17
*BAYAN AURE*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Page 17.
Last freepage.
Sarac Stars R Pen...✍️
Hamida sai taji kamar ta bishi saman ta bashi haƙuri, sai dai kuma bata so tayi magana a gaban Laila dan kar ya dizgata, sai ta bar komar zuwa safe tare da niyyar zata yi musu breakfast. Da wannan tunanin ta kwanta wanda sai da tayi da gaske kafin bacci ya ɗauketa saboda damuwar fushin da Hafiz yayi.
Tun kafin asubahi alerm ya tasheta, ta fito ta shiga kitchen ta fara aiki, a kunnenta aka kira sallar shiga masallaci har Hafiz ya fito cikin sauri ya fita, bata daina aikinta ba ta jira ya dawo saboda tana so ta yi masa magana. Lokacin daya dawo daga masallaci har zai haura sama Hamida ta fito cikin sauri ta buɗe murya cikin dakatar da shi.
Sannu da shigowa, ina kwana.?
Hafiz ya tsaya ya juyo ya kalleta ba tare da ya amsa ba, sai ta cigaba da cewa.
Dan Allah kayi haƙuri da abunda ya faru jiya, bazan sake ba In Sha Allah.
Hmmmm shi kenan.
Ya ambata tare da juyawa zai wuce.
Dan Allah kace ka yafe min kar Mala'ikun Allah su cigaba da tsine mini, wlh jiya da kyar ma nayi bacci saboda damuwa.
Hamida ta yi maganar a raunane kamar zata yi kuka, Hafiz ya sauke ajiyar zuciya domin anzo wajen da yake so, sai ya sauko ya dawo inda take tsaye.
Hamida kin tabbatar ba zan sake samun matsala da ke ba akan abunda ya faru jiya.?
In Sha Allah ba zan sake ba.
Ta faɗa tana gyaɗa masa kai tare da murmushi, shima sai ya mayar mata da murmushin.
Shi kenan na yafe miki. Yanzu me kike yi a kitchen.?
Tun ɗazu na fito ina dafa maka couscous ɗin, har da su Afra sai su tafi da shi makaranta.
Yayi kyau, to amma breakfast fa.?
Doya da kwai zanyi sai na dafa ruwan tea.
OK ni ki yi min kunun gyaɗa kisa a flaks ki saka a basket ɗina da doyar duka, bazan karya a gida ba sai naje office. Sai ku kusha tea ɗin.
An gama ranka ya daɗe.
Ta faɗa cike da farinciki tare da dariya a fuskarta, shima dariyar yayi na jin daɗin ya shawo kan matsalar cikin sauƙi, ya santa tana da sauƙin hali sannan yadda yake ganin soyayyarsa a kwayar idonta to ba zata so yayi fushi da ita ba, shiyasa jiya ya buɗa mata wuta yadda zai gigita lissafinta akan dole ta bi umarninsa, haka ya haura sama zuciyar fes itama ta koma kitchen tana murna, ta tsaya a tsakiyar kitchen ɗin tare da sauke ajiyar zuciya mai nauyi.
Allah na gode maka daya sauko, sai yanzu naji dai-dai. Na yarda ina son Hafiz fiye da tunani, har na rasa yadda aka yi soyayyarsa ta yi mini irin wannan kamun.
Ta ƙare maganar tare da isa gurin tukunyar miyar dake kan wuta. A lokacin bata samu kanta ba sai da ta sallami Hafiz da yaransa suka fita kafin itama ta ɗiba nata ta wuce ɗaki. Bayan ta gama komai ta kwanta sai ta kira Mamansu a waya ta bata labarin komai, Hajjo ta rufe ta da faɗa tana cewa.
Haka kawai zaki tona mini asiri, to wlh ki shiga hankalinki karki ƙara wannan shirmen. Haba Hamida wani irin aikin gida ne baki saba da shi ba, ko saboda hutun da kika fara samu ne kike so ki sangarce.? Girkin nan kin iya, kin kuma saba da shara da wanke-wanke, meye abun wahala a ciki.?
Wlh mama da wahala kawai daurewa nake yi, sannan taya zan riƙa yi wa ƙatuwa girki ba ni ce da miji ba, kawai dai zan cigaba da yi ne saboda bana son ran Hafiz ya ɓaci.
Kul.! Kul nace miki, Hamida kar kice zaki yi faɗa da matar nan, ko ban ce miki ki yi mata biyayya ba ki samu arziki. Ga Babangida nan kin ce zaki turo kuɗi ya cigaba da zuwa makaranta, yanzu gabaɗaya a wuyanki muka rayata tunda kece mai yi min sana'ar kuma kinyi aure, gashi ɗanwake nake jefawa a cikin gida da rana duk da ina ciniki amma ba kamar yadda kike fita da shinkafa ba.
