HADUWAR DARE

Chapter 3&4

by @meenatyandoma

***

BARKANMU DA DARE IN SHAA ALLAH GOBE ZAMU FARA SABON LITTAFI

PLS MU BI DOKA BANDA TURE-TUREN ABUBUWAN DA BASU DACE BA

*HAƊUWAR DARE*

©️Meenat A. 'Yandoma

MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION

Page 3&4
...Da gaske fa Zainab ta Suma. Umar ya fada a cikin zuciyarsa. Rungumota ya yi tare girgixata, Amma ina ta yi doguwar Suma. Ruwa ya dauko a firiza ya Fara shafa Mata a hankali ta ja ajiyar zuciya. Sake firgita tayi ta cacumoshi tare da kulle idonta gam! "Umar aljanu wallahi aljanu ne na gani." Ta karasa maganar tare da rirrikesa. Umar kuwa abin tsoro da mamaki ya Fara ba Shi. "Baby wane irin aljanu kuma?KO dai mafarki kika yi bude idonki ki gani Umar mijinki ne tsaye a gabanki" duk yadda ya so ya taso da ita abin ya ci tura Domin ta ki dago da kanta kwata-kwata. "Zainab" ya Kira sunanta da siririyar murya. Dago fuskarta da ta hade da hawaye da majina tayi. "Subhanallahi! Da gaske Kuka kike yi?" "Ka kasa yarda da ni aljanu da gani da idonta. Bayan yafiyarka gida aka kwankwasa mini na bude daki da idona na ga Ka shigo dakin nan. Cemin kayi ruwa aka yi a waje Shi yasa Ka jiki. Umar tare da muka yi wanka fitowar da zanyi na ga kuma Ka shigo" "what! Wanka tare da wani Zainab! KO daimugun mafarki kika yi ne, wait Bari in tambayi security in ji waye ya shigo da bani nan" kokarin ba Shi amsa take Amma ina mikewa ya yi Bata bata lokaci ba ta fizgo hijabin ta take masa Baya. A binda ya Kara tsoratar da ita Shi ne yadda security din ke fadar babu Wanda ya shigo tun fitar Mai gidan. "Ka dai tuna wallahi ya shigokai ne ma Ka bude kofar da hannunka" ta karasa maganar tamkar zata fashe da kuka. "Sorry madam babu Wanda ya shigo, bayan ni unguwar nan cike take da jami'an tsaro KO ina KO kuntsu indai ansan Mai cutarwa ne ba za a Bari ya shigo gidan nan ba" Security din ya fada. Ganin zata yi magana hannunta ya ja suka shiga ciki "Umar na hauka ce na kasa game komai, KO dai kwalwata ta tabu ne?" "Aa Baby kina cikin hayyacinki kila dai mugun mafarki kika yi kuma in Shaa Allah ba zaki Kara yin irinsa ba" sai da Umar ya tabbatar da ya kwantar Mata da hankalin kafin ya Nemi abinda ya samu ya sha. Kula da yayi har yanzu Zainab a tsorace take ya saka ya kashe masu wutar dakin. Bacci ya ki daukar Zainab har yanzu sai faman mutsuniya take yi. Wani irin azababben fitsari ta ji ya kamata ba Shiri ta ruga da gudu toilet din dakin. Abin da ya bata mamaki tana shiga dif taji fitsarin ya dauke mata. Yunkurin fitowa da tayi ji tayi kamar an daure Mata kafa. Iyakar kokarinta tayi Amma ta kasa daga kafarta, mirror da ke gabanta taji motsi a samanshi. Tsoro Shi ya hanata kallonsa sai dai da karfin tsiya ta yi an kulle kofar. Ba Shiri ta kalli mirror, sai dai lokaci Daya jikinta ya dauki kyarma sakamakon mace data hango tsaye a cikin madubi tana Mata murmushi bakinta sai faman digar da jini ya ke. "Lokacinki ya kare saura nawa zaiiinabbb" wata irin rikitacciyar murya ta fada. Da karfin tsiya aka juyi da ita sulalewa tayi kasa. Daya ta koma sai Zainab ta fice ta nufi wurin Umar.
Umar kuwa bayan asuba tayi ya jima ya jiran Zainab ta fito daga toilet Amma shuru. Kutsa kai ya yi nan yayi tozali da ita kwance a kasa

