Past
***
Another exclusive piece from the passionate writer of AYSAM, INTENSE LOVE, EHSAAS and SCARRED.
Chapter 11
Past
Washegari ta kama asabar, Imsal da sassafe ta tashi kamar yadda ta saba ganin weekend ne yasa ta hutar da Mama Zuhra tace mata ta koma barcinta kawai.
Ita tai musu preparing simple breakfast na waffles and syrup, se gefe ta haɗama Rayyan granola saboda tasan yana so ta tafasa hot ginger tea ma Hajiya.
karfe tara ta gama duk abinda ta keyi ta hau sama tai wanka ta shirya around ten ta sakko, asaman dining ta samu Rayyan da Hajiya har sun fara breakfast sunyi nisa cikin musu ba ma susan ta iso ba seda tai sallama,
kamar jiran ta suke Rayyan yace
"yauwa unique,
kece kikai waffles ɗinnan ba Mama Zuhra ba ko?"
Ya tambaya yana jiran amsa don hajiya ta dage Mama Zuhra ce tayi,
murmushi Imsal tayi ta jinjina kai ya kalli hajiya irin I told you so ɗinnan, yana dage mata gira ɗaya.
kallon Imsal hajiya tayi tana ƙanƙantar da ido cikin rigima irin ta tsofaffi take fadin
"kiji tsoron Allah Imsal wannan ɗanɗanon abincin Zuhra ne ba naki na,"
dariya imsal tayi ta shiga haɗa tea a cup tana fadin
"toh ba itace ta koya min ba kinga kuwa dole taste ɗin girkin mu ya ringa kala," jinjina kai Rayyan yayi kafin yace
"naki ya mafi dadi kinsan nata ya fara sanyi ke kuma yanzun kike tasowa"
rufe baki tai tana fadin
"nidai ba ruwana yaya,
karka bari Mama Zuhra ta jika,"
Natasha ce ta sakko cikin gudu gudu sauri sauri har lokacin kayan barci ne a jikinta ta ƙaraso saman dining din tana fadin
"yah Imsal!
yah imsal!
kinga"
tana nuna mata wayarta,
Imsal kalla tai tana murmushi kafin tace "Masha Allah har time table ta fito kenan" jinjina kai tayi tana fadin
"ina tashi kawai naga notification, it's official next month zamu fara Waec"
Tafaɗa tana ɗan tsalle harda yar rawarta
Rayyan ya kalli Imsal yana fadin
"yara sun kusa zama manya inye congratulations,"
Murmushi tayi tana fadin
"thank you yaya,"
Ya juya ga Natasha itama yace mata "congrats Nats"
tace
"thanks bro"
tana jan kujera itama tai joining, suna breakfast ana hirar SSCE, Rayyan na basu labarin sanda sukai tasu kusan 12 years ago,
Jin Natasha ce ƙaɗai ta keta za kwaɗin jarrabawar Imsal tayi shiru yasa yaɗan kalleta yana fadin
"wai unique me kika cike a jamb ne wace makaranta kikasa as first choice naki?" Natasha ce tai saurin bashi amsa da
"yaya BUK fa ta saka bayan Mummy tace Abuja zamu koma munayin candy, nidai Nile na cike, tace zata biyamin"
Tafaɗa cikeda murna
Kallon Natasha yayi kafin ya ajje bowl din hannunsa ransa ahaɗe yana fadin
"ba wanda ze koma ko ina,
kema zaki green card ne
kidawo BUK, idan kinfison private ɗin seki zaɓi wata anan
itama Mummy ɗin zamanta a Abujan ya kusa ƙarewa,"
Natasha ɓata rai tayi tana fadin
"meyasa kace haka yaya?"
Yace
"zaki sani with time"
ya maida hankalinsa kan Imsal yana tambayarta wana course kika cike,
Shiru tai masa kafin ta dago kai ahankali tace mishi
"Nursing..Bsc Nursing"
Yace
"Nursing kuma Imsal?"
Jinjina mishi kai tai alamar eh,
Jan numfashi yayi yaso ta cike MBBS amman ba yadda zeyi tunda Nursing ɗinne choice dinta he can't force her,
yace
"kin tabbata shine choice ɗinki?"
jinjina mishi kai tai kafin tace
"please don't tell Mummy,"
Natasha dariya ta farayi tana fadin
"aiko kamar taji ta gama tafa gama saka ran ke zaki bi bayanta Imsal, don ta daɗe tana shirin kaiki Harvard kema"
Rayyan yace
"taya zata bi bayanta tana science ai hakuri kawai zatai maybe daya daga cikin ƴaƴanmu su cika mata burin ta," dariya Natasha ta farayi tana kallon Rayyan aranta tana raya lallai wato seta jira ma har sun girma sun haifi yara sannan sune zasu cika mata burinta na zama barrister kamarta.
Yace
"ke kuma dariyar me kikeyi?"
