Chapter --- 10
Bismillahir Rahmanir Raheem.
****Namiji Ƙanin Ajali****
By
Amdeey Tejj d'Unique.
Page -- 10
Ƙurr nai masa da idanuna ina kallonshi,na kasa gane me yake nufi,sai kace ni na ɗaurawa mata ciwon ko kuma nike da alhakin bata lafiya,raina ya ɓaci wai ya yake min hakane me yasa yake son sai na kauce hanya dan na taimakeshi,idan wata hanyar ce da ba wannan ba da ko zaima silar kawo ƙarshen numfashina da zanyi,na sauke matsayina na biyoshi na rabu da kowa saboda dashi,yanzu kuma yace na rabu da Allah ma,anya kuwa Habibu yana...nayi saurin kauda tunanin dan a ganina yinsa ma saɓone,duk da raina ya ɓaci amma na kasa nunawa saina ɓige da lallaɓi "Habibu dan Allah kayi haƙuri kasan bazanyi abinda zai cutar da kai ba ko?"da irin waɗannan zantuka na samu na shawo kanshi har ya sakko amma firrr yace ba zamuje gidansu kawunshi ba,ƙarshe tashar muka koma muka samu wani bishiya muka kwanta ga garin lokacin zafine dama kuma duk wanda yasan Lafia yasan garin zafine,muna kwance yana daga akan abin kwanciyar da na shimfiɗa mana ni kuma jingina a jikin bishiyar,aka haskomu da wani tochi mai haske,na kai hannu na kare fuskata,
"Waye anan?"mukaji an tambaya da wani faffaɗan murya,cikina ya ɗuri ruwa dan tsoro har ya kamani dan nayi zaton irin ƴan iskan gari ne,naja ɗan ƙullin ladar kuɗin da ko ƙirgawa ba muyi ba,na maƙale shi jikina na rawa,Habibu ya miƙe ya zauna dani mai irin sambatun nanne idan su kaga abin tsoro da Allah kaɗai yasan yau me zance,muka miƙe tsaye,ya ƙaraso inda muke tsaye sannan bayan ya kashe tochin yace"su waye ku kuma daga ina?"
Habibu ne ya amsashi da"baƙine passengers ne da ɗazu muka sauka a nan to bamu san kowa anan ba,muna bara ne mara lafiya muke dashi za'ayiwa aiki shine muka zo neman taimako to bamu san kowa bane anan shiyasa muka dawo nan dan mu kwana"
Da farko mutumin bai yarda yace saimun fita yasha ganin irinmu da zasuyi ƙarya idan an barsu daga baya su zalunci mutane su gudu a neme su a rasa,sai da muka ta bashi hakuri koma ince nayita bashi hakuri dan Habibu har ya fara ƙufula daga ya barmu yace zai sa ido akanmu.
Yana barin wajen Habibu ya fara shirin dire mitanshi da bansan dalilin yinsa ba nayi saurin tareshi da"dan Allah Habibu Kayi haƙuri ka bar maganar nan dare yayi kuma ba'a gida mike ba,ga dare da ɗaukan magana"bai fasa ba saida yayi,da ƙyar dai na lallaɓeshi ya bar maganar ya kwanta bai jima ba bacci yayi gaba dashi wanda daga gani Kasan da gajiya,niko nakasa yin baccin nayi na zauna ina mishi fiffita saboda zafi ga sauro, haka na zauna na tsura kyakkyawar fuskarsa ido inayi ina murmushi kamar zautacciya tare da sauraron yadda zuciyata take bugawa da sonshi,koda yake na daɗe zaucewa akanshi,haka na zauna ina gadinshi tare da yi mishi fiffita har dare ya tsala baka jin komai sai wucewar ababen hawa lokaci-lokaci da kuma kukan dabbobi irinsu karnuka da sauransu,da zarar gyangyaɗi ya fara ɗaukana haka zan farka zumbur kamar an tsunguleni sai gefin asuba sarkin masu sata yace bai san wannan zance ba dan haka ya ɗaukeni a jingine da bishiyar dake bayana,motsin da najine yasa na farka kasancewar bani da nauyin bacci komai kashin motsi yakan sani in farka koda na buɗe idona kalli inda nakejin motsin Habibu ne ya tashi da alama lokacin sallah ne yayi,ya miƙe ganin yana shirin wucewa da alama bai lura dani yasa nace"ka tashi?" Ya Juyo "Ummm"kawai yace ya wuce ya nufi wajen da ake sallah, ajiyar zuciya na sauke na koma na jingina da jikin bishiyar na lumshe ido "gashi"naji an furta,na buɗe ido ruwa ne ya kawo min a buta na karɓa na mishi sannu "ki tashi kizo muje kiyi bawali kada wani ya faɗa kanki"murmushi na ɗanyi a raina nace ashe har yanzu yana kishina,na miƙe nabi bayanshi nina fara shiga shi kuma ya tsaya a waje yanayin bayin bazan iya tsuguno a wunba daga wani waje na samu na raɓe nayi uzuri na duk da ban samu yanda nake soba amma haka na lallaɓa,na fito ya shiga na jirashi shima bai daɗe ba ya fito muka tafi,ya nufi inda maza suke alwala kasancewar akwai passengers ɗin da suka kwana ciki harda mata nima na nufi inda suke nayi alwala na dawo na ɗauki dadduma na shimfida na tada sallah,koda na idar ban tashi ba nan zauna ina lazimi Habibu ma bai dawo ba dan dama ko a gida idan yaje sallar asuba baya dawowa sai gari yayi haske,yana dawowa muka karya da koko da ƙosai,duk sona da wanka haka na haƙura tun jiya banyi ba gaba ɗaya ma ƙyamar kaina nakeyi to ya zanyi,ba tare da ɓata lokaci ba muka dau hanya muka fara abinda ya kawo mu, yau ma tunda daga cikin tasha muka fara.
"Haula"naji ya kira sunana bayan mun fito daga cikin tashar,na juya na kalleshi na amsa"ya kamata mu raba hanya"ya faɗi bayan na amsa
"Kamar yah?"na tambayeshi
Ya bani amsa da"saboda sai nake ganin kamar kuɗin zaifi yawa idan mun raba hanu ni nayi nan ke kikayi can kinsan bahaushe yace hanu da yawa".
Nayi shiru na rasa abin faɗi,tabbas zancenshi gaskiya ne amma matsalar ni ba sanin gari nayi ba bansan kowa ba balle idan na tashi dawowa insan bani da matsala,to ba sai ki hau adaidaita sahu ba,wata zuciyar ta bani shawara,to kinsan sunan tashar ne?"wata zuciyar ta sake tambayata"To ba sai ki tambaya ba kafin ki tafi"ɗayar zuciyar ta sake bani amsa,na sauke ajiyar zuciya jin na samo mafita na kalleshi nace"to amma a ina zamu haɗu? kuma yaushe zaka dawo? dan insan sanda zan dawo"
"Anan mana inda muka rabu"ya bani amsa
"To shikenan sai ka dawo"
Ya ɗanyi murmushin da tunda yazo da batun da naƙi amincewa ban gani,ya riƙo hannu na ya kalleni da kyawawan idonsa masu burkita min lissafi yace"ki kula kanki kinji, Allah ya miki albarka nagode".
Wayyo Allah daɗi kasheni,ba zaku fahimci irin daɗin nakeji ba a duk lokacin da Habibu ya nuna min kulawa ba, sai macen da take son mijinta kamar dai ni,kuma take son a nuna mata soyayya irina......
Mu haɗu daku a page na gaba
Naku har Amdy Tejj
See You next time bye bye.....