SARTSE COMPLETE

Ɗanɗano

by @legendspen

Ɗanɗano daga littafin Sartse. 

Wani irin azababben zafi nake ji yana shiga jikina, kamar ana tafasa ni a cikin tandar gurasa. Kicin ɗin gaba ɗaya ya ɗumame yana fitar da wani irin wuci, sakamakon girkin da nake a kurfoti guda biyu. 

“Wayyo Allah!.” 

Na faɗa a fili bayan na juya ga miyar da take ta fasa akan ɗayan kurfotin, tsumma na ɗauka na sauke ta ƙasa na fara juyata. 

“Maggi bai ji ba, A’a ya ji Sardauna baya son maggi ya yi yawa.”

Na faɗa a dabarbarce, hannu nasa na danna wayata allon wayar ya kawo haske, na yi tozali da kyakyawan hotona ni da mijina a ranar ɗaurin aurenmu, a fili na furta. 

“Ina sonka mijina, ina ƙaunarka, Allah Ya kula mini da kai.” 

Ina faɗin haka na kalli agogon shida da rabi, nasan kowanne lokaci zai iya shigowa, ƙaurin gurasar da nake gasawa ne ya daki hancina, ba shiri na miƙe na sa hannu a kan kaskon da nake gasawa da niyar juyawa, sai dai cikin rashin sa’a na kama dandarrayar kasakon maimakon gusar, wani irin zafi ya ratsani har tsakar kaina, na yi baya da sauri.

 “Ya Allahu.” 

Na faɗa tare da sake komawa na kama gurasar na juya. Bayan na juya na ƙara ɗaukan wani curi ɗaya na ɗorashin akan abinda nake murzawa da shi na fara murzawa ina faɗaɗashi, har sai da ya yi falai falai, sannan na cire takan kaskon na ɗora wannan, daga nan na koma kan miyar na ɗauko plast mai kyau na juye ta a ciki gaba ɗaya, da niyar idan ya ci ya rage ni sai na ci domin azababben ƙamshinta da ya cika mini hanci ya cire mini sha’awarta na lokacin, bayan na juye na ɗauki plast ɗin na fito daga kitchen ɗin zuwa makaken falona na alfarma da ya ƙawato da kayan ado masu kyau da tsari. 

Ɓangaren dinning na nufa, shi kansa abin tsayawa ka kalla ne, domin ni kaina lokaci zuwa lokaci na kan tsaya na kalli gidana da irin ƙoƙarin da iyayena suka yi wajen cika shi da kayan alfarma, bayan ƙoƙarin da Mijina Sardauna ya yi na gina makeken gida a anguwar Takur, ina ajiyewa na koma kicin ɗin na juya gurasar dake kan wuta, sannan na fara ƙoƙarin juye wutar dake cikin kurfotin da na sauke miya a cikin wani bukitin ƙarfe, sabida bana son kashe wutar a cikin kicin ɗin toka ta ɓata minin aikin da na yi, bayan na juye na ɗauki Bukitin na fita bayan gidan ta ƙofar kicin, ƙaramin famfon na nufa na tara bokitin da wutar garwashin a ciki, bayan ruwan ya taru na zubar da iya ruwansa da ya yi sanyi a bakin rariya, da sauri na koma kicin na sauke gurasar da ke kai na ɗauki ta ƙarshen na fara murzawa, bayan ta yi faɗi na ɗora ta akan kaskon, daga nan na koma na shanya gawayen da na kashe ɗazu a ƙasa, sannan na dawo cikin ɗin. 

Daidai lokacin da motarsa ta fara horn, da sauri na dawo falo na buɗe taga na fara kallonsa, tun daga parking ɗin har fitowarsa, yanayin yadda yake tafiya ma kaɗai abin a tsaya a kallani. 


“Wayyo Mijina, Allah Ya ƙara maka arziƙi, lafiya da nisan kwana.” 

Na faɗa a raina, ina ja da baya. 
Ƙamshin turarensa ne ya fara dukkan hancina kafin sassanyar muryarsa ta daki dodon kunne na. 

“Sannu da zuwa.” 

Na faɗa kamar zan durƙusa ma sa, tsabagen biyayya da ƙauna. 

“Yawwa! Sannu da gida.” 

Ya faɗa yana miƙo mini jakar hannunsa, na russuna na amsa, ya ƙara ciro hulal kansa ya miƙa mini kana ya sami kujera ya zauna, ɗakinsa na nufa zan ajiye cikin kakausar muryarsa ya ce. 

