Business gala and the unexpected call
by @zahrabmrs
Sanyin AC dake ratsa katafaren falon Penthouse din Jannah dake tsakiyar birnin Kano bai hana zafin tattaunawar dake gudana a tsakanin kawayen ba. Jannah tana zaune ne a kan wata kujera ta alfarma, idanunta dake nuna gajiya amma cike da kwarjini suna kan Salma, wacce take kuka kasa-kasa.
"Salma, kukan nan ba shi ne mafita ba," Jannah ta fada muryarta a sanyaye.
Salma ta dago kai, idanunta sun yi jawur. "Jannah, ba za ku gane ba. Dukiya da gidan nan na Bilal ba su ne komai ba idan babu gamsuwa a cikin daki. Na gaji da zama kamar hoto, sex life dinmu ya mutu murus. Na rasa yadda zan yi da shi."
Kawayen suka kalli juna. Amani ta numfasa, "Gaskiya ne Salma, amma dole ne ki dauki mataki. Shawarar da zamu baki daya ce: Ki ba Alhaji Bilal dama ta karshe (last chance). Ki zaunar da shi ki fada masa idan bai nemi magani ba ko ya sauya yanayinsa, to babu sauran zama a tsakaninku. Idan bai canza ba, gara ki rabu da shi ki ceci rayuwarki."
Salma ta share hawayenta, tana jin nauyin shawarar amma tana sanin cewa gaskiya ne.
Kiyi tunani salma ki nema mafita wallahi kika sami Kamar Kabir Allah ya sallameki qawata,don kabir yasan sirrin gamsar mace .
A daidai wannan lokacin, Aliyu yana cikin wani daki mai cike da na'urorin bincike a ofishin DSS. Ya kalli tawagar bincikensa, sannan ya fadi abinda yake ta kai komo a ransa tun kafin su tafi Zurich.
"Akwai wani abu game da Jannah Anderson," Aliyu ya fara magana cikin muryar kwararru. "Kafin mu tafi Switzerland, mun ziyarci wani gidan marayu. A can ne na ji ta tana magana da wani salon Hausar yankin Zamfara ko Sokoto (accent). Wannan ba maganar baturiyar da ta girma a kasashen waje bace kadai."
Daya daga cikin jami'an ya kalli Aliyu da mamaki. "Kuna nufin tana da asali a nan Arewa?"
"Ina kyautata zaton haka," Aliyu ya amsa. "Kuma batun mai kama da Elena Anderson a Zurich ya sake rikita mana lissafi. Dole ne mu zurfafa bincike a can yankin Zamfara."
Bayan ya bar ofis, Aliyu bai tsaya ko ina ba sai a ofishin Alhaji Bashir. Ya san cewa don ya samu amana dari bisa dari a wajen Bashir, dole ne ya bashi wani abu mai kima.
Alhaji Bashir ya karkata a kan kujerarsa, murmushi na mugunta a fuskarsa. "Aliyu me ka kwaso mini daga tafiyar taku?"
Aliyu ya gyara zama. "Alhaji, na gano wani abu. Jannah tana da wata alaka ta sirri da yankin Zamfara wacce take kokarin boyewa. Kuma akwai wata mace dake biye da ita a boye."
Bashir ya zabura ya mike tsaye, idanunsa suka yi fari-fari saboda farin ciki. "Zamfara? Lallai akwai zance! Na gode Aliyu Wannan bayanin zai taimaka min wajen gamawa da ita."
Aliyu ya sakar masa murmushin karya, amma a ransa yana karanta yanayin Bashir. Ya lura cewa Alhaji Bashir ya firgita da jin batun zargin asalin Jannah, wanda hakan ya tabbatar masa da cewa Bashir yana boye wani sirrin game da saninsa da mahaifin Jannah, Mr. Anderson.
A week later
Wani katafaren daki na taro ne dake cikin daya daga cikin manyan otal-otal na birnin Kano aka gudanar da taron dandalin kasuwanci na matasa. Hasken lantarki da kide-kide masu sanyaya rai suka cika gurin. Sabeer, sanye da wata tsadaddiyar suit wacce ta zauna dar a jikinsa, yana gefen Jannah wacce kyan da ta yi ya sa kowa a taron ya kasa dauke ido a kanta.
A wajen otal din, a cikin motar Jannah, Aliyu (Tareeq) yana zaune. Idanunsa suna kan agogon hannunsa, yayin da kunnen sa yake sanye da na'urar sauraron magana ta jami'an tsaro. Duk da cewa shi ne PA dinta, yana da kishin ganin yadda Sabeer yake nuna iko a kanta, amma aikin sa ya sa dole ya danne zuciyarsa.
A cikin taron, Sabeer ya kamo hannun Jannah ya shiga gabatar da ita ga manyan baki.
"Ladies and Gentlemen," Sabeer ya fada yana murmushi cike da alfahari, "Ina so ku hadu da Sarauniyar kasuwanci, Jannah Anderson. Ba abokiyar kasuwanci ta bace kadai, ita ce macen da take rike da zuciyata—itace budurwata."
