15
*BAYAN AURE*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Page 15.
Sarac Stars R Pen...✍️
Hamida tana kwance taji ana sallama a ƙofar ɗakinta, sai ta amsa cikin buɗe murya sannan ta sauko ta buɗe ƙofar jin muryar Umma, ta saki murmushi sa'ilin da suka haɗa ido, sai ta koma ciki Umma da su Rashida suka ni bayanta, Suhaima ta jawowa Umma kujarar dressing mirror ta zauna, su suka tsaya a tsaye suna ƙarewa ɗakin kallo, Hamida da ke zaune gefen gado ta ƙara gaishe da Umma cikin sunne kai, ta amsa tana cewa.
Ya baƙunta.? To Hamida zaman aure gabaɗayansa haƙuri ne, yi nayi bari na bari, sannan dan Allah ki kula da abincin Hafiz dan Laila tana da kuiyar girki, kin ga sai ki kama mijinki hannu bibbiyu kina yi masa duk abunda yake so. Sannan in kika kwantar da hankali kika bi Laila zaki ci arziki ne ki bar shi, ki riƙe yaransu tamkar naki, ki dinga gyara gidan dan kar a yi muku shaidar ƙazanta, sunyi masu aiki sun kai biyar amma basu dace bane. Sannan idan sunyi miki wani abu na ɓacin rai ki kira ki faɗa mini ni zan yi wa tufka hanci, ai kina da lambata ko.?
Eh ina da ita, kuma In Sha Allah zan yi aiki da abunda kika ce, nagode Allah ya saka da alheri.
Ameen, to bari muje muyi sallah dan zamu tafi da zarar mun kammala.
Cewar Umma, sai ta miƙe tayi hanyar fita suma su Suhaima suka bi bayanta dama basu zauna ba basu kuma ce komai ba, Hamida ta rakasu tana godiya, akan idonta suka haura sama wajen Laila, daga haka sai ta koma ɗaki ta zauna tana juya maganganun Umma dan gabaɗaya girman matar ya fara zubewa a idonta, tana nufin tunda ita Laila suna da kuɗi ba za a gaya mata ta kula da miji ba, sannan ma wai ta yi mata biyayya zata ci arziki, to dama ita arzikinta ya dame ta ne, aure ya kawota gidan kuma badan haka ba hanyar jirgi daban na mota daban, sai ta tuna da maganar mamansu daga ce tabi Laila taci arziki, sai ta saki tsaki tana cewa a fili.
Zan yi wa mijina biyayya amma ba Laila ba, nifa arzikinsu bai dame ni ba ni mijina kawai na sani.
Tayi kwofa kafin ta koma ta zauna ta ɗauki wayarta ta shiga facebook dan yanzu shi ne abokin hirarta. Bayan wasu mintuna taji alamun sun fito, sai ta miƙe ta saka hijab ɗin da tayi sallah ta fito, a lokacin ta ji umma tana cewa.
Mu ba zamu amsa komai ba, ke kullun ba kya gajiya, mun zo ganin ɗakin amarya ne dan haka ki barshi.
Hamida taja ta tsaya tana kallonsu, ga Laila riƙe da ƙatuwar farar Leda da alama kamar kaya ne a ciki, Rashida ta zunguri Suhaima suka kalli juna sai ta yi wuf ta amshe ledan tana cewa.
Umma in baki so to mu muna so, mun gode Anty Laila Allah ya saka da alkhairi ya ƙara buɗi.
Ta ƙare maganar tana buɗe ledar, sai taga leshi ne guda ɗaya mai tsada da amtamfofi biyu sai rafar kuɗi 'yan ɗari biyar guda ɗaya na dubu talatin, ta waro ido tana cigaba da cewa.
Anty Laila wannan hidima haka, anya bai yi yawa ba.? Anty Rashida kalla ki gani leshi da atamfa biyu har da kuɗi.
Bai yi ba, Haba yaushe rabon Umma tazo gidan nan, farin cikin zuwanta yasa zan yi komai.
Cewar Laila da ta ƙare maganar cikin lallausar murmushi, Umma ta girgiza kai tana riƙe haɓa.
Allah yayi miki albarka 'yar nan, sannu da ƙoƙari Allah ya ƙara arziki.
Duk suka amsa da Amin, sai a lokacin Hamida ta ƙarasa gurinsu tana murmushi tace.
An gode Anty Laila Allah ya ƙara arziki ya ƙara buɗi. Umma a kashe lafiya, Allah ya sauke ku gida lafiya.
