The innocent love and the moral compass
by @zahrabmrs02
Jannah ta fito harabar gidan inda Aliyu yake tsaye jiran oda. "Aliyu," ta kira sunansa, muryarta a dake amma akwai wani irin sanyi a cikinta. "Ba zan koma gida ba a daren nan. Zan kwana a nan wajen Salma. Ga mukullin motar, ka tafi da ita gida, ranar Monday da safe ka zo ka dauke ni a nan mu wuce ofis."
Aliyu ya kalli mukullin motar dake hannunta, sannan ya kalli cikin idanunta. "Are you sure, Ma'am? Barinki a nan ba tare da tsaro ba yana da hadari."
"Ina tare da kawayena, Aliyu. Babu abinda zai faru. Tafi kawai," Jannah ta fada tana murmushin da shi kadai ta taba yi wa tun da suka hadu. Aliyu ya karbi mukullin, hannayensu suka taba juna na sakanni biyu, wani irin shock ya ratsa su duka biyun. Da Sauri ya fice daga gidan, yana tuka motar Jannah mai tsada, zuciyarsa tana tunanin kalaman nadeeya da kuma yadda Jannah take kokarin boye rauninta.
A can cikin gidan Salma, kawayen uku sun sauya shiga zuwa rigunan baccin siliki (silk pajamas). Sun baje a kan katon gadon Salma, ga kwalaben drinks da snacks a gabansu.
Amani tace Jannah, gaskiya ki fada mana, wannan PA din naki Aliyu, shin daga wace duniyar kika samu shi ? Tun da nake ban taba ganin namiji mai kwarjini da kyan fuska irinsa ba."
Salma ta kwashe da dariya Amani,biki ga yadda yake tsaye kamar bango? Ko ni da nake da miji, sai da gabana ya fadi. Jannah,
(Ta dauki drink dinta tana juya shi) "Girls, na fada muku aiki ne kawai tsakanina da shi. Kuma zargin da nake masa na cewa Alhaji Bashir ne ya turo shi har yanzu yana nan." Kuma bana ganin wani kyaunsa kun cika zuzuta Abu wallahi
Koda ma Alhaji Bashir ne ya turo shi, ai kyansa kadai ya isa ya wanke kowane laifi. Kin ga yadda yake kare ki? Jannah, karki tauye kanki. Jikin nan naki yana bukatar namiji irin Aliyu ya taba shi don ya san cewa ke mace ce, ba kankara ba."amani tace Tana kure jannah da Kallo
Gaskiya ne. Kuma kin ga yadda kika bashi mukullin motarki? Wannan alama ce ta yarda (trust). Jannah, heart dinki tana magana, amma brain dinki tana kokarin dakatar da ita ki bashi chance jannah
Jannah ta yi shiru, tunanin yadda Aliyu ya murde hannun nadeeya da kuma yadda ya kalle ta lokacin da yake raɗa mata magana a kunne yana dawowa a ranta. A daren nan, kawayen nata sun tattauna batutuwa da dama, daga harkar kasuwanci har zuwa sirrin dakin kwanciya, inda Amani take ta basu labarin yadda darensu da Kabir zai kasance idan ta koma gida.
Jannah dai tana jinsu ne kawai, amma a ranta, tana hango fuskar Aliyu Yusuf Sada a cikin bakin suit dinsa.
Bayan Aliyu ya bar gidan Salma da motar Jannah mai tsada, bai nufi gidansu dake Hotoro kai tsaye ba. Zuciyarsa tana bukatar nutsuwa, kuma mutum daya ne kacal take iya ba shi hakan: Naima.
Naima diya ce ga abokin mahaifinsa, yarinya ce mai kimanin shekaru 18 dake matakin SS3. Kyanta na asali ne, ba tare da kwalliya ko katsalandan din zamani ba. Aliyu, wanda ya taba yin rayuwar "Playboy" a baya ba tare da ya taba daukar kowace mace da muhimmanci ba, shi Kansa bai San mata adadin nawa suke ce sona sonsa ba,haka yayi ta playing da emotions dinsu har suna aka sa masa a university Mr heartbreaker ,a hankali rayuwar yaudara yanmata ta fita daga ran aliyu ,duk be taba wata muaamala ta banza da ko wace mace ba ,tunda yake ,kuma yana alfahari da hakan ,a dai barshi da love words ,wanda yawa alkawarin aure yawa ne dasu ,shiyasa ma ya mika wuya lokacin da mahaifinsa (Abba) ya zaba masa Naima a matsayin matar aure Soyayyarsu mai tsafta ce, ba tare da wani datti ba.