"Zainab! Me kike yi a cikin toilet?" Umar ya fada lokacin da ya tallafi kanta. Lumsassun idanunta ta bude tana mai saukesu a kan Umar. "Ka kai ni gidanmu. Umar mutuwa zanyi wallahi na gaji" 
"Kin gaji kuma Baby! KO dai wani laifi nayi miki ban sani ba?" da kyar ta mike zaune. "Ni ma ban san me ya sameni ba tun jiya tsakar dare da na shigo toilet domin yin fitsari daga nan ban san me ya faru ba. Umar alamu sun nuna a cikin bayan gidan nan kwana” kallo mai cike da ma’anoni da dama ya ke binta da shi. “Ban fahimci a cikin toilet kika kwana ba, ko dai kin fara shaye-shaye ne ban sani ba?” Rass! Gabanta ya yanke ya fadi. “Shaye-shaye Umar? Ni ce ke shaye-shaye? “ “kwarai kuwa Zainab! In ba shaye-shaye ba ta yaya za ki rika yi min abubuwa tun jiya har yau muna abu daya kamar wasan yara, ita wadda na kwana da ita a gado daya kina nufin aljana ce ko kuma ni ne makaho?” 
Duk da jikinta babu kwari haka ta mike tare da jifarsa da wani irin kallo wanda shi kansa sai da ya shaki zallar mamaki. “Ka fadi duk abin da zaka fada, amma ni nasan bada ni ka kwana ba wata kila kuma kai da wata can ne kuka kwana a cikin dakin ban sani ba?” 
“Whats! “ Usman ya fada da karfi. “Me kike nufi da wata ce na kawo gidan nan”
“Umar ina na sanar maka? Ina nan cikin matsala da tashin hankali kana nan kana sharholiyarka da wata. Wallahi ban taba tunanin zaka yi mini haka ba, Umar ka cuceni” lafiyayyan marin da ya dauketa da shi ne ya saka ji da ganinta daukewa ta wucin gadi. Lokaci daya jijiyoyin kansa suka tashi. "Zainab! Yau ni ne kike kira da Mazinaci? Dama sakayyar da zaki yimin kenan ta aurenmu. Ni za ki shirya ma wasan kwaikwayo kina neman ki ɓullo da sabon tashin hankali a tsakaninmu?" Kukan da take ta kasa furta ko da kalma daya ce ga hannunta dake dafe da kumatu. "Ni ka mara a kan gaskiya ta? Ni Umar?" Ta karasa maganar tana cizgar kuka. Bai saurareta ba haka ya fice ko alwallar bai yi ba ya nufi masallaci. Zaman dirshan tayi a saman gadon tana cizgar kuka. Ya zama dole a yau ba sai gobe ba zata tattare kayanta ta koma gidansu, Umar mutumin da ta so tamkar ranta a cikin rayuwarta yau shi ne ke daga hannu ya na dauketa da mari. Sake fashewa da kuka ta yi a karo na ba adadi. Mikewa ta yi ta cika karamin akwatinta ta haɗa kaya duk da asuba ce haka ta yi sallar asuba ta fito. Mai gadinsu yayi tambayar duniya amma kalma daya ta kasa bashi sai faman jifarsa da kallon banza take, ba arziki ya bude mata get ta fice. Bayan su umar sun gama sallah, samun kansa ya yi sam baya bukatar komawa cikin gidan. Ba shi ya koma ba sai da garin Allah ya washe tara da wani abu. Kallon da security din ya yi masa ya tabbatar mai da akwai matsala, gidan ya kutsa kai sai dai tun daga falo ya tabbatar da Zainab bata nan. Rai a matukar bace ya tunkari security din. “ina matar gidan nan ta tafi ?" 
"Sorry sir! Gani na yi bani da hurumin dakatar da ita shi ya saka na barta ta tafi. " Rai a matukar bace Umar ya canza kaya ko breakfast Bai yi ba ya fice. Kunar zuci ya ke ji matuka, bai taba samun matsala da matarsa irin haka ba sai jiya. Tunaninsa ne ya kawo karshe sakamakon Zainab da ya hango zaune a cikin motar wani sai faman dariya suke. Murza idanuwansu ya yi ko mafarki ya ke sai dai har yanzu ita ce, bai bata lokaci ba ya bi bayansu a guje...

Meenat A. 'Yandoma