FARASHIN IZZAH

Chapter 1

by @hauwajaywrites

*Bismillahir Rahmanir Rahim 🤍*

Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Maɗaukakin Sarki, Wanda Ya sake bani ikon dawowa da wani sabon labari.

Bayan irin ƙauna da goyon bayan da kuka nuna min a *Beyond The Veil*, kalmomi ba zasu isa su bayyana farin cikina ba. Na ji ku, na karɓi ƙaunarku, kuma hakan ne ya ƙarfafa ni na sake ɗaukar alƙalami domin kawo muku wani sabon tafiya.

Ina fatan wannan sabon labarin zai samu karɓuwa a zuciyoyinku kamar yadda na baya ya samu ko ma fiye da haka. Domin na rubuta shi ne da zuciya, da ji, da kuma fata cewa zai taɓa wani ɓangare na rayuwarku.

Ku kasance tare da ni a wannan tafiya…
Domin wannan ba kawai labari bane rayuwa ce, darasi ne, da kuma wani ɓoyayyen sirri da zai bayyana a hankali.

Nagode sosai da kasancewarku tare da ni. 🤍

Jiddatulkhayr writes taku ce✍️




Tik... tik... tik...

Ƙarar agogon ɗakin ce kaɗai ke ratsa shirun gidan, tana sanar da cikar ƙarfe 12:00 na dare

A daidai wannan lokacin ne ta firgita daga zurfin tunanin da ta nutse a ciki, kamar wacce aka taso daga wani mafarki mai nauyi. A hankali ta ɗago kai, idanunta suka sauka kan agogon dake jikin bango.

Ganin lokacin ya sanya zuciyarta yin wani irin nauyi, kafin ma ta ankara, hawayen da suka cika idanunta suka gangaro a hankali, suna bin kumatunta kamar an kunna pampo

Ta miƙe a nutse, ta nufi window ɗin parlom. Hannunta ta kai ga curtain ɗin, ta ja shi gefe kaɗan. Duk da duhun dare, hasken fitilun compound ɗin ya watsa wani irin haske mai ɗaukar ido, har zaka yi zaton ba dare ba ne. Gidan ya cika da tsari da kyau, amma zuciyarta kuwa cike take da wani irin duhu.

Ta janye kanta daga window ɗin, ta juya zuwa stairs. A hankali take taka su kamar mai tsoron kada kowanne motsi ya fallasa wani sirri da take ɓoyewa a ranta.

Da ta iso ƙofar ɗakinta, ta kama handle ɗin a hankali, ta murɗa. Kafin ta shiga, ta tsaya cak ta juya zuwa babban ɗakin da ke opposite nata... ta tsaya na ɗan lokaci, kamar mai son tuna wani abu amma sai ta girgiza kai ta shige nata ɗakin.

Ta cire kayan jikinta, ta daura towel, ta wuce toilet. Ba ta jima ba ta fito amma ko mai ba ta iya shafawa ba. Idan ka kalleta, zaka fahimci cewa jikinta yana nan tare da ita, amma zuciyarta tana can nesa, a wani duniyar da ba kowa zai iya kaiwa ba.

Turare kawai ta fesa, sannan ta saka kayan barcinta. Ta nufi gado, duk da cewa an gyara shi tsaf, sai da ta sake karkade shi kafin ta kwanta kamar mai neman nutsuwa da ba ta samu ba.

Addu'ar bacci ta yi, ta shafe jikinta, sannan ta ɗan ɗaga kai ta kalli agogo.

12:55am.

Ta lumshe idonta, ta daura hannunta a kirji, cikin murya mai rauni ta furta

"Ya Allah… ka sauƙaƙa min wannan halin da nake ciki..."

Hawaye suka sake zubo mata. Ta share su da sauri, sannan ta juya ta kwanta, ta rufe idonta.

Sai dai… baccin bai zo mata ba.

Kamar a mafarki, ta ji karar buɗe gate. Da sauri ta miƙe, ta nufi window ɗin ɗakin, ta ɗan yaye curtain.

Motarsa ce.