Tace
"yaya da ace inada kaifin basira kamar Imsal babu abinda ze hanani bin bayan Mummy look at how far she's become, ta zama SAN is not easy, she sacrificed alot her time, us and daddy,"
Taɓe baki Rayyan yayi kafin yace
"Is all her choices"
ya miƙe kawai yana barin gurin don inya tina kalar rayuwar da akeyi agidan nasu ransa ɓaci ya keyi haka kawai meyasa family ɗinsu baze zama normal family ba kowanne daga cikin iyayensu ya tafi building career ɗinsa,
ya tabbata da ace babu hajiya dabe san yadda rayuwar yan matannan biyu zata kasance ba idan shi namiji ya iya cupping sufa, tun ta sowarsu basu taɓa wata guda tare da iyayensu ba.
*Past*
Da farko a yadda ya samu labari tun yana ƙarami, Mummy da Daddy auren soyayya sukai,
don soyayyace mai ƙarfi da shaƙuwa a tsakaninsu kafin suyi aure,
Mummy sunanta Aisha Khalid Galadima ƴa mace ɗaya tilo gurin mahaifinta SAN Khalid Galadima, haifaffiyar garin Abuja ce.
Iyayen ta attajirai ne na gaske kuma kaf family ɗinsu babu talaka a ƴan uwa na kusa sedai nesa.
Mummy susu biyu kacal mahaifinsu ya haifa itada yayanta, Engr Bello K. Galadima kafin ya rasu awani haɗarin jirgi tare da mahaifiyarsu tin Mummy tana ƙarama da yake akwai ta zara mai girma tsakanin Mummy da yayanta Bello dake zaune a Massachusetts.
Se riƙon Mummy ya koma hannunsa alokacin yanada aure amman be taɓa haihuwa ba, ahannunsa ta fara karatun jami'a a Harvard inda take karantar law, rayuwa ta keyi cikin gata da jin daɗi don burin duniya yayanta ya ɗakko ya ɗaura mata kasancewar shi har lokacin Allah besa ya samu ƙaruwa ba ita yake kalla tamkar yar cikin sa.
Hajiya nafisa babbar aminiyarta,
Ƙanwar matar yayan ta ce Nadra wacca asalinsu fulanin garin yola ne dake jehar Adamawa.
tareda nafisa ake riƙon su agidan yayanta, sun ta sone kamar yan biyu don bazama ka taɓa cewa suɗin ba yan uwa bane na jini idan ba sune suka ɓude baki suka faɗa maka ba.
rayuwa sukeyi cikin hutu da jin daɗi, inda suna shekarar su ta uku a jami'a Allah ya haɗa Mummy da Daddy awani taron ɗaliban jami'ar Harvard da aka gabatar a shekarar,
ba tareda Mummy ta ankare ba wata irin shaƙuwa ce da soyayya ta shiga tsakaninta da Daddy wanda yake kamar Bae magnet ne alokacin, don Umar Farouk heartthrob ne almost every woman turawan da foreign student din duk sonshi suke sakamakon baiwar kyau da Allah yayi masa,
farin ba fullatanine dogo samɓal ga ƙira mai kyau ga kaifin basira duk kuwa da cewa shiɗin ba ɗan kowa bane hasalima a ƙarƙashin tallafin kuɗin makaranta na scholarship yake karatu.
Mahaifinsa haifaffan jahar kano ne mahaifiyar sace itama fulanin yola amman akano ta taso iyayenta ma ma zauna kano ne dan haka ya kasance Daddy ɗan kano ne gaba da baya.
Koda Daddy ya kammala fellowship ɗinsa komawa Nigeria yayi inda sukai sallama da Mummy kan cewar itama tana kammalawa zata dawo tai law school se suyi maganar aure.
Babu yadda ƙawarta nafisa da already ita ta fitar da nata gwanin kusan family friend ɗinsu ne,
arrange marriage za'ai musu babban malami ne a ƙasar Nigeria Sheikh Suhail bin Abdulra'uf,
amman fa shahararran attajiri ne yana da arziƙi fiye da tinanin me karatu shiyasa koda aka haɗa auren su nafisa batace komai ba don shine kalar mijin da take mafarkin ta mallaka amatsayin nata dukda kalar yadda yanayin son more rayuwarsu da wayewar su tazo ba ɗaya ba amma kuma haka ta kwantar da kai saboda Suhail ya bata kusan shekaru ashirin sanda ta aureshi.
aurene kawai beyi da wuri ba,
biyayya take mishi sauda ƙafa tana tara arziƙi aƙarƙashin sa.
itakam babu yadda ba'ayi da Mummy ba daga dangi, yayanta, ƙawayenta ta ƙe ƙashe ƙasa tace ita se Daddy babu yadda yayanta ya iya da ita saboda tana da mugun taurin kai idan ta saka abu aranta tace tanaso shi zatayi toh fa babu wanda ya isa ya tanƙwarata yace ga yadda za'ai haka suka aura mata shi amman kowa ya tsaneshi cikin family ɗinta sakamakon makauniyar soyayyar da take mishi amman shima yana bala'in sonta saboda ita macece yar ckai tsaye,
kawai idan tanason abu tanaso idan kuma bataso bataso baza kuma taso shiba har abada.