“Ranki ya daɗe takalmin fa.” 

Murmushi na saki sannan na ce. 

“Ina shirin fara shiga da waɗannan ne.” 

“Ko dai kin barni na cire?.” 

Na dawo kusa dashi, na tsugunna na cire masa takalmin, bayan na cire na kwaɓe mai safar sannan na ɗauka na shiga dasu cikin ɗakinsa, komai a mazauninsa na ajiye su na ƙara gyara inda na ga kamar bai gyaru ba a ɗakin sannan na shiga toilet na haɗa masa ruwan zafi daidai yadda nasan yana so.


*******
“Nana ai naga alamun kamar ana son shiga tsakanin mu a wure miki kunne.” 


Ya faɗa fuskarsa ɗauke da murmushin da nake kallo a matsayin soyayya mai girma, sannan ya ƙara cewa. 


“Nana ina son na nemi alfarma a wajenki guda ɗaya.” 


Na gyaɗa masa kai sannan na ce. 

“Ina sauraronka.” 

“Nana ka da ki bari wani ya shiga tsakanin ki da mijinki, ina faɗa miki hakane a matsayina na mijinki.” 


Cike da farin ciki da gamsuwa da soyayyarsa na ce. 
“Tom in sha Allah, yanzu kaje ka yi wanka zan kunna wutar gawayin na soya na kawo ma.” 
“Tom ki yi sauri kinsan dai fita nake son yi.” 
Ya faɗa yana juyawa ya fice, ni kuma na kulle ko ina na kicin din na fara ƙoƙarin kunna wutar. Gaba ɗaya kicin ya turniƙe da hayaƙi wanda ya tsaya mini a maƙwogarona na fara tari babu ƙaƙƙautawa. 
Tsuggunawa na yi a ƙasa ina kakari, ina jin kamar hanjin cikina zai fito waje, da ƙyar na iya tashi na fara buɗe kokafin bayan na ga wutar ta kama. Idona fal da ƙwallar da ta taru sabida hayaƙi na tashi na ɗauko farantin silba na shiga firfita wutar har takama. 

