Chapter 15
đ *HAĆIN ĆADDARA* đ
By
AyshaNalado
Sadaukarwa ne a gareki Ć´ar uwa rabin jiki *RUKAYYATU* (Aunty Ummi) Son so fisabilillahđ
BOOK 1
Page 15
Kansa a Ćasa yana gyara Éaura agogon dake hannunsa, ya shigo office Éin laÉÉansa Éauke da yar karamar sallama. Har ya iso tsakiyar office Éin bai lura da mutum a ciki ba, sai da ya ja kujera zai zauna sannan idanuwansa suka sauka a kan fuskarta.
Dakatawa ya yi da zaman da ya yi niyya, ya zuba mata idanu na yâan wasu sakanni, kafin yasa hannu ya zare glass din da ke manne a fuskarsa.
Wani irin kallo Ćurillah yake bin ta da shi alamar yana son tuno inda yasan fuskarta, can kuma ya murza yatsunsa biyu suka bada wani sauti tass! tare da pointing Éinta ya ce "At dausayi ko, me gudu bata kallon gabanta right?" Ya faÉa cikin siyar tambaya?
Yau shine karo na uku da ta sanya shi a idanunta kuma karo na farko da ta yi wa fuskarsa kallon sosai, yayinda ya zama karo na biyu da ta saurari muryarta, wanda ya haifar mata da matsanancin faduwan gaba, zuciyarta ta shiga rawa, ta nemi miyau a bakinta ta rasa balle ta zamu zarafin bude baki ta bashi amsar tambayar da ya yi mata, kuma ta kasa dauke idanunta a fuskarta, wani dan siririn tabon yanka dake gefen fuskarsa take bi da kallo.
âBabangida ne. Wallahi shine, mutumin da ya ÉaiÉaita kyakkyawar rayuwarki da ta ahalinki tare dasa miku dawwamammen bakin ciki mara yankewa, shine a gaban ki, mutumin da kika shafe, shekaru takwas masu kyau kina bulayin nema, domin ki danĆwafar da shi a gabanki ya kwashi kashinsa a hannu.â Zuciyarta ce ke raya mata hakan, yayinda take Ćara nutsa idanuwanta cikin nasa, wanda hakan ya kara bata tabbacin akan abinda zuciyarta ta raya mata, lokaci guda wani irin Éaci ya dabaibaye zuciyarta, take kallon da take masa ya juye zuwa wani irin mugun kallo mai cike da tsantsar kiyayya da tsana, zuciyarta na wani irin tafarfasa sai wani irin zazzafan huci take fesar wa kamar wata kububuwa.
Ganin irin mugun kallon da take jifan shi da shi ya sa ya hade rai, ya lura yarinyar kwata kwata bata da kunya, shi kuma a yaruwar shi baya shiri da fitsararre take ya ji tsanar ta ya dâarsu a ransa, ranar da suka fara haduwa a Dausayi ya rasa dalilin da yasa fuskarta ya kasa bace mai a idanun shi, bini bini ta fadâo mishi a rai abin da bai ta6a faruwa dashi ba a tarihin rayuwar shi, tunanin wata mace bayan *NUR* dakyar ya samu yakice ta a ranshi ya watsar, har ya manta da kamannin ta sai kuma kwatsam ga shi yau ya sake hadâuwa da ita a inda bai taba tsammani ba, sai dai kuma yadda ya ke zaton ta Ashe ba haka take ba.
Takowa ya yi yazo gabanta ya mata rumfa kamar za su hadâe don spaces din da ya bari a tsakanin su baifi taku daya ba, kusancinsu ya haifar mata da miji mummunar tashin hankali, amma ta dake a zahiri yayinda daga ciki Zuciyarta ke rawa. Sai da ya gama karewa fuskarta kallo, kafin ya mika hannu ya kama ha6ar ta, da sauri ta saka hannu ta buge hannunshi, tana watsa mai mugun harara kamar kwayoyin idanunta zasu fadâo âkasa.
Wani irin kayataccen murmushi ya saki na gefen baki wanda da gani kasan na zallar takaici ne, a take kuma ya daure fuska, kamar ba shi ne yayi wannan murmushin ba, a zuciyar shi yace "lallai yarinyar nan tana bukatar na nuna mata other side dâina."
