TALES OF THE WAZEERIS

friendship

by @surayyahms

13....🦋

Tales of the wazeeris

sanye dawasu irin bakaken wuluk din kayan horo yaron yatsura ma shamsan Ido zuciyarsa na kan aunashi harya gama takawarsa acikin nitsuwa ya iso daf gabansa da takobin a hanunsa fuskrsa batareda wani hayaniya ba

acikin kankanin lkci suka karewa junansu kallo daga sama har kasa yaga tabbas yaron nan ya ɗan fi shi girma kaɗan snn jikin sa a ƙarfafe yake hatta motsin numfashinsa cikin sauri yakeyinsa kominsa da zafin nama har wano rawa rawa hannunsa yake kamar wanda yake zuba zancen zuci.

daga ganinsa kasan Wnan ba É—alibi bane ko dan sarki yaro ne da akariga aka gina shi da horo mai tsanani.

Shamsan ya tsaya calk yana karantarsa batare daya motsa ba kwasam sai yaron ya kalli takobinsa dake wajen shamsan din ya wani hade rai yace“i believe this isnt urs..

still shamsan bai amsa atake ba yabishi da wani irin sting silence nd dead stare irin direct kallon izza da shirun nan mai masifar É—arsa bugun zuciya da fargaba

harsaida yaron ya hadiyi yawu snn yakara matsowa kurkussa dashi a hankali zuwa gabansa snn yace "..hey..are you deaf?...

dede nan ruwan Idanunsu suka kara haÉ—uwa dana juna basu ce kala ma junan sun ba har saida wani É—an lokaci mainauyi ya wuce snn shamsan ya dauke idonsa a bazata yajefar da sword din akasa a walaknce dan yaga meye yaron zaiyi

da kallo yaron yabishi kafin nan ya tsuguna ya daga takobin yana É—an murmusawa kÉ—an fuskarsa a dore cikin karkada kai ahnkl yace "hmmm..Taurin kai ko..

yana daga takobinsa sama da kyau ya nuna shamsan din dashi da ƙarfi yace 'You..Bloody royals! daga gani baka cancani tsayawa anan wajen ba why dont u show me who you are

tun begama rufe bakinsa bayaga yadda Shamsan din yabishi dashi da takobin nasa dawani irin kllon wlknci dana rainin wayo snda zazzafar huci me ƙara ya kwace ma yaron ma baisani ba.

batare da wani gardama ko tsoro ba ya shiga tsakiyar fili babu wanda yace musu start yaron ya fara kawoma shamsan hari tako ta ina da sauri sauri kuma kai tsaye batare da jinkiri ba duk dama yaga da hannu kawai Shamsan din yake tarewa wani lkci da ƙyar ma sbd shi baidauki wani takobi ba karantar move din yaron kawai yakeyi atsanake,sai can da yaron ya samu yabuga masa kasar takobin a hannunsa snn Idanun sa suka ɗan canza kala yagane wannan fa ba wasa bane aransa yace hmm

Hari na biyu yazo da sauri fiye da na farko shamsan still yasake bashi dama amma yanayi yana karkata jikinsa tareda kaucewa sukar wukar akan lkci

akaro na uku ne komai ya Canza salo yaron yana kawo hari baiyi zato ba shamsan daya gama karantsesa yay wuf ya kama hannunsa daya riqe taqobin cikin nuna masa girman jiki bashine ƙarfi ba,atake ya murda hanunsa sai da yasakashi yay ƙara yasaki takobin kasa bai sani ba..

cikin yan mintina shamsan ya dauki takobin akasa ya fara kai masa hari da irin salonsa zak xak amma cikin nuna masa cewa yafi iya sauri da iya kai hari mai hatsari, dan kai tsaye ya yayyanka masa rigarsa yacire hannun rigar da jikin rigar gabaki daya ya kusan yimasa tsirara awajen atake..

ganin yaron ya matukar tsorota yana jajja da baya yana haqi nan wani murya daga sama ya dakatar da su da sauri sauri yaron ya ja can baya yana wani irin razannen haqi

shamsan ya hade rai kamar bai taɓa dariya ba yana kallon yaron daga sama har kasa can ya sauke takobin kasa ahnkli yace baka shirya ba kake tunanin sanin koni waye..hmm

yaron yana haqi bai ce komai ba har sai dai ya gyara tsayuwarsa yana kallon shamsan kai tsaye ya mika masa hannu with respect yace

i am...Itban bin Maleek.

shamsan baice masa uffan ba yamiƙa masa takobinsa

Itban ya karba snn ya juya kmr zai tafi sai kuma ya tsaya kaÉ—an batare da ya waiwayo ba yanadan murmushi yace nine darasinka na farko ayau da ka samu ka tsallake sai kuma mun sake haduwa a wajen horo.