Na sakko da kaskon daga kan gas ɗin na ɗora akan kurfotin, ina yi ina firfitawa har man ya yi zafi na fara sanya fanken ina soyawa. Kusan minti talatin sannan komai ya kammala na juye a filas na fito falo, yana zaune kan kujera ɗaure da tawul ɗin wanka. 
Kan dinning na nufa na ajiye plast ɗin, sannan na koma Kicin na ɗauko kufuna da faranti na dawo na jera akan dainin sannan na dawo cikin falon. 
“Komai ya kammala.” 
Na faɗa ina ƙoƙarin zama sabida sandarewar da na ji bayana ya yi, sakamakon durƙushen da na yi na soyawa fanken, kallona ya yi sanan ya ce.
“Ni ai ban kammala ba! Ko ni zan shirya kaina ne?.” 
Murmushin yaƙe na yi sannan na ce. 
“Aha ba dai! Ya zaayi ka shirya kanka ni ina nan, mene amfanina?.”
“Babu kam, idan har ba zaki yi mini biyayya ki faranta raina ba, babu.” 
Ɗakin nasa na nufa, wanda daman ban kai ga zama akan kujerar ba, sai dai shiga ta ɗakin numfashina ya tsaya na wasu daƙiƙa, sakamakon abinda nagani. 
“Mene haka?.” 
Na faɗa ina shirin juyawa, sai dai na ci karo da shi a bakin ƙofar ɗakin, na tsaya ina kallonsa shi kam ya huce ni ya zauna akan gadon. 
“To na buɗe zan shirya tun da naga kina kicin, kuma ni banga kayan da suka yi mini ba shine sai na fito dasu duka.” 
Ya faɗa yana turu baki kamar ƙaramin yaro, wanda hakan ya yi matuƙar burgeni, ya kuma goge mini dukkan ɓacin ran da sheɗan yake son sanya mini. 
Na yi murmushi ina matsowa sannan na ce. 
“Ai da ka jirani, amma bari na duba maka nina san waɗanda zasu yi maka kyau.” 
Na tsugunna a ƙasa na fara kwashe kayan da ya zuzubar a ƙasa ina zuba su kan gadon, sai da nagama kwashe su tsaf sannan na ce.
 “Bari naga wanda zaifi maka kyau.” 
“Hon!.” 
Na ji ya kira wannan sunan, sunan da na daɗe banji ya kirashi ba, sai soyayya ta yi nisa yake faɗinsa, cikin zaƙuwa na ce. 
“Naam Hon!.”
“Kayan nan kamar ba’a taɓa gogesu ba ko?.” 
Ya faɗa yana taɓa kayan a yamutse kamar ba na sa ba. Da mamaki na kalleshi, kayan da ya biya kuɗi aka wanke aka goge, suna jere a cikin sif yazo ya wargatsa su, amma yake cewa kamar ba’a taɓa gogewe ba, ‘ko ya fara ciwon ido ne?’ Na tambayi kai na a zuci, a fili kam sai na ce. 
“Me ka gani Hon?”
“Duk sunyi wani sikwizin, kamar an ƙwato su daga bakin kura.” 
Na yi dariya ganin yadda yake taɓe hanci, kamar yana riƙe da kashi. 
“To ai duk kaine ka yi musu haka.” 
Na faɗa ina ci gaba da duba kayan. 
“To ai bansan zasu yi haka ba, yanzu haka zan dinga fita kamar almajiri?.” 
Ya faɗa kamar zaiyi kuka, gaba ɗaya naji nustuwata tana shirin barin gangar jikina, a ruɗe na ce. 
“A’a Hon! Ya zaayi ka fita a haka? Zan bawa Madu ya kai wajen guga a sake gogewa, tun da kaga mu nan bama amfani da abu mai jan huta, dutse, Tv, hita, kukin gas, wani lokacin ma cewa kake a kashe fanka sabida Mita kuɗin wuta da wahala.” 
“To ya zaayi idan abu yakama dole ayi, ki yi amfani da dutsen kawai ki gogesu, amma kafin na dawo fa dan Allah Hon.” 
Haka kawai sai naji jikina ya yi wani iri, Miji na da nake so, nake ƙauna sama da komai shine zai dinga haɗani da Allah akan na yi masa guga, guga dai abar banza. 
“Haba Hon! Haba Haba! Kafin ka dawo amgama in sha Allah.” 
Na faɗa ina miƙa masa wani light bulun yadin. 
“Kaga wannan bai yi sikwizin sosai ba.” 
Karɓa ya yi yasa, ni kuma na ɗau mataji na hau taje masa gashi, sai da gashin ya yi kyau sannan na sa masa hularsa, na fesa masa turare muka fito. 
“Nifa na makara gaskiyya, na yi birek fas a ofis kawai.” 
Ya faɗa yana niyar ficewa. “Haba Hon, ka tsaya dan Allah.”
“Hon it is almus 10:30, na makara sosai fa, ki ajiye min idan na dawo na ci.”

*******
“Sunana Bilkisu, anan baya nake ina yawan cewa zan shigo Allah Bai nufa ba sai yau da na zagayo gidan kisto.” 
Ta faɗa tana nuna hannunta baya alamun kwatancen inda take, na yi mata wani murmushi mai wuyar fassara, domin ni kaɗai nasan irin bugun da zuciyata take, lokacin dawowar Sardauna ne yanzu, kowanne lokaci zai iya shigowa, gashi baya ƙaunar ya ga wata ƙawa ta kusa ko ta nesa ta zo wajena. 
“Zauna mana to.” 
Na faɗa ina nuna mata kujera, ta yi min wani irin murmushi sannan ta ce. 
“Ai sauri ma nake, amma zan dawo.” 
Ban kai ga buɗe baki ba na ji horn ɗin Sardauna, wanda yake yi daidai lokacin da zai kashe motarsa, wanda yake yinsa domin sanar dani ya dawo. 
“Mai gidan ne ya dawo?”
Ta tambaya ne, na yi murmushi sannan na ce. 
“Eyh shine.” 
“Ayyah to kinga kuwa ba sai na zauna ba, amma in sha Allahu zan dawo.”
Ta faɗa tana juyawa zata fita, daidai lokacin kuma shi ya shigo. Kamar ana buga ganga haka na ji zuciyata na bugawa, da sauri na runtse idona sannan na buɗe. 
“Sannu da zuwa.” 
Na faɗa ina ƙarasowa inda yake, ga mamakina ya sa hannu ya komo ni tare da faɗin. 
“Wifey baƙi ne damu?”
Ya faɗa yana shigewa ciki, na bi bayanshi ina faɗin. 
“Ina zuwa.” 
“Uhmm.”
Ta faɗa tare da zama, ni kuma na bishi ciki. 
“Sannu da zuwa.” 
Nasake faɗa ina ajiye jakarsa a ma’ajiyinta. 
“Yawwa” 
Ya amsa yana zama kan gado, tsugunnawa na yi tare da fara cire mai takalmi ina faɗin. 
“Wallahi bansanta ba, yanzu ta shigo wai anan baya take.” 
Kallona ya yi tare da kamo hannuna
“To mene a ciki? Ai hakan yana da kyau sosai da sosai, ka yi ta zama a waje bakasan kowa ba? Ta shi kije ku gaisa.” 
Da wani irin yanayin mamaki nake kallon Sardauna. ‘Sardauna dai? yau shi ke barin wata tazo gidan nan, har da cewa ayi ta zama a waje ba asan kowa ba, Sardauna da ya tsani ganin baƙo a gidan?’ 
“Ki tashi mana.” Muryarsa ta katse min tunanin da nake, na miƙe na nufi falon. 
“Ki yi haƙuri na bar ki.” 
“A’a babu komai fa, ai mai gidan ne ya dawo, bari na zo na wuce amma zan dawo.” 
“Tom shi kenan na gode sosai da sosai, nima idan na samu fita zan shigo gidan naku in sha Allah.”
Na faɗa ina rakata waje, a gurguje na dawo haɗa masa ruwan wanka sai na tarar yana toilet ɗin ma.
Na fito na dawo na jera masa abinci akan dinning, bayan na fito masa da jallabiyar da zai sanya na ajiye mai kan gado, nima na tafi ɗakina na gabatar da magariba na dawo falon. 
“Ko ka kirani na yi serving ɗinka.” 
Na faɗa ina zama kan dinning ɗin. 
“Ah bakomai, har baƙuwar ta tafi?” 
Ya tambaya, na gyaɗa masa kai sannan na ce. 
“Ta tafi wai amma zata dawo, ni ba ma so nake ta dawo ba, nasan kai baka fiya son mutane suna zuwar mana ba. Zan ma taka mata burki.” 
“Nina faɗa miki, kawai dai akwai waɗanda ban yarda dasu ba ne.” 