Har gida guda yayanta ya ɗauka ya basu a GRA itada Daddy saboda yace a kano zasu zauna amma Daddy yaƙi karɓa saboda yana da gudun abin hannun wani da gudun abin duniya duk wani abu da zesa mutuncin sa ya zube ko daga baya azo a goranta mishi ko ƴaƴansa yana kaffa kaffa dashi.
A gidansa na gado dake tal'udu wanda da farko Mummy ita kanta ta raina amman ganin ta dawo kusa da kusa da nafisa yasa ta yarda ta zauna cikin aminci tare dashi inda ta fara shirye shiryen zuwa law school kwatsam sega ciki ya bayyana atattare da ita.
tayi baƙin ciki sosai alokacin saboda tana ganin cikin ze zamar mata cikas tsakaninta da cikar burinta na zama babbar Barrister kamar mahaifinta,
duk wani karatun ta kuma yayanta ne ke sponsoring saboda karatune take yinsa me tsadar gaske wanda ɗan albashin da Daddy ke samu ko kwatan kuɗin da ake kashe mata beyi ba.
kusan tare sukai laulayin cikin Rayyan da Abdullah ita da Hajiya nafisa wacca sanadin shakka, soyayya da kwaɗayin abin duniyar da mijinta yake ta mallaka mata sakamakon samun cikin yasa ta tattara career ɗinta na burin zama mashahuriyar mace yar siyasa ta ajjeta agefe.
tana ganin duk wani abin jin daɗi na duniya yana mata providing, kusan sati biyune tsakanin haihuwar Abdullah da Rayyan inda ba tareda sanin mazajen nasu ba suka za gaya suka je sukai family planning domin sunce ba zasu saki ciki suyi ta haihuwa rayuwarsu ta ƙare abanza ba akan yara.
Se daga baya Daddy ya gane kasancewar sa likita kuma alokacin sukai tashin hankali da basu ta ɓayi ba harta tattara kayan ta tabar gidan tace mishi ta gama auren nasa baki ɗaya.
Shikam Suhail kwata kwata be fahimta ba da zarar ya mata maganar haihuwa se tace mishi ai Allah ne be kawo ba kawai.
Aisha haka ta sayi ticket ta koma Massachusetts gurin yayanta inda ya goya mata baya yace indai har Daddy nason zama da ita dole se ya taya ta, ta gina tata rayuwar don ba zata ƙare a haihuwa da wahalar ƴaƴan shi ba.
ko damuwa da Rayyan da ko shekara uku beyi ba data bari agidan batayi,
tacigaba da Masters ɗinta.
Daddy kasa haƙuri yayi haka ya tattara yan kudaɗensa yasai ticket ya bita ya shiga bata haƙuri domin bayason rasata har abada yana sonta kuma yasan itama tana sonsa bazeso ɗansa ya taso yaga ya rabu da mahaifiyarsa ba.
dakyar yayan ta Engr ya yarda ta dawo tareda sharaɗin zata cigaba da jagorantar law firm ɗin da mahaifinsu ya mutu ya bari a Abuja,
kuma acan zata zauna da aikinta bazata sake zaman kano ba itada kano sedai zuwa ziyara ko in taga dama.
Ba tareda dogon tinani ba ya amince da hakan, bukatarsa kawai ta dawo gareshi.
tanada gida da komai nata acan Abujar ba don ya soba ya ɗauko Rayyan suka biyota suna zaune cikin aminci da soyayya duk da shi alokacin nasa aikin ya jingine akano ya biyota don ɗansa ya kasance tare da mahaifiyarsa.
duk yadda ya ringa shige da fice gurin samun wani aikin a Abuja ya gagara ita kuma a lokacin ta ta samma shahara da ɗaukaka saboda tanada kaifin ƙwaƙwalwa ga baki, kusan rabin yan siyasar ƙasar duk abinda ya taso musu ita suke nema don karyane akadata a Shari'a.
haka taita taka matsayi iri iri, shikuma yana zaune agida yana rainon mata Rayyan har ya isa fara zuwa makaranta,
seya zamana idan ya kai Rayyan makaranta inya dawo gidan baida abinda zeyi se zaman banza kawai.
ƙawayenta da yan uwanta ne suka fara ankarewa da cewar baya aiki itace take tafiyar da gidan.
Nanfa aka fara gasa masa magana ahankali ahankali hakanne yasa ya kirata yace mata shi ze koma kano ƙila ya samu ɗan abinyi acan tunda anan ya rasa.
duk kala boren da ta masa harda mai barazana baze tafi da ɗanta ba be tanka mata ba donshi mutum ne me hakuri da kawar dakai, se ankaishi bango yake ɗaukar action.
Se tashi tai kawai taga babu shi babu Rayyan ya tattara ya koma kano batareda sanin taba.
Agurin hajiya ya bar yaron ya shiga ƙoƙarin ganin ya samu aikin daze tallafi rayuwarsa da ɗansa da mahaifiyarsa don ya gane idan ya biyema soyayyar Mummy dake ransa babu abinda ze tsinana ma tasa rayuwar, Suhail ne ya te makeshi yatayashi neman aiki inda ya kowo masa tayin komawa Harvard tunda acan yayi graduation kuma first class honour gare shi za'a ɗauke shi da gudu.
