TALES OF THE WAZEERIS

formations

by @surayyahms

11.

Dagata dayan bangaren kuwa sarauniya Arisha ce a dakinta ita dayanta tana kwance bisa royal bed mai laushi yanayin jikinta a sakarce kamar wacce bata da wani damuwa a duniyar nan

dan tunda suka dawo daga cikin mansion din wazeeris take cikin wani irin yanayi na tsananin jin dadi da nishadi, bata sake kulawa da halin baqin ciki da mahaifinta da mahaifyta suka shiga ciki akan sharudan yarjejnyn aure da tharim vale ta bayar akan yayansu ba.

itadai tasan duk tsiya itace kawai zata kare a matsayin matar yarima daga zuriar waxeeris tunda itace yar sarkim zamkora ta farko dole ne itace za'a zaɓa, dan haka atake tafara ji kmr destinynta ne na son kasancewa acikin babban gida da zuria me balain daraja ya fara nuna alaman cikawa batare da tasha wuya ko wahala ba.

hannunta na rike da crayon as usual tana jan layi ahankli akan secret drawing book inta dake gabanta tun jiya take zane har sai da ta cimma gama zana ilahirin tharim vale tabi tazana mansion din wazeeris da ko wanne detail data dauko shi tun daga golden gates har zuwa majestic greek buildings din kamar yadda ta gansu ranar nan suka makale a ranta.

a gefen zanen ta aje ita kanta sanye da kayan sarauta masu nauyi tana tsaye a tsakiyar gidan kamar matar yarima

murmushi tay har saida lebenta ya dan motsa cikin lumshe da ido da budewa tace "future princess of the wazeeris…” ta furta a hankali cikin zuciyarta na wani irin bugawa da zugin dadi. dan tuni tay hasashen wannan matsayi nata ne. ko kadan bata tunanin akwai wani abu da zai hana hakan faruwa sabd itace babba koda anzo zaɓe dole babban ƴar sarki zaa dauka

murmushi me fadi ke wanzuwa a fuskrta tanamai cigaba da shading din zanen tana dada kara gyara fuskar ta da kullum na yar uwarta ushna kawai take sawa ajiki.

buga kofar da akayi yasa ta dan dago kai a fusace tana kallon kofar tay tunanin maman ta ne dan haka tay sauri ta kwashe zanen ta cusa su ajikin wani jaka ahnkli tace

“shigo...

ahankli kofar ta buɗu wata baiwa ta shigo cikin ladabi ta dan sunkuyar da kai tace

“ranki ya dade… mai martaba ummu harira na jiranki.

dan tsaki arisha ta saki ahankli batace komi ba ta mike ahankli ta sauka daga kan gadon, tana gyara rigarta snn ta dau mayafi mekyau ta rufe jikinta dashi ta fito tana tafiya cikin nutsuwa mai dauke da izza.

already bayi biyu da zasu kaita sashen kakansu wato ummu hareera suna jiranta awaje tana fitowa suka rufa mata baya

tsabar yadda take nuna wa kowa acikin fadar cewa ita din me tsananin hankali da sanyin nitsuwa ce ya saka tun ahanyar zuwa bangaren kakarta duk wanda tagani a hanya sai tabishi da sanyin murmushi ko ta amsa gaisuwarsu cikin sakin fuska wasu harma tana cire kudi tana dan mikawa musmn ma bayi da talakawan da suke gefen hanya suna aikin dake gabnsu

duk ta wuce sai kaji ana cewa“Allah ya kara arziki ranki ya dade…” kusan kowa yana yi mata godiya.

bata fiye amsawa saidai ta dan daga kai sama kadan da wani irin kamun kai dan ta riga ta saba da irin wannan girmamawr

koda ta isa bangaren ummu hareera an riga an sanar da zuwanta.

kai tsaye ta shiga cikin falon acikin nutsuwa ta sunkuyar da kai kadan cikin gaisuwa tace

sannu da hutawa kakata.

ummu harira datke dattijuwa mai cike da kima da hikima ta daga idanuwanta a kanta tana dan murmushi tace “arisha… zo ki zauna kigaya min dalilin dayasa kike son ganina, kode kina kewar yar uwarki ce,

ahnkli ta mike ta zauna kusa da ita cikin ladabi ko kula batun ushna da aka ambata batay ba

bata ɓata lokaci ba tana zama tace"kakata dama inason jin bayani akan yarima ne, nasan babana ya gayamiki abunda ake bukata daga garemu

dan murmushi ummu hareera tayi tareda gyara zama kafin ta fara magana cikin nutsuwa mai nauyi.

