Namiji Ƙanin Ajali (Book 01)

Chapter --- O9

by @amdeeytejjdunique587

Ajali***

                              By

          Amdeey Tejj (d'Unique).

Bismillahir Rahmanir Raheem.

=Page 0️⃣9️⃣.

Haula.

Shirye-shiryen tafiya ta kan kama,ko da Habibu ya dawo na faɗa mishi shawarar da muka Ni da Rabi'ah bai amince ba wai zamu zubar mai da mutunci ne a gari,da ƙyar na shawo kanshi ya yarda, amma ba shi zaije rabawa ba, Garba ne ze kai masallatai, Rabi'ah kuma zata bi Gida-Gida matan aure,mu kuma zamuje,Sam dai ranshi bai soba amma nidai da dai na bi son Zuciyar wancan azzalumin in saɓawa Allah,na gwammaci nayi abinda yafi haka indai ban kauce hanya ba,da haka muka gama shirin tafiya yana ta baƙin rai shiga ɗari fita ɗari ya dinga magana kenan yana cewa ina da hanyar da zan taimake shi cikin sauƙi amma naƙi sai na tozarta shi,idan ya faɗi hakan ina jin zafi amma ina yi mishi uzuri dan ko ba komai mahaifiya ake magana akai,duk da idan yayi wani abun mamaki ne yake kamani saboda ni irin sadaukarwar da nayi mishi a rayuwa amma idan ya nuna min banbanci da kum.... tunanin nawa ne ya katse sakamakon kiran da naji yana min,ba shiri na miƙe na fito falon,tsaye na sameshi ya kalle ni sannan kamar me jin haushina ko da yake haushinnawa yakeji yace

"meye kike wani kallona bazaki fito mu tafi ba,na kiraki ne kawai dan ki kalleni"

nayi murmushi sannan nace"to ai idan kallonka nema ka kira inyi ai ba gajiya zanyi ba"ya watsa min harara na juya ciki ina ƴar dariya,ban ɓata lokaci ba na ɗauki hijabi na nasa dan na shirya shi kawai nake jira,na ɗauki jakar da nasa mana kayanmu a ciki na janyo na fito,ban tarar dashi a falon ba dan haka na fita a can na sameshi ya tare mana ɗan sahu,ban jira cewarsa na shige ciki me napep ɗin kuma ya ɗau hanya,tasha ya kaimu waishi bazai je Lafia ba,muna isa muka  samu wani zaije akwai mata ɗaya a ciki muka shiga muka cike ya ɗau hanya, Kasancewar ba nisa tsakanin Shabo da Lafia yasa bamu ɗau lokaci muna tafiya ba muka isa,a tasha napep ɗin ya sauke mu, nan kowa ya fita matar nan hawa wata motar tayi da alama dai gaba zatayi, nidai sai ido ina jiran jin ta ina zamu fara,dan dai ni sai ficikon azo din amma ba sanin ko ina nayi ba dan ban cika zuwa ba,dan bani da kowa a garin shi kuma danginsa ba wani sona sukeyi ba hakan yasa bana tusa kaina cikinsu.

Na kalleshi shima kallona yakeyi

Yace"tunanin me kikeyi ina miki magana amma shiru"yayi maganar cikin taushin murya

Ɗan murmushi nayi,dan aƙalla ko ba komai yanzu na samu kulawa dan tunda Hajiya ta kwanta ciwo rabona da na samu kamar wannan ɗin,a hankali cikin wata irin murya kamar wata sabuwar amarya nace"tunani nakeyi ina ace hutu mukazo da yau mun sabunta soyayy...."

Uban tsakin da yaja shi yasa nagane katoɓarar da nakeyi.

"Dama haukan da kika shirya min kenan yasa kikace muzo Lafia,ina tambayarki ta ina za'a fara kina min hauka,da yake ba mahaifiyarki ake magana ba ko?"

Nayi saurin katseshi da faɗin "wallahi ba haka bane, kuma ko wani ne zaiyi wannan zancen ai kai ya kamata ka musa"komai baice min ba yayi gaba ya barni,banyi ƙasa a gwiwa ba da sauri na bishi,dan nasan laifina ta ya yana cikin wani hali zan kawo mishi wannan maganar, amma sone yaja min dan duk abinda Habibu zai min bana jin sonsa ko kaɗan na raguwa a raina ba, kullum kamar mu dawo sababbi ma'aurata nakeji musamman yanzu da daga ni sai shi sai kuma ace akwai yaranmu da komai ya tafi daidai ba tsangwamar danginsa,na sauke numfashi mai ƙarfi amma zan kama kaina dan alama idan nayi wasa son Habibu zaisa na fara losing control,na kai hanu na riƙo hannunsa,nace"haba Habibu kayi min uzuri kaima kasan ko wani ne yace maka zanyi hakan da gangan zaka Musa, Wallahi sonka ya zarce duk inda kake tunani a cikin raina, kayi haƙuri"