Ba tareda yaƙinin samu ba haka yayi applying, cikin rashin sa'a be samu ba.
Daga karshe dai awani state government hospital ya samar mishi ya cigaba da aiki yana ɗan lallaɓawa har Rayyan ya shekara biyar a duniya kuma be sake zuwa Abuja da sunan ganin Mummy ba.
Se tayi fisha kawai se tazo gurinsa tana samun abinda ya kawota zata hau jirgi ta koma inda ta fito,
ta maida zuwa kano to Abuja kamar ta ɗaukar ruwan leda pure water tasha ta ajje.
Wata irin rayuwar aure sukeyi kamar ba ma'aurata ba, ganin haka yasa Hajiya mahaifiyarsa ta shiga nema masa aure a dangi don ta gaji da ganin ɗanta ahaka kullum cikin rashin nutsuwa mace ta maida shi kamar wani shashasha se abinda take so yakeyi wanda bataso kuma baza ayiba.
Hajiya Nafisa ce ta guntsa mata maganar kai kuɗin auren Daddy ɗin aikuwa cikin tashin hankali ta tattaro ta dawo kano ba tareda shawara da kowa ba don baya nanma tasa aka buɗe mata gidansa na tal'udu ta gyareshi ta zuba sabbin kayan ɗaki ta tare aciki.
Hakan ba ƙaramin farin ciki ya bawa Daddy ba, Hajiya kam bata taɓa ganin fitinanniyar yarinya kamar Mummy ba don da ta saka shi aɗaki ta shiga tafita batasan me tace masa ba,
yazo har gidanta yace mata don Allah tayi haƙuri shi matarsa ta dawo bashida ra'ayin yin mata biyu ba shida ma karfin riƙe su, tabarshi da matarsa kawai zasu zauna cikin aminci in sha Allah.
Batace mai komai ba tace Allah ya kyauta kawai saboda ajikinta take jin Mummy tuban muzuru kawai take, zamanta akano yasa nan ma tafara shahara don ba dena aiki ataiba ta cigaba har Allah yasa Rayyan yashekara goma sha biyu ta samu cikin Imsal.
kamar haɗin baki sega nafisa itama da ciki, alokacinne suka kashe kuɗin su akan cikin gurin siyayyar haihuwa tattali da komai don alokacin suke jin they are ready zasu zama iyaye.
Mummy bata taɓa cikin data kwallafa rai akansa kamar na Imsal ba, duk da tasha baƙar wahala don kamar bazata rayuwa ba haka ta ringa ciwo hankalin Umar ya tashi don alokacinne yayanta yafara tako kafarsa gidanta don dubata shima ko kwana ɗaya beyi a kano ba ya koma.
ba ita tasamu lafiya ba seda ta haifi Imsal,
Hajiya Nafisa kuma tahaifi Mubeena,
wata irin soyayya takewa yarinyar wanda ko Rayyan da yake ɗanta na fari bata jinsa aranta haka, for the first time ta ɗau two year leave a career ɗinta don ta kula da Imsal dakanta yadda ya kamata. musamman yadda duk inda ta shiga anringa so aɗau yarinyar saboda kyau da gashin da take dashi,
wani irin kula da tattalin da take mata ko ita kanta batama kanta haka ya zamana batada lokacin kowa arayuwarta sena Imsal, duk tsadar abin gayu cire kuɗi take ta siya mata ɗakine guda ta ware mata don ta gama saka ran itace autarta ta gama haihuwa tunda Allah ya bata both genders.
kamar yadda aka wancan karan suka zagaye,
hakama wannan karan ma suka zagaya itada Hajiya nafisa aka sake musu wani planning ɗin.
Kusan yaran duk tare suka tashi a gidajen biyu kamar yan uwa musamman Rayyan da Abdullah don har kwanciya tare suke wani lokacin saidai duk dare haka Suhail ze kwankwasa musu ƙofa abashi Abdullahi don wani irin mugun so ya kema yaron da baya iya rintsawa in yasan baya cikin gidan.
Mummy ta gama sakankacewa itada ciki har abada kwatsam sega cikin Natasha ya bayyana ba kalar tuburen tuburen da bataima Daddy kan cewar itafa ta gaji bazata iya ba.
amman haka ya lallaɓata ta haifi Natasha cikin aminci, shekara ɗaya kacal Imsal ta bata kwanikarsu tai hakanne yasa suka tashi atare.
duk da yadda take ƙaunar Imsal tafi jinta aranta amman kasancewar yarinyar ta tashi da hali sak irin na mahaifinta yasa kusan kullum cikin faɗa suke, idan ta shiryasu tai musu wanka taimusu adon gashi don daga ita har Natasha Allah ya basu yalwar gashi tace sutafi wasa se Imsal ta faki idanuwanta ta saka ɗan kwali tafice.
sam yarinyar duniya bata dameta ba duk yadda taso ta maidata irin yadda takeso abin gagara,
saboda kullum tana jikin mahaifinta idan bata tare da shi tana tareda Rayyan da Abdullah wanda kusan sune suke daɗa yi mata tarbiya wanda Mummy bata musu ita da Natasha.
