Bayan Murmushi

83

by @zahrabmrs02

Daren Juma'a ta yi. Farhana ta tashi da daddare ta yi sallar tahajjud, ta roƙi Allah ya ba ta sa'a. Ta fito sanye da kakin matuƙan jirgi (Pilot uniform) 


Farhana tana zaune a wani ƙaramin ofis a Hanscom Field, fuskarta tana kallon Mr. ANTONY wani tsohon matuƙin jirgi ne mai shekaru talatin yana tashi. Mutum ne mai tsauri da ba ya yin dariya.

"Candidate Maryam," ya faɗa yana buɗe manyan littattafai a gabanta. "Mun san kina iya tashi a jirgi, amma shin kin san me yasa yake tashi? Bari mu fara."

Tattaunawar Ilimi (The Oral Session)Ya tambaye ta dalla-dalla yadda tsarin mai (fuel system) da na wutar lantarki (electrical system) na Cessna 172 yake aiki. Farhana ta ba shi amsa ba tare da shakka ba"Idan kina sama kika ga gajimare mai launin baƙi sannan iska ta sauya salo, me hakan yake nufi?"• Farhana: "Wannan alama ce ta Thunderstorm Cell, kuma dole ne in karkata jirgina akalla mil 20 daga wurin don kauce wa hatsari."Ya tambaye ta dukkan dokokin sararin samaniya.

Kusan sa'o'i biyu suna tattaunawa. Farhana tana zufa duk da sanyin AC, amma duk tambayar da ya jifa mata, sai ta tuna da wahalar da ta sha a baya, hakan ya ba ta kwarin gwiwar ba da amsa daidai.

A ƙarshe, Mr. ANTONY ya rufe littafin, ya gyara gilashinsa, sannan ya yi ɗan murmushi  karon farko. "Excellent work, Maryam. Iliminki na kasa ya cika. Yanzu mu je mu hau jirgin mu ga ko hannunki yana da sauri kamar harshenki."


Farhana ta shiga jirgi tare da Mr. Antony ,suka yi shawagi a sararin samaniya na tsawon awa ɗaya. Ta yi dukkan matakan gaggawa da ya buƙata cikin kwarewa. Suna sauka a kan kwalta, Antony ya ciro alkalaminsa ya sa hannu a kan takardarta.

"Congratulations, Captain Maryam Farhana. You are officially a Private Pilot."

Farhana ta kasa magana, sai kawai sai kuka. Amma Antony ya ce mata, "Ki goge hawayenki, akwai mutane da yawa dake jiran ganin sabuwar Captain ɗinmu."

Biki



Tana fitowa daga filin sauka, sai ta ga babban falon ajiye jirage (Hangar) an kawata shi da fitilu da furare. Ga mamakinta, duk mutanen dake rayuwarta sun hallara:Isabella, Hailey, da Liam: Suna rike da wani katon banner: "WE HAVE A CAPTAIN IN THE HOUSE!"Su Lamido da Sultana: Suna sanye da kananan kakin Pilot, suna tsalle suna cewa "Our Pilot Mummy!"duka Yaushe aka tsara hakan farhana ta tambaya cikin mamaki 

A tsakiyar wurin, Farhana ta hango Farooq tsaye kusa da wani babban tebur dake dauke da wani cake mai siffar jirgin sama.

Farooq ya karaso gare ta, idanunsa suna sheki da alfahari. Ya ciro wani ƙaramin akwati, ya buɗe. A ciki akwai Zinariyar fiffike (Golden Wings) wadda ake maƙalawa Pilot a ƙirji.

"Maryam," ya faɗa cikin muryar dake nuna tsantsar ƙauna. "Wannan ita ce kyautar jarumtarki. Na san kin sha wahala, kin yi kuka, kin yi aiki tuƙuru. Yau, babu wanda ya isa ya sake kiran ki da sunan da bai dace da ke ba."

Ya maƙala mata fiffiken a jikin kakinta. Farhana ta kalli Farooq, kishi da zargin "Dear" duk suka narke. A wannan lokacin, ta ji kamar ta rungume shi, amma sai ta tsaya saboda mutunci.