*********
A hankali na tura ƙofar falon na shiga, zaune na tarar da su ‘yan mata ne sun kai su biyar da alamu ma wasu ƙawayenta dan ba ‘yan gidansu ba ne, duk da nima wannan ne zuwa na na farko gidansu. 
cikin wani irin yanayi kamar na isgili haka ta tarbeni. 
“A’a Nana kina ƙaraso.” 
Na yi mata murmushi sannan na ce. 
“Eyh wlhi, ya gida?” 
“Muna lafiya.” 
Zama na yi sannan na kalli sauran matan dake ɗakin, sannan na ce. 
“Sannunku.” 
Bansaniba ko sun amsa ko basu amsa ba, nidai abinda ke gabana shine kaɗai ke damuna. 
Gaba ɗaya tunanin maganganun da muka yi da  Sardauna ya cika min ƙwakwalwa, bana iya tuna komai sai ita. 
‘Nana nagaji, ina danne zuciyata ina sonki, bana son abinda zai cuceki, amma Hajiya ta dage wai tana son ganin jikokinta, Nana ko zuwa gidan Hajiya bana son yi, bana so na ji an soke ki ko anci mutunciki, Nana bana son zaluntarki, bana son cutar sa zuciyarki, bazan iya ƙara aure ba kwata kwata, karki ga yadda ake zancen nan a family house kamar akaina aka fara shekara uku da aure ba haihuwa. Hon haihuwar nan dole ne?.’
“Allah Sarki Mijina.” 
Na faɗa a zuciyata, a fili kuma sai na ce. 
“Dan Allah magana nake so mu yi dake, ina son mu shiga daga ciki.” 
Dariya ta yi ita da mutanen nan nata sannan ta ce. 
“Haba Nana kamar ba wise ba.” 
Ɗaya cikin ƙawayen ta ce. 
“Baiwar Allah kizo ki ganmu tare sannan ki ce wai ta tashi ku shiga ciki a wane dalili?” 
Baki sake nake kallon ikon Allah. 
“Nana waɗannan ƙawayena ne duk wani sirri zan iya yi dasu, dan haka ki faɗi abinda zaki faɗa.” 
Ji nai na yi wani irin muzanta, ‘ƙawayenta ƙawayena ne?, ko da ƙawaye na ne kowacce magana yakamata na yi a gabansu?.
“Hon ina cikin damuwa, ina cikin tashin hankali, rayuwa ta yi min baƙi mutuncina yana tangarirya Hon, na yarda amma ki je da kanki kisan yadda zaki yi da ita ta amince, Hon ki durƙusa mata a ƙafa, ko ni naje na durƙusa mata kawai Hon, da mutuncina ya zube a idon duniya, gwanda na yi haka.” 
Kalaman Sardauna suka dawo kunnuwa kamar yanzu yake faɗinsu. 
“Bazan taɓa bari ka hulaƙanta ba in sha Allah Mijina.” 
Na faɗa, sannan na kalleta tare da tasowa zuwa inda take, nasanya gwiwoyina a ƙasa sannan na ce. 
“Ki taimaka ki auri mijina.” 
Wata shegiyar dariya na ji ƙawayen na ta sun kice da ita. 
********