Se Allah yasa ita kuma Natasha ra'ayin ta yazo ɗaya da nata toh fa shikenan tun daganan aminci ya ɗinke tsakaninsu, Imsal da Rayyan ya zamana sune na Daddy. Natasha kuma ta Mummy san duniyarsu iri ɗayane da iyayi da kamanni babu abinda ta manta bata ɗauka na Mummy ba, kwatsam se Allah ya kawo sanadin daya ƙara raba family ɗin daga zaman guri ɗaya mutuwar Suhail bin Abdulra'uf.
wacca ta kawo tsananin ƙunci cikin rayuwar iyalan guda biyu, Hajiya Nafisa ta rasa bango da majin ginar rayuwarta kusan depression Abdullah ya shiga alokacin shine suka yanke shawarar ɗauke shi daga garin don ya samu yatafi can wani guri far yayi healing daga rashin mahaifinsa.
Mummy ce ta kawo shawarar Nafisa tai na'am da ita nan da nan akai musu visa shida Rayyan su suka biya kuɗin komai da kansu suka turasu karatu Boston,
Hankalin Daddy kasa kwanciya yayi saboda lokacin ba sufi shekara goma sha takwas takwas ba, yana ganin kamar bazasu iya zama susu kaɗai ba, Gashi gidan Engr zasu zauna kada alalata masa tarbiyyar yara su zama sangartattu kamar Mummy.
ga nauye nauye daya ƙaru akansa wanda albashinsa ma ba isarsa yake ba kuma duk yadda taso ta te makeshi baya yarda saboda yana gudun yan uwanta suzo suyi mishi gori kamar yadda suka saba.
cigaba da applying aiki yayi a MGH cikin ikon Allah kuwa wannan karo sukai accepting ɗinsa da albashi mai tsoka, ayadda ya tsara tare da ahalinsa gaba ɗaya ze koma har su Hajiya Nafisa idan ta amince don ze so ya cigaba da kula da tarbiyyar Mubeena da Abdullah har karshen rayuwarsa sedai yana kawo Maganar Hajiya nafisa da Mummy suka ce sufa sun gama zaman ƙasar waje ba dai saboda kuɗi ake zuwa ba.
toh su Allah ya rigada ya gama rufa musu asiri suna da abinyi aƙasar su duk da yasan Hajiya Nafisa bata aiki be matsa mata ba sanin cewar bazata taɓa rasa ci ko sha ba idan aka duba tarin dukiyar da suhail yabar musu,
Mummy ya shiga lallaɓawa ita ma tace bazata bishi ba seda yasa tabar aikinta a Abuja tazo ta tare gurin kula dashi da yaran sa,
shine kwatsam kuma zezo yace ze tafi toh itama bakin aikinta zata koma a Abuja se dai yayi duk abinda zeyi.
ganin idan ya biye mata ze iya rasa aikin kuma har abada ba lallai ya sake samun irin damar ba kawai ya kyaleta.
Yace taje duk inda zata je amma be yarda ta ringa mishi gantalin aiki tare da yaransa ba,
yaransa mata ne agurin mahaifiyarsa za'a barsu, nanma wani bala'in tatayar kan babu wanda ya yi ya raba ta da ƴaƴan ta, ananne ya nuna mata shi namiji ne yace idan ta isa ta ɗaukesu ta tafi dasu zata ga me zeyi ya tsallake ƙafa yabar ƙasar baki ɗaya.
Duk zigata da Hajiya Nafisa tayi kan ta kwashe ƴaƴanta karta barsu ahannun tsohuwar,
kasawa tayi don tana mugun son Daddy kuma tana tsoron ta kaishi bango kar yace ze rabu da ita dama ga mahaifiyar sa tasan ba sonta take ba haka ta haƙura ta kyale Imsal da Natasha tare da Hajiya ta kama gabanta ta cigaba da sabgoginta a Abuja,
Ita kuma Hajiya Nafisa anan ne tai tsalle tafaɗa harkar siyasa tsundum.
shi kuma Daddy ya fara aikinsa wanda yake rufa mai asiri duniya da lahira yana kula da iyalinsa dashi daidai gwargwado kuma yana samu ya kula da Rayyan da Abdullah acan,
Yana saka musu ido kan duk irin rayuwar da sukeyi, susu biyun duk agidan yayan Mummy suka zauna Engr Bello k. galadima wanda manyance da tsufa ya fara kamashi, yafara yin sanyi, kuma har lokacin shida matarsa basu samu haihuwa ba hakanne yasa suka riƙesu tamkar ƴaƴansu na cikinsu, Abdullah ɗan kanwar matar ne,shikuma Rayyan ɗan kanwar me gidan ne hakanne yasa sukai karatunsu suka gama comfortably acikin gidan Engr ba tareda wata ta kura ko wani abin ba.
