Dangerous Desire
by @zahrabmrs
Salma ta shigo Murtala Nyako Sports Center (i-Fit Gym) sanye da kayan motsa jiki da suka fi ƙarfin kuɗin da talaka zai iya tunani.
Tana cikin motsa jiki, idanunta suka sauka akan Arch Kabir, mijin ƙawarta Amani. Maimakon ta yi tunanin kuɗinsa, sai ƙwaƙwalwarta ta fara hasko mata dukkan labaran da Amani take ba su game da yadda Kabir yake sex da ita ( kalubale gareku masu bayyana wa kawayen su bedroom activities dinsu )da kuma yadda yake da wani irin jiki mai ban sha'awa da ƙarfi.
Salma ta kalle shi, ta ji wani irin kishi yana taso mata. Ba kishin kuɗi ba, a’a, kishin cewa me ya sa Amani take da miji mai kula da ita haka? Me ya sa Kabir yake da wannan "energy" din da mijinta ba shi da shi? Ta ji tana son dandana abin da Amani take tinkaho da shi.
Ta matsa kusa da shi, tana goge wuyanta da ƙaramin tual dinta. "Arch Kabir! Ashe kaima kana zuwa nan? Na zaci irinku manyan mutane sai dai a kafa muku gym a gida," ta faɗa tana wani lallausan murmushi.
Kabir ya ajiye abin ɗaukar nauyi (weights), yana haki kaɗan. "Salma, ashe kina nan? Gaskiya ne, amma wani lokacin "environment" na nan yana sa mutum ya fi ƙwazo. Ya gida? Ya Khalid ?"
Salma ta ɗan taɓe baki, tana ƙoƙarin rage nisan dake tsakaninsu. "Khalid Sun tafi umrah jiya da babansa . Gaskiya arch Kabir, Amani tana yawan ba mu labarinka, Wani lokacin idan ina jin Amani tana ba mu labarin yadda kake nuna kulawa, nakan ji kamar ma wasa take yi. Amma yanzu na fara gani da idona..." ta ƙare maganar tana kallon cikin kwayar idonsa cikin wani salo na yaudara.muna godiya da yadda kake kula mana da kawarmu
Kabir ya yi dariya, bai kawo komai a ransa ba. "Amani dai akwai yabo. Amma ai ke ma naga mijinki ba baya ba ne wajen kula da ke."
"Mijina?" Salma ta faɗa a ranta, "
Wannan lusarin?amma a fili tace Hakane amma kasan kowa da salon sa na Wajan kula da mace and a yadda amani take yabonka you’re extraordinary
Salma ta lura cewa Arch Kabir mutum ne mai son aiki da girmama kwarewa, sai ta sauya salon maganar daga shauki zuwa harkar kasuwanci.
"Gaskiya arch Kabir, akwai wani babban shiri da nake yi na bude wani katafaren Supermarket mai hade da Pharmacy a wani fili da na saya a hanyar Zaria," Salma ta fada tana nuna alamun muhimmanci. "Ina bukatar babban Architect mai hangen nesa irinka ya zana min shi yadda zai zama na zamani, wanda babu irinsa ,
Kabir ya gyada kansa, sha'awar aikin ta bayyana a fuskarsa. "Wannan babban tunani ne Salma. Kuma zan so in ga yadda zan iya taimakawa wajen fito da wani tsari mai kyau."
Salma ta yi murmushin jin dadi, ta dauko wayarta ta iPhone 16pro. "To bari in karbi lambar wayarka, sai mu rinka tattaunawa akai. Amma don Allah arch Kabir, ina so ka bar maganar nan a tsakaninmu... kar ka fadawa Amani tukunna."
Kabir ya dan daga gira, "Me yasa? Ke fa kawarta ce."
Salma ta dan sosa wuyanta, tana nuna kamar tana son yi wa kawarta abin mamaki ne. "Ka san halin Amani, idan ta ji maganar nan yanzu za ta fara rantsuwa sai na sanya ta a ciki ko kuma ta fara tallata wa kowa kafin komai ya kankama. Ina so in ba ta mamaki (surprise) ne idan komai ya kusa kammala. ..." ta fada tana masa fari da ido.
Kabir ya yi dariya, ya karbi wayar ya sanya lambarsa. "To babu damuwa, asiri ne ya rufu. Zan jira jin sakonki don mu fara aikin."
