awa. Ta ɗan murmusa ganin kallon da yake mata ta ce masa "Sannu da zuwa Yallaɓai." Ta ba shi hanya don ya shiga.   Sai da ya shiga sannan ya amsa mata yace "Yauwa sweetyna fatan na same ku lafiya?" Ta ɗan rausayar da kai  kaɗan sannan  tace "Lafiyar mu lau."
tayi masa waje a falon sannan ta wuce na ta gun ta zauna.Nan suka sake gaisawa suka ci gaba da hirar su.Ba a  jima ba  Simah ta yi musu sallama da trey mai kyau cike da fruit dangin ayaba,lemon ɓawo,kankana,inibi apple a kai ta ajiye masa a gaban sa. Ta kuma komawa ta kawo amsa  ruwa ta ajiye cike da kuulawa da Jin dadin wannan abu da aka masa yace "Na gode da wannan karamanin da kuka yi."Sima tayi dariya tace "Haba Yallaɓai ba komai ai mu mun ji daɗin ganin ka kuma an ce ka kyautatawa wanda ke kyautata maka,ya hanya fatan an dawo lafiya?"
"Alhamdu lillahi."ya faɗa sannan ya ɗora yace  "Fatan na same ku lafiya?"
Sai da gyaɗa masa kai sannan tace "Ga alamu  nan ma kana gani agun gimbiyar taka."
"Shakka babu." ya faɗa  ya ce "Ai ke dai kin riƙe min amana kin kula da amana ta Allah ya saka miki da khairan."
Sima tace "Amin bari na ba ku guri ku gaisa"
Ya sake yi  mata godiya sannan ta shige ciki.
Samha tana ta nuku- nuku irin nan rashin sabon nan yana kula da ita sai murmushi kawai take.
"Ba ka sha fruit ɗin ba ai." ta faɗa  da ƙyar. Yace "Ina kuwa zan ci gimbiya ba ta bani izinin ba?ki sauko ki taya ni aikin ci."
Ta yi dariya  tace "Afuwan Wallahi na ƙoshi dama naka ne ai ina godiya ƙwarai." Ya sha fruit ɗin sosai sannan ya yi hamdalah.
Samha tai masa jagora kan kujera ya zauna sannan ita ma ta zauna ya ɗan n kalle ta yace "To Samha da farko dai ina gode wa Allah da ya sa na samu karɓuwa don an ce labarin zuciya a tambayi fuska kuma da na gaba ake gane zurfin ruwa ba da wasa na zo ba,sannan mu ba yara ba ne kamar yadda na gaya miki ba wasa na zo ba to ba shi ya kawo ni gun ki ba soyayya ce mai kyau da tsafta sannan kuma wacce zamu gina bisa tafarkin sunna don mu bauta wa Allah mu kafa soyayya mai kyau kuma abar kwatance,sannan mu samu zuri'a daiyyaba kin amince na fara neman auren ki ko kuwa akwai bayani?"
Ta gyara zaman ta gami da ƙura masa Ido tamkar mai ganin wani abu sai kuma ta ɗauke hawayen ta tace "Zan gaya ma wacce ni tukunna kafin aje ga batun aure, ya na da kyau ka san wacece ni mai ya sa  na shiga wannan rayuwar." Ta faɗa tana ɗauke hawayen ta.Cike da tausayi ya kalle ta tabbas yana so ya ji labarin na ta.Ta ɗago ta kalle  shi.Yace "Ni na yarda da ke ba sai kin ce min komai ba ina son ki a haka babu wani bincike da zan yi." Sai da tayi ɗan murmushi sannan tace "Ya na kuwa da kyau ka ji ni ko don gudun zargi a gaba yana da kyau ka san tushe na kamar kowa."
Ya ja numfashi sannan yace "Haka ne to ina sauraron ki, amma magariba ta taho dole mu haƙura mu ji komai a haɗuwar gaba zan ji yadda za'a yi."
"Haka ne na kuma gamsu na gode ."
"Babu godiya ai a tsakanin mu dear,ki kira Sima muyi sallama idan na yi sallah wucewa zan yi gida."
 "Shi kenan mun  gode da ziyara."
Ta shiga ta kira Sima bayan ta fito tace "Har za ka tafi?"
"Magariba tayi. By the way na gode da karamci."
"Haba Yallaɓai babu komai an zama ɗaya mun gode sosai." Ya wuce gaba suna bin sa a baya har gun motar sa,ya buɗe baya ya fito musu da leda yace "Na Gimbiya ne." Sima ta karɓa tana godiya sannan ya dauƙo wata ya ce ga na ki  ke ma." "Kai amma mun gode sosai." Sima tayi masa sallama ta wuce da kayan ciki. Ya kalli Samha yace "Zan wuce Gimbiya sai jibi zan zo mu tattauna."
Tace "To na gode a gaida family."
Ya ji daɗin yadda ta kula da su yace "Za su ji please a rinka sa mayafi ba na son ganin ki haka."
Kunya ta ɗan kamata ta rufe fuska tace "Zan kiyaye Allah  Ya tsare hanya."
Yace "Amin na gode sai mun yi waya."
 Tace "To ina jira." Sai da ya bar gun ta shiga gida cike da farin ciki.Bakin ta ya ki rufuwa sosai take kaunar Junaid ba don komai nasa ba sai don ƙaunar ta asali da ta ratsa ta.Sima tayi baja -baja da ta ta tsarabar tana yabawa da mamakin alherin yallabai Junaid atamfofi super guda biyu da dan dasheshen Les sai jaka amma ba takalmi ciki ya danganta da Rashin sanin size ɗin ta,da kuɗi a ciki. Samha ta kalle ta tace "Wai har kin kasa haƙuri kin buɗe?"
Simah ta ɗan girgiza  tace "Saboda daɗin alkhairinai son ƙawa ta ko laifi ne?"
Ta daga hannunta sannan tace "Uhum uhum ina zan faɗa kin sani a shafa labari,kun fi kusa ai ke da shi na ga ke ce gwanar sa."
Simah tayi dariya tace "Ƙwarai kuwa 'yar sa Ido na yadda.Allah saka masa muna godiya."
"Bari nayi sallah nima na zo na buɗe nawa amma ba zan buɗe a gaban ki ba,tun da kika bude na ki ba ki kira ni ba."
"Au abun haka ne haba tawan ki zo dai mu buɗe tare ai kike ayi ci tare wasa bam-bam kenan?"
"Eh haka nake nufi."
"Na ƙi wayon ai ke ki ka fara." Samha ta faɗa tana dariya.