Na fito falon sai dai ban ganshi akan dinning ɗin ba, sai da na ƙarasa shigowa falon na hango sa acan kan kujera yana yana faman danna waya, kan dinning ɗin na nufa na zauna, buɗe plast na yi zansa gurasar sai sai guda ɗaya na gani, murmushi na yi a raina na ce.

 “Yau Sardauna anji daɗin girkin kenan.” 

Na ɗauki ɗayar nasa a plate ɗin da ya gama ci, na buɗe plast ɗin miyar zan zuba sai dai fa sam babu miyar a ciki ya shanye, karo na farko cikin abubuwan da Sardauna yake yi mini na ji babu daɗi, buɗe plast ɗin da farfesun naman ragon yake na yi shima dai babu.

 “Me ya faru haka?.” 

Na tambayi kaina, dan nasan dai Sardauna ba zai taɓa cinye duka wa’yannan ba, dole wani wajen ya kai ko ya kai kitchen.

 “Ka kai ragowar kicin ne?.” 

Na tambaye shi, muryata na rawa kamar wacca ta yi tseren gudu, ko dayake ba shakka tsere na yi, domin na yi tsere da zuciyata kafin bakina ya iya fito da wanann tambayar.

 “Ban ɗauke komai ba, ai aikin ne ko?.” 

Naji kakkausar muryarsa ta faɗa, zama na yi akan dinning ɗin, gaba ɗaya raina babu daɗi na rasa abinda ke mun daɗe. Muryar shi na juyo ya na cewa. 

“Me kike yi anan ne?.” 

Na goge ƙwallar da ta fito daga ido na ce. 

“Babu komai?.” 

“To tawo nan mana.” 

“Abincin zan ci.” 

Na faɗa ba tare da na taso ɗin ba. 

“Tom.” 

Kawai ya faɗa ya ci gaba da abinda yake, na tashi na shiga cikin kicin ɗin, ban masan me zan iya dafawa ba wanda zansa a cikina, ga yatsu na sai wani irin zugi suke yi mini kamar wacca na taɓa attaruhu. 

Haka nagama zagaye na a cikin kicin ɗin na fito zuwa falo, na bude firij na ɗauko biredi na dawo kan dining na haɗa da ragowar romon farfesun naman na ci. 

Bayan na kammala na ɗauke komai na kai kicin, na gyara wajen tsaf sannan na nufo shi zan zauna na huce gajiyar da take cin jikina. Sai dai ban kai ga ƙarasowa ba idanuna suka sauka kan abinda yake yi, ya zuge zif ɗin ɗaya daga cikin fulallukan kujera yana fito da katifar cikin yana gutsirawa a hankali, kamar ƙaramin yaro yana wasa, sai da na haɗiye wani abu a raina sannan na ce.

“Sardauna! Kujerar kake yagawa fa?"
 Na faɗa ina kallon katifar da yake gutsirawa, gabana yana faɗuwa ganin yadda yake ɓarnatar da kayan gidan namu.
Kallona ya yi sannan ya kalli abinda yake yi, sannan ya ce.

 “To kin barni nan ni kaɗai, ba dole na yi duk abinda zanyi ba dan ma banyi miki kuka ba.” 

Murmushi na yi sannan na zauna kusa dashi da faɗin.

“Abinci fa na ci.”

Cuno baki ya yi kamar ƙaramin yaro zaiyi kuka sannan ya ce. 

“To kuma sai ki bar mijin ki da yake sonki fiye da komai shi ka ɗai, babu abokin taya shi zama.” 

“To ai gani nan nazo.”


