13
*BAYAN AURE*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Page 13.
Sarac Stars R Pen...✍️
Hafsa ta zauna a Cushing tana sauke numfashi dan sosai take jin zuciyarta tana tafarfasa, zuwa yanzu bata jin zata sake ɗaukar wani cin kashi da Saminu zai yi mata. Sai tayi ƙwofa tare da nisawa ta ce wa Yazeed yaje ya ɗauko park ɗaya na garin ɗanwake ya kwaɓa, idan ruwan ya tausa zata zo ta jefa, yace mata to sai ya wuce zuwa ɗakinta ya ɗauko kafin ya fita.
...
Bayan anyi sallar magariba suna zaune a falo su duka ga abinci nan Hafsa tana raba musu, da yake a gida tace suyi sallar magriba saboda bata so Saminu ya samu ƙofa a buɗe dan bata shiryawa rikicinsa ba, sun fara cin abincin kenan suka ji tsayuwar motarsa, Hafsa ta kalli Yazeed tace yaje ya rufe mata ƙofar falo, ba musu ya miƙe yaje yayi abunda tace, ya dawo suka cigaba da cin abinci, sai suka fara jin bugun ƙofa, amma shuru kamar babu wasu halitta a cikin gidan ba wanda ya motsa, Saminu ya cigaba da bugun rashin mutunci, amma shiru ba wanda yazo ya buɗe, da farko ya ɗauka da key suka rufe sai ya saka key ɗin amma yaji a buɗe yake, a nan ya fahimci sakata suka saka, haka ya cigaba da buga gate ɗin yana surfa masifa, har sai da maƙocinsu ya fito ya tambaye shi ko lafiya, sai Saminu yace masa cikin faɗa.
Ba ruwanka malam Idi, ko ƙofar gidanka nake bugawa da zaka zo kana tambaya.
To Allah ya baka haƙuri ai ba ni na kar zomon ba.
Yana gama faɗar haka ya juya zuwa cikin gidansa, Saminu ya cigaba da sababi daga bisani ya juya tare da ɗaukar alwashin zai ɗauki mummunan mataki akan Hafsa. Ɓangaren Hafsa kuwa tana jin buga gate amma tayi banza yaran ma ganin yadda tasha kunu yasa babu wanda ya tanka mata, haka suka kammala cin abinci suka kwashe kayan suka mayar kitchen, kafin ko wanne ya yi alwalar sallar isha'i suka dawo falon suka yi sallah, a lokacin aka dawo da wuta suka kunna TV suka fara kallo, Hafsah kuwa ta wuce ɗaki tana tunanin mafitar zamansu da Saminu dan ya riga ya kaita bango.
*****
Hamida.
Ko da ta gama waya da mama sai ta kira Inna Jamila suka gaisa kana ta tambayeta ba wata damuwa tace mata eh babu, sai ta cigaba da cewa.
Hamida kiyi takatsantsan da abokiyar zamanki karki yi sauri zura jikinki a gurinta ki, natsu da kyau ki gane takunta dan gaskiya jikina ya bani da gangan suka rufe gida lokacin da muka kawo ki suka tafi, sannan kina gani jiya har muka ƙaraci zamanmu basu zo ba.
Laaa inna wlh Laila ba muguwa bace, ba kiga tarban data yi min jiya ba.
Cewar Hamida cikin nishaɗi har ta kwashe labarin yadda suka yi jiya da ɗazun kan maganar ajin da zata sakata na koyan girki. Inna Jamila taja tsaki.
To ke 'yar aikinsu ce da zata saka ki a wani ajin koyan girki, ko mijinku ne ya ce lallai sai kin ƙara koyan girki.? Hamida na raba ki da wannan sakarcin! taya daga zuwanki gidan zata ce zata biya miki wani aji, anya babu wata a ƙasa kuwa.? Ki dai yi hankali na faɗa miki.
Kai Inna wlh ba yadda kike tsammani bane, kuma ko da na faɗawa mamanmu cewa tayi na yi mata biyayya sau da ƙafa.
Hmmm Inna Jamila ta murmusa kafin daga bisani da ɗaura da cewa.
Itafa yaya Hajjo komai ma zata faɗa miki kiyi matsawar zaki samu gindin zama a gidan, idonta a rufe yake da ƙaunar aurenki, ba zata so a samu matsala ba shiyasa zata ce kiyi komai dan ki rufa mata asiri, kuma abun ba daga nan bane, ni kawai na kasa samun natsuwa da kishiyarki.
Inna kiyi min fatan alheri In sha Allah babu wata matsala.
Cewar Hamida a sanyaye, sai Inna ta nisa tace.
Shike nan Allah ya baku zaman lafiya, idan an kwana biyu zan zo na duba ki.
To Allah ya kaimu nagode Innanmu.
