BAYAN AURE

16

by @rahmakabir13

*BAYAN AURE*

Na

©®Rahma Kabir MrsMG.

Page 16.

Sarac Stars R Pen...✍️

Wajen ƙarfe sha biyu yaya Isma'il ya aiko da abinci gidan Hafsa da motar shagonsa da suke delivery, sha biyu da rabi suka ƙaraso suka buga mata gate tazo ta buɗe, kafin suka gaisa suka sanar da ita saƙon da suka kawo, tayi musu godiya sannan ta basu dama suka shigar mata da abinci cikin store ɗinsu, babban buhun shinkafa ne da taliya katon da makaroni sai galam ɗin manja da mangyaɗa ɗai-ɗai mai cin kwalba uku-uku, sai parket ɗin Maggi da gishiri guda bibbiyu, sai suka wuce tana ƙara yi musu godiya, bayan ta rufe gate ta dawo ta duba kayan tana murmushin farin ciki, ɗan uwa mai daɗi, ita dai tayi dace da 'yan uwa masu kirki da tausayi, ban da naka naka ke waye zai yi mata wannan gatan, sai ta shiga godewa Allah tana ƙara yin addu'a akan Allah ya cigaba da ƙarfafa zumuncinsu. Sai ta buɗe taliya ta ɗauki ɗaya ta shiga haɗa musu abincin rana saboda suna da sauran kayan miya. 

Zuwa dare yaran duk sun yi bacci tana zaune a Cushing ta kishingiɗa taji tsayuwar motar Saminu, bata motsa ba balle ta tashi dan tasan gate ɗin a buɗe yake, tana ji ya shigo gidan har zuwa ƙofar falo ya buɗe ya shigo da sallama, ta amsa a iya laɓbanta bata motsa daga inda take ba, shi kuma ya zuba kunne yaji ko zata yi masa sannu da zuwa amma sai ya ji shuru kamar bata ganshi ba, har ya wuce ta sai ya kasa haƙuri ya dawo ya tsaya akanta. 

Narantse da Allah Hafsa baki isa kice zaki yi yadda kike so a gidan nan ba, ni ne na ke aurenki ba ke ce ke aure na ba, kuma idan kika ƙara rufe mini ƙofa ki tabbatar da sai igiyar aurenki yayi rawa, mutumiyar banza ana ganinki kamar ta Allah amma baki da zuciya mai kyau. 

Ya ƙare maganar cikin nuna ta da yatsa, Hafsa ko gezau bata yi ba balle ta tanka masa, sai yayi kwafa ya wuce ita kuma ta miƙe ta shige ɗakinta ta shiga ta rufe da key dan ba tada lokacinsa, dama tuni ta saka yaran sun siyo mata sabon kwaɗo ta garƙama a ƙofar kitchen ɗin dan kar ma ya nima sake kwashe mata kayan abinci, duk da ba shi ya kawo ba amma tasan halinsa ba yi da ta ido sai ya kwashe su dan ya ƙuntata mata, saboda sam baya son ganinta a farin ciki sai ƙunci. Ɓangaren Saminu bayan ya rage kayan jikinsa sai ya zura Jallabiya ya fito dan ya yi mata magana ta sirka masa ruwan wanka, amma sai ya ga bata falon sai ya wuce ƙofar ɗakinta ya murɗa zai shiga sai yaji a rufe, ya shiga kwankwasawa yana kiran sunanta amma sai ta yi masa banza, ya girgiza kai yana cizon leɓensa ransa yana ƙara zafi, sai ya juya ya fita tsakar gida zuwa kitchen sai ya ganshi a rufe da kwaɗo, ya dafa bango yana jijjiga kai. 

Lallai yarinyar nan ta raina ni, ni da gidana amma zata iyakance min yanda nake son yi a gidan. Zanyi matukar ɗaukar mataki akan ki. 

