JANNAH YAR GIDAN ANDERSON

Blind date

by @zahrabmrs02


Amani ta matsa wa Jannah lallai sai ta hadu da wani babban attajiri mai suna Barrister sabeer Al-Hassan. sabeer  namiji ne mai shekaru 38, wanda ya kware a harkar shari’a da kasuwancin gidaje. Yana da tsawo, yanayin fuskarsa na nuna cewa ya san abinda yake yi, kuma kyakkyawa ne ta kowane bangare 

Maimakon Jannah ta bari Aliyu ya kaita, ta yanke shawarar tafi da kanta don ta nuna ikonta. Ta fito sanye da wata tsadaddiyar rigar da tafi kowace wacce ta taɓa sawa kyau, inda ta nufi wani babban gidan cin abinci na alfarma.

sabeer  ya tashi tsaye lokacin da ya hango Jannah tana tahowa. "Jannah Anderson," ya fada muryarsa cike da girmamawa. "Naji labarin cewa ke jaruma ce, amma ban taba sanin cewa kyanki zai iya dakatar da numfashin mutum ba."

Sun zauna suka yi hira sosai. Sabeer  mutum ne mai ilimi da fasaha, yana ta ba Jannah labarin yadda ya gina daularsa. Jannah ta tsinci kanta tana sauraron sa, amma a gefen zuciyarta, tana ta kokarin hada kyaun sabeer  da na Aliyu. sabeer yana da kyau na kudi da daukaka, amma Aliyu yana da wani sirri da kwarjini na asali wanda har yanzu ta kasa gano karshensa.


Bayan sun gama cin abinci mai tsada, waiter ya kawo takardar kudi (bill). sabeer ya kai hannu zai dauka, amma Jannah ta dakatar da shi tare da mika tata katin bankin (Black Card).

"sabeer , wannan karon a kaina yake," Jannah ta fada tana murmushin rainin wayo.

sabeer yayi mamaki. "Lallai Jannah, kinyi mini abinda babu macen da ta taba yi mini. Kin nuna mini cewa ke ba kawai kyau gare ki ba, kina da iko." Jannah ta ji dadin yadda ta ba shi mamaki, kuma ta fara tunanin ko ya kamata ta ba shi dama a rayuwarta.


Kafin gari ya waye, wasu hotuna da aka dauka a boye na Jannah da Sabeer  suna dariya a teburin abinci sun mamaye dandalin sadarwa. An sanya wa hoton taken "The King and the Queen of Northern Business: A New Power Couple?"


Washegari da safe, Aliyu yana sanye da suit dinsa yana shirin fita ofis sai ya tarar da Abba rike da waya, ransa a matukar bace.

"Kalli! Kalli kiga Laila!" Abba ya kira Ummi yana nuna mata hoton Jannah dake Facebook. "Kalli shigar yarinyar nan. Wai a haka ake cewa ita Musulma ce? Anya kuwa wannan yarinyar ba ta fice daga addini (Ridda) ba kuwa? Dubi yadda take bayyana jikinta a gaban namijin da ba muharraminta ba, a gaban duniya!"

Ummi ta karbi wayar tana kallo, ita ma ranta ya bace amma saboda tana gudun kada Aliyu ya rasa damarsa. "Malam, ai wannan harkar duniyarsu ce. Kasan wadannan 'yan boko..."

"Wace harkar duniya, Laila?" Abba ya katse ta. "Wannan ita ce matar da kike son ɗanki ya cigaba da yi aiki ? Aliyu! Dubi nan. Idan har wannan yarinyar ba ta sauya hali ba, to karshenka da ita ya zo. Ba zan taba yarda jinina ya gauraya da irin wannan tarbiyyar ba."

Aliyu ya kalli hoton Jannah da Sabeer . Wani irin kishi ne ya ziyarci zuciyarsa wanda bai taba jin irinsa ba, amma sai ya dake. "Abba, aiki ne kawai ya hadamu.dan Allah ka kwantar da hankalin ka