Ta ƙare cikin dariya tana yage baki, haka kawai tace bari tayi godiyar dan bata san me zata yi ba in ba shi ba tunda ta kula Laila tana son haka, sannan ma ita ba tada abunda zata basu dole ne itama ta bi yarima asha kiɗa, suka amsa da amin sannan suka rankaya har waje suka yi musu rakiya zuwa gate, bayan sun fita sai suka jero Laila tana cewa.
Suna da kirki sosai ba suda matsala, shiyasa ban san matsalar dangin miji ba.
Gaskiya kam nima na ga haka dan ko ranar dana kwana a gidansu sun karrama ni.
Ta faɗa tana murmushi, a zuciyar ta kuma tace.
Dole kice ba kida matsala da su duk kuwa da matsalolin da kike da shi a gidan aurenki, saboda kina lasa musu Zuma a baki suna tanɗewa, kwaɗayayyu.
Bayan sun shiga ciki Laila ta wuce Cushing ta zauna tana danna waya, ita kuma Hamida ta wuce zuwa ɗaki amma sai ta tsinkayi Laila tana cewa.
Hamida wannan kayan abincin ya kamata a kwashe su.
Kamar zata ce mata ke aikin me kike yi da baza ki kwashe ba amma sai ta fasa ta juyo, ta kwashe kayan abincin da suka ci ta kai kitchen ta dawo ta share gurin kafin ta koma ɗaki dan ta samu bacci, duk da ta ɗaura niyyar yau ba zata girka komai ba wannan sauran fried rice ɗin zasu ci zai ishe su, dama da yawa tayi dan haka ba ruwanta da wani girki duk da ba itace da miji ba amma suna niman ɗaura mata yin girki dole, ita ko gaskiya kamar ba zata jure ba dan aikin gyaran gidan kaɗai ma babba ne, da zasu ɗauki 'yar aiki da ta huta amma ga dukkan alamu babu niyyar yin haka.
*******
Hafsa.
A ranar bata samu yin bacci ba dan tsakiyar dare ta shi yin Nafila, bayan ta idar ta zauna ta yi karatun Al-Qur'ani wanda yasa zuciyarta tayi sanyi ta shiga kuka ba tare da sauti ba, a gaskiya ta gaji! ta gaji da halin Saminu, tana jin ita auren ma ya fice mata a cikin rai, sai dai kuma auren ya zame mata kamar ƙarfen ƙafa dan ba ta isa ta yakiceshi ba duba da irin yadda iyayenta suke kaffa-kaffa da auren basa so ya mutu, balle tayi tunanin idan ta kashe auren zasu bata wajen zama, a yanzu Allah kaɗai ne take kai kukanta dan ba tada madafa sai shi, ta bar masa zaɓi domin shi ne zai kawo mata mafita cikin sauƙi, ta jima a zaune a gurin kafin ta je ta kwanta ta rufe ido da addu'ar Allah yasa bacci ya ɗauketa dan idanunta sun soye ko baccin bata ji. Har asubahi tayi kafin ta gabatar da Sallah a daddafe dan kanta yayi mata nauyi, kuma cikin ikon Allah tana kwanciya ta samu bacci ya ɗauketa.
Bangaren Saminu kuma wajen hajiyar da suke sheƙe ayarsu yaje ya kwana, amma ya ƙuduri aniyar sai ya ja Hafsa a ƙasa ta yadda ba zata ƙara gigin yi masa wani wulaƙanci ba. Da safe ya yi wanka ya mayar da kayansa na jiya ya fito falo yana gyara agogon hannunsa.
Ba zaka tsaya ka karya ba.?
Cewar Hajiya, Saminu ya yatsine fuska.
Bana jin daɗin bakina zuwa anjima zan nemi abunda zan ci.
To shi kenan, amma ya batun aurenmu.? har yanzu baka ce komai ba.
Akwai abunda nake so na kammala In Sha Allah.
Ya kare maganar yana yin gaba, sai ta taɓe baki tana cewa.
Allah ya kaimu.