Ya ƙare maganar ransa a ɓace kafin ya juya zuwa cikin falo ya zauna a Cushing yana mai tallafe kucinsa da duka hannu biyun, sosai ya jima a wannan yanayin kafin daga bisani ya tashi ya koma ɗankinsa ya kwana ya ɗaukar waya ya kira Zinatu suka kwashe lokaci suna soyewa, sai da dare ya raba sosai kafin suka yi sallama ya kashe wayar ya kwanta babu addu'a ba komai. Da gari ya waye yara sune suka yi abin karyawa kafin suka shirya kansu suka tafi makaranta, ita kuma Hafsa ta fito ta shiga gyara gidan, da ta gama shara ta haɗa wanke-wanke ta soma yi, sai ga Saminu ya fito ya shiga kitchen da bokiti, Hafsah bata bishi ba bata kuma tanka masa ba, ba jimawa ya fito riƙe da bokitin ya juye ruwan zafi dake cikin flakes, yaje yayi wanka ya fito ya shirya ya fesa turaren kafin ya fito tsakar gidan bai tanka mata ba ya fice abinsa. Bayan ta gama wanke-wanke tana cikin haɗa tea a kitshen taji ya dawo tare da masu aiki, cikin ƙanƙanin lokaci suka fitar da kayan cikin ɗakunan da bata cire su ba, suka fara aikinsu shi kuma yana faɗa musu yadda yake so suyi gyaran. Babu hijab a jikinta dan haka dole ta warware ɗankwalin atamfarta ta yafa a kai kafin ta ɗauko kayan breakfast ɗinta ta shiga falo ta karya. 

....
Haka zaman nasu ya cigaba da tafiya har tsawon mako guda basa yiwa juna magana, yara ma basa ganinsa dan lokacin da zasu tafi makaranta da safe bai fito ba haka ma in ya dawo da daddare sunyi bacci saboda sai wajen sha biyun dare yake shigowa, Hafsa kuma bata damu ba domin ta saba da irin wannan zaman zuwa yanzu ma tafi jin daɗin yadda baya shiga lamarin ta, harkar sana'arta take yi tare da kyautata ibadarta da kula da tarbiyyar Yaransu daya sakar mata, ba ruwansa da zancen sun ci ko sun sha tunda ya kwashe abincin, babu kuɗin cefane ko kuɗin break da biscuit na makarantar yara, rayuwarsa yake yi shi kaɗai ya ci mai daɗi a waje, dan a yanzu ma Zinatu yake bawa cefane ta girma masa abunda yake so, abincin da ya kwashe ya kai gidan ummansu akan ya samu buɗi shi ne ya siya mai yawa ya kawo, ta riƙa saka masa albarka da farin cikin buɗin da Saminu ya samu, bata san wainar da ake toyawa ba a gidansa, dan babu mai bata labari, dama sai Hafsa taje ta faɗa mata, ko yaran in sun je gaisheta Hafsa tana kwaɓarsu da surutun abunda ya shafi gidan, shiyasa basa faɗa mata komai. 

Kwana goma aka gama gyaran ɓangaren Zinatu da yake akwai kuɗi a ƙasa. A kuma washegari aka mayar da aurensu, wanda Zinatu tayi ƙaramin taro a gidan iyayenta, wajen ƙarfe sha biyu Saminu ya shigo gidan niƙi-niƙi da ƙatuwar Leda, ya aje a tsakar gidan ya kwalawa Hafsa kira, tayi mamakin jin muryarsa yana ambaton sunanta, sai ta miƙe daga kwancen da take ta fito tsakar gidan ta ɗaura idonta akansa da yake danne-danne a waya gashi yasha manyan kaya, kuma ta san ɗazun da zai fita ba sune a jikinsa ba, sai dai bata yi mamaki ba dan tasan halinsa hawainiya ne shi mai rikiɗa, ya bar abunda yake yi a waya ya dubeta yana cewa. 

Hafsa ga wannan ledan kayan abinci ne shinkafa loka uku, zaki dafa wa 'yan kawo kaya anjima, na manta ban faɗa miki ba an mayar da aurena da Zinatu dazun ƙarfe goman safe, kuma In Sha Allah gobe zata tare. 

To Allah ya sanya alkhairi yasa abokiyar zama ce. 

Hafsa tace ba tare da wata damuwa ba, ya juya zai fita yana cewa Amin da alama yana sauri dan sai kiransa ake yi, sai ta dakatar da shi tana cewa. 

Batun girki ni fita zanyi ba zan samu dafawa ba, zai fi ka kai musu su girka kayansu in zasu taho su zo da shi, In Sha Allah zan bar musu gate a buɗe. 

Da waji irin juyi Samuni ya juyo yana kallonta harta ƙarasa magana, ya ƙanƙance idonsa. 

In baki umarni kice ba zaki yi ba kai tsaye saboda kina baƙin ciki da aurena ko Hafsa, to wlh ki tabbatar da kinyi girkin nan in ba so kike ranki yayi mummunar ɓaci ba. 

