HADUWAR DARE

Chapter 1&2

by @meenatyandoma

*HAƊUWAR DARE*
             
©️Meenat A. 'Yandoma

MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION

Page 1&2
... Edo State. 
GRA Benin, Unguwa ce ta masu hannu da ƙumbar susa. Duk da duhun dare da ya fara hakan bai hana unguwar haskaka ba tamkar da safiya. Duk inda idanunka suka sauka gidaje ne na alfarma tsit! Babu surutu bare hayaniya, ko ina jami'an tsaro ne ke gudanar da aikinsu. Juyi take saman rafkeken gadon nata da ya gaji da haduwa. Kyakkyawa ajin farko kwance kanta ya kalli sama ta fada duniyar tunani ta yi zurfi a ciki. Gilmawar wani abu da gudu tamkar kyanwa ya sakata zabura. Doguwar ajiyar zuciya ta saki, tare da mikewa ta zauna. Wutar dakin ce ta fara fafarniya tamkar zata dauke. Da sauri ta rufe idonta domin In akwai abinda ta tsana bai wuce duhu ba. Jin wutar dakin ya dawo ya sakata bude ido a dan tsorace. Tafiya ta ji a cikin falonta alamun za a shigo daki. Gabanta ne ya yanke ya fadi zuciyarta ta karaya "wannan ba tafiyar Usman ba ce. Anya kuwa ba aljanu bane a cikin gidan nan?" Ganin bata da amsa ya sakata mikewa. Cikin sando ta rika tafiya har ta karasa bakin kofar. Sai dai wayam babu kowa " ta ya za a yi har Usman ya dawo ba tare da jin sa ba. Ko dai kun manta bakin kofar gidanku akwai mai gadi" wata zuciyar tayi saurin tunatar da ita. Ƙarar tsayuwar muto da taji ita ta kawo mata karshen tunanin da take yi. Kwankwasa kofar dakin ta ji yayi. Cikin farin ciki ta nufi kofar, sai dai Usman ta gani jingine da kofar yana faman sakar mata murmushi. Shigowa ya yi jikinsa sharkaf da ruwa. "Ruwa kuma? Yaushe aka yi ruwa naga jikinka a jike?" Ba tare da ya kallata ba ya bata amsa. "Inda naje ruwa akayi mana sosai, kune dai ba a yi ma ruwa ba." Wani iri ta ji Muryar Usman duk ta canza ta so yi masa magana, sai kuma ta tuna da ya ce ruwa aka yi masu don haka bakinta taja tayi shuru. Toilet da taga ya fada ya sakata bin bayansa...
Gudu ya ke shararawa saman titin tamkar zai tashi sama. Lokaci bayan lokaci sai ya kalli agogon dake hannunsa tare da sakin karamin tsaki, A rikice ya taka birki gabansa na dukan uku uku. Abin da ya ba shi mamaki shi ne tsaye take ko gezau bata yi ba. Sai ma ɗago idanuwa da ta yi ta kallesa. Ras! Gabansa ya yanke ya fadi, zai iya cewa tunda ya ke tsawon rayuwarsa bai taba yin tozali da kyakkyawar mace irinta ba. Kafin ya fara magana ji ya yi ta fara "malam mai mota zaka kadeni kuma ba zaka fito ka bani hakuri ba, ku fa dama ance wani lokacin mazan nan kun rena mace. " 
Tamkar sakarai haka ya saki baki yana kallonta. Hakika maganarta ko ince muryarta ta tafi da imaninsa abu tamkar ana busa sarewa. Ba tare da jiran amsarsa ba ta bude murfin motar ta shigo. Kallonsa da tayi shi ya saka shi jin tamkar ba a wannan duniyar ya keba. Lokaci daya ya ji wani abu na shiga jikinsa. "Kiyi hakuri ban kula ba. Ni a suwa In kade wannan kyakkyawar halitta, hukuncina da yayi tsauri da yawa"
Ya karasa maganar yana kallonta. "Kamar ka sani, kaf a cikin lamurran bana yafiya ko alama"
