12
*BAYAN AURE*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Page 12.
Sarac Stars R Pen...✍️
Sun ɗauki minti biyu a haka kafin Hafsa ta janye jikinta duk yaran suka samu gurin zama, sai ta kalle su ɗaya bayan ɗaya tana murmushi.
Duk ku share hawayenku kuma yanzu ba lokacin kuka bane, mu haɗu mu godewa Allah domin ya rufa mana asiri bamu rasa komai ba, wasu fa haka suke ruyuwa ba Uwa ba Uba duk sun rasu, to su sai suce me.? Ita Duniya fa kurkukun Mumini ce Aljanna ce kuma ga Kafiri. Ina so ku zama masu haƙuri akan ko wace irin ƙaddara domin ko wani baƙin ciki bayansa akwai farin ciki, saboda dukkan tsanani yana tare da sauƙi. Ku ƙara haƙuri da halin mahaifinku, kamar yadda Annabi Ibrahim A.S Allah ya jarabce shi akan mahaifinsa wanda har tallar Gumaka ya saka shi yayi, dan haka ko wani bawa da akwai inda Allah yake jarabtarsa. Yanzu ku tashi muje ku yi shirin hadda duk da akwai sauran lokaci, sai mu fita tare dan zan je gidanmu ni da Bilal zuwa yamma zamu dawo.
To suka ce mata cikin farin ciki, sun miƙe kenan sai ga Saminu ya faɗo gidan ko sallama babu ya tsaya yana kallonsu cikin jin haushi.
Wai uban me ya zaunar dake baki tafi ba. Kin haɗa kan yara kina kitsa musu munafunci ko, to baki isa ki rabani da su ba Hafsa, idan kin so kiyi ta zama dama kin saba, ko da yake idan kin je ma koroki za a yi ki dawo dan kar kiyi musu asarar suruki kamata. Ku Kuma ku ɓace min da gani mutane zasu shigo.
Ya ƙare maganar cikin daka tsawa, yaran suka tashi cikin sauri suka faɗa falo ko wanne ya nima gurin zama, Hafsa ta yunƙura ta miƙe tana kallonsa, sai yace cikin haɗe fuska.
Kayan da suke wancen ɗakin ki tattara su ki san inda zaki aje, dan masu gyara zasu fara aikin ɗakin Zinatu, dan dawowar ta babu fashi.
Allah yasa alkhairi, ai gwara ta dawo dan ita ta zama nakiyar kan kashi, kun haɗu kun dace.
Tana gama faɗar haka ta shige ɗaki ta bar Saminu yana ta zage-zage, har masu aikin suka shigo suka gwada aikin kafin suka fice Saminu ya bi bayansu suna magana, da suka gama ya wuce bai sake shigowa gidan ba. Ba ɓata lokaci ta shirya dan tayi alƙawarin gobe In Sha Allah Monday Bilal zai tafi yayi registern makaranta dan shi ne kaɗai abunda zai rage masa zaman gida da zuwa shagon Abbansu, a yanzu ba taso ya cigaba da zama a office ɗinsa dan bata ƙaunar ya yi gadon sana'ar baban, dan aikin dillanci bai dace da matashi kamarsa ba, gwara ko zai yi ya zama akwai ilimi a cikinsa. Haka suka fita ta rufe ko ina har ƙofar gida suka rufe da key dan tasan da wuya Saminu ya dawo yanzu, suka tare napep suka wuce gidansu, sai da suka tsaya a makarantarsu Samira suka sauka kafin ta wuce ita da Bilal, a hanya yake nuna mata hannunsa yana cewa.
Mama wuyan hannun haguna zafi yake min, kamar na samu rauni.
Ba mamaki, dan nasan ba suyi maka duka na imani ba, In Sha Allah Allah sai ya saka maka, bari mu ƙarasa gida sai muje gidan Malam mai ɗauri ya duba maka hannun.
Ya ce to tare da gyaɗa kai kafin suka yi shuru ko wanne ya fara saƙar zuci, Hafsa tayi nisa a cikin tunanin makomar aurenta dan ga dukkan alamu ga shi ya fara shafar yaranta kuma babu alamar Saminu zai sauya, wani lokaci tana mamakin irin soyayyar da Saminu yayi mata kafin aurensu har gani take kamar zai haɗiyeta dan so, sai dai gashi yanzu zaman su ya koma kamar zaman Annabi da Kafiri, kwata-kwata basa jituwa saboda son zuciyar da ya saka a cikin zamansu.
