HADUWAR DARE

Chapter 5&6

by @meenatyandoma

*HAƊUWAR DARE*

Meenat A. 'Yandoma

***


MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION

Page 5&6
...A guje ya ke bin bayan motar don kada su bace masa amma ina, kafin ya ankara sun bacewa ganinsa. A rikice ya dauki hanyar gidansu Zainab. 
Zainab Kuwa tun bayan data shiga cikin gidan take faman cizgar kuka tamkar ranta zai fita, tambayar duniya anyi amma ta kasa magana. Kaka kuwa duk tafi kowa rudewa domin Zainab ita ce Auta a cikin jikokin ta, soyayyar duniya kaf ta ɗorawa Zainab. "Tunda ba za kiyi magana ba shi mijin  aki bari mu kira shi ya zo da kansa" Umma ta fada rai a matukar bace. "Aa kada kiyi saurin kiransa. Kika sani ko cutar mini jikalliya ya yi domin da ganin wannan kukan da take yi na wanda aka zalumta ne. Ke kuma na ga sai faman yi mata fada kike kina kokarin bata mini rai, ni fa ba don nasan ke ce kika haifi Zainab BA da sai In CE musanyarta aka miki a asibiti. Kinbi duk kin takurawa yarinya" ta karasa magana a fusace. Inda sabo Umma ta saba da halin surukarta, idan ta ce ma zata tanka to ranta ne zai baci. “Ubangiji ya baki hakuri" Umma ta fada tare da jan bakinta ta yi shuru. "Amin idan da gaske kike yi. Jikalliya za ki iya fadar abin da ya yi miki a nan ko kuma mu tashi mu koma daki, kada waccan matar ta rika jefa miki kallon da zai saka ki kasa magana"
"Kaka marina ya yi" ta karasa maganar tana mai fadawa a jikin kaka. Dafe kirji Kaka tayi tare da yin wata iriyar zabura "mari kuma jikalliya! Yaushe Umar ya samu wuyansa ya yi kauri har da zai daga hannu ya tsinke mini Ke da mari? Kai ba zata saɓu ba, bindiga a ruwa. Ke je kira mini ɗana" Ta karasa maganar tare da kallon Umma. Mikewa Umma ta yi bata ce uffan ba domin sanin hali ya fi sanin kama. Ko da ta shiga dakin kwance ya ke yana bacci amma ya zame mata dole ta tayar da shi, in ba haka ba daga ita har shi yau sai sun gane shayi ruwa ne. "Alhaji!" Umma ta kira sunansa a hankali. "Mikewa yayi zaune da alamun bacci bai gama sakinsa ba"
"Akwai matsala! Amma don Allah kada ka boyewa Hajiya"
"Wace irin matsala?"
Ajiyar zuciya Umma ta sauke. "Zainab ce suka samu sabani da Umar har ta kai ga ya mareta. Hajiya na can ta kasa ta tsare bata ji laifin da Zainab ta yi masa ba har ta hau yanke hukunci ba ta dauki laifi ta ɗora masa"
"Subhanallah! Hajiya sai rarrashi. Tashi mu je don In ta ga mun jima ba mu fito ba nan ma wata masifar ce ta daban"
Hajiya na hango su ta fara magana tun kafin su zauna. "Ya na ga fuskarka ta canza Hadi! Ko wani abu ta karanta maka ne"
"Subhanallahi Hajiya. Me zata karanta mini ni Kuwa, cewa ta yi In zo kina kira"
"To yanzu na ji baka. Dama Zainaba ce ga ta nan mara kunyar yaron can ya sameta ya zazzabga mata mari tamkar ya samu baiwa"
"Amma Hajiya kin tambayeta kinji laifin da tayi masa. Na san bata da kunya wani sa'in ita ma da laifinta yadda Umar ke kaunar yarinyar nan har ta kai su ga ya sameta ya daka" Ya karasa maganar tare da aikawa Zainab Kallon tuhuma.
“Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun! Shi kenan za ku kashe ni da bakin ciki. Hawan jini na ya motsa, da ma ni nasan baku daukeni a bakin komai  ba. Yanzu karya jikalliya ke yi maka. Tabbas hawan jini zai kasheni shi kenan ya taso mini da ciwo na" Kaka ta karasa maganar tare da mimmikewa ta sulale daga saman kujerar tamkar mai aljanu ta samu ido ta kulle gam. "Subhanallahi! Hajiya ki rufa mana asiri za a yi yadda kike so mun tuba" Jin abin da Hadi ya fada ya sakata bude ido daya ta kallesa "za a yi abin da nake so da gaske?"
"Eh za a yi Hajiya ki taimaka ki mike"