Shamsan bai amsa ba kuma baiyi wata motsi ba haryaron nan ya gama magannsa ya wuceshi yakara da gaba.

after observing the place abit sai yajuya cikin nitsuwa ya koma cikin dakinsa tun daga wann ranan kullum sai ya hadu da itban bin maleek dan atare ake kaisu desert Survival training,combat energy, warrior skills. horo ne masu zafi da wahala Shamsan was pushed to his limits many times amma dake itban bin maleek is always challenging him to a fight daga training patners har suka dawo abokan juna kud da kud dan akaro na farko kenan dayaji hanklinsa yadan kwanta dawani mutum nadaban.

itban is a son to a top security intelligence official na army an jima da kawosa nan ne yay horo sbd wani darajar da ahalinsa suke dashi na rike sirrikan ƙasa.

ata fannin shamsan kuma mahukuntarsu snriga sun zabge mai shekarun da zaiyi anan moroco izuwa 2yrs sbd baiwa na kaifin kwakwarlsa dan haka duk sanda basuda wani training ana kaishi yankin Rabat ne wanda shima Babban birni ne da ake buga games din diplomacy

sabd abashi isashen political exposure aja shi wajen manyan meetings with foreign elites to Learn more abt global diplomacy

wata rana tare da itban bin maleek yake zuwa meetings dinsa sbd shikansa yasan yana da wuyar sha'ani, he is very allergic to stupidty

daga zarar antaru da yaran larabawa da na turawan nan sunxo anfara tattaunawa ko meeting yagane kai sashasha ne to bazai kuma sake cemaka komi ba saidai kawai kaga ya dauki mataki

itban bin maleek ya zama kmr shine kawai yake iya fahimtar different shades na mood swings in shamsan duba da kusan koyaushe suna tare amma shiknsa bai gama tsira daga halin sa ba.

sumtims haka kawai zakaga hes acting so ruthless babu sani babu sabo, cold, nd distant haka zaiki kula komi da kowa, msmn idan wannan shegen misqilanci da kasaitar sarautar dake jininsa na mulki ya motsa

wani bin kuma in aka hadasu a training zai ma itban din dukan gaske sai kaga kamar baida wani tausayi ne kwata kwata amma daga baya kuma sai kaga shine kawai zaiy jinyarsa snn ya bashi kulawa sosai har ya warke.

bayan shekara guda Kamar yadda uwarjini tasaka dokoki sai wan karon snn iyayensa har da kakansa nana hafsa da tuni tagama idda sukazo dahrul zahra dan su dubashi,

nan ma itban yay dokin yagaisa dasu har ya gaji amma shamsan bai gayyace shi private area dinsu ba har can saida sukayi kwana biyu atare kafin nan ya kirashi suka gaisa

nan ma yay tsamanin zaice ma iyayensa shi abokinsa ne amma yay shiru, hakan sosai ya bawa itban din mamaki da takaici.

bayan zuwa da komawar iyayensa haka nan suka koma kan activites dinsu itban yay masa bori yanuna masa fushi amma shamsan bai kulashi ba har yagaji ya hakura suka dawo dede, zaiga shamsan din yana taimaka masa akan abubuwa dayawa amma haryau yakasa gane meyene matsayin sa awajensa alhalin ko wani lokci kusam kara shaquwa suke da juna a dahrul zahra.

daga daya bangaren kuwa within a year da yawuce din nan ko kadan rayuwa bai musu sauki ko dadi ba sbd rugujewar tattalin arziki da tsananta doka akan abinci ga kuma rugujewar tsaro na tharim vale ya faÉ—a akansu.