Yana isa kofar gidan, ya kira ta a waya. Can sai ga ta ta fito, sanye da doguwar riga ta atamfa da katon mayafi dake nuna asalin kamala da tarbiyya.
Tana ganin Aliyu, ta tsaya cak, idanunta suka zaro saboda mamaki da kuma sha'awa. "Yaya Tareeq?" ta kira sunansa cikin muryarta mai sanyi. "Wannan shiga haka? Kai ne yau a cikin Suit?"
Aliyu ya yi murmushi, ya karaso kusa da ita. "Na yi kyau ne, Naima?"
"Yaya, kayi kyau sosai!" Ta fada tana washe baki (innocence). "Suit din nan ta fito da kwarjinka daban da shaddar da na saba gani. Gaskiya haka taba kyau irin na Yau ba kamar Bature Ka zama ."
Aliyu ya ji wani dadi a ransa. Daga dambarwar nadeeya da Jannah, ga shi yanzu yana tare da zuciyar da ba ta san makirci ba. Sun dade suna hira a falon bakin gidan , inda Naima take ba shi labarin karatunsu na makaranta da kuma yadda take kewarsa.
Lokacin da Naima ta fito rakashi har bakin gate, sai ta ga babbbar motar (SUV) dake ajiye, wacce take walkiya karkashin hasken wata.
"Yaya, wace irin mota ce wannan? Ba taka ba ce, ko?" Naima ta tambaya tana kallon motar cikin sha'awa.
Aliyu ya shafa Kansa a hankali. "A'a Naima, motar Oga ta ce. Na yi amfani da ita ne yau don in gudanar da wani aiki, zan maida mata ita ranar Monday da safe."
Naima ta gyada kai, "Lallai Ogar taka tana da dukiya. Allah ya kara daukaka, Yaya. Amma gaskiya suit din nan ta yi maka kyau, kada ka cire ta har sai ka kwanta."
Aliyu ya yi dariya, ya shiga motar ya tada ta. "Zan tafi gida yanzu. Ki yi karatu sosai, Naima. Kina nan a raina."
Yana barin unguwar, murmushin dake fuskarsa ya fara gushewa yayin da yake tunanin ranar Monday. Zai maida wa Jannah motarta, amma zai iya maida wa zuciyarsa nutsuwa bayan ya sake shiga duniyar Jannah mai cike da hadari?
Aliyu ya danno motar Jannah cikin unguwar Hotoro, inda kowa ya bi motar da kallo saboda yadda take walkiya. Sai dai yana isa kofar gida, ya hango Abba tsaye, ransa a bace
Abba ya tsaya kyam, ya nade hannayensa a kirji har Aliyu ya fito daga motar.
"Aliyu!" Abba ya kira sunansa cikin muryar tsoratarwa. "Daga ina wannan motar? Kuma me kake yi da ita a kofar gidana?"
Aliyu ya durkusa har kasa ya gaishe da mahaifinsa. "Abba, motar Oga ta ce. Ta ce in tafi da ita gida sai ranar Monday in kai mata."
Abba bai saurara masa ba. "Ban yarda ba! Aliyu, bamu taba kawo abun wani gidan nan mu kwana da shi ba. Tarbiyyar mu ba haka take ba. Maza maza ka maida shedaniyar ogar taka motar ta , ka dawo gida a kafa ko a motar haya."
Aliyu ya san idan Abba ya dauki zafi, magana ba ta karewa cikin sauki. "Abba, don Allah ka bari na shiga ciki na kama ruwa sai na mayar ." Bai jira amsar mahaifinsa ba, ya shige gidan da sauri don kauce wa fadan.
A falo Aliyu ya sami ummi ko karfe nawa zai kai ummi bata taba bacci sai taga tareeq dinta.
"Ummi, don Allah ki taya ni bawa Abba hakuri," Aliyu ya fada yana goge gumin goshinsa. "Ogar tawa ce ta matsa lallai in tafi da motar saboda akwai inda zan dauko ta ranar Monday. Idan na maida yanzu, zan bata mata lissafi, kuma kina ganin yadda na fara samun fada a wurinta."
