SAWUN KEKE season 1

*🪻SAWUN KEKE...🪻*

by @auntyindo


"Sunana Karimatu sana'ata sayarda Abinci, tafiyayya na yo domin na haɗu da kai,   ɗana ne  bai fi shekaru 17 ba amma sai na ajiye kuɗi ya zo ya ɗauke  ya je su sayi kayan maye shi da oganninsa manya da su amma ba su bashi ko sisi ba sai na sha wahala na nema ya zo ya sace ya kai musu, ya ƙi zuwa Boko ya ƙi Islamiyya aikinsa kenan yawo cikin ƴan shaye-shaye, shi ne sai ka ganshi da sigari ya na sha ba aikin fari ba na baƙi sai wannan, na yi faɗa na yi duka na yi nasiha amma duk ya ƙi ji, shine na samu labarinka,  Ɗannan na yarda da kai ɗari bisa ɗari shi yasa na kawo maka shi ko da zai yi iskancin ma idan ya na ƙarƙashin kulawarka zan fi samun kwanciyar hankali."
sai a lokacin ya juyo  ya ɗan kalleta cike da kulawa ya ce "Gobe ki zo min da shi."
murmushi ta yi sabida jin daɗin samun karɓuwa da ta yi, cikin sauri ta ce "Ai ba zai zo ba gardama gareshi."
Maida kallonsa ya yi kan Ɗan Bakwai gami da cewa "A haɗata da Zabira   ita za ta iya zuwa da shi."
Ɗan Bakwai ya ce "An gama Uban gayya"
Godiya sosai matar ta yiwa Risslan har ta fice duk da bai ce komai ba ita kuwa ba ta fasa ba.

gaba

Misalin ƙarfe 10:37Pm
Garin Kwanar Ɗan Gora babban Titin shigowa KANO..

Ba wani dare ne ya yi ba amma da yake lokacin damuna ne tuni sahun bil'adam ya ɗauke sai ƙarar iska da ke kaɗawa ba ji ba gani, jefi-jefi motoci sukan wuce su ɗin ma in wata ta wuce wata takan jima ba ta zo ba.

Dirowa ya yi daga kan Dokinsa ya fara haske-haske da dalleliyar Fitilarsa  ya na ƙarewa yanayin wurin kallo, ya ɗan ɗauki lokaci ya na haske-haske sannan ya kashe fitilar, dubensa ya kai ga Dokinsa gami da ɗan shafa shi, cikin daddaɗar muryarsa ya ce "Prince! calm down,  ba daɗewa za mu yi ba yanzu zan gama mu koma."
Prince dai da yake baya magana bai ce komai ba sai sunkuyar da kai da ya yi.

Daidai lokacin wata ƙaramar mota ƙirar Taxi ta shararo da mugun gudu kamar wadda jiya ta wuce take shirin kamo gobe.

Dalleliyar fitilarsa ya kunna ya haska motar sannan ya kashe ya nufi kan titin, a tsakiya ya coge gami da riƙe ƙugunsa.

a cikin motar kuwa Direban ne ya kalli na kusa da shi gami da cewa "Ka na ganin abinda nake gani kuwa?"  ɗan zaman banza ya ce "Menene?"   "Ba ka ga wata fitila da aka hasko mu ba?  kuma ka ga mutum fa a tsakiyar titi duk irin wannan gudun da nake yi ko ɗar bai yi ba."
Mutum ɗaya da ke a gidan baya ne ya ce "Kuma ba dai ace ƴan fashi ba, in su ne ma da sauki Oga zai iya da su."
"Kutumar Uba Sahun Keke ne!!!!!"  Direban ya faɗa  cikin firgici da razani,  wani mugun burki ya ja wanda ya yi daidai da harbe tayar motar da Akhiee ya yi,  tayar ta bada dammm!!!! ta tarwatse, motar ta yi  dara ta yi tsalle ta hantsila sau biyu kana ta tsaya wuri ɗaya ta na juyawa samanta ya koma ƙasa.

cikin ƙasaitaccen takunsa ya gangara gefen titin inda motar ta ke, leƙawa ya yi ta glass ya cewa direban "Ba ni wayarka"
Direba da ke numfashi da kyar da kyar  ya zaro wayar a aljihunsa na gaba, fizgeta Akhiee ya yi kana ya yi baya-baya ya saita wurin man motar da bindigarsa, bai damu da kuka da magiyar da Mutanen ciki ke yi ba ya bata ɗasss,   nan take ta kama da wuta ba ƙaƙƙautawa.