Hafsat su 'yan asalin jihar Kano ne daga ƙaramar hukumar Rano, iyayenta duk 'yan can ne dan haɗin zumunci aka yi musu, babansu Malam Hadi ya fito cirani zuwa birnin Abuja inda yake siyar da hulan maza na yara da manya yana yawo dashi a hannu, a haka Allah ya bunƙasa ya samu jali mai tsoka. A wata rana wasu mutane suka damfare shi ya samu karayar jalinsa, shi ne ya saka shi barin garin Abuja cikin takaici sai ya yada zango a Kaduna. A nan Kaduna ya kafu har ya buɗe shago a cikin gari kasuwa, ya je Rano ya ɗauko iyalinsa suka fara zama a gidan haya, kafin daga bisani Allah ya buɗa masa yayi gida a Rigachikun suka tare. Su bakwai iyayansu suka haifa yayyinta maza uku, Isma'il shi ne babba, sai Usman, sannan Umar, sai Hafsa sannan ƙanwarta Amina da take aure Kano can dangin babansu, sannan Aliya tana aure a Abuja sannan autan su Aliyu yana karatu anan KASU ya kusa gamawa, duk gidansu shi ne ya samu yin karatun boko mai zurfi dan yayyinta maza duk kasuwanci suka faɗa kuma matakin karatunsu duk diploma ne, su matan kuma iyakarsu secondary ake yi musu aure.
Hafsa ta haɗu da Saminu a hanyar dawowarta daga makarantar boko dake unguwar Kawo, dalet girls secondary school.
(Ina waɗanda suka yi day kawo, ina magana da wanda suka yi candy a 2009, to ga Rahmatu K Muhammad 'yar Science class. Ina miko gaisuwa mai tarin yawa waɗanda suka rasu Allah ya jikansa da Rahma, mu muka Allah ya raya mana zuri'a ya shirya mana su yasa mu gama da duniya lafiya. Ameen)
A lokacin Hafsah tana SS2, tunda Saminu ya saka ta a ido ya matsa mata lamba, musamman in sun taso daga makaranta saboda shagon babansu da yake sayar da takalma yana bakin hanya, to sai ya jirata ta zo wucewa ya bita yana magiyar ta yarda ya mayar da ita gida a mashin ɗinsa, tun Hafsah tana ƙin kula shi har sai da ta saduda ta amince masa har ya fara zuwa hira. Saminu irin mutanen nan ne masu kyauta duk in zai zo hira sai ya ruƙo mata abu, sannan da tafiya tayi nisa sai ya zama shike jigilar kaita makaranta ya kuma dawo da ita in an tashe su, wanda wannan kyautatawar da yake yi masa ya saka shi samun babbar gurbi a zuciyar Hafsa, ta daina kula kowa sai shi, shi kuma ya dage wajen ganin ya siye zuciyarta bisa tarin soyayyar da yake nuna mata da hidimar kuɗi, haka ya jure har sai da ta kammala secondary bai gaji da hidimarta ba, duk wasu kayan kyale-kyale sai dai a gani a jikin Hafsah dan ta fita zakka a cikin ƙawayenta sai dai su zo aro a gurin ta.
Bayan ta gama makaranta Saminu ya turo iyayensa lokacin mahaifinsa yana raye aka saka bikinsu wata uku. Da biki ya ƙarato Saminu ya aro motar abokinsa ya riƙa ɗaukar Hafsa da ƙawarta Zainab suka dinga rabon kati da sweet na aurensu, duk abunda Hafsa ke do shi yake yi mata, har aka ɗaura aurensu tana alfahari da samun miji kamar Saminu, sai dai tafiyar bata yi nisa ba ta ƙara gane Allah ɗaya ne, sannan mutum tara yake bai cika goma ba. Ta azabtu da halin Saminu tsawon shakaru Sha Tara da aurensu, wanda kawo yanzu babu abunda ya sauya daga halinsa sai ma sabbin halayya daya ke ƙara hudo dasu. Ta sauke gwauron numfashi lokacin da Bilal yake ce mata.
Mama mun iso.
To tace, sai ta fito da kuɗi ta bawa mai napep kafin suka shiga cikin gidansu da aka ƙara gyara shi saboda yayyinta maza suna ƙoƙarin gyara gidan. Da sallama suka shiga cikin gidan Innarsu ta amsa daga falo, sai suka shiga ciki Inna ta na cewa.
Hafsatu in ce dai lafiya kika zo a wannan lokacin.?
Haba Innarmu meyasa duk sadda na zo sai kince lafiya.?
To ai naga baifi kwana huɗu da kika zo ba, to marabanku, Bilalu har da kai ja'iri yaushe rabonka da mu.
