TALES OF THE WAZEERIS

dahr zarah

by @surayyahms

12....🦋

Tales of the wazeeris

Bayan komi daya faru na haihuwar ya lafa yau da sassafe ummu salma tattara ahalinta da zimman wucewa gidansu na lagos dake acan ita take zama amma kafin nan tariga ta sanar da uwarjini cewa zasu saukane a kano suyi kwana biyu domin yin sallama da sarki abdallah wazeeri wanda hakan ya dan bawa mutanen gidan mamaki dan ansan bata kaunar zumunci da zaman lafiya amma sai ba a wani damu ba.

Cikin aminci yau ta rabu da kowa ita da ahalinta suka wuce masauratar kano aka musu tarban daraja da karaama duk dama ummu salma tana da giggiwa da mugun son girma..

koda tazo nan she was ignoring everything nd everyone sbd tsabar yadda take mugun ji dakanta ita watace.

chambar dansu sarki abdallah kawai taje ta nanike bata wani fiye kula gimbiya hajarat sakeena ba, tunda suka zauna afada acikin hikima ta sanar da mai martaba komi tare da nuna masa cewa tana sone su fara kallon jikarta leelah a matsayin potential wife na yarima shamsan daga jininsa in Allah ya so

shidai sarki abdallah bai amsa mata ba kuma bai mata musu ba dan yasan daga ya fadi wani magana saɓanin raayinta zata maida abun babba har ma ta nemi ta dora laifin akan matarsa.

farees salman kuwa cikin sauki ya nuna interest dinsa akan rihanna ta hanyar jan raayinta da abota dake ya lura batama da kawaye she is always alone nd shy, sai ya soma nuna mata kamar burgesa kawai takeyi har yake cemata yamata alkwari zaibita duk qasar da zataje dan tay karatu dan su dawo abokan juna sosai.

kwana biyu kacal sukayo a masarautar kano amma bai hana leelah ta nuna banzar halinta na lalaci, son jiki da sangarta ba, dan in ta kama bacci in har ba atasheta ba sai can karfe 12, ko 1 na rana take tashi gata da mugun son kwalliya kamar dawisu, duk dama a ahalinsu na waxeeris ba'a barin kowa yay shigar da ransa yakeso dolene kasaka kaya masu daraja da mutunci da zai killace maka dila sassan jiki stil komi na leelah extra ne.

idan gown zata saka dolene kaga tasaka maka exxergerated style me masifar tsada da kyau ko kuma wnda jelarsa yake jan qasa

akaro na farko bata wani samu fuska sosai awajen gimbiya hajarat sakeena ba saidai bata damu ba dan tasan she have enuf time to win her heart musmn idan tafara zuwa hutu gidan tasan dolene zasu saba da juna.

kwanansu biyu anan masarautar kano kafin nan sukayi bankwana da kowa suka wuce lagos abunsu.

kamar da wasa rayuwa yadawo dede ma kowa abubuwa na cigaba suna dada bunkasa..

acikin tharim vale daga uwarjini, sai nana A, sai shugaba imran wazeeri da matarsa ummu zulaiha da babbn yarsu mareeda da ake shirin turawa karatun tattalin arziki a kasar france

sai dattjiuwa nana hafsa datake kkrin kammala idda domin ta tattara komi nata ta koma wajen danta sarki abdallah acan kano, babban gidan mulki aka ware mata inda zata zauna a matsayin queen mother nacan masarautar dala.

Masarautar zamkora kuwa haryau kiciniyar kwace kanta take daga ragwabewar tattalin arziki da abinci da tsaro datake kkrin hadiyesu...

babu kwanciyar kullum sabbin dokokin tharim vale kara toshe musu hanyar arziki da abinci da tsaro yakeyi

ayayinda babban yarsu sarauniya Areesha tay xurfi wajen bincike akan irin kalar macen daya kamata ta zamo kafin ta zama matar yariman tharim vale.

sosai tafara tunanin amfani da mummunn halin rugujewar tattalin arziki dayake kkrin shigarsu nan tafara bude charity programs da porvety alleviations schemes da zatana saukaka ma talakawa da marasa karfi dan sunanta da labarinta yajeshi har fadar dala, at same time mhaifinta zai cigaba da mata kallon yarinyar kirki datake kkrin rufa masa asiri ta hanyar amfani da personal kudadenta da lokacinta wajen nuna tsantsar tausayi da kulawa ga talakawa da marasa karfi.