Hmmm ni dai zan tattaro abunda nake da shi ranar da zan fara fita zan kawo miki.
To yanzu Naji batu, kuma dan Allah karki ƙara wani shashashanci, dan wannan gidan naki sai mutuwa nake fatan ya raba ki da shi.
Cewar mama cike da gargaɗi, Hamida ta saki dariya.
Mamanmu idon Nera.
Kin ci gidanku ai gaskiya ne kuɗi abun so ne, baka shi daga yin aurenki ba darajata ta ɗagu a gidan nan da 'yan unguwa ba, wlh ana mutunta ni fiye da da. Ai kuɗi ƙumbar susa ne.
Ta ƙare maganar tana 'yar dariya, daga bisani suka aje wayar Hamida tana ƙara ɗaura niyyar cigaba da aikin gidan, saboda bautar aure take yi, kuka aure Ibada ne ko ba komai zata samu lada.
Haka zaman ya cigaba da gudana bata sake nuna gazawa ko gajiyawa akan aikin gidan ba, watarana har da wankin kayan uniform ɗin su Khalil tana yi in mai wankinsu bai zo ba, ita danama tana yin wankinta ne na sauran mutanen gidan ne kuma me wanki yake zuwa duk sati yayi tare da guga, Hamida har sama take hawa ta gyara sashin Laila gabaɗaya sannan ta gyara ƙasa, tun tana yi tana jin gajiya har jikinta ya fara sabawa.
Kamar yadda bayan wata ɗaya zuwa biyu za a ga amarya tayi cikar ɗaki da kyau, to ita Hamida haske kawai tayi amma babu wannan cikar sai rama, saboda bata samun hutu sosai ba duk da tana cin mai kyau. Zuwa lokacin har sun fara online class na girki kuma Alhamdulillahi Hamida tana ganewa sosai, kuma tana gwada wasu snacks ɗin a gida su ci, Laila tana yaba mata tare da ƙara mata ktarfin guiwa, wani lokacin har ɗaukar ta take yi a mota su fita yin siyyan kayan da take buƙata, sannan ta sakata ta zaɓi abunda take so dangin kayan kwaɗayi, wannan yasa Hamida ta ƙara sake jiki ta gazgata maganar mama da ke cewa ta kwantar da hankali taci arziki, kuma tana ci sosai dan idan suka fita tana kwaso kayan zaƙi wanda bata taɓa ci ba ta jibge a gida.
Ranar data fara zuwa gidansu lokacin watanta biyu da kwana biyar da aure, haka ta kwashi kayan zaƙin da take tarawa, ta zuba a ƙaton Leda ta tafi dashi a matsayin tsaraba, a ranar Hafiz ne ya kaita ya aje ta, ba ƙaramin farinciki mutanen gidansu suka yi da ganinta ba, sai kowa ya shiga nan-nan da ita babu sauran kyashi da kishin da ada suke nuna musu, itama da yake ta yi hankali ta raba tsarabar gabaɗaya ga mutanen gidan, haka ta yini da mama a ɗaki suna hira. Duk wanda yaga Hamida ya san ta samu hutu saboda wannan duhun fatarta ta ɗan yi ja sai dai tana nan da rama kamar ta karye, shiyasa wasu suka shiga cewa ko ciki take da shi saboda ramar data yi, murmushi kawai take yi musu. Sai zuwa dare Hafiz yazo tare da Laila har gidan suka shiga, duk da ranta bai so ba amma saboda basaja haka ta shiga ta saki fuska suka gaisa da matan gidan, basu zauna ba suka yi musu sallama suka fito, a lokacin Hafiz yasa yaran gidan suka shigo da abinci, babban buhun shinkafa da katon ɗin taliya da makaroni har da hubun semolina, ga ruwan gora da drinks na companyn baban Laila har da biredi da kayan kwalama, aiko sun sha godiya da sa albarka dan har ƙofar gidan mama da kishiyoyinta suka rakosu suna godiya, Hamida kuwa tsabar farinciki kasa magana tayi dan sun gama biyanta, haka suka dawo gida da ɗimbin farin ciki. Shiyasa Hamida inta tuna da wannan tagomashin arzikin da suka kai gidansu bata kuiyar hidimta musu, balle ma yanzu da hannunta ya faɗa ta iya snacks kala-kala, wata uku suka yi suna gabatar da Class ɗin kafin suka gama, har an tura musu certificate irin na online ɗin nan ance kowa ya cire. A lissafinta yanzu wata biyar kenan da aurensu har yau bata yi ɓatan wata ba, bata wuce pereod ɗinta duk wata sai ta yi, yanzu ma saura kwanaki ta yi na watan daya kama, kuma babban burinta a yanzu bai wuce ace ta samu ciki ba, tana so ta ga gudan jininsu wanda zai tabbatar mata da sun fara cin ribar aurensu.