ƴan danne-danne ya yi a wayar ba ɓata lokaci ya cire key ɗinta tamkar ta shi,  kira ya tura gami da kara wayar a kunne, bugu biyu aka ɗauka, JD cikin farin ciki ya ce "Direba Dangin kura, ina fatan kun isa, na kasa rintsawa har sai na ji kyakkyawan Albishir."
"Ba kyakkyawan Albishir a wannan karon sai dai a tarawa gaba,  na kamaka kuma na mamayeka!!!"  Akhiee ya yi maganar cike da zarra.
Zumbur JD ya miƙe daga kan luntsumemiyar kujerarsa ta alfarma,  a take guguwar tashin hankali da firgici ta tashi a cikin cikinsa,  ido a burbuɗe ya ce "Sahun Keke!!! What do you mean!!???"
"Ohh! Nothing, i mean, your car had an accident,  ka ga yanzu saura kai kenan.
Safa da marwa JD ya fara yi a tamfatsetsen falon nasa, ya kai tsayin minti ɗaya bai iya cewa komai ba sannan ya ce "Wallahi! Tallahi!  ni ne maganin iskancinka,  ni za ka yiwa wannan yankan ƙaunar?  ka jira abinda zai biyo baya, billahillazi  sai  na jefaka a bala'in da za ka gwammace ba ka zo duniya ba."
"Ina jira idan har kai hafaffen cikin tsohuwarka ne kar ka barni na ƙara kwanan duniya, ina jiran duk abinda za ka yi.
daga haka ya katse wayar gami da jefata  kan motar da take ci da wuta,  juyawa ya yi  ya haye kan dokinsa su ka ɗau hanya.

Kwantsam!!!  JD ya maka wayarsa da ƙasa ya na huci,  yatsansa manuniya yasa ya na nuna ƙirjinsa gami da cewa "Ni???  ni za ka yiwa haka? wallahi ko me ka ke taƙama da shi sai na azabtar da rayuwarka."
Dukan dafkeken kansa da ke juyawa ya fara yi hannu bibbiyu kamar sabon mahaukaci, sai da ya gaji da zagaye sannan ya jaɓe kan kujera gami da dafe kai ya fashe da wani azababben  kuka  wanda shi kansa ma bai san dalilin yinsa ba.


washegari

Fitowarsa daga ɗakin baccinsa kenan ya tarar da matan gidansu a tsakar gida sun kafa dandalin hirarsa kowacce ta na tofa albarkacin bakinta,  bai kula su ba ya wuce hanyar fita, da gudu Zara ta ƙarasa inda yake ta na cewa "Akhiee Abhi na kiranka."
Bai yi magana ba ya juyo zuwa cikin gidan, ɗakinsa ya koma ya canja kaya  ya sanya jallabiya da hula sannan ya nufi turakar mahaifin nasu.

Hamza na zaune kusa da  Abhi ya na bashi labari Akhiee ya yi sallama, tsohon  dake zaune kan kujerarsa ta marasa lafiya ya amsa fuskarsa ɗauke da yalwataccen murmushi, ƙarasawa ya yi ya durƙusa a gabansa gami da cewa "Good Morning Daddy!"  Abhi ya amsa da cewa "Morning Dattijo!  ka manta da ni ne kwana biyu?  dama abinda ya sa na kiraka  na ji a gidan ba zancen da ake yi sai naka, ba kwanciyar hankali a ƴan kwanakin nan  naji sai cari su ke yi ba matan ba mazan, me ka yi ne Dattijo??"
Da sauri ya ɗago kai ya na kallon Mahaifin nasa cike da rashin sanin abin faɗa.
Murmushin gefen baki Hamza ya yi a ransa ya ce "Ai yau taka ta ƙare faɗen gaskiya ya zama dole."


kamar yadda Risslan ya ce a zo masa da yaron da ke yiwa ummansa sata hakan ce ta faru,  tare su ka shigo da Zabira da Ɗan Bakwai da Salansa sai kuma Mama Karimatu mahaifiyar yaron sai yaron da ke ta famar rarraba idanu kamar an ɗaure zakara ana shirin yankawa.

Akhiee na zaune kan benci ya na aikin shan wiwi su ka shigo da sallama, duk su ka  ja   su ka tsaya su na jiran cewarsa.