dukiyarsu sosai ya fara jan baya baya kmr yadda uwarjini take so hartakai ga masarauta tafara cin bashi daga attajiran gari wanda hakan ya jawo ikon da sarki murad yake dashi agarin zamkora yadan fara yin sanyi.

wasu hakimansa suka fara jin haushinsa tare da dora masa laifi dan aganinsu da baiy taurin kai yaqi bude sakon zuwa taron nan na yarjejeniya na uwarjini ba da duk wann balai bazai same garinsu ba.

dadin karawa tsofin sarakuna da zuriyoyi da aka saukesu a kano sanadiyarsa ynxu sun tsanesa sosai takama global deals dinsa da wasu contracts dinsa duk sai rugujewa suke sbd yawan maqiya

ynxu haka yarsa Arisha ce kawai take kkrin kankaro masa daraja da mutunci dan sosai tay nisa wajen jawo talakawan garin jikin ta da siyasa da makirci.

yanxu kaf garin ana mata wani irin kallo na yarinya mai tsananin hankli da kyaun zuciya kuma jajirtaciya me tausayin kasa da ita

wasuma tausayinta suke ji suna ganin kmar bata kulawa da karatu sosai gata soo young but she is now secrificing her life for the less privildege

a shekarar saida kowa da kowa yasan da ita har wasu manya suna harsashn cewa zata iya gaje kujerar mulkin zamkora tsabar iya adalcinta.

sosai idanun mhaifinta yakara rufuwa akanta dan ynxu ko maganar uwarsa ummu hareera da matarsa gimbiya amani noorain basu yin tasiri a kunnensa kamar nyarsa Areesha.

gani yake kmr yarsa ce kawai take kan tsaya masa kai da kafa tana rufa masa asiri a wann lokcin da kominsa yake kkrin karewa shiyasa duk abunda arisha ta fada masa baya musu baya wani bincike komi tay kuma dede ne,

sosai ya aminta da ita idan aka taɓata kuwa ji yake yi kmr zuciyarsa ake taɓawa shiyasa da wuya kaji ana batun yarsa ushna agidan dan Arisha will neva let him think abt his oda dota saidai ma takara kashe masa jiki akan ushna tareda nuna masa cewa ai mtsalar dake a gabansu anan masarauta yafi bukatr kulawa ba ushna ba.

ita kuwa ushna tunda aka turata london karatu kusan sau daya kawai taga mamanta tazo mata a shekarar nan dubata na kwana biyu

anan ma tasamu already full time boarding schll kawai take yi irin wnda bata dawowa gida hutun nan, dan masu kula da ita acan din suma kusan kulle suke mata dan farkon zuwanta london basu bari tay waya da gida she was depressd shiyasa tay hakuri kawai ta zaɓi tay full time boarding house din abunta a st.qeorge junior year

ushna tana da ilmi na masifa gata da wayo sosai in ana hutu ta gwammci ta shirya tabi kawayenta na schl dan suje wajen da ake yin extra curricular activities, da tours, da educational field trips, dai ababen da suke kara bude ma mutum ido dakara masa dumbin ilimi da wayewa. kawayenta anan duk halfcaste ne akwai khadija datake pure kanuri amma irin african american din nan ne anan london aka haifeta, sai Zahra from tehran birnin iran, sai tasleem youseef daga turkey da wata baturiya mai suna ziyada.

sune suke debe mata kewa arayuwa har taji ta dena kewar gidansu sosai, bata taɓa gigin gayama kowa cewa ita princess din zamkora bace dan addarta arisha tasha gaya mata cewa is a bad thing to be a princess wai ai bazata cimma burinta na rayuwa ba intana kallon kanta amatsayin princess.

dake ita karamar yarinya ne sai kuwa tabita riqe wnn abun aranta sosai dan tana da burin tay karatu me nisa dan ta zama independant kodan babansu yadena mata kallon tijajarrriya me yawan rashinji da laifi.

dagata bangaren tharim vale kuwa ummu zulaiha ce kawai take baza iko duk dama haryau bata dena shaye shayen herbs dan ta samu ciki ba sedei haryau shiru batay batan wata ba

gashi an tura yarsu marida france zataje ta karanta fannin tattalin arziki, sai aiki yay mata mugun yawa dan haka bata wani samu cikar burinta ba tukuna.