Yace amin kafin ya fita tare da alwashin daga ranar ba zata sake ganinsa ba, gabaɗaya ma ya rasa me ya saka shi hulɗa da wannan tsohuwar matar, jiya ba ƙaramin gajiyar da shi tayi ba, kuma yaji wani wari-wari a jikinta wanda ya rasa ko na miye, shiyasa ma ya wayi garin ransa a dagule ba farinciki. Ya fito ya shiga motarsa ya wuce can kasuwar gari shagon Isma'il yayan Hafsa, yayi sa'a ya same shi, nan ya zauna suka gaisa kafin ya shiga koro masa ƙarya da faskiyar abunda ya faru tsakaninsa da Hafsa, akan ta rufe masa gida dan kawai zai mayar da aurensa da tsohuwar matarsa Zinatu, kumq ta saka Bilal yayi masa rashin kunya, Isma'il dai ya ji shi ne amma ya tabbatar Hafsa ba zata yi haka ba, amma sai ya bishi da to ya bashi haƙuri da alƙawarin zai je ya samu Hafsah, nan yayi masa godiya suka yi sallama ya tafi, Isma'il ya cika da takaicin Saminu tare da jin danasanin aura masa Hafsa da suka yi, tabbas da ana kwankwasa hali kafin aure to da sai sunyi wa Saminu kafin su bashi aurenta, wanda ya tabbatar ba zasu taɓa aura mata shi ba dan bai cancanci zama miji a gareta ba, gashi girma ya kama shi amma ya aje girman a gefe sai zuba wauta da rashin hankali yake yi, da alamun yana da ƙaramin ilimin addini, in kuma yana da shi to baya amfani da shi.
Saminu su Asalin mutanen Zaria ne daga garin Lere, amma mazauna cikin garin Kaduna domin mahaifinsu Abdullahi anan Kaduna ya tashi har yayi auren farko dana biyu, iyayensa duk sun rasu sun bar musu gado wanda a sanadin haka ne ya samu gidan kansa anan Kawo, 'ya'yansa Tara, uwar gida Safare tana da yara shida biyu maza huɗu mata, gabaɗaya duk sun yi aure. Sai Murnajatu tana da 'ya'ya uku ɗaya na miji shi ne babba Saminu sannan Ƙannensa mata biyu Fatima tana aure a Lere can dangin babansu sai Hauwa da take aure a Rigasa. Dai-dai gwargwado iyayensu sun basu tarbiyya, duk da Saminu yana basu wahala, shi mutum ne da tun farko baya son a more shi saboda babu irin sana'ar da basu saka shi ba amma yaƙi mayar da hankali ya watsar, sannan ma karatu yaƙi yi da kyar yayi saukar Al-Qur'ani na allo shima dai cikin shiririta, boko kuwa ko secondary bai gama ba daga nan ya fara bin babansu kasuwa, to bayan rasuwar baban ne ya fara yin dillacin gida yana bin ogansa, a haka ya riƙa faɗi tashi yana ciyar dasu Hafsa tare da Ummansu. Dama tun yana saurayi yana da kule-kulen 'yan mata, ko Hafsah ma dan yana mugun sonta ne har ya nace sai da ya aureta, to bayan aurensu yayi kamar ya bari amma daga bisani ya koma ruwa ya fara kula 'yan mata yana rage dare, tun Hafsa bata kula ba har ta fara fahimtar ya sauya, sai dare yayi sosai yake dawowa, wani lokacin kuma in ya shigo da wuri zai tsaya a ƙofar gida yasha waya da budurwa. Akwai wani hali da Ummansu ta ɗaurasu akai na duk abunda ya same su sai tace hannu aka saka musu, kuma tana zargin kishiyarta ce ke yi musu, shiyasa ko bayan rasuwar Babansu da aka raba gado kowa ya kama gabansa basa zumunci sosai sai in sha'ani ya kama suke haɗuwar dole, kuma duk abunda Saminu yake yi umma ta ɗaura alhakin hakan akan Safare ne ta saka masa hannu shiyasa bayi da natsuwa, hakan yasa kullun cikin niman masa maganin tsari take yi tana bashi, shi kuma da wannan damar yake tsula tsiyarsa son ransa yana ƙara ɓatar da tunanin mahaifiyarsa.
Bayan shekaru sun ja Umma da kanta ta fahimci Saminu halinsa ne babu wani asiri, shiyasa yanzu take tsayawa tsayin daka ta yi masa faɗa idan Hafsa ta kai mata ƙararsa, kuma zuwa yanzu ma ba wani jin maganar ta yake yi ba saboda ta tsufa ga lalurar hawan jini da take fama dashi, shiyasa wani abun ko yayi wa Hafsa bata kai ƙararsa dan karta riƙa tayarwa Umma da hankali. Ƙannensa kuwa su nasu ido dan basu isa suyi masa magana ba, kuma da yake yana kyautata musu shiyasa bakinsu shuru sai dai su bawa Hafsa haƙuri dan suna zumunci sosai.
*****
Cigaban labari.