Bayan Mummy ta taka matsayin SAN yasa taji a yanzun babu matsayin da take so ta taka irin na Attorney General of the federation
duk da irin yadda take mu'amala da yan siyasa samun wannan matsayin ya gagara, kasancewar appointment ne,
saboda ƙarancin shekarun ta, kuma taƙibin illegal ways ɗin da akasarin mata ake hillatarsu su faɗa don samun irin wannan babban matsayin.
ta tsaya kai da fata tana ganin ƙoƙarin ta shine ze samar mata da wannan matsayi, kuma tana temakawa Hajiya Nafisa ainun agurin yaƙin neman zaɓenta har ta samu ta hau gujerarta ta farko, itace ta haɗata da Hajiya Farida gagara, matar shugaban ƙasa meci ayanzun bayan ta faɗa mata tana buƙatar amintacciyar lawyer wacca zata ɗaura akan harkokin Farouq ɗa ɗaya tilo ga Mr president ja'afar Babagana, mutumin da Forbes tai ranking as the richest under thirty in Africa, executive chairman na Nexora Holdings, the most eligible bachelor in Nigeria.
Da farko yadda yake bawa sauran legal team ɗinsa wahala haka itama ya fara bata saboda kafin ma kasamu zaman meeting ɗaya dashi se kasha wiya wani irin sangartaccen yarone da se abinda ransa ya keso yakeyi, don sometimes Mummy har wondering takeyi ta yadda akai yayi building business da ƙananun shekaru haka he's just 27,
kuma duk abinda ya taɓa kamar anyi masa wata addu'a ta musamman seya zama kuɗi, sometimes ma sedai idan ana buƙatar ganinsa abishi can US aganshi don se yaga dama yake shigowa ƙasar Nigeria idan ya shigo din baze faɗawa kowa ba sedai kawai aganshi.
Mummy duk da yadda take da principles gurin zaɓar client's haka ta daure ta jure halin Farouq saboda shishi ƙaɗai ne ze zama ladder ɗin da ze kaita zuwa cimma burin ta na zama Attorney General.
don ance mata babu maganar wanda Mr president ya keji kamar ɗanshi Farouq,
yau Farouq ya kalleka yace yana so ka kasance cikin cabinet's ɗinsa zaka shiga,
idan kuma yace baya son ka toh duk girman ka duk matsayin ka ka fita kenan har abada,
wata irin daƙiƙiyar soyayya yake wa yaron maraji, kuma mara gani duk abinda yakeso shi yake yi saboda yana matuƙar tausayinsa da maraicin rashin mahaifiya da ya tashi aciki,
mamarsa macece me tarin arziƙi baturiyar Portland, acan Ja'afar Babagana ɗan asalin jahar Borno ya aurota inda tazo Nigeria tai building businesses iri iri,
wanda bayan rasuwarta komai ya zama mallakin Farouq shiyasa tun yana ƙaraminsa yake juya akalar manya yadda ya keso saboda dukiyar da take hannunsa ga gata da yayi masa yawa,
don yasa uban shi ya kori mata sunkai bakwai sanda yana yaro,
kafin Allah yasa a auro farida wacca ta shiga ta fita ta tabbatar ta mallake zuciyar Farouq da kissa da kisisina da siyasa itace kaɗai ta iya zama da ubanshi ta juri duk wata kalar tijararsa da rashin arziƙinsa idan ya tashi yi.
Kuma Mummy duk ta samu labarin hakan kafin tama yarda ta ƙarbi aikin da zatai masa ta ɗaura ɗamarar jure koma mene indai itada aminiyarta zasu sami matsayin da suke so su taka.
Ranar daya fara ganin Imsal wata rana ce cikin kwanakin meeting ɗinsu…
Mummy ta iso Nexora Holdings headquarters ɗinsa dake Abuja.
Gini ne mai tsayi, glass ne gaba ɗaya ta ko ina everything about it screamed power kana kallon tsarin ginin kasan fintech world ne wanda babu irinsa akaf faɗin ƙasar.
Tun daga reception har zuwa private floor ɗinsa, security ne tako ina saboda ansan yana ƙasar kuma ze halarci taro awurin yau.
Ko cikin ma'aikatan sa ba kowa ne yake samu ya shiga wasu wuraren ba,
amman da yake ita legal representative ɗinsa ce kuma tasu tazo ɗaya kai tsaye ta hau elevator ta wuce zuwa conference room directly da yake nan empty,
bashi babu dalilinsa bayan sunyi dashi ta tura mai ta e-mail lokaci da komai.
girgiza kai tayi tana kallon agogonta ganin yayi latti kamar yadda yasaba, he's never serious, lateness a jininsa yake, jan numfashi tayi ta samu guri ta zauna, tana raya
"Wannan yaron baze taɓa sauya halinsa ba"
tayi jira ya kai na minti arba'in kafin taji an buɗe ƙofa da ƙarfi shine ya shigo dogone sosai don ko atsaye Mummy take seta ɗaga ido zata iya ganin face ɗinsa yana sanye cikin wata crisp white designer shirt,
da yayi unbuttoning kaɗan daga sama, cikakken ƙirjinsa yayi tightening rigar
ya tattare hannun rigar ya kawo shi gwiwar hannayensa jijiyoyin hannayen sun fito raɗau dark brown skin ɗinsa na wani irin kalar sheƙin hutu da jin daɗi,
wandansa wani tailored black shorts ne, hannayensa ɗaure da wani matte black Rolex, gefen wiyansa tattoo ɗin da aka rubuta 1999 awaje yadda kasan wanda ze fita casual outing, kamar ba shine ma mallakin wurin baki ɗaya ba, that's Farouq duk abinda yaga dama sawa yake,
kuma yazo sanda yaga dama babu wanda kuma yake da zarrar ce mishi dan me
Idonsa na kan phone ɗinsa, yana typing.
