14
*BAYAN AURE*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Page 14.
Sarac Stars R Pen...✍️
Sai wajen ƙarfe goma da rabi Hafiz ya shigo ɗakin Hamida ita kuma tana jin sallamarsa ta tashi ta zauna dan tun ɗazu bacci yaƙi ɗaukarta, saboda damuwar data uzzurawa kanta na fushin da Hafiz yake yi mata, da ɗan murmushi ya dubeta ya zauna a gefen gado.
Baki yi bacci ba.?
Ta rausayar da kai tana gyaɗa shi a hankali.
Banyi ba na kasa yi saboda kana fushi dani.
Ba fushi nake dake ba kawai ina nusar dake abubuwa ne dan kar nan gaba Laila ta goranta miki akai, sannan a matsayina na maigida kin ji na shigo amma kika kasa fitowa falo ki yi mini tarba mai kyau, shiyasa na haura sama.
To kayi haƙuri bazan sake ba, kuma ɗazun ka dawo ina sallah ne saboda nayi lattin gama girki shiyasa.
Ayya sannu da ƙoƙari gaskiya Hamida kin iya girki ina yaba miki, dan a yanzu bana sha'awar cin girkin kowa in ba naki ba har kin fi Laila iyawa.
Nagode.
Hamida ta faɗa cikin sunne kai ƙasa tana murmushin jin daɗi, sai ya kwanta rigingine yana ƙare mata kallo dan saƙon daya ke son isarwa yaga amsarsa a fuskarta, sai ya ce yana yin filo da tafin hannunsa duka biyun.
Nifa ina ganin girkin ki kawai zan riƙa ci a gidan nan, dama kinga Laila ba zama take yi ba kullun tana fita sai weekend.
Ni dai kar ka jawo taji haushi na, taya zan riƙa yi maka girki a ranar kwananta.?
Baki San Laila ba ne ai ita ba ruwan ta, in dai akan maganar girki ne kuiya gareta, kuma tana da sauƙin kai.
Ya faɗa yana kai dubansa gareta sai suka haɗa ido ta sunne kai cikin jin kunya tana murmushi.
Ai anty tana da kirki ko rannan tace zata biya mini online class na girke-girke, tana so na iya girkin zamani wai.
To kin gani ba tada matsala, tasan kuma in kin koya zaki riƙa yi mana ko da a ranar girkinta ne, zan taya ki godiya dan nasan ni teke gyarawa hanya.
Hafiz ya faɗa yana murmushi, itama murmushin tayi zuciyata fes ganin sun shirya da Hafiz, sannan ita ba tada matsala in dai Laila zata yarda ta riƙa yi wa Hafiz girki a ranar kwananta to zata yi masa dan babban burinta ta faranta masa ta gyara hanyar samun aljannarta, haka suka yi shuru na wani lokaci kafin daga bisani Hamida ta tuna da batun mai gadi daya hana 'yan uwanta shigowa gidan, sai ta muskuta ta shiga faɗa masa maganar, ta ƙara da cewa.
Ban san meyasa ya hanasu shigowa ba.
Nine na faɗa masa karya bar kowa ya shigo dan kar su takura miki, ina so ki samu hutu, kwakwalwarki ta huta da haniyar da kika sha na bikinmu, idan kika kai wata guda to sai kowa ma yazo, lokacin kin ƙara kyau da cikar ɗaki yadda zasu san na iya kiwo.
Hamida ta ɗan waro ido tana juyasu irin zancensa yayi mata daɗi, sai ta rufe fuska da tafin hannu tana murmushi tare da cewa.
To ya zanyi dasu idan sun kirani.
Kice mun yi tafiya zuwa Abuja, idan mun dawo zaki sanar da su.
Tace masa to cike da gamsuwar abunda ya faɗa sam bata hango aibun haka ba, domin ta bashi yarda ɗari bisa ɗari ba zai cutar da ita ba, sai ta kwanta ta gyara kwanciya tana ce masa sai da safe yace.
Haba gimbiya ki bari muyi tare mana, yauwa kisa alerm a wayarki ƙarfe biyar kafin asuba saboda ki samu damar haɗa mana abincin safe da na su Afrah, kinga kwana biyu kina makara. Goben zaki dafa musu macaroni da miya, ni kuma ki dafa min farar taliya sai nayi amfani da miyarsu, ki haɗa min komai a basket ɗin dana nuna miki rannan, kin san na faɗa miki ina tafiya da abinci office, sannan ki dafa ruwan tea zamu karya da bread sai ki soya kwai.