"Farooq... ban san yadda zan gode maka ba," ta faɗa cikin murya mai rawa.

"Ba ni zaki  gode wa ba Maryam, kanki zaki  gode wa saboda baki karaya ba," Farooq ya rada mata. "Kuma wannan bikin fari ne kawai. Akwai wani babban labarin dake jiran ki nan gaba."

Da taimakon farooq da connection dinsa farhana ta Sami aiki a matsayin private pilot .inda ta rasa yadda zata gode ma farooq for supporting her ,making her dreams come true 

Kusan sati uku kenan da fara aikin Farhana, kuma abin mamaki, Farooq ya sake ja baya. Saƙonnin sa sun yi ƙaranci, kuma idan suka yi waya, yakan ambaci "shirye-shiryen wani abu na musamman" da yake yi, wanda hakan yake ƙara wa Farhana zargin cewa batun aure yake yi da wata daban.

Ta yi ƙoƙarin toshe zuciyarta. Ta kan ce wa kanta, "Maryam, ke fa yanzu Pilot ce. Kar ki bari wani namiji ya sake dagula miki lissafi." Amma duk lokacin da ta rufe idonta, fuskar Farooq take gani.


Wata ranar Laraba, Manajan kamfanin jirgin su ya kira ta. "Captain Maryam, yau za ku kai wani babban VIP zuwa San Francisco. Mutumin yana da mahimmanci sosae a kamfaninmu, don haka muna son komai ya tafi daidai."

Farhana ta gyara kanta, ta nufi filin jirgin. Tana tsaye kusa da jirgin kirar Gulfstream G650, sai ta ga wata baƙar mota ta faka. Zuciyarta ta buga sanda ta ga Farooq ya fito, sanye da wata tsadaddiyar bakar suit da gilashin gani na zamani. Ya yi kwarjini sosae, yana tafiya cikin takun sa 

"Good morning, Captain," Farooq ya faɗa yana mata wani kallo mai nuna kamar bai san yadda take ji ba.

Farhana ta dake, ta yi salon soja. "Good morning, Sir. Barka da zuwa jirginmu."

A cikin jirgin, yayin da suke sararin samaniya, Farooq yana zaune a ɓangaren VIP yana duba wasu takardu. Farhana ta fito daga cockpit don duba ko komai yana tafiya daidai.

"Maryam," Farooq ya kira sunanta ba tare da ya ɗago kai daga takardun ba. "Kin iya aiki sosae. Na ji daɗin yadda kika saita jirgin nan."

"Na gode," ta ba shi amsa a taƙaice, za ta juya ta tafi.

"Wait," ya tsaida ita. "Kina ganin wannan launin furaren zai yi kyau a wurin biki? Akwai wata da nake son faranta wa rai, kuma ina son komai ya zama perfect." Ya nuna mata hoton wasu hadaddun furare a wayarsa.

Farhana ta ji wani daci ya taso mata. Ta danne zuciyarta, ta nuna masa wasu launin furare na daban. "Wannan ya fi kyau idan tana son abubuwa masu sanyi."

"Gaskiya ne. Thanks, Maryam. You're a lifesaver," Farooq ya faɗa yana murmushin da ya sanya ta jin kishin ya kusa kashe ta.


Bayan sun dawo daga San Francisco, Farhana ta iske saƙon banki a wayarta. Albashinta na farko ne a matsayin Private Pilot. Adadin kuɗin ya firgita ta; ya ninka albashin da Abdulkadir yake ba ta a matsayin alawus sau biyar.

Farhana ta zubar da hawayen murna. Ta kira Isabella ta gaya mata. Ta fara lissafin yadda za ta tura wa Diddi da Abbi kuɗi don Neman Albarkar su .

Sai dai kuma, farin cikin ya gauraye da damuwar Farooq. Ta kira shi a waya da daddare don ta sanar da shi ta sami albashi.

"Congrats, Captain! Hakan yana nufin zan iya samun kyauta kenan?" Farooq ya faɗa cikin zolaya.

