The golden gesture
by @zahrabmrs
Chapter 12: The Golden Gesture
Bayan kwanaki biyu na bincike da dambarwar zuciya a birnin Zurich, lokacin komawa gida Najeriya ya yi. Duk da abubuwan da suka faru a "Pool Side," Jannah Anderson ta dawo cikin asalin kamalarta ta "The Iron Lady." Ba alamun rauni, ba alamun kuskure; steez dinta yana nan daram, tana tafiya cikin takun kwarewa (professionalism).
"Aliyu, kafin mu nufi filin jirgi, muna da sa'o'i uku," Jannah ta fada yayin da suke karyawa a restaurant din hotel din. "Zamu biya ta Bahnhofstrasse mu yi shopping. Ina son ka yi yan gidan ku tsaraba, komai a kaina yake (Bills on me)."
Aliyu ya kalle ta da mamaki. "Ma'am, wannan ai ya yi yawa. Albashina kadai ya isa in yi musu komai."
Jannah ta gyara zamanta, ta kalle shi cikin ido ba tare da wani shauki ba. "Haka nake tafiya da mutunena, Aliyu. Kar ka saba mini."
Suna shiga manyan shagunan alfarma na Zurich, Jannah ta fara zabo kayayyaki masu tsada. Ta debi agogo na zamani, turaruka na "Designer," da kuma riguna masu kyan gaske.
"Wannan na mahaifinka ne," ta fada tana mika masa wani agogon Rolex mai matukar tsada. "Wadannan kuma na 'yan uwanka ne."
Daga karshe, suka tsaya a wani babban shagon kayan ado na zinare (Gold). Jannah ta dade tana duba wani zobe (Ring) na zinare mai sulbi da sheki, wanda aka kawata shi da kananan duwatsu masu daraja. Ta saya, sannan ta mika wa Aliyu.
"Wannan ka ba wa mahaifiyarka (Ummi). Ka gaya mata cewa wannan karramawa ce daga wurin Jannah Anderson," ta fada muryarta babu wasa.
Aliyu ya karbi zoben, zuciyarsa ta buga. Ya duba farashin zoben, ya kusa sakin sa saboda tsada. A daidai nan, ya ji wani sabon girmamawa (respect) ya kara shiga zuciyarsa game da Jannah. Duk da girman kanta da kuma yadda ta kware wajen nuna mulki, Jannah mace ce mai hannun kyauta wacce ba ta taba barin na kusa da ita ya wulakanta.
Suna kokarin fita, Jannah ta tsaya, ta kalli Aliyu da wani irin kallo na gefen ido.
"Na ji kana waya jiya... Naima ko?" ta tambaya ba tare da ta nuna wani kishi ba, koda yake Aliyu ya lura da yadda ta ambaci sunan.
Aliyu ya dan sosa kai, "Eh, Ma'am.
Jannah ta nuna masa wani shago na kayan kwalliya da jakunkuna (Bags) na Louis Vuitton. "Je ka can, ka zaba mata tsaraba mafi kyau. Kada mace ta zauna tana jiran ka daga Turai ba tare da ka kaita matakin 'International' ba. Bill dinta ma a kaina yake."
Aliyu ya kasa magana. Lallai Jannah ta gama da shi. Ta nuna masa cewa ita ta wuce duk wani matsayi da yake tunani.
"Mutane da yawa a duniyar nan sun fi fadar mugun halina, Aliyu," Jannah ta fada tana takawa zuwa mota. "Suna cewa ni 'bitch' ce mai girman kai. Amma ba su sani ba, Jannah Anderson tana girmama sadaukarwa. Mu tafi, kano tana jiran mu."
Zafi da hayaniyar Kano suka tarbi Jannah da Aliyu yayin da jirginsu ya sauka. Jannah ta fito cikin takunta na alfarma, idanunta sanye da bakin gilashi (sunshades), yayin da Aliyu yake biye da ita yana tura kayayyakin da suka kwaso daga Zurich. Ba tare da wani bata lokaci ba, ta sanya aka kai shi har gida Hotoro a motar kamfani don ya huta.
Aliyu ya shiga gida dauke da jakunkuna makare da tsaraba. Lokacin da ya bude zoben zinaren (gold) da Jannah ta bayar aka ba wa Ummi, .
"Innalillahi, Aliyu! Wannan ai ya yi yawa," Ummi ta fada tana zare idanu, tana mamakin irin karamci na Jannah Anderson. Ummi ta ji dadi sosai, har ta so ta karbi lambar Jannah don ta kira ta ta yi mata godiya, amma Aliyu ya dakatar da ita.
"Ummi, ba sai kin kira ba. Ita Jannah ba ta cika son surutu ko godiya irin wannan ba. Kawai mu yi mata addu'a," Aliyu ya fada, yana son ya rage mu'amala tsakanin mahaifiyarsa da "Iron Lady."
Su Aysha da Khadija kuma sun kasa zaune, sun kasa tsaye lokacin da suka ga turaruka da jakunkuna na designer da aka kwaso musu. Jannah ta riga ta gama birge su
Duk da wannan shagalin, Aliyu ya kasa fito da agogon Rolex da sauran tsarabar da Jannah ta bayar a kai wa Abba. Ya san halin mahaifinsa—idan Abba ya san cewa daga hannun "Yar Gidan Anderson" wadannan abubuwan suka fito, to tabbas wuta zata tashi a gidan.
Aliyu ya boye tsarabar Abba a kasan akwatinsa, yana lissafin cewa sai nan gaba idan abubuwa sun lafa, zai fito da su ya ce shi ne ya siya da kudin albashinsa don ya samu lada a wurin mahaifinsa.
Bayan sallar isha'i, ya shirya tsaf ya nufi gidansu Naima. Zuciyarsa tana dukan sauran kishirwar daren jiya da ya yi da Jannah, amma yana ganin Naima, ya dake.
Ya mika mata hadadden jakar Louis Vuitton da kuma kayan kwalliyar da suka taho da su daga Zurich. Naima murna take bakin ta yaki rufewa .
"Wannan duka kai ne ka siya min yaya tareeq ? Gaskiya na gode sosai!" Naima ta fada tana rungume jakar.
Aliyu ya yi murmushi, amma bai fada mata cewa asusun Jannah ne ya biya kudin ba. Ya bar ta tana jin dadi, yayin da a ransa yake tunanin yadda Jannah take jujjuya rayuwar kowa da kudin ta.