leelah da farees salman kuwa duk akayi hutu zakaga sunzo su masarautar kano kowa da motive dinsa, sosai yafara shakuwar bogi da rihanna wanda tsabr kirkinta zakaji yana ce mata softie..

ita kuma leelah babbn damuwarta shine taga ta samu shigewa cikin zuciyar gimbiya hajarat sakeena amma kuma inaa even as a young girl tana zuwa zata fara lazyng around the palace tana dada ji aranta kmr she really belong here sbd kayan duniya datake gani

chocolate, sleep, and shopping are her most favourite things to do inbasu ba haka kawai zata wuni a daki tana kwalliya kala kala tana cancanza kaya ga uban walakanta bayi da servants she is not harsh but she is very rude koyaushe sai an samu matsala da ita kafin sugama hutu

*******

haka rayuwarsu yafara kasancewa akowani fanni, lokaci yadan jaa babu wani jira aka tura leelah wazeeri qasar canada karatu, shi kuma farees salman sawa yay aka sauya masa wajen karatunsa izuwa private american university kasar egypt dan kawai yana samun damar dawowa akai akai dan ya shaqu da rihanna da har yanxu take gaban iyayenta.

shide baida jiki sosai shi ba fariba ba baki ba yanayinsa is just like neymar yanada wani irin yaudararen kyau da dadin baki amma akwaishi da dan uban neman mata na tashin hankali, sosai yabi ya jawo ra'ayin rihanna da abotarsu mai kama da soyayya wanda tun batayi wayo tagane inda yadosa ba har yanxu tafara wayon zugin sonshi yafara kamata dan bata da kowa data mugun aminta dashi yanxu saishi.

Daga fannin shamsan

kuwa yau ana saura wata uku yacika 2yrs a dahrul zahrah ilimi da duk wani training din da aka bashi yariga ya gama bin jikinsa fiye da yadda ake zato.

wann karon babansa ne kawai yazo ya duba shi sukayi bankwana sbd gaba zaikara daga nan zaije qasar waje dan ya karace sauran rayuwarsa a united states of america ya nemo sauran kwalayen karatunsa da real world experience ba gida zai koma ba.

abotansa da itban sosai yay nisa duk dama kusan da shekara daya kawai ya girmesa amma itban yadan fishi girman jiki, shiyasa shima din yake mutuwar son yaje U.S navy training hakan yana nufin nan da wata uku idan suka bar cikin dahrul zahra hala ba zasu sake ganin juna ba sai in Allah ya nufa.

itban bin maleek yana bala'in kaunar shmsan har ransa yake masa kallon dan uwa kullum aranshi yanaso yasan ko shamsan ma yana jin hakan amma inaa that guy is always an emotionless piece of shit.

tun yana cakalarsa da abun har yagaji yabari

aranakunsu na karshe bakaramin activities da kwaje kwajen masu wuya suka samu ba amma koyaushe sai yaga shamsan ya cinye jarabawarsa sbd shi babu ruwansa da kowa da komi, he is ruthless nd focused duk baqin da aka kawo musu wanda sukazo dan sumusu training yana iya karawa dasu

har saida aka kawo musu wani yaro marar ji daga afghanistan to dake anfi tsananta ma itban combat skills sbd shi classified US navy training zaije sai aka hadashi wani deadly karawar karshe da sabon yaron dayazo

fadar tasu was so intense fada ne na ko inkashe ko akasheni

shamsan is strickly forbiden a irin wnn fadar sbd shi royale ne horo ne nashi amma ba aso ma wani abu ya same jikiinsa na ciwo bare mutuwa anan

yaron dayazo kuma irin disposable agents din nan ne zallan training dinsu akeyi domin su tunkare mutuwarsu a irin wnn training din dan haka fadar ya zamo very deadly idan baka kashe ba to lallai zaa kashe ka

shamsan yana tsaye daga inda ake kallon komi duk dama yasan fate din itban yau ko rai ko mutuwa ne amma baisaka komi aransa ba tukuna

dakyar da wuya kuwa itban din ya kwace kansa a wajen yaron duk sunyi makansu jina jina da duka da kyar ya sumar dashi amma dake irin intense passing out training in nan ne sai yaron yana dan hutawa kadan ya farka yay wuf ya fito da irin kananan wuƙar nan yay wuf zai cakka ma itban din akirji