To tunda na zo sai hankalinki ya kwanta, dama nasan kin yi kewata.
Cewar Bilal yana dariya, inna tayi masa daƙuwa tana murmushi. Duk suka zauna suka gaisa kafin suka shiga hira, ba jimawa babansu ya fito dan bai fita kasuwa ba, yau Lahadi ranar hutunsa ne, shima ya zauna suka gaisa sai Hafsa ta ce cikin damuwa.
Baba nifa gurinka nazo, ina so Bilal ya dawo nan gidan da zama na wani lokaci.
Saboda me yaro da gidan ubansa zaki ce yazo nan, meya faru.?
Cewar inna data katseta, Hafsa ta nisa ta ɗago kai ta kalli Bilal tace ya basu guru, sai ya miƙe, ta dakatar da shi ta miƙa masa ɗari biyar.
Kaje gidan Malam me ɗauri ya duba maka hannu sai ka bashi sadakar ɗari biyar, ka yi wa Aliyu magana ya raka ka nasan yana nan.
To yace mata ya fice sai Hafsa ta gyara zama ta basu labarin abunda ya faru ɗazu duk da ba komai ta fito fili ta faɗa ba, babansu ya girgiza kai cike da takaici.
Ai Saminu ya wuce yadda nake lissafi, kiyi haƙuri Hafsu saboda ba kiyi dacen miji ba, dan wlh yanzu ko dariya kika yi nasan na yaƙe ne. In dai tani ne babu matsala yazo ya zauna muga yadda hali zai yi, kuma maganar makarantarsa cikon nawa ne kike nima.?
Yanzu dai akwai dubu goma a hannuna sannan a cikin satin nan zan kwashi adashi dubu hamsin, to ina niman cikon dubu arba'in ne ya zama dubu ɗari sai yaje yayi register. To yanzu ma na zo niman aron kuɗi ne gurin su yaya Usman, nan da ƙarshen wata zan haɗa na basu inna amsa dashi na.
To Allah ya kyauta, ki cigaba da haƙuri kinji wata rana Saminu sai ya Nima yafiyarki, sannan karki gaji, ki cigaba da hidimar yaranki gaba ke zaki ci riba, dan haka ni zan bada kuɗin registration ɗin ba zai gagara ba.
Haba malam ya zaka ɗauki nauyinsa bayan kasan Ubansa ba mutunci ne da shi ba, ni wlh ban goyi bayan a kula da jinin Saminu ba.
Cewar inna ranta a ɓace, baba ya yi galala yana dubanta.
Ba jinin Saminu bane kaɗai har da na Hafsu, kuma duk abunda nayi ban faɗi ba saboda domin Allah zanyi domin Hafsu, yau da ina da halin yadda zan yaye mata baƙin cikin da take ciki wlh zanyi, amma ko yanzu ban gushe ba wajen yi mata addu'a.
Nima ba ina nufin wani abu bane kawai dai takaicin Saminu nake ji amma akwai Allah, ki je ki ta haƙuri dan ko kin bar masa yara kin dawo nan ba zaki taɓa samun kwanciyar hankali ba, duk wuya duk runtsi kiyi zamanki a ɗakinki dan aurenki yafi miki akan zaman gidan nan, bana yi miki fatan Zawarci gwara ki zauna ko da mutuwa kika yi a ɗakin ki ne, kuma zaki samu kyakkyawar sakamakon haƙurinki.
Cewar Inna cikin sigar rarrashi, wasu hawaye suka kawo idon Hafsa, tasan dama ko dawowa gidan tayi ƙarshenta zasu ce ta koma, ba zasu bari ta zauna ba saboda basa ƙaunar tayi zawarci sunfi son ta zauna a ɗakinta duk wahala da ƙuncin da take fuskanta. A zuwa yanzu ta fara tunanin ta jingine auren Saminu saboda tana tsoron ya goga mata ciwo, sai dai tasan babu mai mara mata baya hatta yayyinta ra'ayinsu iri ɗaya dana iyayensu, ko ta kai musu kukan halin da take ciki sai dai su bata haƙuri su haɗa mata kayan abinci da kuɗi suce ta zauna ta cigaba da haƙuri. Sai ta sauke ajiyar zuciya ta share hawayenta ta shiga yi musu godiya musamman Baba daya ce zai bada kuɗin makarantar Bilal, daga Nan sai suka shiga hirar bikin da zasu tafi zuwa Rano na ɗiyar ƙanin babansu, sai tace itama a saka da ita cikin masu zuwa saboda a motar yaya Isma'il zasu tafi.