.
Yau ya kama talata, haka ta yi aikin data saba ta gama tazo ta kwanta tana jin ciwon kai, dama tunda gari ya waye take jin ciwon kai kaɗan-kaɗan amma sai bata ɗauke shi komai ba tasha masa paracetamol, tana kwance yaji an buga mata ƙofa, sai ta tashi ta zauna tana cewa.
A shigo, a buɗe yake.
Sai taga Laila ta shigo ta ci ado sai ƙamshi ke tashi a jikinta, ta ƙaraso ciki riƙe da wani ƙaramin kati a hannuta ta miƙa wa Hamida, ta amsa tana dubawa.
Ina gayyatarki bikin Birthday ɗin ƙanwata Zahida ranar Alhamis.
Jibi kenan, to Allah ya kaimu In Sha Allah idan Babansu Khalil ya bar ni zan je.
Laila ta yi mata hararar wasa.
Gidanmu ɗin ne ba zai barki ki je ba, haba dai, to tare ma zamu tafi sai ki zama cikin shiri, dama akwai ayyukan da nake so kije ki taya masu aikin gidanmu dan naga hannunki ya faɗa da snack, kin iya.
Kai anty ban gama iyawa ba.
Duk da haka ina buƙatar kije.
To ba damuwa anty Allah ya kaimu.
Hamida ta ambata tana murmushi, sai Laila ta amsa da amin ta wuce tana murmushi. Bayan ta wuce sai Hamida ta koma ta kwanta ta kira mama tana faɗa mata labarin zata je gidansu Laila, mama ta saki ƙaramar guɗa tana cewa ta tabbatar da tayi abunda kowa zai yaba mata, da suka gama wayar Hamida ta yi murmushi ita kanta tana ɗokin taje taga ya gidansu Laila yake tasan an narka kuɗi sosai.
...
Ranar Alhamis kamar yadda Laila ta faɗa Hafiz bai yi musu ba, haka suka tafi tare da Hamida gidansu, tun daga gate Hamida take kallon gidan cike da zaƙuwa, a ranta tace dole Laila ta yi jiji da kai ashe abun daga gidansu ne, sai taga shigar ta kamar bai yi daidai da zuwa gidan ba, doguwar riga ta saka ash color mai kyau da zanen manyan fulawa a jiki, ɗaya daga cikin na akwatinta ne da kuɗinta ya kai dubu sittin, ta yane kanta da gyalen ta ɗauki jaka da takalmi baƙi, haka suka fito tana ganin ta ƙure gayu itama yau ta kwaikwayi Laila, amma sai da suka shigo gidan ta raina kanta, haka suka yi parking suka fito suka nufi babban falon gidan, ko da suka shiga sun tadda mutane da dama 'yan gayu dasu sai turanci ke tashi, Hamida a ɗarare ta shiga ta soma gaisawa da mutanen, wasu su amsa cikin sakin fuska wasu kuma cikin haɗe fuska, nan da nan taji sun juya harshe suna yare wanda bata jin komai a ciki, sai a lokacin ta gane ashe Laila suna da yare shiyasa komai nata yasha bamban da na Hausawa, haka ta cigaba da bin Laila har suka hau sama zuwa ɗakin Zahida. Laila ta tace.
Yauwa kin ga yanzu sai ki sauya kaya karki ɓata wannan, ki saka wanda kike aikin gidan da shi dana ce ki saka a jaka.
Aiko yanzu kuwa, ina ne kitchen ɗin dan da zafina nazo na gwada nawa bajintar.
Kai Hamida da sauri haka.? ai ina ganin ma anyi oder ɗin komai, ni kawai aikin da zaki min shi ne zaki kula da kawayena, dan Allah ki kula da duk abunda suke buƙata karki bani kunya.
In Sha Allah zanyi duk yadda kike so.
