*🪻SAWUN KEKE...🪻*
by @auntyindo
Ep-4
Har ya sauka ƙasa, binsa ta yi da kallo cikin tsananin tausayinsa, ji take da da yadda za ta yi ta hana su tafi da shi da ta yi, Zahra ce ta ƙaraso wajen jiki a sanyaye, har ya fice daga makekiyar harabar makaranta idanunsu na kansa, sun kasa ko da cewa ƙala.
Wajen da ƙoshashshen Dokinsa ke ɗaure ya nufa ba tare da ya bi takan Inspector Khalil ba, ganin haka ya sa Inspector Khalil cewa "Kai dakata min!! Kama ka fa mu ka zo yi amma ka ke shirim guduwa, kar ka wahalar da ni kasa in harbeka.
Kalaman nasa in da dama dariya Akhiee zai yi don kuwa sun fi kama da haka, sai dai dariyar haÉ—ari ce gareshi, ya kalleshi ya kauda kai sannan ya buÉ—i baki cikin nutsatstsiyar muryarsa ya ce "Ba zan hau muku mota ba, ka barni zan je akan dokina."
Fakam-fakam Inspector Khalil ya yo kansa a fusace ya na cewa "Mu za ka rainawa hankali? ya za mu kama tantirin ɗan ta'adda irinka amma sabida ka maida mu masu ƙwaƙwalwar yara sai ka ce za ka tafi a doki??"
Cikin sigar lumana ya ƙara cewa "Ba na son ku cutu ne shi yasa ba zan hau motarku ba!"
Inspector Khalil ya ƙara hayayyaƙowa kamar zai doki Akhiee, jin suna taƙaddama ya sa Sheikh Auwal matsowa gurin, fuskar sa ba alamun wasa ya ce ''Ba su san hatsabibancinka bane da ka ke tunanin su barka ka tafi kai kaɗai? wuce ka shiga ko ranka ya ɓaci."
Cikin kurari Inspector Khalili ya ce "Bar ni da shi Ya Sheikh, sai na nuna masa bambancin É—an sanda da É—an ta'adda."
Duk wannan kurarin da Inspector ya ke yi damisar takarda ce kawai don a gaskiyance tsoron ma kallon fuskar Akhiee yake a wannan lokacin bare har ya je daf da shi hakan ne ya sa ma ya basar da labarin handcuff.
Akhiee ba tare da ya ce komai ba ya koma ya shiga motar Ƴan Sandan hankali kwance.
Sheikh Auwal ne ya dubi Inspector Khalil cikin ɓacin ran abinda ɗan uwan nasa ya aikata ya ce "Ba na so ku sake shi har sai kun hukunta shi a bisa laifinsa, kar ku biyewa son Zuciyarsa ku barshi ya dawo ba tare da kun ƙwatowa wanda aka cuta haƙƙinsa."
Inspector Khalil ya shaƙi iskar da ke kaɗawa ya busar sannan ya ce "Calm down Ya Sheikh! hakan fa aikina ne, don hakan na kama shi."
Da haka su ka yi sallama, Inspector ya shiga mota zuciyarsa fari ƙal kamar anyi masa Albishir da Aljannah.
Ƙoƙarin kunna motar direba yake amma ina ta ce ba ta san zance ba ko motsi ba ta yi da sunan ta na da rai, abun kamar wasa mota ta ƙi ko da harbawa sau ɗaya har an kwashi lokaci me tsayi ana ta fama, Inspector Khalil sai kai kawo ya ke yi hankalinsa duk ya tashi ya rasa yadda zaiyi ga jama'a da su ka taru domin kallo sai dariya su ke masa, zuwa yanzu ya fahimci cewa Akhiee ne matsalar motar don haka ya lallaɓa kusa da shi, cikin muryar raɗa ya ce "Muhammad ka sauka to ka hau dokin naka ka ga motar ta lalace mu ma tawo daga baya amma don Allah kar ka gudu kawai tambayoyi zan yi maka ba wani abu ba." cikin zuciyarsa mugun ƙuduri ne akan Akhiee kawai ya faɗi hakan ne a ganinsa ya lallaɓa shi zai fi zuwa.
cikin ko in kula Akhiee ya ce "Ƙaramin Sufeto, ka je ka canja shiri ka zo ka same ni a Office ɗinka na riga na yi niyar zuwa so zan je ba sai ka yi min ƙarya ba, kuma ina so ka sani ba a shiga dawa don ƙarya."
