Roots and shadows (Asali da Inuwa )
by @zahrabmrs02
Bayan Jannah ta kammala taron dake cike da hargitsawa da manyan ma’aikatanta, ta koma ofis dinta ranta a bace. Ta danna intercom, "Aliyu, zo ofis dina yanzu."
Bayan minti biyu, Aliyu ya turo kofar. Har yanzu yana sanye da farar shaddar tasa, tsaye yake a gabanta tamkar bango, fuskarsa ba alamun fara’a, sai dai natsuwa da ladabi na ma’aikacin da ya san abinda yake yi.
Jannah ta nuna masa wani daki dake gefen ofishinta wanda aka cika shi da akwatunan takardu na shekaru uku da suka wuce. "Wadancan takardun duka na reshenmu na Kaduna da Abuja ne. Ina son ka raba su, ka fito min da dukkan kwantiragin da aka bayar ba tare da sa hannuna ba. Ina son rahoton akan teburina kafin karfe takwas na dare."
Ta fada hakan ne tana zaton zai nuna gazawa ko rokon karin lokaci, ganin girman aikin. Amma Aliyu sai kawai ya gyada kai. "An gama, Miss Anderson."
Aliyu ya shiga mini office din , ya ninke hannun rigar shaddar sa ya fara aiki. Ga duk wani ma’aikaci, wannan aikin azaba ne, amma ga Aliyu, wannan wata dama ce ta DSS .Yayin da yake duba kowace takarda don Jannah, idanunsa suna farautar kowane asiri da zai taimaka wa aikin sa na jami'in tsaro.ya Saba aiki cikin speed and accuracy kuma
Yana aiki ne cikin tsari da sauri (Professional precision). Bai yarda gajiya ta bayyana a fuskarsa ba, sannan bai bari ko takarda daya ta fadi a kasa ba ba tare da ya san abinda ke ciki ba.
Karfe bakwai da rabi na dare (7:30 PM).
Jannah ta mike daga kan kujerarta, ta nufi dakin ajiye takardun don ta tabbatar da cewa ya gaza. Ta saba ganin mataimakan da suke kuka ko rokon gafara idan ta dora musu irin wannan aikin.
Tana tura kofar, ta tarar da Aliyu tsaye, ya riga ya kammala komai. Akwatunan suna jere fes, dakin ya yi tsaf. Shaddar dake jikinsa tana nan radau, ko gumi bai sa shi ba.
Ba tare da ya kalle ta ba, ya mika mata file guda daya. "Wannan ne rahoton. Akwai kwantiragi goma sha biyu da aka bayar ba tare da amincewar ki ba. Sannan akwai kuskuren lissafi na miliyan hudu a kowane wata a reshen Abuja."
Jannah ta karbi file din, tana dubawa cikin mamaki. Komai ya kasance dalla-dalla, babu kuskure ko guda daya. Ta dago ta kalle shi, wannan karon kwarjininsa ya dan firgita ta, amma ta dake.
"Yaya aka yi ka gama wannan aikin cikin kankanin lokaci?" Ta tambaya cikin dakiya.
Aliyu ya kalle ta, muryarsa a sanyaye amma mai nuna isa. "Na zo nan ne don in yi aiki, Miss Anderson. Kuma aiki ne zan yi miki. Idan har kwarewa kike nema, to kin riga kin samu."
Not so fast Mr Yusuf Ka Bari ni da kaina idan na ga Ka cancanta Zan yabeka for now 3/10
Ta fice ta bar tareeq da mamakinta
Karfe 8 na dare ta gota, amma har yanzu fitilun babban ginin Anderson Global suna kunne. Jannah Anderson mace ce da ba ta san gajiya ba; tana daya daga cikin mutanen da suka yi imani da cewa idan ba ka riga kowa tashi ba, ba za ka taba riga kowa samun nasara ba. Sai da ta tabbatar kowa ya fice, sannan ta dauki jakarta ta nufi elevator.
Tana fita harabar kamfanin, iskar Daren ta kadeta. Cikin takunta na isa, ta yi kusan karo da wani mutum da yake tsaye jingine da jikin bango.
Tareeq ne Idanunsu suka sarki juna na wasu dakiku. A cikin idanun tareeq Jannah ta ga wani irin sanyi da kaifin basira; shi kuma a idanunta, ya ga gajiya da aka boye a karkashin fuskar izza.