Sake kamo ha6ar nata yayi wannan karan da mugun karfi ya dâago fuskarta , kici kicin kwatar kanta ta shiga yi, amma duk yadda taso ta kwace ko ta buge hannunshi ta kasa, ganin baza ta iya ba yasa ta dakata tare da watsa idanunta da suke rine zuwa launin ja cikin nashi.
Kallo cikin idanun juna suka shiga yi kowa a harzuke , a kausashe ya ce "ke wacece da zaki ringa jifana da irin wannan mugun kallo, ni tsaran wasan ki ne ko kinga na miki kama da dan iska ne." Yana maganar yana kara matse mata ha6a da 'karfi.
Cikin tsananin azaba tace " mugu bakin azzalumi, dama nasan duk tsawon zamani baza ka tana canzawa ba, Babangida na tsane ka " ta karashe maganar kicin kaurara kalman *na tsane ka*
A tsawace yace "Ahmad kangiwa I said,karki sake kirana da Babangida, tukunna ma Wacece ke me kike nema a wajena waya turo ki?" Ya karashe maganar Tare da kara shakar wuyar ta, zafin da taji yasa ta saki yar 'kara, sake danko kanta yayi yace "lallai kinyi gaskiya ni mugune azzalumi, don kin tsane ni sai me? Ya fada da karfi ,sai kuma yayi low da voice din shi, ya ci gaba da cewa "Dubban mutane so na suke, kuma daga yau bana son na kara ganin wannan kodadden farin fuskar taki a in da nake idan kuma kika yi kuskure kika bari muka sake yin ido biyu dake sai na saba miki kaman...." Kafin ya kai karshen zancen shi ya ji sauka kakkuran miyau mai hade da majina a bakin shi, be san sanda ya sake ta fa kafin ya gama dawowa hayyacin sa ta kai wajen kofar fita office din da mugun gudu, tsayawa tayi tana kallon shi yana ta faman kakari.
Murmushi ta saki na zallar bakin ciki, ta ce "kodaddiyar fuskata yanzu ka fara ganinta bazan kyale ka ba har sai naga bayan ka sai na rusa dukkan farin cikin ka, mugu kawai *na tsane ka*" ta sake maimaitawa a kausashe, saboda fahimtar da ta yi kalmar na dukansa sosai.
A zuciye ya dago idanunsa da suka rine saboda Éacin rai tare da kawo mata wawura. tuni ta fice a office din da mugun gudun.
Bango ya kaiwa naushi, tunda yake a rayuwar shi ba a taÉa ci masa mutunci kamar yadda wannan yarinyar dako sunan ta bai sani ba ta ci masa yau, babu abin da yafi kona mishi rai kamar kalaman *na tsane ka* da take jifan shi, tun da aka haifeshi soyayya Kawai ya sani kowa sanshi yake , dan me yasa ita zata ringa cewa ta tsane , tabbas zai tsumayi haduwar su ta gaba kamar yadda tace kuma sai ya tabbatar ya koya mata ladabin zaman duniya.
*************************
Sai da ta kusa Éulla wajen da mutane suke sannan ta dakata da gudun, ta gyara zaman hijab dinta, kafin ta ci gaba da tafiya a hankali, sai lokacin hawaye masu dumi suka samu damar sauko mata, jefe kafa Kawai take duk inda ta samu don kwata kwata bata ganin gabanta, tsawar da ya daka mata lokacin da ta ce *Babangida na tsane ka* ke amsa kuwwa a kunne da kwakwalwarta, "Ahmad kangiwa I said, karki sake kira na da Babangida, tukunna ma wacece ke me kike nema a waje na waya turo?" Shin da gaske bai gane ta ne? To ko kuma da gaske ba shine Babangidan da take nema ba, ko shine ko ma bashi bane zata bibiyi sawun shi idan ta tabbara shine wasa yake mata da hankali zata yi wasa da nashi hankalin ta inda bai ta6a zata ba.
Bata san ta fita daga babba get din school din har ta hau titi ba sai da taji wani gigitaccen horn, a firgice ta dago kai tare da kwallah wata uwar salati,tare da rintse idanu.
A firgice ya taka birki ya fito daga motar, hakuri ya shiga bata kamar bakin shi zai tsinke duk da yasan ba laifin shi bane, ganin yadda take kuka ne hankalin shi ya tashi duk a tunanin kukan abin da ya faru take yi, ganin yadda duk ya rude yana bata hakuri duk da laifin ta ne, yasa ta dagowa ta zuba mai idanu, turuss ya yi kafin kuma yace yace "Maamah?" Bata saurare shi ba sai ma tare mai napep da ta yi ta fada tare da gaya mai inda zai kaita.