Hamida ta faɗa tana ƙara gyaɗa kai, Laila ta koma ta zauna tana waya ita kuma Hamida ta sauya kaya ta zauna, da Laila ta gama sai suka sauko ta kai ta zuwa sashin momynsu suka gaisa sannan suka fito, a lokacin suka haɗu da Anty Saudat, Laila ta gabatar da ita ga Hamida cikin girmamawa ta gaishe ta amma ta amsa mata cikin yatsine fuska kafin ta wuce tana ɗaga waya, Laila ta yi murmushi kawai ta wuce Hamida tabi bayanta kamar raƙumi da akala, Laila ko abun yayi mata daɗi saboda tana treating Hamida yadda take so, shiyasa har gobe bata taɓa yarda da aikin malamai ba balle boka, ta fi gane amfani da izzarta da kuɗi hadi da kissar siye Zuciyar duk wanda ya raɓeta ta yadda zata juya kowa cikin sauƙi. Haka suka jera suka tafi wani falo daban, shima babba ne amma bai kai main falo girma ba, ta juyo tana nunawa Hamida falon.
Nan ne baƙina zasu sauka kafin a fara event ɗin, ga kuma kitchen can da aka zuba komai naci, ki tabbatar kin kawo musu duk abunda suke so.
Hamida tace mata to kafin suka zauna ta cigaba da waya da mutanenta. Hamida ma ta zauna a Cushing tana ginjina girman arzikinsu Laila, sai take ganin kamar alfarma Hafiz yayi mata daya aureta dan kamar bata kai tayi kishi da Laila ba, dan haka dole ta ƙara godewa Allah domin ba wayonta bane ba kuma dabararta ba.
Wajen ƙarfe biyun rana mutanen Laila sun gama haɗuwa, manyan mata ne lyan boko masu aji, shiyasa Hamida ta kama kanta sosai ta shiga yin aikin data saka ta babu kuskure, lokacin data kawo musu kayan ciye-ciye taji wata daga ciki tana cewa.
Fauza wai ko kinsan kayan BOJUWA HERBS.? ya Subahallahi! wlh kayan matar nan duniya ne, yanzu da shi nake kafa daular mulki a gidana ina cin sabon amarci.
Ta ƙare maganar tana fari da ido fuskarta ɗauke da murmushi, Fauza ta waro ido waje.
Shegiya Biba faɗa mana sirrin, a ina zan samu.? Kinsan bana wasa da oza room.
Wani tightening set nayi amfani da shi ya dawo min da sabon budurci, na ci kazar sababi da tantabarun alheri, hmmmm! magungunan Bojuwa Herbs ƙarshe ne, kun sanni da tsantseni bana son abun gargajiya, amma kamar wasa lokacin dana je Kano wata sister ɗina ta bani labarinta, sai na ce bari na gwada, aiko da nayi amfani da kayanta na samu biyan buƙata.
Ta ƙare maganar suna tafawa da Fauza, Laila taja tsaki.
Nan kuka fi auki, Allah ya kyauta.
Dalla can da ziki aje wannan girman kan da iyayi ki kwashi kayan Bojuwa Herbs wlh da kin gama siye zuciyar Hafiz, ke mazan nan fa dole sai da gyara, amma ke kullun kin tsaya a supplement, Hajiyata ki je ta haɗa miki parkage na musamman na Uwargida, ke hatta na Amare da masu Jego duk akwai nasu, ki kankaro jarajarki kiga aiki da cikawa.
Cewar Biba tana dariya, Laila ta taɓe baki takai dubanta ga Hamida tace cikin haɗe fuska.
Sai ki bamu guri ko.
Sum-sum Hamida ta wuce amma kuma ta riƙe sunan Bojuwa Herbs a cikin kanta kamar karatu, tana shiga kitchen ta rubuta sunan a cikin wayarta dan karta manta, saboda ta san zai mata amfani anan gaba, dan dole zai ta shiga sahun manyan Mata ta kankaro mutuncinta a gurin Hafiz. Ɓangaren su Laila kuwa tace.
Nifa bana amfani da irin wannan kayan.
To ki zauna kanki a murfi, Biba bani number ɗin matar nan dan ba za ayi bani ba.