Ummi ta kalle shi, ta yi ajiyar zuciya. "Tareeq , kasan mahaifinka ba ya son abun da zai kawo magana. Amma tunda batun aiki ne, bari in je in kwantar masa da hankali. Amma ka tabbata Monday din nan tana kaiwa ka maida mata abunta, kaji ko?"
"An gama Ummi. Allah ya kara miki nisan kwana."
Bayan Aliyu ya shige gida, Abba ya ci gaba da tsayi wa a ƙofar gidan yana kallon motar, ransa a ɓace. Abba ya tsani halayyar Jannah Anderson tun ranar da ya fara jin labarin yadda take tafiyar da rayuwarta ta mulki da kuma yadda take wulaƙanta mutane. A gare shi, Jannah ba mace bace mai mutunci da ya kamata ɗansa mai tarbiya ya hada ma hanya da ita ba shiru shiru aliyu be fito ba abba ya bi Bayan sa
"Aliyu!" Abba ya sake kira daga tsakar gida, muryarsa tana dukan bango. "Na faɗa maka ka mayar da wannan motar yanzu! kuma ba na son wata alaƙa tsakaninka da ita. Wannan motar fitina ce
Ummi ta fita zuwa wajen Abba, inda ta yi amfani da dabarun mace wajen lallashinsa. "Habiby ka bar yaron nan ya huta. Motar nan fa amana ce aka bashi, kuma idan ya maida yanzu zai iya rasa aikinsa tunda ta ce sai Monday take da bukatarta. Ka bar shi ya ajiye ta a nan karkashin kulawarsa ,tunda kai ma kasan Aliyu ba ya taba taba abun wani."
Abba ya danyi shiru, sannan ya girgiza kai. "To shikenan. Amma idan Monday ta yi bai maida motar nan ba, to ya nemi wani uban amma ba ni ba."
Wajan get ummi ta leka , idanunta suka sauka a kan motar dake walƙiya karkashin hasken wuta. Zuciyarta ta buga; ta daɗe tana jin labarin kyautar Jannah ga waɗanda suka saba da ita. A ranta, tana ganin wannan dama ce ta Aliyu ya fita daga talauci.
Bayan Abba ya shige ɗakinsa yana ƙunkuni, Ummi ta fito ta jawo hannun tareeq zuwa gefe.
"Tareeq , karka damu da fadan Abba, kasan halinsa ," Ummi ta raɗa masa muryarta ƙasa-ƙasa. "Amma ni ina gaya maka, ka ƙara jajircewa wajen yi wa Jannah biyayya. Na ji labarin cewa duk wanda ya saba da ita, tana yi masa kyautar da zai rabu da talauci. Wannan motar ma ai alama ce ta cewa ta fara yarda da kai."
Aliyu ya kalli Ummi, zuciyarsa ta raba biyu; tsakanin bin umarnin Abba na tsantsaini, da kuma goyon bayan Ummi na neman rufin asiri.
"Ummi, ina ƙoƙari na samu amincewarta (trust), kuma komai yana tafiya yadda ya kamata," Aliyu ya faɗa yana tuna kiran Alhaji Bashir.
Ummi ta shafa kansa tana murmushi, "Haka nake so. Kayi biyayya, kayi ladabi. Idan ka samu kuɗin nan, dukanmu mun huta."
Yanzu kaje gidansu Usman ya bude maka gidansu tunda suna da space ya ajiye maka motar
Ranar Monday ta zagayo, Aliyu ya tashi da wuri ya gyara motar ta yi ƙal-ƙal. Ya sanya wani Deep Blue Suit wanda ya dace da launin motar. (Jannah ta ba tareeq wadrobe allowance da take ba ko wani sabon maikaci don siyan suits da cooperate Kaya na zuwa office )Yana isa gidan Salma, ya iske su Jannah da Amani suna hira a harabar gidan.
Tana ganin sa, Amani ta saki baki: "Jannah, dubi PA ɗinki! Look at how handsome he is in that suit again."
Jannah ta kalli Aliyu, sannan ta kalli motarta da take sheƙi. Ta ji wani sanyi a ranta ganin yadda ya kula da amanar motar, amma ta dake ta ce: "Aliyu, ka makara da minti biyar. Maza buɗe mana ƙofa mu wuce."
Aliyu ya buɗe kofa tare da durƙusawa kadan, "Ina ba ku haƙuri, Ma'am. Motar tana jiran ku."