A matukar mamakan ce mutumin ya bi napep din da kallo har ta bace wa ganin shi, kamar wanda akan tsikara kuma ya zaro wayar shi tare da lalubo wata lamba da yayi saving da my Queen ya danna mata kira, d'aga wa tayi muryar ta cike da barci tace "Yayana ina wuni." Bai amsa ba sai ce wa da yayi "kina ina ne Sister.' Tace "ina gida bacci ma nake wayar ka ne ya tashe ni." Jiki a sanyaye yace "OK to koma kiyi baccin ki anjima zan shigo Estate mu gaisa." Bayan ya maida wayar shi aljihu tasbihi ya shiga jerowa ubangiji, lallai Allah mai hallita buwayi gagari misali.
****************************
Sai gurin Karfe uku su Salmah suka dayo su uku harda Suraj, kan sallaya Salmah ta same ta, sai dai kallo daya ta mata gabanta ya yanke ya fadi, da sauri ta isa gareta tana cewa "sister Eshart lafiya meya same ki, kukan me kika yi." Murmushin karfin hali ta kakaro tare da cewa "babu komai cikina ne ke ciwo."
"Wani irin ciwon ciki naga lokacin period din ki bai yi ba." Ta fada tana tsatsareta da ido, memakon ta amsa ta sai mikewa tayi zata bar mata dakin, har ta kama handle Salmah tace "ba'a boyewa abokin kuka mutuwa." Juyowa tayi ta watsa mata jajayen idanunta kafin tace "I will tell but latter." Ta sa kai ta fice.
Ajiyar zuciya Salmah ta saki, a bayyane tace "Allah ga baiwarka Allah ka shiga lamarinta." Message din daya shigo wayar ta ne ya dauke hankalin ta, karantawa tayi kafin ta saki murmushi, reply tayi, sannan ta shige toilet.
A dining ta samu Suraj da Salman suna cin abinci, kujera taja ta zauna tare da sakin murmushi,duk kallonta sukayi Suraj yace "sister Eshart ina wuni." Ta amsa da "lafiya kalau ya school." "School ba dadi, wlh ni da ace mother zata yarda Kawai tasa father ya bani kudi na fara business Ya B ya bani gida da mota a aura min Salmah kawai mu yi zaman mu ba sai munje school ba."
Karaf a kunnen Salmah da ta iso wajen yanzu. Salman ko mai zai yi banda dariya, A'isha ma yanayin da take ciki ne ya hanata darawa amma duk da haka sai da ta murmusa.
Ganin yadda suke dariya ya kara kona ran Salmah, kankance ido tayi cike da bala'i ta ce "wallahi Suraj ka fita ido na na rufe." Juyowa sukayi gaba dayan su suka zuba mata ido sai lokcin suka san da wanzuwar ta a wajen.
Marairaice fuska yayi yace "meye aibuna da yasa bakya so na." A masife tace "kayi min âkanâkanta." Ya ce "wlh ban miki kankanta ba namiji baya kadâan." Wani mugun harara ta watsa mai tare da zan dogon tsaki kamar bakin ta zai tsinke, fuu ta juya ta bar gurin ba tare da zauna dan cin abincin daya kawo ta ba.
Salman dariya ya kwashe dashi yayin da Aisha ke bin shi da kallon tausayi.
Kallon Salman yayi ya tabe baki cikin irin yanayi na shagwababbun yara, can kuma ya dafe goshi, zirrr sai ga hawaye kamar an kunna famfo.
Duk zaro ido suka yi Salman cikin mamaki yace "kuka! Akan Salmah." Bai kula shi ba sai dauke kai da yayi daga kallonsa, alamar yana cikin ciki da shi.
A'isha ta ce "ya isa Suraj ka share hawayen ka, ni na fahimce ka, ka daina saurin yin kuka idan ta gani zata kara raina ka, ka yi ta addu'a idan Salmah matar ka ce , zaka aure ta."
Ya ce "sister Eshart me nayi da Salmah bata so na? Hala ni mummuna ne shiyasa." Cike da tausayawa tace "A'a wlh Suraj kama fita kyawu." Ya ce "ta6a nan dina kiji." Ya fada yana nuna saitin heart din shi, zuciyar shi dâaya harga Allah da gaske yake ta ta6a kirjin shi.
