JANNAH YAR GIDAN ANDERSON

The glass mask and the Zurich kiss

by @zahrabmrs02

Sanyi mai ratsa kashi ya tarbi Jannah da Aliyu lokacin da suka sauka a birnin Zurich. Jannah ta sanya wata hadaddiyar rigar sanyi (Fur Coat) kalar fari, wacce ta kara fito da kyaunta da alfarmar ta. Aliyu yana bin bayanta da sauri, idanunsa na yawo ko'ina don tabbatar da tsaro.

Sun nufi babban bankin Credit Suisse kai tsaye. Wani babban bature, Mr. Schneider, ne ya karbe su a wani daki na musamman na sirri.

"Miss Anderson," Mr. Schneider ya fara magana bayan an kawo musu shayi. "Mun ga sako daga bangarenku na son bincikar sa hannun da aka yi amfani da shi kwanan nan. Abinda zan iya gaya muku shi ne, wanda ya yi wannan 'transaction' din, ya zo nan bankin ne da kansa."

Jannah ta tashi tsaye cikin fargaba. "Da kansa? Elena Anderson ta mutu shekaru biyar da suka wuce! Ta yaya zata zo nan?"

Mr. Schneider ya kalli Aliyu sannan ya kalli Jannah. Ya kunna wani screen dake jikin bango. "Wannan hoton kyamarar tsaro ne (CCTV) na ranar da aka yi kwasar kudin."

Hoton ya bayyana. Wata mace ce sanye da bakaken kaya, fuskarta a rufe da siririn yafi, amma idanunta da yadda take tafiya... duka na Elena Anderson ne.

Jannah ta kusan faduwa, sai ga Aliyu  ya yi saurin taro ta. A karon farko, Jannah ta bar shi ya taba ta, hannunta ya damke na Aliyu cikin tsananin tsoro.

"Bata mutu ba..." Jannah ta rada, muryarta na rawa. "Elena tana raye."

Aliyu  ya kalli hoton kyamarar da kyau. A matsayinsa na jami'in tsaro, ya lura da wani abu da kowa bai gani ba. Macen da ke hoton tana da wani tabo a hannunta na hagu—, tabon Elena ba ta dashi a hotunan baya.

"Wannan ba Elena bace, Ma'am," Aliyu  ya fada muryarsa kasa-kasa a kunnenta. "Wannan wani ne da yake son kiyi tunanin tana raye... domin ya janyo ki cikin wannan tarkon."

Daidai lokacin, wayar Aliyu  ta yi kara. Sakon Alhaji Bashir ne ya shigo: 'Ina fata kuna jin dadin sanyin Switzerland. Ka tabbatar ka gama da ita a can, Aliyu. Lokaci ya kusa.'

Jannah ta dago ta kalli Aliyu har yanzu hannunta yana cikin nasa. Ba su sani ba, ashe a wannan lokacin ne babban asirin gidan Anderson ya fara bayyana—cewa makiyin Jannah ba Alhaji Bashir bane kadai, akwai wani na kusa da ita wanda take tunanin ya dade da mutuwa.


Bayan fitowar su daga bankin Credit Suisse, shiru ya ratsa tsakanin Jannah da Aliyu  har suka isa katafaren hotel din da suke sauka. Dakunansu suna kallon juna, amma kowannensu ya shige nasa dakin cikin yanayi na tunani.

Karfe daya na dare (1:00 AM).

Sanyin Zurich ya kara tsananta, amma Jannah ta kasa zama a daki. Zuciyarta tana mata kuna, ga kuma yanayin "period" dinta da ya kusa, wanda yake sanya ta jin wani irin rauni, damuwa, da kuma bukatar kulawa (emotional and needy). Ta saka wata riga ta bacci mai sulbi da wani siririn mayafi, ta fito zuwa harabar hotel din kusa da babban tafkin ninkaya (pool side).

Ta tsaya a bakin ruwan, tana kallon inuwar kanta. Hoton Elena dake banki ya ki barin idonta. Ta tuna rayuwarta ta baya, ta tuna kadaicin da take ciki duk da tarin dukiyarta. Hawaye daya ya zubo mata.

A daya bangaren kuma, Aliyu yana tsaye a jikin labulen dakin sa, yana kallon Jannah daga sama. Ya sani sarai cewa idan har yana son gano sirrin yarinyar nan, dole ne ya yi amfani da tsohuwar dabi'ar sa ta Playboy. Dole ne ya shiga jikinta ta yadda ba za ta iya fita ba. Duk da cewa ya lura Jannah ba mace bace mai rawar kai akan kyaun namiji, amma yau ya ga wani abu daban a idanunta—ya ga bukata.

Ya fito sanye da rigar sanyi kalar baka, ya sauko kasa cikin takun sa na natsuwa. Jannah tana juyowa don komawa daki, suka yi kusan karo da juna.

Aliyu  ya yi saurin sa hannunsa ya taro ta ta hanzari, tafukan hannunsa suka sauka daram akan kugu (hips) dinta. "Ma'am, kiyi hankali... sanyi ne sosai a waje," ya rada cikin muryarsa mai ratsa zuciya.

Jannah ta dago kai, idanunta suka rincike cikin nasa. A wannan lokacin, duk wani aji, izza, da bossy behavior dinta suka narke. Yanayin jikinta da radadin zuciyarta suka hade waje guda. Kafin Aliyu  ya ankara, Jannah ta sanya hannayenta biyu ta damke wuyan rigarsa, ta manna shi da karfi a jikin bango.

