Hint?
by @zahrabmrs02
Jannah ta ba Aliyu umarnin su biya ta wani gidan marayu dake gefen gari. Aliyu ya yi mamaki, domin bai taɓa tunanin mace mai girman kai kamar Jannah tana da lokacin marayu ba.
Suna isa, Aliyu ya ga wata New Jannah. Ta cire takalman ta, ta shiga cikin yaran tana wasa da su, tana dariya sosai—irin dariyar da bai taɓa gani ba a ofis ko a taron kawaye. Wannan gidan marayun nata ne, ita take ɗaukar nauyin komai na cikinsa.
Matron ɗin gidan ta matso kusa da Jannah, fuskarta ɗauke da damuwa. "Ma'am, akwai wata yarinya yar shekara takwas da aka kawo mana jiya. Tun da ta zo ba ta ce uffan ba, kuma ba ta cin abinci."
Jannah ta miƙe ta nufi inda yarinyar take zaune ita kaɗai a gefe. Ta zauna a ƙasa kusa da ita, ta kama hannun yarinyar. Aliyu yana tsaye a nesa yana kallon ikon Allah.
Abinda ya fi ba Aliyu mamaki shi ne lokacin da Jannah ta fara yi wa yarinyar magana. Domin kusan minti sha biyar, Jannah tana magana da yarinyar ne cikin Harshen Hausa, amma ba irin wacce ake yi a Kano ba. Jannah tana amfani da asalin harshen Hausa da lafazin (accent) mutanen Zamfara ko Sokoto.
Muryarta ta sauya, ta zama mai daɗi da ratsa zuciya, tana lallashin yarinyar da kalaman da Aliyu bai taɓa jin ta yi amfani da su ba. Tunda yake aiki da ita, kashi 90% na hirarsu da Turanci suke yin sa, kuma idan ta yi Hausa, takan yi ta ne irin ta mutanen birni. Bai taɓa sanin tana da asali da yankin Zamfara ba.
Daga ƙarshe, yarinyar ta fara murmushi har ta rungume Jannah. Jannah ta sumbaci goshin yarinyar, sannan ta miƙe ta goge hawayen dake idonta, ta dawo wurin Aliyu tare da sake daura fuskar "Boss Lady".
Aliyu ya buɗe mata ƙofar mota, amma zuciyarsa tana ta faman juya abinda ya gani.
"Ma'am," Aliyu ya kira sunanta cikin muryar kwarewa. "Ina ba ki hakuri idan na shiga hurumin da bai kamata ba. Amma Hausar da kika yi amfani da ita a gidan marayu yanzu... accent dinki ya yi kama da mutanen yankin Zamfara ko Sokoto. Ko kina da wata alaka da can ne?"
Jannah, wacce take cikin duniyar tunani, gabanta ya fadi ras! Ta manta gaba daya cewa Aliyu yana kusa da ita lokacin da take lallashin yarinyar nan. Cikin sauri ta sauya yanayin fuskarta zuwa asalin Jannah Anderson mai zafi.
Ta daka masa wani kallo na tsana ta madubi. "Me kake nufi, Aliyu? Me kuma ya hadani da waccen yankin?" ta tambaya cikin muryar dake nuna bacin rai.
"Ka manta cewa iyayena Turawa ne (Mrs. Elena Anderson)?" Jannah ta fada muryarta tana rawa kadan. "Na koyi Hausa ne kawai saboda kasuwanci da kuma mu'amala da mutane. Wannan accent din da kake magana a kai, kila tunaninka ne kawai ko kuma yadda kake son jin maganar."
Ta jingina bayanta da kujerar motar tare da daure fuska sosai. "Stay in your line, Aliyu. Kar ka sake kuskuren shiga cikin rayuwata ta sirri ko kuma ka fara bincike akan asali na. Aikinka shi ne kiyaye tsarona da kuma kula da bukatun kamfani. In ba haka ba, karshen zamanka a matsayin PA dina zai zo da wuri fiye da yadda kake tsammani."
Aliyu ya yi shiru, ya gyada kansa kawai. "Ina ba ki hakuri, Ma'am."
Amma a cikin zuciyarsa, Aliyu ya san cewa ya tabo inda yake masa kaikayi. Yadda ta razana da sauri ta karyata shi, ya kara tabbatar masa da cewa akwai wani babban asiri dake binne a Zamfara wanda Jannah Anderson take tsoron kada duniya ta sani.
text ya turawa office dinsu akan first hint dinsa