Da sauri ta girgiza kai gabanta na faduwa, tunawa da wani abu makamancin wannan daya taba faruwa da ita acan baya, yayin da Salman ya sake kecewa da dariya.
Daker ta samu ta Kore wancen tunanin a kanta ta shiga rarrashin shi, tare fa mai alkawarin zata taya shi shawo kan Salmah, jin haka yasa ya fara jin dadi yana zuba mata godiya cike da matsanancin farin ciki yace "idan Yayana ya hau governor zan saka ya baki kyautar mota." Rass gabanta ya fadi jin abinda ya ce take kuma wani shawara ya fado mata a zuciya wannan wani dama ne ta samu.
Da sauri tace " wai da gaske kai kanin Mr AA kangiwa ne." Salman ne ya kalleta da sauri can kuma yace "da gaske ma kike tambayar shi' kenan tum dama baki yarda da magana ta ba Ashe."
Suraj kam murmushi yayi tare da cewa "Eh cousins brother na ne."
"Wow Ashe da gaske ne ta fada." Cikin farin ciki, can kuma ta langwave murya "Dan Allah Suraj ina son na ganshi ido da ieo naji ance yana da wuyar gani."
"In dai kika bi ta hannuna ganin sarkin fawa yafi ganin shi wahala."
Ta ce "da gaske." Ya gyada mata kai yana murmushi,
"Yau she zaka hadanI da shi?." Ya ce "Yaushe kike son ganin shi."
"Ban shirya ba amma idan na saka date zan gaya maka."
"To shi kenan no problem."
Fira ta ci gaba da jan shi akan Mr AA kangiwa yana bata amsa, har suka kammala cin abinci, sai da ta gama tattara duk abin da take bukatar sani sannan ta mike ta musu sallama tunda taga alamar fita zasuyi, ta wuce ciki.
Tana juya baya Salman ya daga wayar shi dake kife kan dinning table din ya kalla tare da sakin murmushi sannan yayi saving din recording din shirar su da yayi.
****************************
Har suka gama cinye wunin bata ce ma Salmah komai ba ita ma bata tambaye ta ba duk da irin zaâkuwar da tayi da son jin me ya same ta.
Bayan sunyi shirin kwanciya wuraren 10 :30 wayar Salmah ce ta fara ringing, ganin me kiran ne yasa ta kalli Eshart itama kallonta tayi, kafin kuma ta mike ta fice daga dakin da sauri. Murmushi Eshart ta saki zuciyarta na kiyasto mata wani abu cen dabam.
Falo ta nufa ta nemi daya daga cikin kujeran falon ta zauna, ta kwashe mintuna tana waya kafin ta mike ta koma dakin su,mikawa Eshart dake zaune bakin bed wayar tayi tare da cewa "ana magana.â
**********************************
Tsaye yake gaban mirro a cikin hadadden bathroom, babu riga a jikin shi sai dan guntun short wanda iyakar shi Rabin cinyoyin shi, Ćuri ya kurawa mirron ido kyakkyawan fuskar nan tashi a mugun hade, surar jikin sa yake kallo daga sama har kasa, so yake ya gono makusan sa da kuma dalilin da yasa ta ce ta tsane ni, ya fi mintuna talatin a tsaye a gaban mirror bai ga wani aibi a halittarsa ba, a zuciye ya dunkule hannu tare da kaima mirror naushi ji kake taratsatsatatat! â Me yasa na damu da lamarinta,? Mai yasa maganganunta su ka yi tasiri a gareni, mai yasa haduwarmu ya kasance a hakaâ ya dakata yana kallon jinin dake diga dis dis daga hannunsa saboda yankewar da yayi kadan, sai kuma ya saki wata shegiyar murmushi da ta yi bala'in yi masa kyau, kafin a hankali ya furta, â Bibiyats take yi tabbas, wannan karon kuma wanene daga cikinsu yake son mu yi yaĆin sunĆuru.â ya dage gira yana kallon fuskarsa a dan sauran ballin madubin da ya yage, kafin ya sake cewa, â Koma wanene, I will find out, it's kuma tabbas zan nuna mata kuskure ta na hada kai da makiyana da ta yi ..............
Aradu Allah akwai gwarama a gabađ
Oum Khadijah ceđ
***