********

Dahrul zahra

marakkech

morocco.

Ranar da yarima shamsan yabar tharim vale ya isa ancestral private home dinsu mai suna dahrul zarah acikin qasar morocco kai tsaye masu kulawa sukazo akawuce dashi inda zai zauna batare da ɓata lokci ba.

Acikin dankareren mansion dinsu dake marrakech babban sashen da aka ware masa na daban ne inda babu wani ma'aikacin da yake yin gigi ko mafarkin giftawa ta wajen dayake saida cikakken shaidar izini.

Tun daga ranar farko, rayuwar Shamsan ta sauya gaba ɗaya dan ba wajen hutu ko zama bane wajen horone dn haka kowane motsinsa ana kallo, yadda yake tafiya, zama, magana… komai dai na nufin wani abu a idonsu.

snn ba aza a ba shi hutu sosai ba kuma bazaa abar shi yafara sabawa da uban kowa ba Domin a nan ana so aginashi ne bawai dan kawai yazama dan sarki ba saidai ya zama irin mutumin nan da maqiyansa bazasu iya rushe shi ba sbd tushen tarihi dukiya da matsayin tharim vale yana da bukatar kariya anan gaba sosai.

washe garin isowarsa dahrul zarah da safe aka kai shi babban harabar cikin gidan inda dattawansu na hukunci da horo suke zaune cikin nutsuwa.

ÆŠaya bayan É—aya ya gaishesu a matsayin tsari na iko saidai kowanne kallo da kuma tambaya dayake cinkaro dashi awajen kamar gwaji ne.

kowani irin yaro zai iya jin tsoro a irin wannan wuri Amma Shamsan bai nuna musu alaman haka ba saidai sosai ya fahimci abu É—aya, ya lura kamar anan wajen ba'a ba da girmamawa wa mutum kai tsaye ana neman girmane ta hanyar nitsuwa da kuma jajircewa.

dan haka yake lura da komi a zuciyarsa da kwakwalrsa msmn ma da kai tsaye suka bashi official title dinsa na SULTAN shamsan waxeeri ma'ana the crown prince,shi dan sarki ne amma wanda zaina daukar wasu hidimomin mulki, iko kasuwanci, siyasa, da kuma hukunci agefen mahaifinsa ana nufin bazai kuma sake amsa yarima kawai ba..

sbd sunan yarima yayi kadan yakuma kasa ma reponsiblitynsa.

dan karamin gwajin hutu aka bashi inda aka killace shi awajen da babu kowa he had just few servants to communicate with, Ba a barkowa yazo kusa dashi ba har Saida ya dan fahimce kanshi anan snn aka tabbata a shirye yake babu kewan gida ko tsoro a yanayinsa sai snn aka tsara masa abubuwan da zainayi kowani rana

tun daga ranar farawa rayuwar Shamsan ta sauya gaba ɗaya anan dahrul zahra aka fara masa darasinsa na farko wato tarihi na asalin Gado Ana koya masa zurfin tarihin zuriyarsu ta waxeeris, yaƙeyaƙe,yarjejeniyoyi, da yadda aka kafa iko da ƙarfin mulkinsu.

wani ranar kuma sai a koya masa dabarun Sarauta kamar Yadda ake magana da iko da yadda ake sarrafa taro, da yadda ake iya ɓoye rauni a fuska ko agabn maqiya.

shiyasa dolene saida uwarjini tabar tharim vale tazo nan dahrul zahra dakanta tadan yi musu sati biyu sabida da akwai abubuwa da dayawa wanda dole itace dakanta zatazo ta koya masa game da tarihin zuriarsu musnm irin abubuwa da yawa wanda taso ace ya iya ma tsafi da kuma wasu wanda takeso ya musu kallo da idon basira.

