JANNAH ANDERSON

THE LONGING

by @zahrabmrs



Bayan maganar sa ranar Aliyu da Naima, Jannah ta ji dakin ofishinta ya fara mata kuncin da ba za ta iya jurewa ba. Kallon Aliyu a kullum yana kara rura wutar kishin da ba ta taba sanin tana da shi ba. Don haka, ta yanke shawarar yin abin da ta saba: Guduwa daga matsalar.

"Aliyu, zan tafi Dubai tare da su Amani  na tsawon mako guda," ta fada masa a takaice, yayin da take hada takardun dake gabanta, ko kallon inda yake ba ta yi ba. "Zan bar dukkan ragamar ofis a hannunka. Ina son duk abin da ya taso ka magance shi, sai dai idan abin ya fi karfinka ne ka kira ni."

Aliyu ya kalle ta, ya san cewa guduwa take yi. "Fine, Miss Anderson. Have a safe trip."


A cikin garin Dubai, a daya daga cikin manyan hotels na Palm Jumeirah, Jannah tana kwance a gefen pool, sanye da bakaken gilashin ido. Kawayenta suna ta faman hirarrakinsu na nishadi, amma Jannah tana wata duniyar daban.

Duk motsinta yana cike da tunanin tareeq . Iskar Dubai mai dumi tana kara tuna mata da dumin numfashinsa a wuyanta. Ta kalli hannunta, ta tuna yadda ya sarrafa ta a daren nan—yadda ya sanya ta mance cewa ita ce Jannah Anderson mai iko, yadda ya sanya ta mance ma cewa ta girme shi. A hannunsa, ta ji ta kamar yarinya karama mai bukatar kariya.

'Me ya sanya hakan ke faruwa da ni?' ta tambayi kanta, yayin da take kara matse cinyoyinta. Tana kishirwar tabawar sa, tana son sake jin yadda bakinsa yake sarrafa kirjinta. Guduwar da ta yi don ta mance da shi, ta zama silar da take kara nukuwa a cikin ruhinta.


A kano kuwa, Aliyu ya yi amfani da rashin Jannah wajen zurfafa bincikensa. Ya shafe kwanaki yana binciken kauyukan Zamfara da Sokoto da , yana neman asalin jannah " ko wata yarinya da aka taba sace wa wani attajiri. Amma sirrin  Jannah yana da zurfi; babu wani "hint" mai karfi da ya samu tukuna, sai kara rudewa da yake yi.

Ranar Asabar, Aliyu ya dauki Naima suka tafi Park. Naima tana ta bashi labarin yadda take shirye-shiryen aurensu, fuskarta cike da farin ciki.

"Yaya tareeq , ka ga wannan kalar leshin? Ina jin zai yi kyau a ranar walima," Naima ta fada tana nuna masa hoto a wayarta.

Aliyu ya yi murmushin yake. "Eh, yana da kyau Naima."

Amma a ransa, Jannah yake gani. Yana kallon Naima ne, amma muryar Jannah ce take masa gamo a kunne. Ya tabbata yanzu—rage son Naima ba. Soyayya ce ta zumunci da tausayi, amma abin da yake ji ga Jannah wata irin guguwa ce da ba ta san sauran dangi ba. Ya ji nauyin yadda yake yaudarar Naima, amma zuciyarsa ta riga ta zama mallakin macen da take Dubai yanzu haka.


Yayinda Jannah take Dubai tana lissafin kwanakin da suka rage mata ta dawo ta ga tareeq  dinta, Alhaji Bashir yana zaune a kebantaccen daki.

"Alhaji, mun samu labarin asalin 'yar Anderson dake boye," wani mutum ya fada masa a asirce. "Ba a kasashen Turai asalin ta yake ba. Akwai wani tsohon sirri  dake da alaka da wani gidan malamai dake sokoto 

Alhaji Bashir ya saki wata dariya Wannan shi ne makamin da zan yi amfani da shi in gama da ita. Aliyu yana tunanin shi kadai ne yake wasan, bai sani ba zan ruguza su gaba daya."


A cikin satin da Jannah take Dubai, Aliyu ya yi kokarin danne kowane irin tunaninta ta hanyar kusantar Naima. Ya wallafa hoton sa da Naima a status dinsa na WhatsApp, suna zaune a park suna cin ice cream, fuskarsa dauke da murmushin da ya kware wajen yi don boye gaskiya.

Jannah, wacce take kwance a dakin hotel dinta a Dubai, ta ga hoton. Take ta ji wani irin daci ya taso mata. Ta kashe wayar ta wurga ta gefe, tana jin kamar ta sanya kuka. Amma kawayenta   basu bar ta ta huta ba; sun kaita siyayya, nishadi, da hirarrakin da suka sanya ta dan mance radadin zuciyarta na wucin gadi.inda salma ta ce fada masu cewa ta samu mafita Akan matslar da mijinta 

Duk da haka, kowace rana tana kirga sa'o'in da zasu rage kafin ta dawo Kano . Tana kewar kamshinsa, tana kewar yadda yake kallonta cikin shauki 

A tsawon zaman Dubai, bar . Sabeer  bai kyale ta ba. Suna yawan waya, inda yake ta nanata mata cewa akwai wata magana mai matukar muhimmanci da yake son yi da ita da zarar ta dawo.

"Sabeer , kasan dai bana son takura," Jannah ta fada masa a waya ranar karshe kafin ta dawo.

"I know, Jannah. Amma wannan maganar ta shafi makomarmu ce. Please, give me a chance when you return."


Jannah ta sauka a filin jirgin Aminu Kano  da yamma. Aliyu ne ya je daukarta tare da tawagar tsaro. Lokacin da ta fito daga cikin filin, idanunta suka sauka akan Aliyu. Ya yi kyau cikin shigarsa ta Smart Casual, fuskarsa babu alamun shaukin daren nan.

Aliyu ya kalle ta, ya ji wani abu ya daki kirjinsa. 'Lust ce kawai,' ya fada a ransa don ya kwantar wa kansa hankali. 'Sha'awa ce kawai kake yi mata, ba so ba.' Ya karasa ya karbi jakarta.

"Welcome back, Miss Anderson," ya fada muryarsa a dake.

"Thank you, Aliyu," ta amsa a takaice, tana kokarin danne yadda take son ta rungume shi a gaban kowa.

Suna cikin mota, shiru ya ratsa tsakaninsu. Jannah tana son yin maganar hoton sa da Naima, amma izzarta ta hana ta. Shi kuma Aliyu yana son ya tambaye ta yadda Dubai ta kasance, amma baya son nuna damuwa.