Wani murmushi ya kuɓuce mata, irin murmushin da ba shi da sauƙin fassara. Ba lallai ka fahimci me fuskanta take nufi ba

Ta sake rufe curtain ɗin, ta koma ta kwanta kamar ba komai.

A waje kuwa, ya fito daga motar tasa da nutsuwa irin ta masu iko. Tafiyarsa cike da kwarjini, yana nufar cikin gidan kamar wanda baya son taka kasa

Kai tsaye kitchen ya wuce. Ya ɗauki bottle na ruwa, ya buɗe, ya ɗora a bakinsa ya fara sha.

Kittt…

Ƙarar buɗe ƙofar bedroom ɗin ta ratsa kunnen ta.

Nan da nan ta rufe idonta, ta mayar da kanta pillow kamar mai barci da gaske.

Ya ajiye wayarsa a gefe, ya fara cire kayan jikinsa, sannan ya wuce toilet.

Yana shiga toilet, ta buɗe idonta a hankali. Ta tashi zaune, idanunta suka sauka kan wayarsa. Ta zuba mata ido kamar wacce take son ganin amsar wata tambaya da ke damunta.

Ba ta san tsawon lokacin da ta ɗauka a haka ba… sai jin motsinsa yana fitowa.

Da sauri ta koma ta kwanta, ta rufe idonta.

Ya tsaya gaban mirror, ya goge ruwan kansa. Daga nan ya wuce wardrobe, ya ɗauki pajamas, ya saka.

Sai ya nufi gadon.

Ya tsaya kallonta na ɗan lokaci… idanunsa suna nazari kamar yana neman fahimtar wani abu da bai bayyana ba.

Daga bisani ya kwanta.

Ba da jimawa ba, sautin numfashinsa ya canza alamar bacci ya ɗauke shi.

A hankali ta buɗe idonta.

Ta miƙe zaune.

Idanunta suka sauka kansa… sannan ta taɓe baki

A haka bacci ya kwashe ta. Washegari da asuba, karan alarm ɗinta ya tashe ta. Ta mike tana murza idanunta, sannan a hankali ta furta:

Bismillahil ladhi ahyana ba'da ma amatana wa ilayka an-nushur.

Bayan ta sauke kafafunta kasa, ta wuce toilet ta yi alwala. Bayan ta fito, ta shimfida sallaya sannan ta fara raka'atainin fajr. Tana zaune, ta ji motsin sa ya tashi, ya wuce toilet yana fitowa kuma ya nufi kofa. Jin an tada sallah, ta tayar da sallah. Bayan ta idar, har 6:30 tana kan sallayan tana addu'a, sannan ta mike ta wuce kitchen.

Tunanin abincin da zata ɗaura ya fara zuwa mata, ta fara fere potatoes. Can ta ji an buɗe kofar kitchen, sai ta ji ya shigo. A kofar kitchen ɗin ya tsaya; ko ɗaga kai bata yi ba, balle ta gaishe shi. Shi kuma ya yi folding hannayensa yana kallon ikon Allah, kamar mai tsoron magana, ya ce:

"Ba a koya miki gaisuwa ba ne a gidan naku?"

Itama, kamar ba zata tanka masa ba, ta buɗe baki a hankali ta ce:

''Ai kaima kasan gidanmu akwai tarbiyya."

Wani kallo ya watsa mata, yace:

"Me kike nufi Zahra?"

A takaice ya ce "Ka tsargu ne?"

Ya juya ya bar bakin kofar, kamar wanda zai fire sama, ya wuce dakinsa.

Ta gama breakfast, ta je ta jera a dining, ta wuce ɗakinta ta yi wanka ta fito. Ya yi daidai da lokacin da shima ya fito, hanyar kofar parlorn. Ta kalli dining kamar ba a taba ba, ta ce:

"Haka zaka fita ba tare da kayi breakfast ba?'' Ko kallonta bai yi ba yana gyara briefcase ɗinsa

Ya fita ba tare da ya kula ta ba.