sati biyu tay anan tare dashi masu kyau har sai bayan komawarta tharim vale ranar da dare aka wuce dashi wani waje waishi yankin FES, Tsohon birni ne sosai acikin moroco da tasamu waje a tarihi tana da wasu sirrika acikinta

dan anan garin ne kawai ake koya musu hidden knowledge kai tsaye daga bakin old scholars, wanda sune zasu bashi asalin Ilmi arabi da na boko da Sirrin Ancient Power na zuriarsa wanda zaina amfani dasu wajen shawo kan duk wani abuna barazana da zai tunkarosu nan gaba

dakin dayake kwana anan Fes azagaye yake da wani irin Rare herb ana cemai flower of memory it is Said to heighten pattern nd recognition speed ana shukawa domin zallan royal heirs ne na ahalin jinin wazeeris ayayinda sukenan wajen training phases dinsu.

kowani safe za'a bashi ganyen mint da apple as meal staters dinsa, awajen Study sesssion dinsa kuma green tea ne da almonds wata rana kuma sage tea ko sidr da honey ko black grapes ko zallan olive da figs kominsa daga abubuwane da suke kara kaifi da karfin jiki da kuma boostin mmry da kuzarin kwalwalwa

Littattafan da yake karantawa Ba a bar masa kowani tarukuce ya karanta ba An zaɓa masa Littafan siyasa, dabarun sarauta, yaƙi, da mulki,Tarihin dauloli yadda suka tashi da yadda suka faɗi, da psychology,manipulation, negotiation,sau ɗaya kawai yake da buƙatar karanta book sai kaga ya haddace

saidai Amma abin da ya fi nauyi a horonsa shine Addini da ilimin

Qur'an dan ba karatum kawai bane akeso yay ana bukatan ya fahimci abubuwa dayawa daga rayuwar Manzon Allah ï·º da yadda ake yanke hukunci da adalci anan

Aka koya masa cewa ba'a mulki da iko sai da tsoron Allah.

kafin yaci wata hudu anan Fes kusan dukan Malamansa sun lura da abu ɗaya shamsan baya maimaita kalma kokaga yay tambaya sau biyu, snn ba ya mantuwa cikin sauƙi, baya kuma karatu cikin gaggawa amma yana da matukar fahimta maizurfi Wani lokaci kafin agama bayani

yariga ya fahimci in da aka dosa he had dis photographic memory with a hypercognitive mind hakan yana nufin yana iya koyan abu extremly fast, zai iya haddace complex systems snn zai iya processing many possibilities at once almost like parallel thinking.

wann special baiwar tasa yasa akasauya tsarukan horonsa dayawa abubuwnda zaiyisu a shekara guda anga yana iyayinsa a watanni, dan haka suka yanke hukunci gajararta lokacin yimasa horo dan nan da shekara biyu suke so samu a turasa yaje United states yay aiki ya kara nisan karatu.

universal languages shida sune abu na karshe da aka koya masa fannin ilimi.

yaren larabci harshen addininsa, da english domin diplomaciya sai yarukan french da spanish domin siyasa da hulda da al'adu da kasashen yamma, sai turkiyanci don fahmtr tsofin daulali akarshe aka koyamai mandarin domin kasuwanci da duniya,wanda acikin watanni suma ya iyasu sosai after many days and sleepless nights of practise nd training

bayan nan aka fara hade mai schedules dinsa da Horar da Jiki kamr Koyon yaƙi, tsaro, da juriya,domin yarima bazai taɓa zama mai rauni ba

sai can dare aka kaisa yankin ouarzazate inda ake musu desert survival training,.

ranar farko ya dawo daga sallan fajr kenan yana kkrin kammala karatun qur'ani da ya sabayi acikin dakinsa kullum yana dago kai ya hango wani yaro jarumi kusan kamrsa

a shekaru saida yaron yafishi girman jiki dan kuwa murdaddem dantsen sa akarfafe yake, suna haÉ—e ido yaron ya masa wani irin kallo wanda ya isa ya razana shi amma ko ajikinsa ganin hakan yasaka yaron ya wurgo masa takobi cike da kwarewa direct zuwa saitin zuciyarsa yay sauri ya capke tareda mikewa tsaye suna kallon juna batare da sun furta komi ba sai can kafin nan shamsan ya aje qur'ani ya bude kofarsa ahnkli ya fito....

TALES OF THE WAZEERIS

BY

SURAYYAHMS

2026

***