tace yarimansu ba kmr kowani yarima bane areesha,jininsa jini ne mai tsabta mai cike da iko da girman kai. tun yana karami yake nuna alamun shugabanci da tsananin basira.

ta dan dakata kadan kafin ta kara da cewa,

“naji labari ance yaron ba mai saukin sha’ani bane. zuciyarsa kamar dutse ce, baya yarda da kowa cikin sauki.

dede nan numfashin areesha ya dan tsaya cak kai zaka dauka wani tumin fargaba taji amma kuma sha’awa ce.

ummu harira ta cigaba dacewa“duk macen da zata shiga rayuwarsa… dole ta kasance mai karfi, mai hakuri, kuma mai sanin darajar kanta. domin gidan wazeeris ba wajen wasa bane. duk yadda zamuso ayi hadin nan ba lallaine su kalle jinin mu a matsayin me tsafta shiyasa iyayenki suke cikin damuwa.

Areesha batace komi ba wani dan karamin shiru ya ratsa tsakanin su na dan lokaci duk dama a zuciyar arisha maganganun ba su rage mata buri ba saidai ma kara mata shi da sukayi

sai can ta dan sauke numfashi qasa ahankli karamin lebenta nadan motsawa dawata kalar shuumin murmushi mai sanyi ahnkli tace kaka inaji ajikina kmr ni zan iya zama dasu acn banga amfanin daga hankli da su baba sukeyi ba.

murmushi ummu hareera tay da tunanin Areesha batagama mallakan hanklin kanta bare tagane irin fitinar dake cikin wann yarjejinya, amemekon tay mata bayani sai kawai ta shanstr da maganan dan bata son ta cusa mata tsanar tharim vale aranta itama, nan suka dawo batun karatu sunayi tana jefa ma kakansu tambayoyi akan tarihin tharim vale da kuma waye yarima.

saidai ita kanta ummu hareera batasan asalin sunan yarima na yanka ba tadai san labarin rayuwarsa da arxikinsa snn tasan kuma waye ubansa da kakansa haka kaf ta kwashe labari ta gaya ma arisha komi atsanake

atake wani irin girmammen buri ya fara ginuwa aran areeshan musmn dataji cewa tun a wann shekarun already yariman da ake magana akai multi billionaire ne kuma ma mai girma shugaba khaleefa wazeeri shine kakansa, babansa kuma shine yake mulkn dala, tsatson sa shine wanda yafi kowa ne daraja da kima a tharim vale.

tun anan wajen tafara tunanin irin rayuwar da zata sauya makanta danta kasance dede da zaɓinsa da kuma irin ajinsa da dukiyarsa

,dolene ta nitsu tay karatu me daraja, snn tayi kaurin suna wajen taimakon talakawa sunanta ya rika yawo abakin marasa karfi da talakawa dole ne tafara koya wakanta rayuwa mekyau irin na manyan sarauniyoyi.

sun jima suna hira kafin nan suka rabu ta koma fada saidai bata wani bada hankli akan halinda iyayenta suka shige ciki ba itadai burinta na samun yarima me jinin tharim vale kawai ynxu ta sako agaba.

bayan kwana biyu abubuwa sai kara rikicewa sukeyi wa sarki murad da matarsa, kudi ya tsaya musu cak, ga sbbin dokoki da aka saka akan gona, dabbobi, da sojojinsu ya tsayar da walwalansu gabaki daya. gabaki daya sarki murad ya dawo baya da nitsuwa kullum cikin lissafi yake ta inda zai ceto masarautarsa daga economic nd financial collapse dayake kkrin tunkaraso.

Dagata dayan bangaren kuwa ummu salma batay wani garaje ba saida ta tsaya tayi tunani me zurfin gaske gameda dukkan shawarwarin da Nana A ta bata.

sanin cewa bada jimawa matar zafar xata haihu ayi suna anan tharim vale kafin nan ta koma lagos yasaka tay tunanin gara kawai yau yau ta fara jawo jikarta leelah cikin plan din nan.

yau da safe an shirya breakfast an gama komi akan dinning amma har yanxu leelah bata fito ba tukuna, an aiki servants sashenta yafi sau akirga amma ina saida ummu salma ta hatsala ta taho wajen dakanta

tafi minti goma a bakin kofar tana bugawa" leelah..?faleelah..