"To a nemomin yaron nan kuma Kada a sake a tauyewa yarinya hakkinta. Idan ya zo a Bari kowa ya Fadi abinda ke bakinsa, dudu auren yau watansu shida Amma har ya Fara Kai hannu a jikin yarinya. To ba zai yiwu ba ya sakamin Jikalliya bin hanya da wannan uwar safiya haka" ta karasa maganar tare da kallon Hadi. Sunkuyar da kansa yayi kasa, inda sabo ya ci a ce ya Saba da halin HAJIYA KO ya ki KO ya so yi Mata biyayya ya zame masa dole. "Ina magana Ka yi shuru tamkar ina magana da dutse? Shi Kenan na gane nufinku Kai da matar Ka ba Ku da wani buri da ya wuce Ku doramin hawan jini in fadi in mutu Ku Sami damar da za Ku ci gaba da azabtar da Jikalliya. Wayyo Allah zuciyata zafi jini na zai hau" ta karasa maganar tana dafe zuciya. "HAJIYA don girman Allah kiyi hakuri ki mike, ya za a yi muyi Miki fatan mutuwa, zamu yi duk yadda kike so yanzu Bari in leka tsakar gidan nan naji alamun tsayuwat mota wata kilama Usman din ne" 
"Yi sauri Ka duba ja'irin yaro zai gamu da ni ne" Bai ce Mata uffan ba ya Mike. Umma dake gefe ita ma mikewa ta yi. "Ina za ki je? Wato ga shasha na magana duk kun tarwatse kun bani wuri KO?" "Ubangiji ya baki hakuri. Ni ba haka nake nufi ba " ta karasa maganar tare da dawowa ta zauna. Bayan Alhaji Hadi ya fita a tsakar gida ya tarar da Usman da ke tsaye ya na faman rarraba idanu. Bayan sun gaisa samun kansa ya yi da kasa magana sai faman Sosa keya da yake yi. "Usman ga dukkan alamu babu lafiya KO?"
"Eh Daddy! Zainab ce, yanzu haka a motar wani na ganta Shi ya sa na yi saurin zuwa gidan nan. Saboda ni lokacin da na bi bayansa bat! Suka ba ce mini"
"Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun! Da yaushe haka ta faru Domin Zainab tayi awa Daya a cikin gidan nan" da sauri ya kalli Daddy "awa Daya kuma?" 
"Kwarai kuwa zata ma iya fin haka a cikin gidan nan. Shin ko dai wata CE Ka gani a wajen?" Shuru Usman ya yi Domin wannan al'amari ya daure masa kai. Yanzu fa ya ganta to yaushe har ya zo gida haka? Kai tsaye falon suka shiga KO Zama Kaka bata Bari ya yi ba ta Fara masifa. Da kyar da jibin goshi Alhaji Hadi ya shawo kanta ta yi shuru. "Allah bazan koma ba sai dai ya sakeni ya auri yar iskar da suka kwana a tare " Zainab ta fada tana Shirin kuka. "Kiyi mana shuru ko kuma inyi kasa-kasa da ke. AI kema da naki laifin motar waye kika shiga har mijinki ya ganki ?" Fiddo idanuwa Zainab ta yi cike da mamaki. "Ni kuma Daddy?" 
"Kada Ku yarda da maganar yaron nan ya na fadar duk abinda ya zo bakinsa ne Domin ya kare kansa" cewar Kaka. "Aa Hajiya. Ni a yadda na fahimci abin da suke fada kamar wani bakin al'amari ne ke neman kusanto su. Akwai bukatar su dage da addu'a" "to duk da haka dai Jikalliya ba jaka ba ce ranar da Kara Bari hannunka ya Kara sauka a jikinta! Hukuma ce zata rabamu" 
"Ayi hakuri wannan ma kuskure ne haka ba zata sake faruwa ba." " Yawwa haka nake son ji. Sannan nan da kwana biyu zanzo gidan naku Inga yadda lamurra ke faruwa, don na fahimci sai ana saka maku Ido ana koya muku yadda zaman aure ya ke na fahimci ba Ku San komai ba" 
"HAJIYA ba sai kinje ba da sai ki barsu tunda Shi Usman ba yaro bane" Alhaji Hadi ya fada. "Sai na je in kuma zaka Hana ni ne Ka nunamin ba ISA ba bisimillah"
"Allah ya huci zuciyarki ni ban isa ba tuba nake"
Ganin Hajiya na neman tuburewa ya saka Usman daukar matarsa suka baro gidan. A hanya sai da ya tsaya yayi Mata siyayya kafin su wuce gidan tamkar ba Wadan nan masu fadan ba ne. Yinin ranar Usman Bai fita gida ba suna tare har magriba ta yi. Bayan ya fita sallar magrib Zainab na zaune a falo ta ji wayar Usman ta dauki ruri. Da farko bata dauka sai da ta ji an Kara Kira, dauka ta yi sai dai tun zuwanta duniya sai yau ta Fara ganin kalar wannan number ta Rasa ta wace kasa ce. Wata zuciyar ce ta turata a Kan ta dauka, kara wayar da ta yi a kunnuwan ta ji tayi ana wata iriyar rikitacciyar magana da muryoyi da dama tamkar ana dambe KO kuma fada. Ba Shiri tayi saki wayar tana Mai ja da Baya. Faduwar wayar ya yi daidai da fara fafarniyar wutar falon. Fankokin dake cikin falon wani irin gudu suka Fara lokaci Daya labulayen dake wajen suka Fara tashi Sama. Ga wani irin fafarniya da wutar dakin ta fara lokaci Daya...

Meenat A. Yandoma