JANNAH ANDERSON

Jealousy ?

by @zahrabmrs

Kafin karshen weekend din, Aliyu ya biya gidan yayarsa  Nafeesah. . Ya iske ta tana koyawa  yaranta homework da gudu su Hameedah da  muneef suka taso suka rungume favorite uncle dinsu .inda already ya Saba duk zuwa da abinda yake kawo masu .

"Tareeq , Wai Yaushe zaa tsayar da auren ku da Naima ne?nifa na gaji da ganin Ka kullum kana makale a cinyar ummi .Nafeesah ta tambaya tana masa kallon tsokana.

Aliyu ya yi murmushi, yana tunanin Jannah a gefe guda, Naima a gefe guda. "Aure nan tafe Nafee. Lokaci ne kawai."kuma aure bazai raba ni da cinyar ummi ba ,ni kuwa Ina Ogar Ka jannah Anderson ummi kullum cikin maganar ta take ,tace baa taba mata kyauta irin wacce jannah Anderson ta mata ba ,murmushi Aliyu yayi ,wallahi tana nan lafiya tana nan tana mulkar mu.

A ransa kuwa, Aliyu yana ji Jannah ta riga ta fada tarkonsa. Ya san yanzu ta amince masa, kuma tana bukatar sa. Wasan yanzu ne aka fara shi da gaske.


A gefe guda, Jannah tana zaune a wani tsadadden ice cream shop tare da Dr. Sameer. Iskar wajan tana kadawa cikin kamshi, amma yanayin fuskar Jannah a hade yake, cike da izza da isa irin ta Anderson.

Sabeer yana ta kokarin nuna mata hoton Aliyu na daren jiya, yana neman ya bata masa suna.

"Sabeer , stop it!" Jannah ta fada, ta buga hannunta akan teburin. "Aliyu ba ma'aikaci na bane kawai. He is a partner in my security and business. Abinda ya faru daren jiya aiki ne na tsaro, kuma ni na ba shi umarnin ya zauna kusa da ni."

Sabeer ya hade rai. "Amma Jannah, hoton nan ya nuna..."

"Hoton nan ya nuna jarumtakar sa ne!" Jannah ta katse shi cikin isa. "Kuma ina son in gaya maka abu daya, bar sabeer . Kar ka kara kuskura ka bayyana a inda nake, ko ofis dina, ko gidana ba tare da na ba ka izini ba (unannounced).Dan  kaga na baka fuska, to ka kiyaye iyakar ka."

Ta tashi tsaye, ta gyara zaman  rigarta, ta kalle shi da raini. "I am Jannah Anderson. Ba zan bar wani namiji ya sanya min doka a rayuwata ba. Goodnight, bar ."

Ta fice daga gurin tana takun ta na isa, yayin da Sabeer  ya mike  tsaye fuskarsa tayi jawur saboda jin kunya da haushin Aliyu.

A cikin mota, Jannah ta lumshe ido, tana jin wani irin farin ciki da ta kare Aliyu. Ta san cewa yanzu zuciyarta ba tata bace; ta kusa mika mukullin rayuwarta ga tareeq namijin da ya sanya ta jin ita mace ce a daren jiya.


Ranar Litinin ta waye da wani irin sanyi a ofishin Anderson Global. Aliyu ya shigo ofis, amma a ransa akwai nauyin maganar da mahaifinsa ya gaya masa a daren jiya.

"Aliyu, mun riga na tsayar da magana da mahaifin Naima," in ji mahaifinsa cikin tattausan murya mai cike da nuna iko. "An sa ranar aurenku nan da wata biyar  masu zuwa. Allah ya sanya alheri."

Aliyu bai iya cewa uffan ba, domin biyayya ga iyaye tana daya daga cikin ginshikan rayuwarsa, duk da cewa zuciyarsa tana can tana dukan sauri akan wata mace daban.

ummi taja aliyu gefe 

rabin raina tareeq ya naga kamar baka Farin ciki da sa date din aurenka da naima ?

idan akwai wacce kake so ka fada min zan san yadda Zan shawo kan abban ku 

hannun ummi ya kama cike da kauna ,ina son Naima ummi kawai dai ban zachi abba zai sa abin da wuri haka bane 


Aliyu ya shiga ofishin Jannah dauke da wasu fayiloli. Jannah tana zaune, kanta a kasa tana nazarin wasu alkaluman kasuwanci. Ta sanya wasu siraran gilashin ido wadanda suka kara mata kwarjini.