*** Surayya Dee sunanta a kano take, amma fa in zaki fara ki fara da sanyi flusher zaki bani labari.
Nan take Fauza ta yi mata godiya ta yi saving number ɗin, bama ita kaɗai ba duk sauran sun aje number ɗin a wayarsu banda Laila da take ganin tafi karfin amfani da wannan magungunan. Zuwa ƙarfe huɗu aka tafi wajen taro can bayan gidan akwai ƙaton fili da aka yi masa kamar lambu, anan aka gudanar da shagalin sai bayan magariba aka watse kafin Hamida ta samu kanta, tayi mugun gajiya bacci kawai take buƙata tayi dan har wani jiri take gani, da suka isa ɗakin Zahida taso ta watsa ruwa tayi wanka amma sai ga kiran Hafiz a wayar Laila wai ta fito su tafi gida, da yake Laila a gida zata kwana, ba yadda taso ba dole ta shirya ta fito suka kama hanyar gida cike da sha tara na arziki, Hamida taji daɗin yadda mamansu Laila ta amshe ta tare da sauran ƙannenta, anty Saudat ce kaɗai bata ga alamar ta amshe ta ba, kuma dama ba zai yuwu kowa ya sota ba.
Bayan sun isa gida ta samu ta watsa ruwa a jikinta amma sai zazzabi ya rufe ta, da kyar ta samu ta ci abinci kaɗan tasha magani ta kwanta. A zaton ta idan aka wayi gari zata warware amma sai sabon ciwo ya taso mata dan tun asubahi ta fara amai har zuwa Safiya abun ba sauƙi, ganin haka ya sa Hafiz yace ta shirye suka tafi asibiti.
A gwajin farko da aka yi mata na jini ya tabbatar tana da Maleria da shigar sabon ciki, daga ita har Hafiz sun samu kansu a cikin farin ciki, dan yana son yara musamman da aka jima babu ƙaramin yaro a gidansu, yanzu Khalil shekarunsa sha uku, Afrah kuma tana da shekara tara, shiyasa ya ji daɗin samun cikin Hamida, haka aka haɗo musu magani tare da bayanin yadda zasu kula da cikin, suka yi godiya suka dawo gida bayan yayi mata siyayan kayan ciye-ciye, daya sauketa sai ya wuce gurin aiki, dama ya kira ya bada uzurin zuwa litti.
Da yamma data ji ƙarfi a jikinta sai ta shirya musu abincin dare bayan ta dawo ɗaki ta gabatar da sallar magrib, tana idarwa a lokacin ne Laila ta dawo tare da yara suka haura sama, Hamida ta ce sai anjima zata je ta gaisheta. Wajen takwas Hafiz ya shigo bayan ta idar da sallar isha'i, bai shigo nan ba dan ranar Laila ce da miji, dan haka sai da ta gama kimtsawa ta fito ta shirya musu abinci a dinning sai ta wuce sama dan ta gaisa dasu sannan ta gabatar musu da abincin, tana kama handle ɗin ƙofa taji Laila tana magana cikin ɗaga murya.
Narantse bazan taɓa karɓan cikin Hamida ba, dole ne a cire shi, kaima kasan yarana ba zasu samu ƙani daga wata mace ba in ba ni ba. Tun farko shiyasa ban yarda ka kusanci yarinyar nan ba amma kace kana da intrest akanta, haka dole nayi haƙuri badan rai na ya so ba. To ka sani wlh ko a cire cikin Hamida ko na bar maka gidanka.
Haba Laila ya zaki ce haka, dan Allah ki bar Hamida ta haifeshi tunda ba shege bane da ubansa, in ya so nan gaba sai ta fara planning, kinga koda bata sake haihuwa ba tana da wanda zata kalla a matsayin ɗa, muyi mata adalci itama mutum ce kamar ke.
Ohhh haka kace.? Hafiz ko dai son yarinyar nan ya zarce wanda kake min ne ban sani ba.? to bari kaji wlh sai an zubar da cikin nan, ai tun farko ka aureta ne a matsayin wacce zata kula mana da gida saboda rashin dace da ba muyi da 'yan aiki ba, akan wannan maganar yasa na amince maka ka aure ta, shi ne yanzu zaka zo kana ce min muyi mata adalci, ai adalcin kenan ka barta a iya matsayin daka aurota.
Ta faɗa tana ɗaga hannu sama ranta a ɓace, Hafiz ya zauna a Cushing ya dafe kansa zuciyarsa a dagule tare da danasanin sanar da Laila cikin Hamida, a zatonsa wai ko zata taya shi murna zasu samu ƙaruwa, ashe wani tashin hankali zai kunnowa kansa.
Hamida wani irin sanyi ne jikinta yayi wanda yasa da kyar ta iya ɗaga ƙafafunta, ta sauka daga benen ta wuce ɗaki suf-suf tana haɗa hanya idanunta ciccike da kwalla har bata gani da kyau.
Ƙarshen book 1.
Last freepage.
*Akwai babban cakwakiya a gidan Hafiz. Ga kuma Hafsa da Saminu ko ya lamarinsu zai kaya oho. Ku biya kusha labari da fadakarwa.*