Zama ta yi ba tare da ta shirya ba. Ta yi tagumi tana kallon wani waje, zuciyarta cike da tunani wannan wace irin rayuwa ce ta fara?

A hankali ta lumshe idanunta, tana mamaki ko dama haka ne auren yake nufi?

Ta miƙe ta nufi dining. Ganin ko yunwar ma bata ji, yasa kawai ta zuba tea a cup ta fara sha. Bayan ta gama, ta ajiye cup ɗin, sannan ta koma ɗakinta. Ta fara tattare tattare, tayi shara, har da wanke toilet. Bayan ta gama, ta saka turaren wuta, nan da nan gidan ya cika da ƙamshi mai daɗi.

Ta ɗauki wayarta ta zauna bakin gado, sannan ta kwanta ta kunna data. Ta shiga Instagram, sai ta ga comments da DMs sun yi yawa. Har yanzu mutane suna taya ta murnar aure.

Wani ajiyar zuciya ta sauke.

Followers ɗinta sun ƙaru sosai saboda trending ɗin da ta yi a wannan watan. Ta shiga kallon yadda suka kai 1 million ta sauke ajiyar zuciya. 

Aka yi tagging ɗinta a wani post. Ta shiga account ɗin…

Sai ta ga shi ne ya yi posting video ɗinsu na after party tare da wani romantic caption.

Na tsawon minti biyar tana kallon caption ɗin

Amma ko like ɗin post bata yi ba… balle ta yi reply kamar yadda take yi a satin bikin.

A hankali ta kashe data, ta ajiye wayar a gefe.

Tunani ya sake lullube ta
Shin haka ne auren yake? Ko nata ne daban?

Me yasa yake nuna wa duniya kamar ita ce mace mafi sa'a… alhali…?

Hawayen da bata shirya ba suka cika idanunta, suka fara zubowa a hankali. A haka bacci ya kwashe ta.

Da misalin ƙarfe 11 na safe, vibration ɗin waya ya tashe ta. Ta ɗauka, Suhaima ce.

Ta murja idanunta, sannan ta amsa da sallama.

''Amarya, kar dai bacci kike na tashe ki?''

Zahra ta ce, "A'a… bansan sanda baccin ya kwashe ni ba. Shi kuma ya fara fita aiki tun jiya ai"

Suhaima ta ce, "Toh ki zo ki buɗe mana gate, muna ƙofar gida"

"Really?" Ta ce

Da sauri ta miƙe zaune, ta sauka ƙasa. Ta kusa isa gate ta haɗu da Mai gadi ya fito yana cewa zai buɗe gate ɗin ya ɗan shiga ban ɗaki be, amma ta ce "Na riga da na zo ai Baba"

Da ta buɗe gate, sai ta gansu tsaye kowannensu da murmushi, ta rungume su tana cewa, "Ku shigo ciki"

Kalle kallen gidan Saudat take yi ta kasan ido. Cike da fara'a Zahra ta kai su parlour

Suna shiga, Asiya ta ce "Lallai na tabbatar gidan Fatima-Zahra na zo. Ke da kamshi da tsafta, ba a raba ku. Ango dai ya yi sa'a"

Dariya suka yi gaba ɗaya.

Amma da Saudat tana shiga parlour ɗin… sai nan da nan fuskarta ta canza.

Zahra ta ce "Saudat, dama ke ce baki ga gidana ba ko? Banso bikin nan ya zo ba tare da ke ba"

Saudat kawai ta ce "It's fine"

Zahra ta yi shiru tana kallonta don amshinta ya bata mamaki

Suhaima ta ce "Matsalata da ke kenan. Ko ɗan rikicewa ba zaki yi ba? Ko baki kalli gidan da kyau bane? Kalli fah kamar ba'a kasar nan ba fah"

Ta ciro wayarta daga jaka ta ce "Na gani. Gidan ya yi kyau… saura kwanciyar hankali....."

Maganar ta tsaya a zuciyar Zahra, ta dinga ksllonta da mugun mamaki

Suhaima ta matsa kusa da Zahra tana shafa ta
''Zahra, kin yi kyau sosai… amma kin rame. Ko dai ciki ne?''