********
“Bangane abinda kika faɗa ba fa.” 
Na faɗa kaina na wani juyawa, ji nake kamar akan gaushin wuta nake zaune ba kujera ba. 
“Abinda kika yi ne ya dawo miki.”
Ta faɗa tana yi min wani irin kallo. 
“Wallahi bangane abinda kike nufi ba, abinda nasani ban taɓa shan wani abu da zai hanani ɗaukan ciki ba, hasali ma akwai wani likita da nake zuwa wajensa, kullum yana ce min mahaifata ta fara ƙwari, kuma bai taɓa yi min irin wannan zancen ba.” 
“Uhm, shi waye likitan?” 
“Sunan shi Dakta Ɗan Adala, kuma abokin miji na ne.” 
“Kina nufin da kanki baki taɓa shan wani abu ba da zai hanaki ɗaukan ciki ba wanda gashi ya haifar miki da lalacewar mahaifa, kuma tuntuni ba yanzu ba.” 
“Wallahi Allah ban taɓa sha ba.”
Na faɗa kaina yana wani irin juya min, jiri yana ɗibana duk da ina zaune.
Hannuna takama sannan ta ce. 
“Mrs Ta’ambo ki nutsu, ki saurareni.”
Kallonta na yi babbar macece, nasan tabbas ta haifeni ta haife Yayata ma. 
“Tom.” 
“Mijinki ya kuke dashi, ina nufin yanayin. Zamantakewar aurenku?”
Sai da na goge hawayen idona sannan na ce. 
“Komai daidai yake.” 
“Bai taɓa nuna miki ɓacin rai ko damuwa akan rashin haihuwa?” 
“Eyh… bai taɓa ba, shi da abokinsa suke kwantar min da hankali ma. Sai dai daga baya bayan ne ya fara nuna dumuwa akan rashin haihuwar, har takaishi ga ƙara aure.” 
“Hhhm, auren soyayya ne ko haɗin gida?” 
Ta tambaya, sai da na kalleta sannan na ce. 
“Soyayya ne.” 
“To akwai matsala gaskiyya, tabbas ko da saninki ko akasin haka, amma kin sha kwayar dake hana ɗaukan ciki kuma da alamu kindaɗe kina amfani da ita har aka kai ga wannan matakin.” 