Har ya ƙaraso gurin zamansa
“Sorry, I’m late,” ya faɗa ba tare da ya ɗago kai ba, he just said sorry amman ko daga yadda ya faɗa kasan he's not
Muryarsa sounding very steady… da wani shegen arrogance a ciki.
Mummy kallonsa tai na ɗan lokaci ta girgiza kai tana faɗin
“Mr Farouq, wannan ‘sorry’ ɗin naka inaji da ka adanashi domin gobe sake wa zakayi.”
ɗagowa yayi yana kallonta da dark eyeballs ɗinsa don yana mamakin kaf cikin workers dinsa ita kaɗai ce take iya faɗa mishi maganar da taga dama ba tareda ta duba ta ba, duk sanda taga dama, idon sune ya haɗu yayi wani kafirin smile da yasa dimples ɗinsa dake both cheeks suka bayyana yana ɗage gira kwayar ɗaya yace
“Then maybe you should get used to it.”
murmushi tayi kaɗan, irin na mace mai experience wacca tai aiki da kala kalar mutane tsawan shekaru tana faɗin
“Ko kuma kai ka koyi discipline ba”
Zama yayi yana ajje wayarsa, ya jinjina kai yana saka hannunsa cikin messy hair ɗinsa yace
“You’re bold.”
“Na fi haka ma,” ta amsa masa cike da gadara.
Murmushi ya sake yi yana umartar ta da ta fara abinda ya kawota, bayani ta shiga yi masa akan wasu legal documents da ake buƙatar saka hannunsa da wasu strategies daya kamata kamfanin su sauya gurin amfani da doka.
sunayi yana jan waya yana dannawa kamar ma baya sauraran me take cewa,
duk yadda yake bata hard time bata ƙosa ba kuma yana lura da hakan kwata kwata Barrister Aisha ba mace bace wacca take quitting abu cikin sauƙi, she doesn’t shake, ba kamar sauran lawyers ɗin da ya yiyyi abaya ba, wanda se abinda yace shine akeyi kuma tsoronsa yana bayyana ƙarara akan fuskarsu ita kam ko sau ɗaya be taɓa ganin shakkarsa ko bin umarninsa blindly cikin ɗabi'unta ba,
inya faɗi abu be mata ba straight take cewa beyi ba ta kawo nata idea ɗin tabashi kuma tai convincing ɗinsa kan cewar shine daidai,
duk sanda yabi yana ganin alheri sosai cikin harkokin sa, ganin sunyi kusan minti talatin suna abu ɗaya ya ɗanyi pouting jajayen lips ɗinsa tana ganin haka tasan ya gaji, jingina yayi da kujerarsa yana faɗin
“Let’s take five minutes,”
Ba tare da jiran amsa da zata bayar ba ya ɗauki phone ɗinsa ya fara latsawa,
shiru tai tana jiran ya gama hutawar,
Su cigaba kawai wayarta ta hau ringing, ɗaukar wayarta tai tana kallon sunan daya bayyana jikin screen ɗin da yake wayar na gefen sa yasa ta gefen ido shima ya kalli wayar tata da hoton Imsal ne ya cika screen ɗin tana wani irin murmushi idonta arufe kamarma batasan anyi hoton ba,
Murmushi ne ya bayyana saman fuskar Mummy don tun ɗazun ta kirata tana school se yanzun ƙila ta dawo take biyo bayan call ɗin, ɗagawa tai tana faɗin
“Hello durlin…”
Farouq kasa haƙuri yayi saboda aransa yanason ya ƙara kallon hoton yarinyar nan akaro na biyu amman yana ɗan shakkar abinda Barrister zatace masa.
A hankali ya jingina yana kallonta.
Ba ya jin duk abinda take faɗa sosai…
amma yana kallon yadda fuskarta ta sauya daga very professional zuwa something else, something different dabe taɓa gani atattare da itaba,
Jiyayi tace
“Kin ci abinci?”
Sai ta ɗan yi dariya kaɗan.
Kafin tace
“Okay, okay… zan kira ki later.”
Ganin Farouq na kallonta yasa ta katse wayar, ɗan ɗage gira yayi guda ɗaya yana tambayar ta
“Your daughter?”
Jinjina kai ta ɗanyi tana faɗin
“Yes.”