Wani irin dadi ya ziyarci zuciyar Sabeer ganin yadda kowa yake jinjina musu, amma Jannah sai ta ji gabanta ya fadi. Bada amincewar ta Sabeer ya fito fili ya kira ta da budurwarsa ba a gaban taron jama'a haka.
Aliyu, wanda yake cikin mota, ya ga sakon gaggawa (emergency) ya shigo ta na'urar sa daga ofis. An samu wani sabon labari dangane da binciken Alhaji Bashir da kuma wani motsi da aka gani a asusun bankin Jannah.
Ba tare da bata lokaci ba, Aliyu ya kira wayar Jannah. Tana ganin sunan 'Aliyu P A ' a jikin wayar ta, ta san cewa ba wasa bane. Ta dauka tana fadin, "Yes, Aliyu ?"
"Ma'am, kiyi hakuri ki gaggauta fitowa yanzu. Akwai wani Emergency dake faruwa a ofis wanda yake bukatar sa hannun ki cikin gaggawa. Ina jiran ki a mota,
Jannah ta kalli Sabeer, "I'm sorry, Sabeer. Dole ne in tafi yanzu, akwai gaggawa a ofis."
Sabeer ya hade rai, ransa ya baci kwarai yanzu fa muka zo, Jannah! Kuma a gaban wadannan mutanen zaki tafi? Wane irin emergency ne wannan da PA dinki zai kira ki a daidai wannan lokacin?
"Sabeer, aiki ne. Zan kira ka daga baya," Jannah ta fada yayin da ta juya ta nufi hanyar fita, ta bar Sabeer a tsaye cike da kunya da kuma bacin ran yadda Aliyu yake da ikon janye ta daga gefensa a kowane lokaci.
Bayan fitowar su daga taron kasuwancin da Sabeer ya shirya, Jannah da Aliyu sun nufi ofis cikin matsanancin gudu. Jannah tana zaune a bayan mota, zuciyarta tana bugawa. Tana isa ofis, ta tarar da ma'aikata cirko-cirko, wasu na latsa kwamfuta cikin kidima.
Babban manajan Jannah ya zo da gudu yana haki. "Ma'am, babban kwangilar da muke sa ran samu daga gwamnati (The Big Contract) an soke shi! Sannan kuma... akwai jami'an binciken kudi (Anti-Fraud Unit) a cikin ofishinki, suna zargin cewa kamfaninmu yana harkallar kudi ta haramtacciyar hanya (Fraud)."
Jannah ta ji jiri yana neman kwashe ta. Ta san Alhaji Bashir ne ya hada wannan makircin don ya lalata mata babban kwangilar da zai kai kamfaninta mataki na gaba. A daidai wannan lokacin, jami'an suka fito daga ofishinta tare da wasu takardu.
"Jannah Anderson, kuna karkashin bincike ne saboda wasu asusun banki da muka gano ana tura kudi daga wani suspected account zuwa nan, wadanda ake zargin na haram ne," in ji jagoran jami'an.
Aliyu, wanda yake tsaye a matsayin PA, ya lura cewa idan bai yi sauri ba, za a tafi da Jannah kuma asirin sa ma na iya tonuwa. Ya matsa gaba cikin nutsuwa, ya nuna musu wata ID card ta daban wacce jami'ai kadai suka san ma'anarta, sannan ya yi gyaran murya.
"Ranka ya dade," Aliyu ya fara magana da kwarin gwiwa, "Muna sane da wadannan asusun. Amma abinda ba ku sani ba shi ne, mu ma kwanan nan muka gano wannan matsalar. Mu ma mu ne 'victims' a wannan harka."
Jami'an suka kalle shi da mamaki. Aliyu ya ci gaba da cewa, "An yi amfani da sunan kamfanin Jannah Anderson ne ba tare da saninmu ba don yin wadannan mu'amalar. Muna cikin gudanar da bincike na sirri ne don gano wanda ya kulla mana wannan zagon kasar. Don haka, kamata ya yi mu hada kai don kamo masu laifin na gaske maimakon tsayar da ayyukanmu.
Dabarar Aliyu ta sanya jami'an suka dakata da nufin su na garkame ofishin. Sun amince su ba su lokaci don mika rahoton binciken da Aliyu ya yi ikirarin suna yi.
Bayan sun tafi, Jannah ta fada kan kujera, tana kallon Aliyu da wani irin kallo na godiya da kuma mamaki. "Aliyu , ta yaya ka san abinda zaka fada musu? Kuma wace takarda ce waccan?"
Aliyu ya sakar mata murmushi mai sanyaya rai a ransa yana fadin 'Idan har kika san wane ne ni, za ki san cewa wannan kadan ne daga cikin abinda zan iya yi don kare ki.'
A daya bangaren kuma, Alhaji Bashir yana zaune a ofishinsa yana jiran labarin an kama Jannah. Amma lokacin da ya sami labarin cewa "bincike ne ya tsaya" saboda dabarar PA dinta, baiji dadi ba ,amma yasan duk cikin shirin Aliyu ne na son kai jannah kasa