********
Dum! Haka na ji zubar sassanyan ruwan a jikina, ban kai ga gama tantance ko mene ba na ji an ɗauke ni da wani azababben mari, da sauri na riƙe kuncina tare da ƙwalla uwar ƙara. 
“Ahhh.” 
Idanuna har wani dishi dishi suke, amma haka na iya ganesu yana tsaye ita kuma ta dafa kafaɗarsa hannunta riƙe da jug da alama ita ce mai watsa ruwan sanyin, shi kuma ya ɗaure fuska, wai ni ce yau Sardauna yake mari wannan wace irin rayuwa ce. 
“Na sha faɗa miki ki fita sabgar mata ta da abinda ke cikinta kin ƙi ko, wallahi Nana ina jiye miki ranar da zanyi miki Ɗan bara uban duka a gidannan, jaka kucaka.” 
Wani irin abu ya toshe mini ƙirji, na ji kamar na faɗi ko zan samu faɗuwar ta zama sanadiyar da zan rasa rayuwata baki ɗaya, rayuwar da ba ta da wani amfani, a yanzu ba wai juya min baya da sardauna ya yi ba ne yake damuna ba, takaicin da danasin biyewa Sardauna da na yi, na zaɓe shi na watsar da ‘yan uwana, na zaɓe shi na watsar da kowa, tabbas namiji ba Ɗan goyo ba ne, kuma duk wacca ta ɗauki miji uba zata mutu marainiya. 
“Na faɗa miki dai, jaka ballagaza da bata da ilimi.” 
Ya faɗa yana barin wajen, a take na tuna lokacin da Sardauna ya ce dani. 
“Nana, ina da arziƙin da zan riƙe ki bake kaɗai ba har da gidanku, muna da arziƙin da bazamu taɓa talauci ba, Nana a cikin gidan nan zaki zama kamar sarauniya ne, Nana bana son karatun boko nan, Nana bana son cuɗanya da maza, ina miki so mai tsanani, ina miki kishi mai zafi Nana dan Allah dan Annabi ki haƙura da karatun.” 
Wasu zafafan hawayene suka biyo kuncina, a fili na furta. 
“Allah Yana ji Yana gani.” 
“Kutumar uban can, Baby ta zageka, wai kaine shege.” 
Ni ban ma san tana wajen ba, dan ban kula da ita ba sai da na ji ta yi wannan maganar, ban kai ga gama kallonta ba na ji saukar wani marin a kunci na, tare da sa ƙafa ya kwarfeni na zube a ƙasa ya shiga duka na da hannu da ƙafa, tun ina ihu har na sauti ya daina fita. 
******
“Wannan ai yafi ƙarfinki Rawasiya, bama haɗi wallahi.”
Na ji muryar Malika ta faɗa, a take Amina Aminu ta cafe da cewa. 
“Ni ban ma yarda ba, gashi dai gani nake da idona, amma na kasa gasgatawa.” 
“Kinsan kuwa wane ne Fahad Ta’ambo?” 
Malaika ta faɗa, daidai kuma lokacin ya fara takawo kusa da mu, ni kam gaba ɗaya sai na ji maganganunsu sun tsayan a raina, ni kaina nasan tabbas wannan saurayin yafi ƙarfina, bazan taɓa samun wannan saurayin ba domin kuwa duk wani abu da ake nema ya haɗa. Kyau, kuɗi, Nasaba, gayu, ilimi da duk wani abu da ‘ya mace ke nema wajen datattacen Namiji. 
Gaba ɗaya daskarewa na yi na kasa motsi, kar na yaudari kaina Fahad ba tsarar aure na ba ne. 
“Yau ba magana ne, kin wane tsari ni da ido kamar yau kika fara kallona?” 
Ya faɗa daidai lokacin da ya iso, gaba ɗaya yau sai na rasa wannan yanayin da nake ji idan yana gabana, jikina sanyi ƙalau na ce da shi. 
“Ina wuni?” 
Kallona ya yi sannan ya kalli ƙawayena ya ce. 
“Baki da lafiya ne?” 
“A’a, ina da lafiya.” 
Na faɗa ina kallonsa.
“Uhm.” 
Ya faɗa yana taɓe baki irin bai damu ba. Ganin na yi shiru kusan minti biyar, kuma ban tafi ba ya sa shi cewa. 
“Ina so mu yi magana ranki ya daɗe, naga yau a saurauniyar ki kike.” 
Bin shi kawai na yi a baya, ƙawaye na dai suna bina da na mujiya. Har mu ka ƙarasaa bakin motarsa ina jin idanunsu akaina. 
“Me yake damunki?”
Ya faɗa yana kallona, girgiza kai na na yi sannan na ce. 
“Bakomai” 
“ƙawayenki ne?”
Na ɗaga sannan na ce. 
“Wai sun ce idan kai saurayi na ne yaudarata zaka yi ba zaka taɓa aurena ba. Sabida kafi ƙarfina.” 
“To ke me kika gani?” 
Ba tare da wani lissafi ba na ce. 
“Da gaske suke.” 
Ya yi murmushi sannan ya ce. 
“Rawasiya daman ni na ce saurayinki ne?” 
Na gwalalo ido waje sannan na ce. 
“Kasan suna na? Aina?” 
“Taambayar da na yi miki kenan?”
Na girgiza kai sannan na ce. 
“A’a da a’a.” 
“Mene a’a da a’a?” 
Ya tambayeni yana kallona. 
“Da ka ce tambayar da ka yi min kenan shine a’a ta farko, a’a ta biyu da ka ce daman ka ce kai saurayi na ne?” 
Murmushi ya yi sannan ya ce. 
“You’re very funny, I love it girl.” 
Na yi murmushi sannan ya ce. 
“Baki tambayeni me nake yi anan ba?”
A raina na ce. 
“Duk inda nake ganinka da na taɓa tambayarka me kake yi a wajen?” 
“Sabida yau wajenki na zo shi ya sa na tambayeki.” 
Na ji muryarshi ta katse min tunani na. 
“Shekararka nawa?”
Na tsince kaina da tambayarsa, sai da ya ƙare min kallo sannan ya ce. 
“Ashirin da shida.” 
Wani daɗi na ji ya ratsani, irin mijin da nake so. 
“Ke fa?” 
Na ji ya tambaya. 
“Goma sha bakwai da rabi.” 
“Ko ba rabi ba?.” 
Ya tambaya yana dariya.
“Yau na ganka da sauƙin kai, daman haka kake?” 
Na tambayeshi, sai dai ya yi dariya sannan ya ce. 
“Au da da zafin kai nake zuwa kenan?” 
“ƙawayena bari na tafi.” 
Na faɗa ina nuna masa su, nan take ya haɗe rai ya dawo asalin Ta’ambo da nasani. 
“Je ki.” 
Ya faɗa cikin wani irin amon murya, ba shiri na tsaya na kasa tafiya. 
“Je ki mana.” 
Ya faɗa yanzu muryarsa da alamun fusata. 
“Ka yi haƙuri.”
“What do you do? Kin nuna sun fini amfani da muhimmanci to sai me?” 
Gaba ɗaya jikina ya fara rawa, duk na rikice lokaci ɗaya, bakina har rawa yake na ƙara cewa. 
“Ba haka ba ne fa.” 
Bai ko kalleni ba ya shige mota ya tafi, na kusa minti biyu a tsaye sannan na juya ga su Malaika. 
“Ku zo mu tafi.” 
“Wallahi Nana ban yarda saurayinki ba ne sai yanzu.” 
Fauziyya ta faɗa bayan sun ƙaraso inda nake. 
“Ni har yanzu ma mamaki nake, kinsan su waye familyn Ta Ambo kuwa? Kaf jihar jigawa suna cikin manyan masu kuɗi guda biyar, yan kasuwa ne na gaske masu arziƙi, duk a turai suke rayuwarsu baki ɗaya, wannan ma kina ganinshi kinsan ba rayuwar nan ba ne, gashi duk ‘ya’yan attajirai suke aure.”
Tin da Malaika ta fara magana har ta dire idanuna na kanta, domin nasan gaskiyya take faɗa zalla ma kuwa. 
“Idan kuwa hakane tabbas wannan yafi ƙarfinki Nana, ina baki shawarar karki ɗaurawa kanki abinda ba zai ɗaure ba, kizo ki sha wahala a banza.” 
Fauziyya ta faɗa tana da fa ka faɗa ta, ni basu san abinda ke damuna ba wannan ba ne, fushin da ya yi ya tafi yabarno yafi komai ɗaga min hankali. 
‘Yanzu yaushe zan sake ganinsa?’ 
Na tambayi kaina sai ba mai bani amsa, tsoro na ɗaya kar ya yi dogon fushi, fata na dai Allah Ya kawo shi da wuri, sai dai fatan ba ai amso ba dan haka aka yi sati ɗaya babu shi babu alamunsa, duk na damu gashi ni irin mutanen na ce da ba su iya faɗar damuwarsu wa wani ba, sai dai mu bar abu a zuciya ya yi ta cinmu, ni kam sai dai aga ina ta rama duk ja zagwanye. Haka kuwa aka yi na yi ta faman rashin lafiya a tsaye babu zazzaɓi sai ciwon kai sama sama, tari da kuma ɗacin maƙwogwaro, haka na yi ta fama sati ɗaya sati biyu har sati uku, hankali Hajiya da Alhaji duka ya tashi, kowa yasan akwai abinda ke damuna amma nakasa faɗa. 