"Tabbas," Farhana ta ce. Zan kaika cin abinci bills on me ,hope dear Dinka bazata damu ba 

Farooq ya yi shiru na ɗan lokaci, sannan ya yi wata ’yar dariya mai ma’ana. "Karki damu, Maryam. Ba da daɗewa ba za ki haɗu da ita. Kuma ina kyautata zaton za ku yi abota sosae."

Farhana ta kashe wayar tana jin tamkar ta fasa ihu. Tana son shi, amma wasan da yake yi da kwakwalwarta yana neman haukata ta. Ta rantsa ba za ta sake nuna masa tana kishinsa ba, ko da kuwa zuciyarta za ta tarwatse.


Ta tura wa Abbi da kuma Diddi kudi masu yawa. Ba tura kudin kadai ta yi ba, ta hada da sakon waya:


"Abbi, wannan kadan ne daga cikin kudin da Allah ya azurta ni da su a nan kasar waje. Ina so ku yi amfani da su don kula da kanku. Kuma Ina Neman albarkar ku .Karku damu da ni, Maryam dinku tana nan tana fadi-tashi, kuma Allah ba zai taba barina ba."


Farhana ta riga ta yanke shawara: Ba za ta gaya musu tana tuka jirgi ba yanzu. Tana son ranar da zasu ganta, su ganta a tsaye a filin jirgi Nnmadi azikew sanye da kakin matukan jirgi na kasa-da-kasa (International Pilot)

A week later 

Farhana ta nufi ofishin Farooq cike da shauki, tana sanye da kakinta na Pilot wanda yake karawa kyan fatarta haske. Tana son yi masa albishir ne akan wani sabon mataki da ta samu a aiki, amma tana tura kofar ofishin, sai ta ji numfashinta ya tsaya.

Farooq yana zaune a kan kujerarsa, yayin da wata mace kyakkyawa, sanye da riga da wando na kamfanin Gucci, take tsaye kusa da shi. ta rissina kai tana nuna masa wani abu a cikin kwamfutar sa.

"I told you, Farooq, wannan tsarin zai fi kyau matar ta fada cikin wata lallausar murya mai dauke da salon kissa.

Farooq ya dago kai yana murmushi, "You're right, saudat. Shi ya sa kika zama ta musamman a wurina kin San me kike yi 


A daidai nan Farhana ta tura kofar gaba daya. Farooq ya zabura ya tashi tsaye sanda ya ganta, fuskarsa ta sauya daga annuri zuwa fargaba.yasan kishin farhana 

"Maryam! Kin zo?" Farooq ya fada yana kokarin karaso wa 

Saudat ta juya ta kalli Farhana daga sama har kasa, ta saki wani murmushin isa. "Oh, is this the pilot you were telling me about? She's cute."ranar dayake ban kalleta sosai ba Ina Sauri sai yanzu  Naga cuteness dinta .

Farhana ta ji gabanta ya fadi. "The pilot you were telling me about?" Wato hira ta yake yi da wasu matan kenan? Kuma kalmar "cute" da aka kira ta da ita, ta ji ta tamkar wulakanci—kamar ana maganar wata yar yarinya.

"It seems you're busy Mr. Farooq," Farhana ta fada, muryarta tana rawa amma tana kokarin daurewa. "Dama hanya ce ta biyo da ni nace bari nazo mu gaisa. I didn't know you had important company."

"Maryam, wait! Ba yadda kike tunani ba ne..." Farooq ya nufi inda take.

Amma saudat  ta sake kamo hannunsa, "Farooq, we need to finish this list. The florist is waiting for the 'Dear's' confirmation."

Wannan kalmar—"Dear"—ta sake dukan kunnen Farhana. Ta tabbata wannan matar ita ce "Dear" din da take ji a waya take Ta ji ofishin yana yi mata kadan.

"Excuse me!" Farhana ta fada cikin zafi, ta juya ta fice da sauri, takun takalmanta yana bada sauti kwas-kwas-kwas a corridor din ofishin.

: "Dama me Farooq zaiyi dani?Am just fucking deceiving myself. Ya samu wacce ta fini , kyakkyawa, wadda ta dace da matsayinsa. Me zai yi da ni? Tsohuwar matar Abdulkadir?"