"Good morning, Miss Anderson," Aliyu ya fada, ya ajiye takardun.

Jannah ta dago kai, ta kalle shi na dakika daya—kallon da ya sanya dukkan dumin daren jiya ya dawo musu sabo fil—sannan ta maida kanta kan aiki. "Morning, Aliyu. Is there anything else?"

Aliyu ya jingina da teburin nata, ya kura mata ido. "Ina son in sanar da ke wani labari ne. Jiya mahaifina ya kira ni... an riga an sa ranar aurena da Naima. Nan da wata biyar masu zuwa."

Aliyu ya zuba mata ido sosai, yana jiran ya ga yadda zata girgiza, yana jiran ya ga kishi ya bayyana a fuskarta, ko kuma ta nuna bacin rai akan yadda suka kusa cinye juna a gado kwanaki kadan da suka wuce.

Amma, abin mamaki, Jannah ba ta ko kyafta ido ba. Ta ajiye biros dinta a hankali, ta gyara zama, fuskarta ta koma tamkar kankara—ba alamun damuwa, ba alamun kishi.

"Oh, really?" Jannah ta fada cikin muryar nan tata ta sanyi dake nuna ko oho. "Congratulations, Aliyu. Naima yarinya ce mai kirki, tabbas zaku dace. I'll make sure to clear your schedule when the time comes."

Aliyu ya daskare a wurin. Wani irin radadi ya ji a ransa. Shin daren jiya ba komai bane a wurinta? Shin ta riga ta manta yadda take kiran sunansa "tareeq cikin kukan dadi?

"Shi ne kawai abinda zaki ce?" Aliyu ya tambaya, muryarsa ta dan nuna bacin rai.

Jannah ta dago kai, ta kalle shi cikin ido da wani irin kallo na isa. "What else do you expect me to say, Aliyu? Kai ma'aikaci ne a nan, kuma ina murna da cigaban rayuwarka. Ko kana tunanin daren da muka yi romance zai sanya in hana ka auren wacce ka zaba ne? We are adults, Aliyu. Don't mistake passion for commitment."

Ta maida kanta kan takardunta. "You can go now. I have a lot to do."

Aliyu ya juya ya fice, ransa a jagule. Ya ji kamar an watsa masa ruwan kankara. Bai sani ba cewa Jannah tana yin masking ne kawai.


Aliyu ya rufe kofar ofis din, Jannah ta saki biros din hannunta. Hannunta ya fara rawa, numfashinta ya sarke. Ta ji wani irin zafi yana taso mata daga tafin kafa har zuwa makogwaro.

"Wata biyar ..." ta rada, hawaye guda daya ya zubo mata wanda ta yi saurin goge shi.

Ta duba date din  dake jikin wayarta, ta ji kamar ta fasa wayar. Kishi ne yake neman haukatata, amma izzarta ba zata taba barin ta nuna wa Aliyu cewa maganar auren sa ta taba ta ba. A ranta, tana jin kamar an soka mata wuka. Ta tuna dumin sa, ta tuna yadda yake tsotsar kirjinta, sannan ta yi tunanin cewa nan da wata biyar wata mace ce daban zata mallaki wannan dumin.

"Bazai taba faruwa ba," ta fada a ransa, idanunta suka sauya kala. "Aliyu, kana tunanin zaka iya barina bayan ka riga ka shiga jini na? Zaka gane wacece Jannah Anderson."


A lokacin da wannan kishin yake cin zuciyar Jannah, bar sabeer yana zaune tare da wani mutum dake bashi labarin binciken da suka yi a kan Aliyu.

"Bar , binciken mu ya nuna cewa Aliyu yana yawan zuwa wasu ofisoshi na sirri," in ji binciken. "Kuma akwai alamar yana aiki da jami'an tsaro na undercover. Amma bamu da tabbaci har yanzu 

Murmushi Jin dadi bar yayi ,Aikin Ka na kyau ku cigaba da binsa har sai kun sami full evidence Akan sa