Itban ya farga yay sauri yatsaresa frm no whwr sai kawai wasu daga cikin abokan yaron su biyu suka shigo masa, suka kama itban suka buga masa kai da wani abu kmr engine belt yaron nan har ya samu dama knn zai cakka ma itban wukan a kirji da mmaki itban yaga shamsan ya aje girman kansa ya shigo tayashi a bazata,

daga wukar da yaron zaiy kuwa saiya cakka ma shamsan agefen kafadarsa jini ya fara zuba tamkar wanda yajima yana jiranshi ne yashigo atake kuma suka taru masa akai su ukun kowa yana kawo masa hari.

itban yayi ihun da bai taɓayi ba arayuwarsa yana rokon shamsan da Allah akan ya bari ya fita dan karsu kashe shi a filin amma inaa 3 guys againts 1 shmsan yana da masifar taurin kai haka yaqi yafita

akaro na farko kenan da itban ya fara lura da cewa ashe he mean alot to shamsan ganin duk da d injuryn da aka masa amma yaro na farkon ya fara ɓararwa ta hanyar sliting throat dinsa da wukarsun ya kaisa har lahira.., sai dai bai karasa ganin yadda shamsan din ya kwace kansa ahannun sauran biyun ba yabi ya suma.

sai can tskiyar dare daya farka ne yagan kansa akwance a dakinsa har masa dressing an lankaya masa canular ana bashi ruwa duk abubuwan da suka farun yaji suna dawo masa kai, tsananin fargaba da rauni ya saka yay ignoring zafin dayakeji ajikinsa ya ture likitan dake kansa kasa yay maza ya dira kasa jikinshi na rawa rawa yana Allah Allah kar ace masa wani abu ya same shamsan dan yasan sai yafi kowa a duniyar nan shiga uku

tsananin tsoro da fargaban tunanin rasa amininsa yasaka tun be isa kofa ba yafara fiddaa hushi me karfi ta hanci ta baki da wata iriyar ƙakkarfan emotions yafara kiran sunan shamsan da uban ƙarfi dake sultan suke cemai anan garin

...

tsabar firgici kasa rikeshi liktansan yay

saidai bai kai ga bakin kofa ba bazata yaji an rikesa da karfi suna hade ido yaga shamsn din atsaye sai kuma ya sakeshi ahankli liktan yazo da sauri ya masa wata allura danya dawo hayyacinsa daga haka harsuka maidashi kan gadonsa ya dan kwanta sai kallon shamsan yake da yaga shima har an daure masa hannunsa

suna kallon juna dake yaji wano baqon rauni atake ya kama shi,a tinaninsa shine yake kaunar shamsan fiye da kima saigashi yau shamsan yay kisan kai na farko a rayuwarsa domin kawai ya ceto rayuwarsa

hawayensa suka fara zubowa muryansa na fita dakyar ya damke hannun shamsan din ya fara bashi hakuri... yanata magana masu abun tausayi amma shamsan baice mass uffan ba

sai can dayaga itban bazai kyalesa ba snn yadan mrmusa ahkli yace masa its fine, nafi son haka da akan na zama aboki mai rauni..

yana furta hakan saiya dan juya kansa itban ya lumshe idonsa tare da sakin murmushi me matukar sanyi dan bai tabajin shamsan ya kirashi da sunan aboki ba face wann gaɓar dasuke kkrin rabuwa da junan na har abada.

wani irin shiru ne ya mamaye dakin for almost 20 mins kafin suka fara mgn akan inda zasuje da abubwn da zasuyi. they agree to visit each oda after ibtan's navy training passing out nd first succesful mission in the U.S. kusan shekra daya da watannni 6 kenan....

SHARE UR LOVELY COMENTS ZUWA

MONDAY ZAMU CIGABA

TALES OF THE WAZEERIS

BY SURAYYAHMS

***