..tsabagen kira datayi sanda ta jawo hnklin kowa dake sashen.

wai ina leelah ta shiga ne kodai bata farka bane? or did she go for yoga..

tana maganan tana duban pure gold watch dinta lokcin ana neman wajen karfe goma da rabi saura.

wata servant ne tace

"bataje koina ba tana ciki rankishid dade kmr Bacci takeyi bata farka ba.

ummu salma tana waigowa tace What? wani irin bacci?kuna nufin duk uban ihun danakeyi bacci takeyi

Dukan su sukayi shiru suna ciccire idanu kasa cemusu komai tayi takada kanta ta bar wajen within few minutes ta dawo da spare key ta bude kofar ta shigo ciki a fusace

a hargitse tayo kan gadon ta yaye bargon nata da karfin tsiya cikin yanayin fada ta watsar akasa inda duk surar jikin leelahn ya bayyana tasaka wani dan ubansu milk nite gown dan guntu Inda dukan kyaun surarta yake nunawa..

da ihu tace 'Ke da Allah ki tashi Baccin nan ya isa haka You are sooo lazy leelah..ki tashi kar raina ya karasa baci

Cikin wata malalacin qwuiya leelah ta wulla kafarta sama ta buga akan gadon da karfi tana kukkuni,"grand ma dan Allah meye haka shikenan kuma Mutum bazai huta ba..ni wllh shiyasa nafison lagos kin kawo mutum nan gidan kullum sai an hanani beuty sleep dina na safe.. oh my gosh am going to be soo ugly..

amasife tace 'fuck ur beauty sleep, ki dubi agogo is late yau bazakiy breakfast bane

leelah ta mike da kyar tana mutsaka idanun ta a sangarce tana turo baki "grandma Yaushe aka fara gaya min abunda zanyi agidan nan?ni dan Allah kibarni..i need this sleep

ummu salma tayi shiru tana ta kallonta cikin rasa mema zatace

Can ta tabe baki tace nifa bansan ta ina kika dauko wann halin kin ba Nidai im not this lazy kuma uwarki ma ba haka take ba

idon leelah alumshe tace aaaaa i'm not lazy i am just preserving my beauty, grandma what did u want? waiko so kike saina fara tsufewa kmr ki..ki kalle ki fa ure not even suppose to be getting wrinkles ur mum is way younger..

daukar pillow tayi da fusata ta gwada mata akai 'leelah ni sa'arkice da zakice min haka?ni kike cewa nafi uwarjini tsufa nd am der just thinking abt ur future kullum tunani na shine ta yane rayuwar ki zai yi kyau harma ki iya rike mijin aure kekuma ashe baki da aiki sai tunanin beauty...u will not leave here with me forever kinsani aiko?

atake leelah ta takune fuskarta tana dada gyara zamanta cikin kukkunni tace "Haba grand ma saurin me kikeyi haka am still young ko karatu ban fara ba beside maza in kanada kyau aji ilmi kuma ka iya kwaliya ai shikenan.

ummi salma dake kallonta tace hmmmm

Haka ko?to tsaya kiji

Nan ta same waje ta zauna ta shiga gaya mata abunda ake ciki batun cusata acikin rayuwar shamsan tare da bata tabbacin cewa itace kadai jininsa daya dace ayi musu auren daraja anan gaba...

leelah bata wani fahimce abun ba saida ummu salma ta dau lokci tana bata labarin abubuwa dayawa na dukiya da daraja da zata rasashi idan bata kasance matar yarima shamsan a duniyar nan ba...

cewa da tay uwarjini da shugaba imran sun yi naam da wann batun yasaka leelah taji abun ya fara shigewa ranta saidai ita macece da take bala'in shakkar shamsan, koda suke yan uwan kurkusa agidan basu taɓa magana ta fatar baki dashi ba, dan tsawon shekaru tana kallon sane a matsayin yaro me wuyar shaani da kuma girman kan tsiya

koda kamasa magna ba lallaine ya kalleka ba bare ya amsaka.

ahnkli saiga kakarta ta cusa mata kwadayin son kasancewa a cikin duniyarsa tare da nuna mata cewa lallai itace zabinsu itace kadai kuma ta dace dashi a duk fadin duniyar nan.

ranar gabaki daya a tunanin wann maganr leelah ta kare, musm ma da ummu salma tay mata alkwarin cewa idan suka koma gidansu zata na barinta tana zuwa kano tanadan zama tare da gimbiya hajarat sakeena dan su saba sosai.

bayan ta tabbata da ta samu kan leelah bada jimawa ta dawo kan farees salman da batun rihanna, saidai shi bata tunkaresa kai tsaye ba, mijinta alhaj fuad ta fara jawowa cikin batun, tare da jan hanklinsa ga auren zumunci tanamai nuna masa cewa damuwa datay da dan uwansa yasaka takeso ya kulla alaqa da rihanna waxeeri watakila Allah yasa sutaso da kaunar juna har amusu aure.