"Bakya sona Haula dan da kina sona da baki walaƙantani haka ba ,kina da hanyar da zaki taimakeni ba sai nazo nan ba, amma kinƙi kin gwammaci nayi bara kamar ni"yayi cikin ɓaci rai da alama yana jin haushin abinda nayi, zuciyata tayi nauyi inama dai wani abun ya nema daban,"Astagfirullah" na faɗa a raina yayin da wani tunani ya gifta a cikin kaina,na sauke wani numfashi mai nauyi sannan nace"Wallahi ni mai sonka ce,dan mai sonka ne kawai zaiga zaka kauce hanya ya dawo da kai,kuma mu muke neman sauƙi a wurin Allah ya kuma zamu kauce mishi..."ya katseni da faɗin"to ai Allah Mai gafara ne"nayi ɗan murmushin da zan iya kiranshi da yaƙe, yana bani mamaki idan yayi maganar kamar shi ɗinnan,nima kenan na yarda zanyi balle shi nasan idan batun asali akeyi da nagarta, da kare mutunci kai dana sunan ahali, bai kaini ba,ni ya kamata nayi wannan tunanin tunda yasan gidan da na fito, shima kuma ya sani amma na yarda zanyi balle kuma,wani abu mai kama da ɓacin rai ya yinƙuro min dan abin ya fara bani haushi shin wai ko ya daina sona ne,yo inba haka ba,wani tunani ya sake katse min wancan to ai Mahaifiyarsa ce kuma ni shaida ce yadda yake son mahaifiyarshi ƙila yana cikin rɗaɗine da ɗimuwa yasa yake haka, wannan tunanin yasa na sake mai uzuri akaro na ba adadi kamar yadda na saba,nayi ajiyar zuciya bayan na sauke wannan tunanin sannan nace"wannan bashi bane zai baka lasisin saɓa mishi,dan shi mai rahama ne ba"

"Auuuuw karatu zaki koya min kenan"ya faɗa da alama zai fara fitinan nashi.

Ganin zai sake magana yasa nayi saurin tareshi da faɗin"mubar wannan maganar tunda dai yanzu munzo,muyi abinda ya kawo mu, kaga hankalin mutane ya fara dawowa kanmu"zaiyi magana nace"dan Allah,kaga mu baƙi anan" ya jijjiga kai kawai sannan yace "ta ina zamu fara".

Na sauke numfashi sannan nace" Kasan nima baƙuwa ce bansan ko ina Gara kai tunda akwai danginka anan, amma sai mu fara daga nan cikin tasha ko?".

Bai ce komai ya nufi inda wasu mutane suke zaune da hoton Hajja a hannunsa nima na nufi wani ɓangare na tashar,na fara nuna musu hoton ina musu bayani da neman taimako da haka na fara inyi can inyi nan mai ishirin mai goma mai hamsin wasu ma har dubu, haka muka dingayi har wajen tashar, wasu su bamu wasu suce Allah ya bada sa'a wasu kuma muna wucewa su zagemu suce ƙarya kawai mukeyi haka masu barar keyi suyita ƙaryar jinya da marasa lafiya suna karɓar kuɗin mutane,da dai makamantan maganganu irin waɗannan,banga laifin su ba dan wasu suke ɓata wasu kuma dagaske ne akwai masu yin haka,nan shiga gida-gidan matan aure shi kuma yana bin majalisun maza da masallaci,a wani gida nayi sallar azahar, bayan na fito na jirashi ya fito daga sallah inajin sanarwar da yayi a masallacin,bayan ya fito muka ɗau hanya muka cigaba daga inda muka tsaya,a wani bakin hanya muka tsaya muka siya abinci,na ƙule ƙuryar shagon mai abincin naci nawa duk da ma dai cakala nayi kawai ba wani cin kirki nayi ba,muna gamawa bamu ɗau lokaci ba muka wuce muka cigaba,Hmmmmm idan nace muku nagajima  ɗaya kenan gajiya,ciwon kai, ciwon jiki,ƙafa,baya duk suka taru suka min rubdugu sai bayan sallar magariba wanda daga gefen wani masallaci nayi,ina zaune yazo ya sameni na kalleshi idanuna sukayi jah ya nemi waje ya zauna a gefena nace"Baban Yusra ya batun wajen kwana,zamuje gidansu kawu ne mu kwana?"

Bai kalleni ba yace"a'a ba can zamu ba"

"To ina zamuje?"na sake tambaya

"Inda mabarata ke kwana"

Da sauri na kalleshi nace"amma me yasa?"

"Saboda mu dasu bamu da banbanci"

"Wani irin magana kakeyi haka? Habibu wai ko__"

Ya katseni da faɗin"ƙarya nayi Iye? ko ƙarya nayi? Muna da banbanci da mabaratanne? Muma ai baran mukeyi,ko so kikeyi naje gidansu kawu na walaƙanta kaina su min dariya na tsiyace yanzu?,dama burinsu kenan,duk dama dai yanzunma bana tsira bane tunda dai na zo sai an samu munafikin da zai kai musu zancen, gaskiya Haula kinsa na walaƙanta"...........

Mu haɗu a Page na gaba

Na gode da bani lokacinku ina alfahari daku......

Naku Amdeey