“Interesting,” ya faɗa kawai,
Kafin yace su cigaba da aiki,
Yana sane on purpose ya tambaye ta wasu documents da suka gama dashi gaba ɗaya last week wai yana so ya ƙara reviewing ɗan shiru tai kafin tace masa
"ban taho dasu ba,
but I think inada pictures nasu da na tura ma Attorney ɗinka dake Seattle,"
Jinjina mata kai kawai yayi yana wani shegen murmushi ganin haƙarsa ta cimma ruwa,
Mummy ta shiga buɗe gallery ɗinta…
don ta nemo hoton papers ɗin ta nata swiping, kafin ta kai ga samun papers ɗin hoton Imsal ya bayyana akan wayar full screen different picture ne wannan idanuwanta abuɗe, ta karkatar dakai tana kallon Natasha dake ɗan gefe cikin hoton kamar tsokanarta take wani yayi musu hoton,
fuskartace natural babu makeup ko kaɗan balle filter, kamar kai magana ta fito, kalbar ta manya-manya ta zubo ta rufe gefen fuskarta na dama.
kusan dena bugawa yaji zuciyarsa tayi for a moment idonsa ya maƙale akan screen ɗin, dukda Mummy already ta cigaba da swiping, lura da kamar his not himself yasa Mummy ɗagowa tana faɗin
“Any Problem?”
ɗan gyara zamansa yayi ahankali yana basarwa yace
“Nothing.”
Kafin yace
“can you show me that picture again, kamar nasan yarinyar”
Kallonsa tai na ɗan lokaci tasan sarai ba inda ya santa tsabar rainin hankali ne kawai,
Sai tai swiping back ta haska masa da kyau yadda ze gani tana tambayar sa
“Wai Imsal?”
Shi kansa besan sanda yasa hannu ya amshe wayar daga hannun Mummy ba, kawai ta tsaya tana kallon audacity ɗinsa gani tai ya ƙura ma hoton ido kafin yasa hannu yayi zooming ɗinta kaɗan to make sure ba AI bace don ko azagayen duniyar da yake yi kuma yake kan yi betaɓa haɗuwa da macen data fizgi attention ɗinsa lokaci guda irin wannan yarinyar ba,
Ahankali Mummy tace
"Ina kasanta?"
Se alokacin ya ɗauke kansa daga ganin hoton tsaɓar rainin wayo maimakon ya bata amsa seya wani ɗage gira guda yana faɗin
“bakwa kama ko kaɗan…”
Murmushi Mummy tayi tana faɗin
“She look like her father”
Wani miskilin murmushi yayi yace
"You have good taste in..."
Se kuma yayi shiru yana miƙa mata wayarsa ganin kalar kallon da take mishi, hannu tasa zata ƙarba seya riƙe yaki saki ya maida idonsa kan hoton yanajin yarinyar nan ta zauna mishi arai daram,
Sakar mata wayar yayi yana tambayar ta
“Ta na ina?”
“Kano,” ta amsa mishi kai tsaye
jinjina kai yayi kaɗan ya ɗanyi sighing
“Hmm.”
Kafin yace su cigaba da meeting ɗin,
itace tai leading gaba ɗaya saboda hankalinsa baya wurin,
hoton yarinyar ne yake mishi gizo har suka kammala ya karɓa yayi mata signing akan duk takardun da take buƙata, miƙewa tai tana mai sallama zata tafi,
Harta juya ta fara tafiya yace
“Barrister Aisha.”
Juyowa tai tana faɗin
"Yes"
ɗan sosa girar damarsa yayi yana faɗin
“Next meeting…”
Se yayi shiru kafin ya ɗaura da
“Come with that same phone.”
Haɗe girar sama data ƙasa tai kafin tace
“Why?”
Miƙewa yayi yana saka hannayensa duka cikin aljihunsa yana murmushi kaɗan yace
“I might need to see that picture again.”
Kallonsa tai na few seconds ta juya kawai ta fice daga conference room ɗin baki ɗaya da wani boyayyen murmushi cikin zuciyarta ganin the whole executive chairman na Nexora ze shigo hannayen ta cikin ruwan sanyi ta hanyar Imsal kuma zata yi amfani da abinda ta gani wanda yayi mata kala da love at first sight da ya kema yarta don ta sashi yasa mahaifinsa ya cika mata buri na zama Attorney General of federation baki ɗaya.
Its fatoumspassion IMSAL
Don't forget to
Share
Comment
Like
Vote
SPECIAL ANNOUNCEMENT
Ina farin cikin sanar muku cewa zan fara posting sabon novel dina IMSAAL a ArewaPen da Wattpad 🤍
But don’t worry… WhatsApp readers are still my priority 🫶🏽
Nothing is changing here, this is still home ❤️
To celebrate this, I have something special for my real supporters
🎁 The FIRST 20 PEOPLE to:
✔ Follow me on ArewaPen
✔ Follow me on Wattpad
Will get FREE entry into my paid WhatsApp group 💫
🎁 HOW TO QUALIFY 🎁
After following me,
📌 Take a screenshot showing you’re following me on BOTH platforms
Then send it to me on WhatsApp 👇
📩 ***
⚠️ Include your username
⚠️ Only the first 20 valid people will be accepted
⚠️ No screenshot = no entry 👀
ArewaPen @fatoumspassion
Wattpad @fatoumspassion
Hurry… once the 20 slots are gone, that’s all 🔥