Cewar Hamida cikin murmushi jin daɗi, da haka suka yi sallama sai ta kuma kiran ƙawarta Haulat, nan ma hira suka sha sosai sannan Hamida ta bata haƙurin da basu sameta a gidan ba, bayan sun jima suna hira sai suka yi sallama Hamida ta kira kaka suka gaisa, kaka ta daura da cewa.
Dan Allah Hamida karki shagala da jin daɗi ki koma kina wasa da ibada, kamar yadda kika saba yi anan gida ina so ki dage kifi da, domin a yanzu kina da cikakken damar bautar Allah cikin natsuwa, saboda ba kya fita ko ina ga shi kuma kina gidan hutu, ki kuma dage da Azkar ɗinki kin ji.
In Sha Allah kakus zan dage ina godiya.
Sai suka ɗan taba hira kafin suka yi sallama, Hamida tana mai sauke ajiyar zuciya, babu maganar daya fi zama mata a rai irin na Inna Jamila, sai ta saki murmushi kaɗan tana cewa a zuciyarta.
Inna kenan ai yanzu an daina kishin jahilci, ni banga wani aibun Laila ba balle in ce zan kama kaina bayan ta nuna mini sauƙin kai.
Sai ta mirgina ta gyara kwanciya tare da lumshe ido, a haka cike da tunani bacci ya ɗauketa. Bata farka ba sai bayan la'asar shima Hafiz ne ya kirata a waya, koda ta ɗaga sai ya sanar da ita zata dafa masa tuwon semo miyanr kuɓewa ɗanya, Sannan Laila da yaranta zata dafa musu dafadukan taliya da kifi, tace masa to kafin ta aje wayar ta fara gabatar da sallah kafin daga bisani ta fito ta shiga kitchen, tunda ta fara aiki bata zauna ba har sai da ta kammala zuwa bayan sallar magriba, ta samu ta yi wanka ta gabatar da Sallah.
****
Bayan an kwana biyu.
Hamida ta zama 'yar gida dan ta saki jiki sosai musamman yadda Hafiz yake nan-nan da ita sannan Laila bata nuna mata komai ba, dan gane da aikin gidan ta zage ƙarfi tana yi sosai kamar dama tazo da shirinta, kullun maganganun Mama data yi mata sune suke ƙara ingizata tare da samun ƙarfin guiwa musamman yadda kullun Hafiz yake zaɓar musu abincin da zata dafa, ga kuma Laila da ta sake mata, bata yi mata shamaki ba wajen amfani da kayan ta dan har yanzu kayan ta na kitchen data zo dasu suna ɗaure a buhu bata kwance su ba, babu ma ranar buɗewa domin ta adana su a can cikin kaɗan wardrobe ɗinta da yake a kwai gurin ajewa.
Yau ta shiga kitchen da wuri tayi aikinta dan har ta samu damar yin charting, kiran sallar magriba shi ne yasa ta a aje wayar kafin ta gabatar da shi, lokacin data idar tana zaune a dadduma Hafiz ya dawo gidan ta zuba ido taga ko zai fara zuwa ɗakinta amma sai taji hirarsa da yara a falo daga bisani ma taji shuru sun haura sama, ta riga ta jera kayan abincinsu a dining ita kuma ta ɗiba nata ta aje a kitchen akan sai tayi Isha'i zata ci, sai da ta idar da karanta azkhar sannan ta miƙe ta gabatar da isha'i da aka kira a lokacin, data idar ta fito falo har lokacin ba kowa sai tv da yake aiki shi kaɗai, ta shiga kitchen ta ɗauko abincinta ta koma ɗaki taci, sai ta fara tunanin ya kamata taje ta gaishe da Hafiz tayi nasa sannu da zuwa, sai ta yanke shawarar idan ta gama cin abinci zata je ta gaishe shi. Lokacin data kammala sai ta miƙe da nufin kai kayan kitchen sai taji wayar ta tana kuka, sai ta tsaya ta ɗauka taga My heart ɗinta ne, dan tuni ta sauya sunansa kamar yadda Laila ta bata shawara, ta ɗauka cikin sauri ko kafin tayi magana ya riga ta da cewa.
Baki san na dawo bane.? to ki haɗo abinci ki kawo mana shi sama a nan zamu ci.
Bai jira amsar taba ya kashe wayar, ta sauke wayar daga kunnenta jiki a sanyaye tana mamaki, sai ta fara tunanin ashe ta ɓata masa rai da bata je ta yi masa sannu da zuwa ba, a lokacin ta yanke niyyar In Sha Allah zata gyara, sai ta fito cikin sauri ta haɗa kayan abincin a babban tire ta bar sauran kula biyu sai ta haura sama ta tura ƙofar falon da sallama, ta samesu su duka a nan suna kallo, Laila ta amsa tana wani sakin murmushi gashi taci uban ado kamar zata fita anguwa, sai Hamida taji kamar ta muzanta ganin dogon hijab ne a jikinta wanda tayi sallah da shi kuma kayan bacci ta saka lokacin data yi wanka ta ɗaura zani akai, ta ƙirƙiro murmushi.