Haka suka yini ita da Bilal a gidan cikin farin ciki dan hirar data samu da mahaifiyarta da yaya Usman da Umar da suka zo, ya ɗebe mata kewar damuwar da take ciki, kuma suma sun bata haƙuri sosai har suka yi mata alƙawarin zasu siya wa Bilal mashin roba roba second hand ya samu na zuwa makaranta saboda ta huta da kuɗin transport ɗinsa, sannan duk sati zasu riƙa tura masa kuɗin mai, da wannan farin cikin ta dawo gidanta kamar kar ta bar gidansu. Ƙarfe shida da minti shida suka shigo gida, ta buɗe ɗaki ta shiga ta sauya kaya zuwa doguwar riga dan ta shiga kitchen ta ɗaura musu abincin dare ga yamma tayi, Bilal ya zauna a ƙaramar kujera a tsakar gida yana cewa.
Mama banda hannuna yana ciwo dana taya ki da jajjage.
Ai wlh mutanen nan bazan gushe ba wajen yi musu addu'ar Allah ya saka maka na targaɗen da suka ja maka a hannu.
Kar ki ga laifinsu mama ai saka su aka yi. Kuma komai zai wuce, ni har na ƙosa gobe tayi na wuce makaranta, kinga Uncle Aliyu yace naje da wuri mu tafi tare shi zai shige mini gaba nayi registern komai.
Allah dai ya kaimu lafiya.
Cewar Hafsa fuskarta ɗauke da murmushin farin ciki, sai ta shiga kitchen ta kunna gas ta ɗaura ruwa a tukuna wanda zata tafasa taliya suci da miya, sai dai lokacin data shiga store ɗinsu sai taga wayam kamar an yi musu kwalima babu komai a ciki an kwashe kayan abincin, sai ta dafe ƙirji tana salati ta fito da sauri tana faɗawa Bilal, ya kalleta yana murmushi.
Mama wa zaki zarga zai kwashe in ba Abbanmu ba, shi ne kaɗai zai buɗe gidan nan tunda yana da key a hanunsa.
Ya ƙare maganar yana girgiza kai tare da murmushin takaici, Hafsa ta sauke ajiyar zuciya jikinta yayi sanyi kamar an watsawa kaza gishiri, ta girgiza kai tana cewa.
Allah ya kyauta to, amma bari na kira shi dan na kore shakku, in shi ne ma zai faɗa dan nasan ba zai ji tsoron faɗa mini ba.
Ta ƙare maganar tana shiga ɗaki, sai ta ɗauko wayarta dake cikin jaka ta duba dumber ɗinsa ta kira shi, sai da ta jera masa kira ya kai uku bai daga ba ana huɗu ne ya ɗauka yana cewa.
Lafiya kike damuna da kira kamar naci miki bashi. Ko jarabar taki ce ta motsa kika janye ƙudurinki na sai na yi gwajin jini.
Hmmm ni ba wannan ne yasa na kira ba dan bana marmarin abunda ya ke dauke da ƙazanta, har sai in ya tsarkaka daga dafin cutar da nake zargin an kwasa. Na dawo gida na tadda ba kayan abinci shi ne na kira naji ta ina aka haihu a ragaya.
Wannan Dattijon naki mai farin gashi shi ne yake ɗauke da cuta ba ni ba, kuma abinci ni ne na kawo kuma na kwashe, saboda ba zan cigaba da ciyar dake ba kina ƙaton kashi sannan ba zaki bani haƙƙina ba.
Ya ƙare maganar cikin gadara, Hafsa ta yi guntun murmushi.
Ai ina tunanin tsohuwa mai dattin ɗankwali ita ce take ɗauke da cutar hawan jini saboda baƙin cikin da kake ƙunsa mata, sannan kasan ni ba daga gidan yunwa ka aure ni ba, dan haka bazan taɓa kwana ban ci ba, kar Allah yasa ka ciyar dani ba zan mutu ba.
Ni kike zagi Hafsah.?
Ai iyaye basu fi iyaye ba, idan kaji zafi karka sake zagar min nawa iyayen dan wlh in ka zage ni zan rama, yanzu ba da bane.
Sai ƙit ta kashe wayar, ta juya ta kalli Bilal daya shigo ɗakin ta haɗe rai.
Meya shigo da kai.?
Kafin ya bata amsa sai ga su Yazeed sun dawo daga makaranta, suka shigo falon da sallama ta amsa kafin ta fito da sauri ta rufe gate ɗin gidan.