Nan take Saudat ta ɗago kai tana kallonta

Asiya ta ce, ''Nima abin da nake tunani kenan''

Zahra ta ɓata rai
''Ni dai babu wani ciki, yaushe aka yi auren da har ciki zai shiga" sai kuma tayi saurin canza maganar

''Ina kuka bar Firdausi?''

Asiya ta ce, ''Mama ce ba lafiya, shi yasa take tare da ita. Har ma ta sayar da wayarta fah"

Zahra ta ce cikin mamaki, "Kamar yaya? Har ta sayar da waya?"

Suhaima ta ce "Da alama jikin ya yi tsanani ne"

Zahra ta girgiza kai
"Ba zata iya gaya mana mu taimaka ba? Me amfanin zaman tare dan Allah?"

Suhaima ta ce, "Ai ɗawainiya…"

Zahra ta katse ta "No. Babu wani yawa"

Nan take ta ɗauki waya, ta yi transfer na 80k zuwa account ɗin Firdausi

Ta ɗaga kai ta ce
"Please, Suhaima ki biya gidansu ki gaya mata na tura mata kuɗi. Ta sayi waya ko ƙarama ce, sauran ta yi maganin Mama kafin nazo duba ta"

Suhaima ta gyada kai

Asiya ta ce "Allah sarki… kawa kamarki daban ce"

Suhaima ta ce "Wallahix

Zahra ta taɓa Saudat
"Lafiya kuwa? Na ganki shiru"

Ta ce "I'm fine"

Zahra ta ƙyale ta

Ta ce "Ku je kitchen ku yi girki mana"

Suhaima ta buɗe baki "Muna baki zaki bar mu mu yi girki?"

Zahra ta harare ta "ku ne baki?"

Asiya ta ce "Eh mana! Ke yaka mata ki dafa mana"

Zahra ta ce "Bana son jin ƙamshin abinci ne"

Dariya suka yi

Suhaima ta ce, "Toh ya tabbata ciki kike da shi!"

Amma Zahra bata kulasu ba, ta koma ta kwanta.

Suka nufi kitchen.

Saudat ma ta miƙe
"Ni zan tafi… ina da inda zan je"

Zahra ta kasa cewa komai dan ganin yadda ta canza

Da ta fita, Suhaima ta leƙo
"Kin gani ko? Zaki fara yarda da abin da na faɗa miki akanta''

Zahra ta ce "Ya isa. Ku je ku yi girkin, ni zan ɗan yi bacci"

Ba ta tashi ba sai bayan Azahar.

Su Asiya sun gama girki, suka ci, suka haɗa smoothie ma suka sha, suka mata wanke wanke

Bayan sallah ta sauko ta same su suna kallo.

Suka fara shirin tafiya.

A dai lokacin… aka buɗe ƙofar parlour

Sai ga Ibrahim ya shigo

Suhaima ta ce, ''Aaa, ashe ango ne!''

Ya zauna, suka gaisa cikin fara'a''

Zahra ta kasa ɗauke idonta akansa, yadda yake dariya yana nuna musu kulawa.

Bayan sun gama gaisawa suka ce zasu tafi

Ya ce, ''Da zuwana ne zaku tafi?''

Suhaima ta ce "A'a, dama mun shirya zamu tafi ne ka shigo"

Ya ciro kuɗi ya miƙa musu
"Ku yi TP toh"

Suhaima ta karɓa musu, suka yi godiya.

Zahra ta ce "Nagode. Ku gaida gida" suna murmushi suka yi sallama..

Bayan sun fita Asiya ta ce a hankali,
"Har yanzu bana son Ibrahim Khalil a matsayin mijin Zahra… amma tunda aure ya shiga, babu yadda muka iya"

Suhaima ta ce,
"Nima haka. Amma tunda na ga yana da kuɗi… na yi mata murna. Kar alherinta ya tafi a banza, Zahra deserve everything and more"

Kar a manta ayi following acc ɗina sannan ana danna star dan nasan labarin is giving or not