Sannunku da hutawa, sannu da zuwa my heart.
Yauwa suka haɗa baki shida Laila ta aje tiren a center table ta koma ta ɗauko sauran kulolin babu karar da suka yi mata na saka yaran su tayata ɗaukowa, sai da tayi mayawa uku zuwa falon kafin ta yi musu sallama ta fito tana mayar da numfashi.
Gaskiya bazan iya ruyuwa a sama ba saboda wannan hawa da saukan, in mutum bai ci ya ƙoshi ba tuni cikinsa zai zazzage ya zama ba nauyi.
Ta faɗa tana yi wa kanta dariya sai ta zauna a Cushing ɗin falo tana kallon TV, tsautsayi yasa ta ɗauki remote da nufin sauya tasha, ashe na tv ta ɗauka ba na decoder ba sai ta shiga wani guri hasken tv ya ɗauke ya fara wani shooo gashi da volume, da sauri Khalil ya fito dan ya duba saboda har falonsu sun ji, yana gani ya juya sama yaje ya faɗawa babansu ba jimawa ya fito fuska a ɗaure yana cewa.
Me kika taɓa ya nuna haka.?
Wlh nazo sauya tasha ne sai na kuskure ban san ba remote ɗin bane.
Kinga bana son ki ja min asara, kinsan ko nawa ne kuɗinsa.? taya zaki taɓa abunda ba a baki izini ba, wannan TV bani na siya ba Laila ce, dan haka idan kika lalata sai dai ki biya ta ba ruwana.
Kayi haƙuri.
Hamida ta faɗa a raunane, sai suka ji Laila tana cewa.
Haba beb meye TV, ai itama gidanta ne tanada damar yin amfani da komai, 'yar uwa karki ji komai yau Dady ya shigo gidan da rigima ne shiyasa yake niman saukewa akanmu.
Ba komai Anty ai ya dace nasan komai ta hakane zan kiyaye.
Hamida tace tana miƙewa tare da cewa.
Kun gama cin abincin.? ina so na kwaso kayan ne na mayar kitchen zan kwanta.
Karki damu kije ki kwanta ko da zuwa safe zai ki kwashe su.
Cewar Laila, Hamida ta gyaɗa kai tana murmushin yaƙe ,sai ta ce wa Laila sai da safe kafin ta wuce ɗakinta zuciyarta ba daɗi, ta rasa gane kan Hafiz kuma sosai ta shiga damuwa da tunanin dole zata bashi haƙuri dan bata ƙaunar ɓacin ransa. Laila ta raka ta da shu'umin murmushi, sai ta saƙala hannunta a wuyan Hafiz tana cewa.
My man ka riƙa yi mata uzuri baƙuwa ce fa.
Duk da haka dole a riƙa tunatar da ita karta riƙa yi wa mutane ɓarna.
Yayi maganar yana zamewa daga riƙon data yi masa ya haura sama, Laila ta rungume hannunta tabi bayansa da kallo ranta fes, zaman nasu yana tafiya mata yadda take so, abun yayi mata daɗi, kuma fatanta Hamida ta tabbata a yadda take muradi, banda ma Hafiz ya nuna matarsa ce a fili, ai da bai tara da ita ba balle tayi tunanin tana da wani daraja a gidan, amma da sannu haƙƙarta zai cimma ruwa, sai ta sauke ajiyar zuciya ta juya zuwa falon sama, haka suka ci abinci suka bar kayan a gurin, Hafiz ya wuce ɗaki ya watsa ruwa ya gabatar da Sallah, sai ya zauna gefen gado ya soma duba wani aiki a system ɗinsa, ba jimawa sai ga Laila ta shigo cikin wani kayan bacci mai fidda surar jiki, ta ƙaraso cikin takun jan hankali sai saurayar da kai take yi tana lumshe ido, Hafiz ya saki murmushi cike da mamakinta dan ya gane inda ta dota, matar da take gudunshi yau itace ta kawo kanta, sai ya ce cikin ɗage gira.
Beb yane.?
Bata amsa shi ba ta zaune gefensa daga nan ta fara shafa bayansa, tana magana ƙasa-ƙasa bai ma jin me take cewa, Hafiz ya zame jikinsa.
Ni zanje na kwanta.
Wai dole ne sai ka kwana a ɗakinta.? ai nan ne ɗakinka.
To bari nayi mata magana tazo nan mu kwanta.
Allah ya kyauta ba zanga wannan ranar ba, dan can ne inda ya dace da ita, bata da hurumi a nan.
Hmmm Laila kenan.
Cewar hafiz Yana gyaɗa kai, daga bisani ta cigaba da aika masa saƙo, tun yana nuna a'a har sai da ya bada kai bori ya hau.