Tace masa to kafin ta ɗauko wayarta ta saka alerm ɗin ƙarfe biyar duk da ana yin sallar asubahi ƙarfe biyar da rabi ne. A ranar bai nimeta ba suka kwanta bacci.
.....
A tsakanin mako guda da aurensu Hamida ta aikatu sosai har ta fara sabawa, girkin safe dana dare babu wanda tayi fashin yin su kuma sai wanda suke so take dafawa. Yau lahadi tun da garin Allah ya waye take jinta sakayau kamar an sauke mata nauyi domin ta fita daga girki Laila ta amsa, duk da har yanzu Hafiz bai zaunar dasu ya yi rabon kwana ba amma tasan yadda tsarin yake, amarya budurwa zata shi sati ɗaya sannan rabon kwana wasu na yanke kwana ɗai-ɗai ko bibbiyu, to tun jiya Laila ta amsa girki, yau tasan ita ce zata yi girkin, shiyasa take ganin zata huta tare da tunanin zata ɗanɗana girkin Laila taji ko ta iya, duk da Hafiz yasha faɗa mata bata iya girki sosai ba, kuma jiya Hamida ce tayi girki duk da Laila ce da miji amma Hafiz yace ita zata girka, sai ta sauke ajiyar zuciya ta kunna data tana chart tare da duba group ɗinsu na girki ko an fara karatu dan har lokacin ba a fara ba saboda mutane suna ta biyan kuɗi, sai ga Hafiz ya shigo ɗakin da sallama ta amsa tare da aje wayar tana dubansa ta gaishe shi, ya amsa fuska a dan haɗe yana cewa.
Hamida tashi za kiyi ki haɗa mana breakfast dan Laila ba tada niyyar ɗaurawa, kuma kin ga su Afrah zasu tafi hadda.
Amma ai yau ba ni ce da girki ba.
Na sani, kuma umarni na baki, idan kema ba zaki girka ba sai na fita waje na siya, kunga sai kusha zagi wajen mutane, ace ina da mata biyu kun kasa kulawa da cikina.
Ni anty nake ji karta ce na shiga lokacinta.
Ta faɗa fuska a dame kamar zata yi kuka, Hafiz ya saki murmushi yana cewa.
Ni ne na baki umarni, kuma Laila ba tada matsala.
Ya ƙare maganar yana tsura mata ido, Hamida ta sauke numfashi ta sauko daga gadon ta yi hanyar fita tana cewa.
To me zan girka.?
Hafiz ya bita a baya yana jera mata abubuwan da zata yi, har suka isa kitchen ɗin ta fara aiki yana tsaye yana tayata da wasu abubuwan. Bayan ta gama tana shirin ta koma ɗaki ta yi wanka sai ga Laila ta fito tana kwas-kwas da takalmi wanda yasa Hamida ta tsaya tana dubanta, sai taga tasha kwalilliya kamar zata gasar kyau, Hamida tace a ranta.
Sai aukin kwalliya ba a iya riƙe miji ba.
A fili kuma sai ta ce cikin sakin murmushi bayan Laila ta sauko.
Barka da Safiya anty Laila.
Yauwa Hamida, kin ga ni fita zanyi dan Allah ki gyara gidan, sannan anjima da rana ki yi mini girkin mutum uku ina da baƙi zasu zo, dan bazan jima ba zan dawo.
To sai kin dawo.
Me kike so in kawo miki tsaraba.?
Laila ta faɗa tana dafa kafadar Hamida tare da jan numfashinta jin warin zufar data ji a jikinta, ita kuma ta saki murmushi tana cewa.
Duk abunda kika ga ya dace dani.