Ya na gama faÉ—en haka ya dire ya bar Inspector da buÉ—aÉ—É—en baki ya na kallonsa.
Bai saurari kowa ba ya haye dokinsa ya zabure shi.
Inspector Khalil a tunaninsa Akhiee ya na sauka daga motar za ta dawo daidai sai ya ga saɓanin haka, yanzu ya tabbata motar ta riga ta mutu kenan don haka hankalinsa ya kai ƙololuwar tashi, abubuwa da dama ya ƙudurce a ransa wanda zai yiwa Akhiee don ya huce baƙin cikin abinda ya yi musu.
Wurin su Sheikh Auwal ya koma ya nemi alfarmar su kai shi Office da motarsu, ba su yi masa gardama ba su ka amince masa.
Sai da akuyar cikinsa ta juya da ya yi alaragab da Rislaan zaune kan kujerarsa ya ɗora ƙafa kan teburin gaban kujerar ya na zuƙar murzazzar wiwinsa, baki sake ya ke kallonsa tare da shuɗawa duniyar tunani.
Wayarsa ce ta dawo da shi haiyacinsa ya yi saurin ɗauka, a ɗaya ɓangare Corporal Halil ya ce "Sir! yanzu mu ka kammala da gawar nan mun tafi hanyar maida ita gida".
"Wane bayanai aka samu akai??"
"To gaskiya dai ba wata hujja illa iyaka dai rauni ne na wuƙa ba wani abu, sai kuma cewar tin daren jiya ne abin ya faru."
Katse watar ya yi cike da takaici ya soketa kana ya ƙarasa cikin ofishin ya na takun isa da ƙasaita, cikin sigar wulaƙanci da ƙasƙantarwa ya ce "Ka zo ka miƙe ƙafa a teburina kamar na tsohonka, office ɗin nan fa ba gidan manyanka bane da za ka zo ka na min shaye-shaye a ciki, ka na ƙazami da kai ma har ka isa ka zauna kan kujerata? ka sauka ko kuma na yi maka abinda zaman ma sai ya gagareka."
Yadda dutse ba ya magana haka Akhiee bai ce komai ba hasalima ko motsi bai yi ba.
Inspector Khalili ya dinga maganganu amma hakan bai sa Akhiee ya yi ko ɗar ba, gajiya ya yi ya nemi guri ya zauna ya na nazarin ta inda zai ɓullowa lamarin.
"Yanzu ka tsaya mu yi magana, dole kai ne ka kashe Alhaji Salisu don kai ne ka gana da shi a daren jiya.
"Don na gana da shi ba shi ya ke nufin ni zan tsara masa ƙaddararsa ba.
"Kar ka yi min zancen banza, kawai ka amsa laifinka ba sai ka wahalar da hukuma ba, ko ka na nufin ka ce ba kai ne baƙonsa na jiyan ba?"
Jan hayaƙinsa ya yi ya busar cikin salo sannan ya ce "Na baƙunce shi jiya, kuma ni na fara yi masa Albishir da mutuwarsa, amma don ance maka a daren jiya aka yi kar ka yi tunanin irin 12:00am ɗinnan, No daidai lokacin da ruwan sama ya sakko aka shiga gidan ana tsaka da ruwa kuma ruhinsa ya bar jikinsa, na so na ceceshi sai dai kashhh! bai yi min abinda ya dace ba shi yasa na bari ya mutu, Ƙaramin Sufeto ka ƙara bugu don ba ka buga a daidai ba."
Zuciyar Inspector Khalil tsalle kawai take yi kamar za ta ɓalle ƙirjinsa ta fito sabida ɓacin rai,
"Wannan gadarar taka da rainin hankali za ta jefaka a matsala, bayan duk wannan ka na nufin in yarda ba kai ka kashe shi ba? ka faÉ—a min gaskiya kai ka kashe shi ko?? sai fa ka amsa mini sannan za ka samu hutu daga gareni in ba haka ba ka shiga uku da ni.
Banza Akhiee ya yi masa ya ci gaba da zuƙe-zuƙensa sai da ya gama zamansa akan kujerar Inspector Khali kana ya tashi ya na cewa "Haka ake kama mai laifin ba ko handcuff?"