abun ko kadan baiwani dara alhaj fuad ba, amma da mamaki koda ya gaya ma kaninsa farees batun sai yaga shiya dauki abun da zafi da kuma murna, sbd asalinsa yarone da idonsa yake kan dukiya da abun duniya amma yanayinsa da innocent very handasome face dinsa bazai taba nuna maka haka ba.

farkon ganinsa da rihanna yaji aransa kmr yarinyar kwata kwata batay masa ba dan baison yarinya me sanyi da nitsuwa yafi son yara rigimammu,sangartatu kmr irinsu leelah ko masu mulki da girman kai kmr marida amma kuma idan yasamu rihanna ynxu yasan manyan burikansa na zamowa me kudin gaske a wann ahali zai iya zamowa gaskiya.

kamar da wasa rayuwa ta fara tafiya ahaka kusan kowani rana leelah da areesha suna kkrin gina mafarkinsu ne akan shamsan waxeeri kowacce da irin burikan data keso tacika na zamowa cikkeiyar matarsa anan gaba.

bayan kamar sati biyu da faruwar komi naquda ya turnuke matar zafar wato ummu bilqees acikin dare, kafin kace wani abu matan gidan sun isa chamber da ake karban haihuwa duba da jiya uwarjini da hakimnta sun wuce dahrul zahra domin duba yanayin da ake ciki da shamsan acan.

sosai ummu zulaiha ta nuna tausayi, jimami da jarumtar ta a fili gwanin burgewa itace take tsaye akan komi a matsayinta na matar shugaban tharim vale.

babu wanda yasan cewa ta riga tahada baki da mai karban haihuwar akan daga zarar taga namiji aka samu zasu yi amfani da wani irin plant poison sukashesa yau yau dinnan basai ya kwana ba,

da ikon Allah kuwa sai ummu bilqess tahaifi yaranta yan biyu mace da namiji saidai tana haifarsu tay dogon suma sbd wahalar haihuwa datasha

wanda yasaka mai karban haihuwar wajen goge mata jiki tabi ta shafawa bakin nonon uwar gubar mutuwa da ba'a gane ba snn ta dauki baby girl ta wuce da ita wajen jinya sukayi karya cewa yarinyar ta hadiyi rwan mahaifa done ne sai an zukeshi kafin a shayar da ita.

ranar murna akayi agidan bana wasa ba ummu zulaiha tafi kowa nuna farinciki, har saida kowa ya saki jikinsa can bayan ummu bilqees ta farka ana tamata sam barka kafin nan yaron yasha nono bada jimawa ba sai kuma ya mutu aka rasa meyene ya kashesa sai can aka duba cewa ciwon daga nonon uwa ne.

tsabar baqin ciki sumewa ummu bilqess tayi tayi, ganin wai da namijin data haifa ne ma ya mutu, kuma ma matsalar daga ruwan nononta ne,.nan ma haoa ummu zulaiha tay ruwa tay tsaki wajen tsayawa akan ummu bilqees duk makircinka bazaka taɓa cewa dasaninta yaron nan ya rasu ba dan har kuka tay sosai tareda da taya jimami

rashin uwar jini agidan yasaka akayi saurin rufe batun mutuwar aka barsa a matsayin qaddara duk dama abune daya kusa haukata ummu bilqees tsabar tasaka ranta akan cewa ɗa namiji zata haifa kuma ko kadan bata kawo aranta cewa wani ne yake da hannu akan mutuwar yaron ba sbd yadda gidan gaba daya aka tayata jimami.

adaddafe akayi suna aka bawa babyn suna jannat wazeeri, bayan dawowar uwarjini bada jimawa akay zama akan haoa sai dai dake shugaba imran baison maman sa tace zata kawo magn tsafi bai bari anja maganar ba

bayan haihuwar da kwana goma 17 aka sallamesu suka wuce gidansu a zamfara da yarsu jannat haryau zuciyar ummu bilqess bai warke daga rashin ɗa namiji data tafka a zuriar ba.

ata fannin ummu zulaiha ko kadan batay nadama data jawo hakan ya faru ba tun da taga asirinta ya ruhu cikin sauki kai tsaye tafaɗa neman hanyar da zata dauki ciki dan ta samu ta haifa wa shugaba imran magaji kota halin kaka ne dai ace itace tafara samun namiji bawata ba.

idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata

AREWABOOKS

@SURAYYAHMS

WATTAPAD @SURAYYAHMS

WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER *** TO BE ADDED

#SURAYYAHMS

#COMEBACK SERIES

2024/2025