Gaskiya Saminu bazan girka ba domin aure ne na biyu kuka yi, kuma in ka manta bari na tuna maka na farkon ma nice na girka musu abincin ka kai musu can gidan da kuka tare, sannan su ne suke da haƙƙi a kanka da zaka basu a abinci ko.? mu kuma ko oho, yanzu kusan sati biyu kenan daka kwashe kayan abincin gidan nan sannan babu cefane, kuma baka taɓa tambayar mun ci ko mun sha ba, saboda na zama banza a gurinka shi ne zaka kawo abinci na girka maka dan ina tsoronka, to wlh ba zan girka ba dan babu abunda ya shafe ni da aurenka. 

Ta ƙare maganar cikin taɓe baki, Saminu ya matso cikin sauri ya kwashe ta da mari, bata bari ya sauke hannu ba ta kafta masa nata marin daya gigita lissafinsa, ta ja da baya tana hucci idanunta yana zubar da kwalla, Saminu ya dafe kunne yana ƙanƙance ido. 

Ni Hafsa.! ni kika mara saboda samun guri.?

Ai yanzu ba da bane Saminu kana yi mini zan maka, dan babu ragi babu ragowa a tsakaninmu. 

Ohhh haka kika ce.? to tunda wuyanki ya isa yanka mun kawo lokacin da zaki yi fito na fito dani, to kije gida na sake ki saki ɗaya, kuma karki bari na dawo na same ki a cikin gidana kin ji na faɗa miki, mara tarbiyya kawai. 

Yana gama faɗar haka ya juya ya fice a fusace kamar zai tashi sama, Hafsa kuma wani irin duka ƙirjinta yayi jin wai ya saketa, lamarin ya daketa ta yadda bata taɓa tsammanin zata ji haka ba, jikinta yayi sanyi ƙafafunta suka gaza ɗaukarta ta duƙa ta jawo ƙaramar kujera ta zauna tana mayar da numfashi, a yanzu babban fargabanta shi ne ya Iyayenta zasu ɗauki lamarin, dan tasan Saminu sai ya sanar dasu abunda ya faru sannan sai ya ƙara da abunda bai faru ba, marin da ta yi masa shi ne ya hargitsa komai, kuma idonta ne ya rufe ta gaza controlling zuciyarta har ta kai ga ramawa, tasan wannan marin da ta yi masa da shi zai kafa hujja, wanda idan iyayena suka ji ranta sai yayi mugun ɓaci, ba zasu taɓa duba nashi laifin ba sai nata, balle su da suke ƙoƙarin ta zauna a ɗakinta amma gashi tayi sanadin igiyar aurenta, a yanzu damuwarta bana sakin bane sai na iyayenta akan yadda zasu ɗauki lamarin. 

******
Hamida. 

Wajen ƙarfe biyar Hafiz ya kirata ya faɗa mata ta dafa musu couscous da miya sai ta haɗa da cosilo tare da fruit salad, Hamida ta tashi daga kwancen da take ga waya a kunnenta, ta ce masa ai yau su na da sauran abinci ba sai tayi girki ba, ta sanar da shi kalar girkin da kuma zuwansu Umma, Hafiz ya ja fasali yana cewa. 

Wannan abincin ki bawa maigadi da almajirai, na riga na faɗa miki abunda muke so. 

To amma ai bani ce da girki ba my heart, kaga Anty Laila sai ta yi muku ni zanci wannan ɗin na zubawa mai gadi, in ya rage ma zan ɗumama nayi amfani da shi da safe. 

Hamida ni zan ce ga abunda zaki min kice ke ba haka ba, ai nasan da Lailan amma nace ke ce zaki yi girki, amma tunda ban isa dake ba kiyi yadda kika ga dama. 

Sai ƙit ya kashe wayar bayan ya kai aya a maganarsa, Hamida ta sauke wayar tana turo baki ranta a ɓace. 

Wai me kuke so ku mayar dani ne.? Ko dama haka duk waɗanda suka auri me mata suke fuskanta, ko kuma ni ce dai nawa ƙaddarar tazo a haka. Haba tunda nazo gidan nan ban huta ba yau kaɗai ai sai a sarara mini. To wlh bazan girka ba tunda akwai abincin ba wai babu bane. 

Ta ƙare maganar tana dukan cinyarta tare da komawa ta kwanta zuciyarta a jagule. Tana jin lokacin da yaran suka dawo daga makaranta bata fito ba dan basa kulata sai gaisuwa kaɗai ke haɗasu, kuma bata tashi daga kwancen ba sai da aka kira sallar magariba kafin ta miƙe ta shiga bayi ta ɗauro alwala ta zo ta gabatar, ta cigaba da zama a dadduma sai da aka yi Isha'i ta gabatar sannan ta miƙe ta fito zuwa kitchen, sai kawai ta samu su Afrah suna shan cornflakes basu kulata ba ta wuce su, sai ta hango Laila tana kan dinning tana cin indomie, Hamida tace. 