Miyagun idanunsa ya zubawa yaron har na ɗan lokaci kafin ya ce "Mama faɗa masa laifinsa."  da sauri ta ce "To"  sannan ta ƙara maimaita abinda ta faɗa jiya.
Cike da tsageranci yaron ya ce "Ni ba na ɗaukar mata kuɗi, ai idan na yi musu aike ne su ke bani."
Mama Karimatu ta ce "Wallahi ƙarya yake Muhammad ba sile ɗayan da suke ba shi sai dai shi ya kwashi nawa ya kai musu."
A fusace yaron ya ce "Ni fa gaskiya ba na sata ni ba ɓarawo bane, akan me za ki ce ina ɗaukar miki kuɗi bayan ban ma san inda ki ke ajiyewa ba?"
Mama Karimatu ta riƙe haɓa  ta na mamakin irin tsaurin ido na ɗan nata.

Cikin takunsa irin na toron giwa ya ƙaraso gabansa ya na binsa da wani irin kallo me sanya nutsuwa ko ba'a so, "Ya sunanka?"   "Rabi'u"  ya faɗa a ƙagauce,  jinjina kai ya yi sannan ya ce "Me yasa mahaifiyarka ta na faɗe ka na faɗe? ka na nufin ƙaryata take maka??"
ƙara haurowa ya yi kamar zai doki Akhiee ya na cewa "Ni ban ce ƙarya take ba, amma ni ban taɓa ɗaukar mata kuɗi ba!!!!"
Akhiee ya  kalli Mama Karima gami da cewa "Mama janye ɗanki don in na saka masa hannu za ki iya rasa shi."
Da sauri ta riƙo hannunsa ta na cewa "Matso nan"  fizgewa ya yi  ya ce  "Ni rabu  da ni."
Za ta yi magana Akhiee ya ce "Ƙyale shi" matsawa ta yi gefe  ta zubawa sarautar Allah ido,  Akhiee ya dube shi a tsanake  ya ce "Yanayin tsaurin idonka ya burgeni,  a kayan caji da me kake amfani??"
Ƙasa ya yi da ido ya ce "Sigari kawai nake sha"
miƙa masa Tabar hannunsa ya yi gami da cewa "Na san kana so, to  gwada mana!"  karɓa ya yi ba tare da ya ji ko ɗarr ba  shi a dole ɗan zafin kai.

Ja ɗaya ya yi mata ya wurgar da sauran gami da dafe ƙirjinsa da hannu ɗaya ɗayan kuma ya dafe kai ya na wani azababben tari, nan take idanunsa su ka canja launi su ka ƙara yin ja sosai su ka firfito sabi da azaba.
tari yake ba ƙaƙƙautawa ƙafafunsa ma sun gaza ɗaukarsa har sai da ya durƙushe a ƙasa, Ummansa ce ta matso kusa da shi cikin tausayawa ta na yi masa sannu sai dai ba halin amsawa.

Salansa ya ce "Da ka ce kai shege ne, ai a zafin kan ma aji aji ne dan ubanka."
Akhiee ne ya durƙusa a gabansa cikin nutsuwa ya ce "Za ka ƙara ne??"  da sauri ya girgiza kai alamar aa,  Akhiee ya dubi Salansa gami da cewa "Ku haɗa shi da Laita."
ya na faɗen haka Salansa ya kama shi ya fice da shi daga gurin.
Ummansa ta raka su da ido har su ka fice.

"Ki na ba shi kuɗin makaranta?"  girgiza kai ta yi alamar a'a  ya ce "To ki dinga ba shi amma ba da yawa ba, rashin sakarwa yaro hannu yakansa shi fara ɗauke-ɗauke amma idan abin ya yi yawa ya na kawo lalacewa,  In sha Allah zai shiryu, zan sa shi a Islamiyya nan da kwana biyu ko uku."
Mama Karima ta goge ƙwalla ka na ta ce "To Allah i sa, na gode sosai."

Kai kawai ya gyaɗa mata alamar ya amsa.

Kwance yake kan  makeken Gado wanda zai iya kai girman wani ɗakin, gadon ya sha shimfiɗa da tafkeken bargo wanda ake kira duniyar kuliya,  ko ina na gadon ado ne ya yi kyau gwanin sha'awa.
Baccinsa yake cikin kwanciyar hankali ba tare da wata damuwa ba.
Wani samɓalelen Maciji golden collor ya salallaɓo ya hau kan gadon,   can tsakiya inda Akhiee yake ya nufa  sai da ya hau kansa ya zagaya kana ya sauka gefe ya tsaya ya nannaɗe gami da ɗago kansa sama.

Sanyin Macijin  da ya ji ne ya sa shi   buɗe idanunsa cikin nutsuwa ya zubawa Macijin su kafin ya lumshe ido, a hankali ya ce "My Mother!!!"


by Aunty INDO