Ta karasa maganar idonta cikin nasa. "Amma kyakkyawa kamar ki ya kamata a ce tana tafiya domin irinku da yafiya aka sansu" "Ni ba haka nake ba kaima kadan ta hana ka amshi hukuncinka da ace ka kadeni da yanzu wani zancen ake yi" dariya ya yi jin abin da ta fada. "To kyakkyawa a yanzu ma za ki iya hukuntani Indai za ki huce. " Shuru ta yi tana kallon gefen hanya. "Ka tayar da mota muje" ta fada. "Mu je ina? Ai ba ki fadamin inda zan saukeki ba" ya karasa maganar ya na kallonta. "Kafin ka kai Gra Benin." 
"Eyee! Cewa za kiyi kusa da unguwarmu kike. Amma me ya fito dake cikin daren nan kyakkyawa irinki ai kamata ya yi a ce yanzu tana gida ta na bacci” 
“Hmm! Abij da ya fito da ni babbane. Kuma mu dare ai tamkar safiya ya ke a wurinmu” dariya ya kwashe da ita jin abin da ta fada. "Ko dai ke ma danginmu ce?" Murmushi ita ma tayi ba tare da ta ce komai ba. "Sai faman zuba nake yi ba tare da kin fadamin sunanki ba. Ya kamata in San sunanki KO don gobe In dawo bayar da hakuri."
"Suna na ba shi da daɗi, hasalima kaf sunan mutanen gidanmu babu dadin ji"
"Sai kuma kika hadu da wanda tun asali yana kaunar sunayen da nasu da dadi. Duk wani abu da bai burge mutane ni shi nake so, don haka fadi kada kiji kin damu"
"Zulfaidah" ta karasa maganar tare da kallon sa. "Wow wannan suna ai mai dadi ne, tunda nake ban taba jin sunan yan gayu kamarsa ba. Gaskiya sunanki ya dace da ke ko da ya ke ni ba ki bukaci jin nawa sunan ba ni ne dai keta faman zakewa tamkar kwantar da bubu dadi" "Usman" ya ji ta furta. Babban abin da ya ba shi mamaki ina ta san sunansa? "Nan zaka tsaya." Ya ji ta fada. "Kafin ya yi wata magana ta bude kofa ta fice daga motar. Da sauri ya bi bayanta, "haba ke kuwa ina kika san sunana. Kawai sai ki fice ko bankwana ba kiyi mini ba" "lokacin tambayoyinka ya kare don haka yanzu gida zan shige"
"To ki taimaka min da Number ki saboda gobe idan zan shigo sai In kiraki in duba jikinki"
"Ka bani Number Ka ni zan kira Ka"
"To ai banga waya a hannunki ba"
"Eh zan haddace ne in na shiga gida sai In kiraka" Bai yi mata gardama ba domin ya fahimci ta kosa ta shiga gida. Numberta ya fiddo da ke rubuce a jikin karamin kati ya mika mata. “Kada ka zo da safe ko da rana, ba a gani na sai da dare” tana kaiwa nan bata jira me zai fada ba ta shige gidan. 
Usman da ke tsaye tamkar an dasa shi murmushi yayi, sai dai abin da ya ba shi mamaki tunda yake bin hanyar bai taba ganin gidan nan ba. Ga shi dai gidaje duk da hasken wutar Nepa amma shi duhu ne baka shaida yadda kalar gidan take. Kukan kare da ya ji kusa da shi ya saka shi zabura.
Wani irin dakeken karene a tarihin rayuwarsa bai taba ganin irinsa ba. Babban abin da ya tayar masa da hankali idanun karen irin na mutane ga wani irin gurnani da yake yi masa. Ba shiri ya fada mota ya tayar. Hon daya ya yi mai gadi ya bude. Zainab da fitowar su kenan daga wanka ita da Usman tana tsane gashin kanta da sauri ta mike rike da towel din dake daure a kirjinta. Ta nufi kofa, key din dake hannunsa ya saka ya bude falon. Mutuwar tsaye Zainab ta yi ganin Usman ya shigo ya na mata murmushi. "In wannan Usman ne, Wanda ta baro ciki waye?"
Nuna shi take da yatsa cikin tashin hankali, shi kuwa da sauri ya yi kanta ganin irin kallon da take yi masa. Sai dai kafin ya karasa ta yanke jiki ta fadi....


Meenat A. 'Yandoma
***


***