Babu wanda ya ce uffan. Jannah ta rabe ta gefensa, kamshin turarenta na Chanel ya bugi hancinsa. Ta shiga cikin motarta, wata hadaddiyar Lexus LX 600 baka mai gilashin tint. Ta ja motar cikin zafin nama ta bar harabar kamfanin.
Tareeq ya bi motar da kallo, sannan ya saki murmushi mai ciwo. Ya nufi tsohuwar motarsa, Toyota Camry (Big Daddy), wacce koda yake tana da kyau, amma idan aka hadata da ta Jannah, tamkar gidan rarrafe take. Ya tayar da motar ya nufi unguwar Hotoro
Gidan su tareeq gida ne na mutunci. Ko da yake iyayensa ba mawadata bane, amma suna cikin rufin asiri. Malam Yusuf ya hadu da Laila ne wani gidan abinci inda Laila da yan uwanta suke Aikin wanke wanke ,su Laila yan gudun hijira ne daga yamen ,inda babansu Laila ya yada zango a kano ,ya fara gadi daga gida zuwa gida lokacin su Laila suna yan mata daga karshe dai ya samu ya kukuta yasai gida a unguwar birget ,inda su Laila Suma suke zuwa government school ita da yayarta Lubna .sai yayansu tilo abdallah ,idan an tashi school zasu tafi Wajan maman debora su mata aiki ta basu abinci,mahaifiyarsu wacce suke kira da oum tana dan gyaran jiki irin nasu na larabawa wa Amare
Laila ta Riga yayarta lubna aure dan malam Yusuf na nuna mata soyayya itama taji ta kamu da sonsa ,besides that itama Tana bukatar yin aure ta zauna waje daya dan tagaji da bautar shagon maman deborah
Malam sada ya sa yayyen Yusuf bincike Akan Laila da iyayenta kuma an samu shaida mai kyau a kansu ,maihafiyar Yusuf ta dade ta rasuwa itace mace ta hadu a gidan mal sada ,inda Yusuf ya taso a hannun babbar yayarsa da suke uba daya wato anty mariya Wanda a girme ma anty mariya ta girma maman Yusuf ,kanwar Yusuf Asmau ta koma Wajan kanwar mamansu dake Gombe
Sosai anty mariya ta ba Yusuf hadin gudunmawa Wajan auren Laila inda suka fara zama a yan kaba ,dangin Yusuf basu sami matsala a bangaren Laila ba ,don ba laifi ta iya zama da mutane
A haka ta Haifa nafeesah malam Yusuf ya sami aiki federal ministry of education suna rayuwa daidai misali ,Bayan shekara biyu ta haifi Jamil ,daga nan kuma sai khamil
Sai kuma Aliyu (tareeq shine sak kabo mai Kama da Laila duk sauran kama suke da Mal Yusuf
Sosai Laila ta daura buri Akan tareeq Sabida kyaunsa,And ba Wanda yasan boyyyen halin Laila na Son kudiii,Tana boye maitar kudin ta fili a haka Bayan shekara 7 ta Haifa khadija wacce stilll suna kama da Laila sai Aysha auta itama kaf da kaf suke kama da Laila,tachi buri Akan su ,lubna ma tayi aure tana abuja ita da yaranta 3 Tana auren wani dan kasuwa mai kudin da ya sauya rayuwar su gabadaya inda yayansu abdallah yake aiki a daya daga cikin companies dinsa dake abujan ,lubna takan ce Laila kinyi saurin yin aure ,da kin hakura a yadda ba Wanda yakai ki kyau kaf Gidanmu sai dai ki aura governor
Laila tayi murmushi tace lubna idan ni ban aura mai arziki ba Gasu Aysha da khadija nan inshaAllah zasu bani rayuwar da ban samu ba .lubna ta siyawa su oum gida a unguwar gadon kaya inda suke zaune cikin rufin asiri , Jamil da khamil ,duka sun yi aure suna fafutukar rayuwar gidajensu da yaransu. Shi kuma tareeq shi ne ginshinkin gidansu tun Bayan ritayar abba.
Yana shiga falon, ya tarar ummi tana zaune tana kallon arewa24 yayin da kanwarsa Khadija take kokarin hada plates din da aka chi abinci. Aisha, auta, tana gefe tana duba littattafanta na makaranta.