*****
Ban ce babu marubutan da suka fini ba, amma na sani cewa alƙalamina yana da wani irin salo na musamman wanda muddin ka fara karanta shi, ba za ka so ka ajiye ba. Kun saba gani na da salo mai ratsa jiki, kamar yadda muka yi a SAKATA kuma a wannan karon ma, na zo muku da abin da ya fi kowane lokaci.
Ina roƙonku da ku ba ni kyakkyawar shaida da yaƙini, ni kuma zan ba ku nishaɗi da darussan da kuke buƙata in sha Allahu.

TSARIN TAFIYA:
• Free Pages: Zai fara zuwa muku ranar juma’a 08/05/2026. 
• Book 1: Kyauta ne.
• Book 2 & 3: Paid ne 
• Farashi: #700 kacal sai dai akwai special offer, zaku iya biyan naira 500 daga yau har zuwa ranar da zamu kammala free pages daga nan zai koma asalin kuɗinsa 700 (Babu tsarin VIP, sai dai akwai Special Offer ga masu bibiyata a ArewaBooks, tsari na musamman gare ku.)
Kuna iya fara biyan kuɗin karatunku tun daga yau har zuwa ranar da za mu kammala free pages. Babu jira a cikin tsarina; cikin ƙankanin lokaci za mu kammala wannan labarin cikin ikon Allah.
• Asusun Banki: 8165383931
• Sunan Banki: OPay
• Suna: Sani Muhammad Lawan
• Shaidar Biya: Tura shaidar biya zuwa: ***.
'Yan kasuwa masu buƙatar tallata hajojinku a cikin wannan ƙayattacen labarin, kuna iya tuntuɓata kai tsaye ta wannan lambar: ***.
Nagode da soyayyarku da amincewarku akan rubutuna. Allah ya haɗamu a Aljanna Firdausi. Amin.

#SARTSE
#LabarinSoyayya
#ZamantakewarAure
#MugunMiji
#SayyidLegendspen

***