Ba tare da bata lokaci ba, ta kamo lips dinsa, ta fara bashi wani zafafa kuma shafaffan sumba (passionately kiss). Jannah tana kissing dinsa ne cikin yunwa da kuma wani irin yanayi kamar rayuwarta ta dogara ne akan hakan. Aliyu  ya daskare na wasu dakiku, jikinsa ya fara rawa, kafin shi ma ya fara mayar mata da martani.

Wajan ya yi shiru, sai karar numfashinsu da yake fita cikin sanyi. Jannah ta yi nisa, idonta ya rufu, tana son mancewa da kowa da komai a cikin jikin Aliyu .

Kwatsam, sai ta tuna wacece ita. Jannah Anderson.

Ta ja da baya da kyar, numfashinta yana fita da sauri. Ta kalli Aliyu wanda har yanzu yake tsaye jikinsa na rawa, idanunsa cike da mamaki da shauki. Jannah ba ta ce uffan ba, kuma ba ta sake juyowa ba, ta rabe ta gefensa ta nufi dakin ta cikin sanyi.

Aliyu ya tsaya a gun, yana shafar lips dinsa. Ya sani yanzu wasan ya sauya salo. Jannah ta riga ta fada tarkon sa, ko kuma shi ne ya fada nata?


Jannah tana shiga daki, ta banko kofar ta murda sakata, numfashinta yana fita da karfi kamar wacce ta yi tseren gudu. Ta raba kanta da rigar sanyin jikinta, ta fara watsi da kayan dakin ta cikin bacin rai da dana-sani.

"Oh my God! Fuck!" ta fada cikin sanyin murya amma cike da bacin rai. "Jannah, what have you done? Me ya same ki ne?!"

Ta fada kan gado tana ihu a hankali cikin matashin kai, kafafunta suna dukan gado. "Yanzu da wani idon zan kalle shi gobe? Me zai yi tunani? Me ya sanya na bar wannan yaron ya ga raunina?!"

Ta fashe da kuka, kukan kewar mahaifiyarta Elena, da kuma kukan haushin kanta. "Mom... I missed you so much. Komai ya jagule min."

A waje kuwa, Aliyu yana tsaye a bakin kofarta. Ya ji hayaniyar da take yi a ciki, ya ji ihun da take yi. Ya matso kusa da kofar, ya kwankwasa a hankali.

"Ma'am? Miss Anderson? Ko lafiya?" ya tambaya cikin kulawa.

"Get out, Aliyu! Ka tafi dakin ka! Get out!" Jannah ta daka masa tsawa daga ciki, muryarta na nuna cewa ta gama fita a hayyacinta.

Aliyu ya ja da baya, ya koma dakin sa yana kunshe dariyar sa. Ya jingina da kofa, ya shafa labban sa (lips) da har yanzu yake jin dumin na Jannah a jiki, tare da kamshin turarenta na Vanilla mai dadin gaske.

Duk playboy dinsa da yan matan da ya taba yi, bai taba barin mace ta taba lips dinsa ba. Ya dade yana yaudarar yan mata amma bai taba yin "real kiss" ba sai yau. A zahiri, Jannah Anderson ce ta sace masa first kiss dinsa ba tare da izini ba!

"Lallai Jannah kin cika 'yar kishirwa," ya rada wa kansa.

Daga nan tunaninsa ya koma kan Naima, yarinyar da ya fara ji a ransa cewa ita ce gaskiyar sa. Sannan ya tuna mahaifinsa dake gida Kano . Ya yi ajiyar zuciya. Idan har abba ya san cewa mace irin Jannah Anderson, wacce yake gani a matsayin "hedonist" (mai bin son zuciya), ita ce ta sanya bakinta a na dansa, to tabbas hawan jinin sa zai iya tashi a lokacin.

Ya sake shafa bakin sa, ya girgiza kai. "Ba wanda zai yarda da ni a duniyar nan idan na ce The Great Jannah Anderson ce ta fara manna ni da bango tayi kissing dina "

Ya kwanta a gadonsa, idonsa biyu, yana tunanin yadda gobe zata kasance. Wasan ya sauya salo; tana tunanin ta gama da shi, shi kuma yana lissafin yadda zai shiga zuciyarta don ya bankado dukkan asirin da take boyewa.


karshen free page


"First Kiss na Aliyu ya tafi ga matar da ya kamata ya bincika! Shin Aliyu zai iya cigaba da aikinsa na DSS, ko kuma zai fada tarkon Jannah Anderson? Me zai faru idan Naima ta gano abinda ya faru a Zurich? Sirrin dake tsakanin Jannah da Aliyu ya fara narka kankara... amma zai iya kone kowa! 

Wacece jannah Anderson?

Ya akayi Mr and Mrs Anderson suka mutu a rana daya ?

Shin jannah Tana da rayuwar da take boyewa ne?

Ya soyayyar sabeer  da jannah take kansancewa?

Hoton wa jannah take Kallo tana kuka?


Mene ne asirin Zamfara? Me yJannah ta razana lokacin da Aliyu ya ambaci accent dinta na mutanen Zamfara? Shin asalin ta baturiya ce ko kuwa akwai boyayyen dangi a can?


Akwai tarin tambayoyi da zan warware Akan wacece jannah yar gidan Anderson 

Alkalmin Zahra B ,bazai taba Baku kunya ba ,ku biyo ni