Tace to kafin ta saki ƙafaɗarta ta wuce, Hafiz yabi bayanta suka fita yayi mata rakiya zuwa mota, sai da suka ɗanyi magana kafin ya dawo ciki, ita kuma Hamida ta shiga ɗaki dan tayi wanka, ta shiga mamakin irin yadda Laila take nuna ko-in-kula da girkin data yi a ranar kwananta, sai take ganin wautarta na ƙin kula da miji, sannan ita kamar ba zata jure aikin gidan ba kullun, ace tun da tazo bata huta ba daga gyaran gida sai ɗaura-sauke a kitchen, haka ta shiga wanka tana wannan tunanin daga bisani data fito ta shirya cikin riga da wando 'yan kanti wanda basu kamata sosai ba, dan ta ɗaura niyyar itama zata koyi shiga irin na Laila koda ba zata birge Hafiz ba dan tasan in dai kwalliya ne duk wacce zata yi ba zata taɓa kaiwa kamar Laila ba, in dai gayu ne to ta bar mata kayanta, dan ta gama cinye duk wani makin dake zuciyar Hafiz, sai dai kuma itama zata daure ta samu gwaggaɓar makin a ɓangaren girki, tunda ko ba komai ta hakane zata samu nata matsayin a zuciyarsa. Bayan ta karya sai ta kwanta tana charting a waya dan tuni Hafiz ya fita da yaran zuwa makaranta sannan yace zai shiga cikin gari.
Wajen sha ɗaya da rabi na safe ta tashi dan bata samu yin baccin ba, sai ta shiga kitchen ta dafa fried rice da ɗan dama da tunanin in ya rage sai suci da dare, ta yi pepe chicken tare da soya kifi ta aje su a mazubi mai kyau sannan ta haɗa kosilo, bayan ta gama ta shiga goge kitchen ɗin, wanda a lokacin ta ji shigowa motar Laila, ba jimawa ta shigo falon dan ƙarar takalminta shi ne ya sanar da ita, ta wuce sama ba tare da ta nemeta ba, bata damu ba dan ta saba da haka. Tana tsaka ta wanke kayan data ɓata ta ji an buɗe gate an shigo, can kuma taji an kwaɗa sallama an shigo falon, da sauri Hamida ta saki aikinta ta fito sai ta ga Umman su Hafiz ce da Ƙannensa mata, ta ƙarasa da sauri tana murmushi tare da yi musu sannu da zuwa, ta miƙa hannu ta amsa yaron Suhaima da ta riƙoshi a hannu, bayan sun zauna Hamida ta aje yaron a carpet ta zauna a ƙasa ta gaishe da Umma, kafin suka gaisa da su Rashida duk fuskarsu ɗauke da murmushi, saukowar Laila ne ya ja hankalinsu ta ƙaraso da sauri ta rungume Rashida da take zaune bakinta kamar gonar auduga, ta saki Rashida ta kama Suhaima ta rungume kafin daga bisani ta saketa ta koma kujerar da umma ke zaune ta kama hannunta tana cewa.
Sannu da zuwa Umma kun sha rana. Ina wuni.
Lafiya lau 'yar Albarka.
Umma ta ambata baki a washe ba kamar yadda ta amsawa Hamida da murmushi ba, sannan ta gaisa da su Rashida suka fara hira sun manta da Hamida tana wajen, mamaki da al'ajabi ya kashe Hamida a zaune a wajen, da tunanin dama sune baƙin da zasu so amma Laila ta kasa faɗa mata waɗanda zasu zo, ta tattabar zuwan da suka yi ƙila nata ne ita da take amarya tunda umma ba zo taga ɗakinta ba, amma ta saka ta yi musu girki ta kasa sanar mata, sannan gashi yanzu sun nuna tamkar bata wajen babu wanda ya sake kula ta, bata zaci haka a gurinsu ba duba da irin tarba da suka yi mata a ranar data kwana a gidansu, tayi zurfi a tunani ta ji Laila tana cewa.
Haba Hamida ki kawo musu abu mai sanyi su sha kina zaune. Allah yasa ma kin gama girkin.
Na gama tun ɗazu. Bari na kai musu dinning.
A'a ki kawo mana nan bamu saba da cin abinci irin na 'yan gayu ba.
Cewar Suhaima tana dariya, sai itama Hamida ta hangame baki uwa shashasha ta miƙe ta wuce kitchen ba tare da tace komai ba. A cikin 'yan mintuna ta jera musu komai a bisa carpet kafin ta koma kitchen ta ƙarasa aikinta ta ɗauko abincinta data zuba ta fito ta wuce su tamkar basu san anyi ruwan halintarta ba, gabaɗaya sun shagala da hirar da Laila take yi musu akan shagon da zata buɗe, Hamida ta isa ɗaki ta dire abincin data kawo ta riƙe haba tana mamaki.