Yaya Isma'il nan take ya kira Hafsah, wanda kiran ne ya tashe ta a bacci saboda yaran sun tafi makaranta, sune suka haɗa abun karyawa suka shirya suka tafi makaranta, hatta Bilal ya tafi can gidansu wajen Aliyu zasu tafi tare ya taya shi yin register, ita kaɗai ce a gidan shiyasa ta rufe. Ta tashi ta zauna kafin ta ɗauko wayar dake chargy ta duba mai kira, kafin ta kira shi ma ya sake kira, sai ta ɗauka suka gaisa kafin ya tambayeta meke faruwa a gidanta, dan ɗazun Saminu ya kawo masa ƙararta, sai ta yi murmushin takaici kafin ta koro masa duk abunda ya faru, yayi salati yace.
Tund ya kwashe abincinsa zan aiko miki da abinci yanzu, kuma dan Allah karki ƙara rufe masa gida dan baki da ikon yin haka, inda wani ne ma wlh sai kiji ya yi saki kuma mu shi ne bama so. Kuma In Sha Allah ba zaki kwana da yunwa ba tunda kina da mu, Hafsa ki ƙara haƙuri kilallaɓa da shi a haka, wlh wata rana sai labari komai zai wuce.
Shi kenan yaya nagode Allah ya saka da alkhairi.
Yauwa koda ya dawo karki kula shi in yana faɗa, ki tabbatar kuma kin bashi haƙuri.
To tace masa kafin suka yi sallama tana maimaita kamar haƙuri a cikin ranta.
Hakuri.! Hmmm taya ma zan bashi haƙuri bayan nine ya zalunta, idan nayi haka ma tamkar na ƙara buɗe masa ƙofar wulaƙanci ne, Allah ya kyauta.
Ta ambata a fili ranta a ɓace, su danginta sam bata ganin wannan uƙubar da take sha, kawai su ta zauna kar ta bari ya saketa, wannan tunanin yana ɗaya daga cikin abubuwan da zai kai wasu matan wuta, domin kuwa tun mace tana haƙuri da mugun halin miji tana yi masa biyayya tare da bin umarnin iyaye da suke cewa ta zauna karta bari ya saketa, saboda suna yi mata tsoron zawarci, to za a kawo gaɓar da zuciyar mace zata ƙeƙeshe ta bushe ta ji ba zata iya cigaba da yi masa wannan biyayyar ba, zaman nasu ya koma na ƙeƙe da ƙeƙe, ba ragi ba ragowa, da yayi mata zata fara tunanin yadda zata rama dan zuciyar ta tayi sanyi, zata koma babu yafiya sai ɗaukar fansa, zaman ya koma na doya da manja babu biyayyar aure sai zaman 'ya'yanta da take yi, madadin ta riƙa samun lada sai samun zunubi, 'ya'ya su tashi da tsanar mahaifinsu saboda gasa mahaifiyarsu da yake yi, su zama tamkar abokan gaba basa ganin girmansa. A lokacin da shekaru ya ja girma ya kamashi yana buƙatar taimakon 'ya'yansa amma ba zai taɓa samu ba, idan an samu uwa mai ƙaramin tunanin ba zata kwabawa yaran ba, haka zata riƙa izasu suna wulaƙanta ubansu.
Irin wannan gabar Hafsa ta samu kanta a ciki na babu yafiya a tsakaninta da Saminu, a yanzu ba zata zuba ido yayi mata abu ba ba tare da ta yi yunƙurin ramawa ba, gashi yanzu ya kwashe mata abinci ita kuma ta rufe masa gida dan ta rama, ga Bilal ya fara saka musu baki a cikin faɗarsu saboda sun saba yi a gabansu, sannan a hankali ƙiyayyar ubansu ya ɗarsu a zuciyarsa wanda idan ba a yi wasa ba haka zai riƙa sakawa ƙannensa wannan alaƙidar na ƙiyayyar ubansu har su ɗauka, duk da Hafsa a wannan fanni tana ƙoƙarin tarbiyyar yaran amma yau da gobe ƙaryata boka.
*Dan Allah iyaye idan kuna faɗa da juna to ya tsaya a tsakaninku babu ruwan 'ya'ya da faɗarku dan lokacin da zaku shirya ba zasu sani ba, domin yawan yin faɗa a gabansu yana gurɓata tunaninsu, sannan Uwa ki daina hirar mahafainsu da yaranki kina basu labarin abunda yayi miki na ɓacin rai, ke kin faɗa musu dan su taya ki jimami amma kuma wani ƙullin kike zarge musu a zuciya da zasu ƙullaci ubansu wanda nan gaba sai kizo kina kuka da su, ko su kasa samun ladan ubansu a lokacin da yake buƙatar taimakonsu. Allah yasa mu dace.*