JANNAH YAR GIDAN ANDERSON

Lonely in penthouse

by @zahrabmrs02

Aiki ya kankama a Anderson Global. Aliyu yana fuskantar matsin lamba ta kowane bangare. A gefe daya, Alhaji Bashir yana ta kira yana barazanar cewa idan Aliyu bai fito masa da wani sirrin ba, zai dauki mataki. Ga Wajan aikinsu har yanzu be basu wani hint akan jannah ba .A ofis kuma, Jannah tana bin duk wani motsi nasa da idanun:

Aliyu ya gane cewa ba zai taba samun sirrin Jannah ta hanyar takardu ba; dole ne ya samu damar shiga zuciyarta. ya lura cewa Jannah tana son mutum mai nuna damuwa a kanta. Ya fara tambayarta game da lafiyarta da cin abincinta, wanda ya saba da yadda sauran ma'aikatan suke tsoronta.Ya san cewa matakin da ya dauka wajen kare ta daga nadeeya ya bude kofa. Ya ci gaba da nuna mata cewa shi ne kadai mutumin da zata iya yarda da shi a duniyar dake son ganin bayanta.Yayin da suke aiki  a ofis, Aliyu yana kokarin janyo hirar zuwa ga rayuwarta ta sirri, yana tambayarta dalilin da ya sa take zabar zaman kadaici a penthouse dinta.amma shiru jannah bata tanka shi ba .

Wata rana da yamma, Jannah tana duba wasu fayiloli, Aliyu ya shigo ya ajiye mata kofin kofi (coffee) ba tare da ta bukaci hakan ba.

Aliyu: "Ma'am, kin dade kina aiki ba tare da hutawa ba. Wannan zai iya taba lafiyarki."

JannahTa dago kai, idanunta sun yi jawur saboda gajiya) "Lafiyata ba matsalarka bace, Mr. Yusuf. Ka gama abinda na saka ka?"

Aliyu Ya tsaya kyam, ya kalle ta cikin ido "Lafiyarki matsalata ce tunda ni ne 'inuwarki'. Idan kika fadi, inuwar ma za ta bace. Me ya sa kike wahalar da kanki haka, Jannah? Me kike gudu?"

Jannah ta ajiye biro din hannunta, ta ji wani irin Shock a jikinta saboda kiran sunanta da ya yi. Babu wanda ya taba kiranta da 'Jannah' a wannan ofishin.



Lokacin da Aliyu ya kira sunanta "Jannah," dakin ya dauki shuru na wasu dakiku. Jannah ta ajiye biron hannunta da karfi, ta mike tsaye tana kallonsa da idanun da suka sauya launi saboda bacin rai.

"Dakata a nan, Mr. Yusuf," Jannah ta fada muryarta tana rawa saboda fushi. "Wa ya baka ikon kiran sunana kai tsaye? Waya  gaya maka ni sa'arka ce? Ko kuma  mun taba wasan kasa da kai?"

Aliyu ya tsaya kyam ba tare da ya nuna fargaba ba, koda yake ya san ya kure ta.

"Ina ba ki hakuri, Ma'am," Aliyu ya fada cikin natsuwa.

"Hakuri ba zai isa ba!" Jannah ta katse shi, ta zagayo gaban teburinta. "Daga yau, ka kiyaye harshenka. Kai ma'aikaci ne a karkashina, kuma matsayinka ba zai taba wuce hakan ba. Idan ka sake kiran sunana ba tare da 'Ma'am' ko 'Miss Anderson' ba, to ka nemi wani aikin, domin kyakkyawar fuskarka ba za ta taba cetonka daga fushina ba."

Jannah ta koma ta zauna, tana maida numfashi. Ko da yake tana masa fada, a ranta akwai wani sashi dake jin dadin yadda ya kira sunan nata, amma dole ta kare mutuncinta a matsayinta na shugaba mai iko.

Aliyu ya juyo zai fita, amma kafin ya kai bakin kofa, ya juyo ya ce, "An gama, Miss Anderson. Amma kiyi sani, fushi baya canza gaskiyar cewa kina bukatar hutu."

Ya fice ya bar ta nan tana huci, yayin da zuciyarta take ta faman dukan uku-uku


Bayan wannan takaddama ta jiya, Aliyu ya shiga ofis da nufin binciko bakin zaren da zai ba shi damar shiga jikin Jannah Anderson. Cikin nazari da kwarewa irin ta jami’in da aka horar, ya gano wata badakala da aka gudanar a asusun kamfanin dake ƙasar Switzerland.

"Ma'am, an fitar da maƙudan kuɗi daga asusunmu na Switzerland ba tare da sa hannunki ba," Aliyu ya faɗa lokacin da ya shiga ofishinta, fuskarsa ɗauke da yanayin kwarewa. "Dole ne ki taka zuwa can don gano ko wane ne 'snitch' dinki a can."

Jannah ta yi shiru na ɗan lokaci, tana nazarin maganar. "Aliyu, ka shirya," ta faɗa a taƙaice. "Next week zamu tafi Switzerland. Amma yanzu, ka fita, ina da abubuwan da zan kammala."


Bayan kowa ya watse, Jannah ta koma gida, amma wannan karon ba ta jin daɗin mulkin da take da shi. Penthouse ɗin nata mai cike da kayan alfarmar duniya ya yi mata faɗi da yawa.

Ta shiga ɗakinta, ta rage hasken fitilun, sannan ta cire takalman ƙafarta. Jannah ta durƙusa a tsakiyar ɗakin, ta fashe da wani irin kuka mai ban tausayi. Wannan kukan ba na fushi ba ne, kuka ne na rauni da kadaici wanda take ɓoye wa duniya.

Ta jawo wani tsohon akwati , ta buɗe shi da hannaye masu rawa. Ta ɗauko wani tsohon hoto wanda launinsa ya fara fita. Ta kurawa hoton ido cikin shauki da matsananciyar kewar rayuwar da ta shude, wacce take fata da ma za ta iya komawa gare ta ko da na minti ɗaya ne.

Ta share hawayen dake bin kuncinta, sannan ta ajiye hoton a hankali. Zuciyarta ta tafi kan mahaifiyarta, Mrs. Elena Anderson.

"Mom," ta raɗa muryarta a karye. "Dubi yadda rayuwata ta zama. Daga ni sai karnukana (dogs) kaɗai. Kowa yana tsorona, kowa yana gani na a matsayin macijiya, amma babu wanda ya san yadda nake ji a ciki."

Ta miƙe ta nufi wurin manyan karnukan nata waɗanda suka kasance abokan hirarta a cikin wannan katon gidan. Ta shafa kansu tana jin yadda suke nuna mata ƙauna mara munafunci. A daren nan, Jannah Anderson ba shugabar kamfani ba ce; mace ce kawai mai neman wanda zai fahimci kukan zuciyarta.