Bariki iyawa wanda bai iya ba ta kwaɓe masa.
Tace a cikin ranta dan sun mayar da ita baƙuwa, ko da yake ita baƙuwa ce dama kuma duk matar da aka auro ta biyu ba kasafai dangin miji suke karɓarta ba suna wajen uwargida, haka ma mutanen unguwa babu wanda zai yi mu'amala da ita saboda suna tare da uwargida, sai ta zama babu mai yin kyakkyawar hulɗa da ita dan kar ran uwargida ya ɓaci, ta zama kamar mujiya in ta shiga sha'anin dangin miji babu mai kula ta ta riƙa raɓe-raɓe, wannan shi ne abunda dake faruwa a rayuwar wasu mutanen, sun mayar da matar da aka auro ta biyu tamkar mai zunubi babu mai kusantar inda take dan kar suyi mu'amala da ita ace sunyi munafurci, su haɗe kai suna muzguna wa amarya dan kawai ta auri mijin wata, bayan wannan ƙaddararta ce haka Allah ya tsara a rayuwarta, itama zata so ta kasance ita ce ta fari, amma kuma Allah ya ƙaddara sai ta aure mijin wata, sai hakan ya zaba babban laifi a gurin wasu marasa tsoron Allah, a zageta, a yi mata cin fuska, a sakar mata habaici dan kawai tazo a ta biyu, wata ma a shiga yi mata asiri dan kar ta zauna sai ta bar gidan, a wajen miji ne kawai zata ji sauƙi, 'ya'yan miji su zama tamkar sune kishiyoyinta saboda irin mummunar huɗubar da maharfiyarsu ta ɗaurasu akai, ko ƙannen uwargida su zama tamkar dasu amarya take kishi, idan sun zo su riƙa yi mata gani-gani cikin raini, wasu ma sai sun yada mata magana dan kawai ta auri mijin yayarsu, kansu kawai suka sani a hana mace kwanciyar hankili, a matsa mata lamba babu dama ta sake da miji a ɗaki suyi hira sai uwargida tasan yadda tayi ta katse musu wannan hirar, ta riƙa treating miji tamkar ita ce ta halicce shi ko ta haife shi, sai abunda take so zai gudanar a gidansa, kuma a ganin ta dole amarya tayi mata biyayya, irin wannan tunanin wasu matan suke so, kuma masu wannan halin basa tunanin suna da 'ya'ya mata ko ƙanne mata ko dangi mata wanda suma ƙila ƙaddarar aurensu zasu je ne a matsayin mata ta biyu. Wasu kuma dangin mijin zasu karɓi duk matar da ɗan uwansu ya auro babu ruwansu, kyawun halin mace shi ne zai sa su yi mu'amala da ita, ta zama 'yar gida har kowa ya saba da ita.
Tunanin Laila shi ne irin tunanin wasu matan masu son kansu, ta mayar da miji tamkar ita ce ta haife shi, kuma kamar yadda take ganin ta isa ta juya Hafiz to haka take fatan Hamida ta bita. Sai Hamida ta sauke numfashi ta koma ta zauna taci abinci kafin ta gabatar da Sallah, bayan ta idar tana zaune bisa dadduma har lokacin tana jin hirar su Umma, ta shafa addu'a ta kwanta a gado tare da ɗauko wayarta tana duba hotunan bikinsu, bata jin zata koma falon dan alamu sun nuna ba gurinta suka zo ba, shiyasa ma Laila bata sanar da ita sune zasu zo ba dan ba tada wannan matsayin ko ƙimar.
*Duk matar data zo a ta biyu na jinjina mata, domin nasan wasu suna fuskantar matsi daga Uwargida da mutane, kamar yadda wasu uwargidan suke fuskanta matsi daga amare, dama ko'ina akwai ɓata-gari akwai na kirki. Na tabbatar akwai amaren da suke fuskantar ƙalubale dan kawai sun auri mijin wata. To kar ku damu wannan ƙaddararku ne kuma tsarin Allah ne ya fiku sanin abinda ya dace daku, ke dai riƙe Allah ki kuma bar lamarin a hannunsa tabbas zai miki maganin komai.*