"Marhab ya tareeq ummi ta fada tana murmushi.
Tareeq ya karasa ya zauna a kasa kusa da ita, ya dora kansa a cinyarta. "Ummi , na gaji yau sosai."
"Sannu Aliyu. Allah ya taimaka, ya Allah ya maka albarka . Kai ne kake share mana hawaye tun bayan ritayar mahaifinku," ummi ta shafa kansa cikin kauna.
Tareeq ya boye damuwarsa. Ummi ba ta san cewa babban aikin sa shi ne na jami'in tsaro ba (Undercover Agent). Tana tunanin aikin company jannah kawai yake yake yi. Shi yake biya wa Khadija kudin jarabawar WAEC, shi yake siyan maganin hawan jini na mahaifinsa da ya yi ritaya. Nauyin gidan gaba daya yana kansa, domin yayyensa Jamil da khamil kusan kansu kawai suke sani yanzu saboda matsin tattalin arziki.anty Nafeesah mijinta kuwa dan show up ne ,kullum Tana hanyar umrah ita da kishiyoyinta jamaaar gari suna ta ganin yadda alhaji jibril yake kula da matansa amma a badini abinci wannan ba ya basu wadattace
Sannu da zuwa yaya tareeq Aysha da khadija su gaishe da yayannasu,Bayan Khadija ta kawo masa jolof din shinkafa tasha kifi yana cin abincin ummi tana shafa masa Kai cikin soyayyah irin ta uwa .
"Aliyu, anya aikin nan da kace ka samu a kamfanin Anderson akwai alheri?" Ace sai Wajan karfe 9 na dare zaka dawo ?Mahaifinsa ya fada yana fitowa daga daki, rike da carbi. "Ina jin labarin yarinyar nan, Jannah. Mutane suna cewa ba ta da tausayi."Ko dazu na karanta labarin ta a Facebook
Tareeq ya mike tsaye, ya gyara zaman rigarsa. "Baba, kowa da irin tashi kaddarar. Zan yi kokarin ganin na kiyaye mutunci na da naku. Kudi ba su ne komai ba, amma dole in yi aikin nan don mu samu mu rage radadin rayuwa."
A ransa kuwa, tareeq yana Neman yadda zai hada wannan nauyin na gida da kuma binciken sirrin kisan kai da aka turo shi yi. Ga kuma kudin da Alhaji Bashir ya bashi na "advance Akan Shima yana so ya kawo masa jannah kasa ,alhaji Bashir sam be San tareeq undercover bane ,ya nema shi dazu Bayan an fada masa jannah tayi sabon PA ,a tsarin Aikin sa dole ya amsa tayin alhaji Bashir Sabida Shima Akwai ayar tambaya Akan sa . Yayinda yake so ya yi amfani kudin da alhaji bashir ya bashi shi ya gyara wa ummi falon ta dan har solar yake tunanin sakawa ummi , amma yana tsoron kar kudin su zama na haram zai Bari da salary dinsa inshaAllah zai hada mata ,ummi ta cancanci duk wani gata da Jin dadi
A daya bangaren birnin kuma, Jannah tana zaune a cikin babban falon penthouse dinta. Gidan shiru yake tamkar kabari, sai karar na'urar sanyaya daki. Ta cire suturar jikinta, ta saka wata riga ta siliki.
Ta kunna shishar ta, hayakin ya cika dakin. Ta dauki wayarta, ta ga hoton Ameer wanda jami'anta suka turo mata na inda ya nufa.
"Hotoro? Gidan tsohon ma'aikacin gwamnati?" ta rada. "Aliyu kana zaune a gidan iyayenka, kana daukar nauyin kowa... me ya sa kake son sanya kanka a cikin wutar da zata iya cinye ka?"
Jannah ta ji wani irin daci a ranta. Ita tana da kudin da zata iya siyan rabi da rabi na kano amma ba ta da ummi da zata shafa kanta. Ba ta da kanne da zata taimaka musu. Tana da dukiya, amma ba ta da rayuwa.indai da gaske ba turo Ka akayi ba Aliyu Zan taimaki rayuwarka ko dan Sabida nauyin dake kanta
Shafa gashin jikin dogs dinta tayi luuuluuu da Suzy