Sai a lokacin ma Inspector ya tuna da hakan, ya fara cika bakin cewa "Ai so nake na bika ta maslaha shiyasa nake maka tambayoyi cikin lumana, amma tinda abin naka ya zo da haka dole ne ai na rufeka, me ka ke ci na baka na zuba?"
Ko kanzil Akhies bai ce masa ba.
Tin safe har Azhar ta doso Inspector Khalil na famar tambayar Akhiee amma shiru ba amsa, duk wata barazana da zai yi ya yi amma shiru.
Wayarsa ce ta fara ruri a ƙagauce ya janyota gami da ɗaga kiran ba tare da ya duba me kiran ba.
"Waye ya sa ka kama wannan? ya ka ke abu kamar ba ka san abinda ka ke yi ba? yanzu ka na da hujjar da za ka nuna wa duniya ta shaida shine ya aikata?"
Cikin girmamawa Inspector Khalil ya ce "Sorry sir, amma alamu ne su ka nuna shi ya aikata don kuwa shine ƙarshen ganawa da Alhaji Salisu."
a ɗaya ɓangaren ya ce "Wannan rashin lissafi ne irin naka, maza ka sake shi sannan ka ba shi haƙuri, in ba ka yi hakan ba kuma zan cire hannuna daga ciki ko me ya faru kai ka jawa kanka"
"Okay Sir!!!" bai ƙara magana ba ya katse kiran, Inspector Kalil ya bi wayar da kallo ya na mamakin hakan.
"Yallaɓai me ya faru? waye ya kira?" Constable Saleh ya jefo masa tambayoyin a jere.
Cike da tsoro gami da shakka ya ce "Abin mamaki kira ne daga CP da kansa wai na saki wancan É—an ta'addar."
Constable Saleh ya ce ''Yallaɓai dama na gaya maka ko wuni ba lallai ya yi a hannunka ba bare kwana, na gaya maka dabi da wancan shaiɗan ɗin haɗari ne, nan gaba ma za ka iya ganin takardar kora daga aiki ko ta canjin wurin aiki."
Cikin ɗaurewar kai Inspector Khalil ya ce "Anya ba shi ka ke yiwa aiki ba Constable? na ga sai faɗa min kausasan kalamai ka ke yi akansa." cikin sauri Constable Saleh ya ce "Yallaɓai wallahi ka ji na yi rantsuwa ta muslmi ba na yi masa aiki ban taɓa karɓar kuɗin wani na yi masa aiki ba, Yallaɓai ka tuna da iyalina kar ka sa aikina ya lalace ba ni da hanyar samu sai wannan, kawai anyi a gaban idona ne ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba shiyasa na shaida kuma na ke baka labari Yallaɓai."
IP Khalil ya koma ya zauna jaɓar gami da furzar da zazzafar iska, "Ku sake shi!" ya faɗa kamar zai fashe da kuka don takaici.
ya na bada umarni su ka buɗe Akhiee, ya kakkaɓe jikinsa ya tashi, wurin Inspector ya nufa ya tsaya akansa sannan ya ce "Kai ƙaramin Sufeto, idan ka ce uwarka Madam ce to mu haɗu a Coci, ina son ganinta."
Daga haka ya juya, har ya fice Idanun IP Khalil na kansa, dogon tsaki ya zabga gami da dukan teburibɓn gabansa ya miƙe kamar wanda aka cakawa Allura.
"Ya Zama dole ma na san da abinda ya ke taƙama Yaron nan, ya zama dole na gane dalilin da ya sa CP ya ce na sake shi" wannan lissafin IP Khalil ya ke yi cike da ɓacin rai.
Akhiee kuwa tuni ya ɓata a wurin ya san inda dare ya yi masa.
Baya
Cikin sauri sauri Alhaji Salisu ya shigo Falon,, a kusa da Hajiya Laure ya zauna sannan ya ce "Hajiyata na yi baƙo za mu tattauna da shi, to kar ki shigo part ɗina har sai na dawo na same ki"
"To sabida me Alhaji?"
"Kar ki tsananta bincike don Allah kawai ki yi abinda na ce"
"To shikenan Alhajina ka dawo da wuri"
Hajiya Laure ta faÉ—a ta na kwarkwasa.
gaba ya yi ya na cewa "In sha Allahu"
Akhiee na zaune ƙafarsa ɗaya kan ɗaya Alhaji Salisu ya shigo da sallama, bai amsa ba har ya ƙaraso ya zauna kan kujerar da ke fuskantar wadda Rislaan ya ke kai......