Anty sannu da hutawa. 

Yauwa Hamida, yau kuma sai kika barmu da niman abunda zamu ci, ashe baki samu yin girki ba.? 

Hamida ta hangame baki saboda gubar mamakin data shayar da ita, sai tace cikin murmushin yaƙe. 

Au na zata wannan fried rice ɗin zai ishemu tunda akwai saura da yawa ga kuma sauran kifi da kazar.

Gaskiya bama sha'awarta sai couscous muke so, tunda Beb yace shi zai ci. 

To ai shikenan tunda kun samu abunda zaku ci, my heart in ya dawo yaci shinkafar. 

Tana gama faɗar haka ta wuce zuwa cikin kitchen, Laila ta bita da harara tana cewa a cikin ranta. 

Zaki ci ubanki yau bari Beb ya dawo. 

Sai ta cigaba da cin indomie ɗinta ba dan ranta yana so duk da taji kayan haɗi har da kaza a ciki. Hamida ta ɗumama abinci ta shaƙe plate da kifi da tsokar kaza ta fito riƙe da ruwa da drinks ta wuce ɗaki ta zauna a ƙasa dirshen ta mazgi abinci tana ci tana santi, a ranta tace. 

In ba almubazzaranci ba meye wannan shinkafar tayi da ba za a ci ba. 

Sai ta ja guntun tsaki ta cigaba da ci, bayan ta gama ta fito ta mayar da plate kitchen ta zubawa maigadi a kwanon da suka ware masa, ta fita ta kai masa dan bata isa ta aika yaran Laila ba, duba da irin kallon ƙasƙancin da suke yi mata, bayan ta dawo ta saka kayan bacci ta bi lafiyar gado. 

Wajen tara da rabi na dare bacci har ya ɗauketa taji sallamar Hafiz ya shigo fuskarsa a ɗaure, ta tashi ta zauna tana buga hamma ta yi masa sannu da zuwa, amma yaƙi amsawa yana ƙare mata kallo. 

Hamida dama ina wasa dake ne da zan saka ki yi abu amma ki ƙi yi, wlh ni da gidana baki isa ki nuna ban isa ba, ina miki kallon mai hankali ashe ke shashasha ce, to ki san da sani ba zan ɗauki wannan rainin ba, idan kuma kina sha'awar ki koma gidanku ne to ki cigaba da nuna ban isa ba, dama sai da aka gargaɗe ni akan auren 'yar talla nace naji na gani dan ke kina da tarbiyya, ashe zaki zo ki nuna min halin da ban san da shi ba. Ko da yake wani talakan bai iya samun guri ba, kuma kar kice zaki haɗa kanki da Laila ita daban ke daban, sannan ke da nake kyautata miki zaton zaki yi mini biyayya ashe ba haka bane, gashi kinsa Laila tayi mini dariya akan abunda kika aikata. Kin kyauta. 

Yana gama fadar haka ya juya ransa a dagule ya fita tare da banko mata ƙofa, Hamida idonta yayi taf da hawaye ta bi ƙofar da kallo jikinta babu inda baya rawa saboda tashin hankali, musamman yadda taga ya ɗauki lamarin da zafi, maganganunsa sunyi matukar ɓata mata rai sai dai kuma fushinsa yafi komai dagula mata lissafi.

Me yake nufi.? Daga yin aure ko wata guda banyi ba yake maganar zan koma gida akan ɗan wannan abun, bafa girki na bane. Ko da yake ai ya isa dani ne shiyasa yace nayi kuma ya nuna ina da matsayi akanta dan ita ce mai girki amma ya zaɓe ni, gashi yace Laila tayi masa dariya hakan yayi mata daɗi kenan saboda munyi faɗa. 

Tayi maganar a cikin ranta tare da cizon yatsarta manuniya, Sai duk taji jikinta ya mutu tare da jin bata kyauta masa ba, ya dace taje ta bashi haƙuri tun kafin Laila ta samu damar goranta mata ko ta bawa wasu labari, kuma yanzu ta tabbatar tana da matsayi a zuciyar Hafiz tunda ya zaɓi abincinta akan na Laila, kuma ga dukkan alamu akan abinci suke samun matsala da ita ƙila shiyasa ma ya ƙara aure. In ko haka ne dole zata jure cigaba da yin girki ko dan farin cikinsa.