Salma ta kalli lambar dake kan screen din wayarta, wani irin dadi yana ratsa ta. Ta san cewa yanzu ta samu hanyar da zata rinka kiran sa kowane lokaci, kuma tana da dalilin da zai sa su rinka haduwa a boye ba tare da kowa ya zargi komai ba.
Next day Jannah ta sanar da Aliyu cewa Alhaji Bashir ya gayyace ta cin abincin dare (Dinner) a wani babban gidan cin abinci na dake tsakiyar Kano.
Aliyu ya hade rai, idanunsa cike da damuwa. "Ma'am, kada ki je. Alhaji Bashir ba mutumin kirki ba ne, kuma wannan gayyatar tarko ce kawai don ya kara bincikar sirranki."
Jannah ta yi wani murmushin isa, ta gyara zaman mayafinta. "Aliyu, na gode da kulawar ka, amma dole ne in fuskanci makiyi na don in san abinda yake kitsawa. Ba zan taba guduwa ba."
Jannah ta isa restaurant , inda ta tarar da Alhaji Bashir yana jiran ta cikin shiga ta alfarma da fara'ar karya. Bayan an fara cin abinci, Bashir ya ajiye cokali ya kalle ta da idanu masu bincike.
"Jannah, ke kyakkyawa ce kuma mai basira," Bashir ya fara magana cikin muryar yaudara. "Amma akwai tambayoyin da suke damuna game da mahaifinki, Mr. Anderson. Shin ko kin taba tunanin cewa watakila dukiyar da kuke takama da ita ba ta gaskiya ba ce? Kin taba tambayar Mr Anderson yadda ta Tara dukiyar nan ?
Jannah ta ajiye kofin ruwan dake hannunta, idanunta suka canza launi, suka zama masu kaifi da nuna barazana. Ba ta nuna tsoro ba, maimakon haka sai ta matsa kusa da teburin.
"Bashir, na gaji da wannan wasan boye-boyen naka," Jannah ta fada cikin muryar dake nuna karfin iko. "
"mu daina wannan wasan na yara. Ka gayyace ni nan, kuma ka san ba don kaunata ba ne. Me kake so a takaice ?" Jannah ta tambaya cikin muryar da ba ta da tantama.
Bashir ya yi murmushin mugunta, ya jingina da kujerarsa. "Ina son abin da kowa yake so, Jannah. Ina son kashi hamsin cikin dari (50% shares) na kamfanin Anderson Global. Idan kika ba ni wannan, zan daina binciken mahaifinki, kuma zan zama garkuwarki a wannan garin."
Jannah ta yi wata gajeriyar dariya ta raini. "50% shares? Alhaji Bashir, kana mafarki ne ko kuwa ka manta da wacce kake magana da ita? Ba za ka taba samun ko da kashi daya ba na gumi na da na mahaifina. Anderson Global ba ta sayarwa ba ce, kuma ba ta mika wuya ga masu neman abin duniya ta hanyar tursasa mutane ba."
Ganin yadda Bashir ya hade rai yana shirin yin magana, Jannah ta katse shi. "Kuma kafin ka yi tunanin amfani da wata kwangilar don ka ruguza ni ,bari in gaya maka wani abu da ka dade kana boyewa."
Jannah ta matsa kusa da shi, ta rage murya amma mai cike da barazana. "Ina so ka fita a harka ta. Idan har ba haka ba, zan sa a dauko mahaifiyarka dake boye a can Keffi."
Jin sunan garin Keffi da kuma batun mahaifiyarsa ya sanya Bashir zabura, zufa ta fara keto masa duk da sanyin AC dake wajen. Ya zaro ido yana kallon Jannah cikin tsantsar mamakin yadda ta gano wannan babban siirin nasa dake boye.
"Ta yaya... ta yaya kika sani?" Ya fada muryarsa tana rawa.
Jannah ta mike tsaye, ta dauki jakarta. "Kada ka taba zaton kai kadai ne kake da jami'an bincike. Daga yau, duk wani motsi da zaka yi na takalar mahaifina ko kamfani na, to ka tabbatar ka yi bankwana da mahaifiyarka."kuma ba ruwanka da yadda mahaifina ya tara dukiyarsa
Haka suka rabu baran-baran, kowa yana jin kiyayyar daya a ransa. Bashir ya kasance cikin fushi da firgici, yayin da Jannah ta fito tana jin cewa yau ta nuna masa ita 'Yar Gidan Anderson ce ta gaske.