Chapter 16
🌀 *HAƊIN ƘADDARA* 🌀
By
AyshaNalado
Sadaukarwa ne a gareki ƴar uwa rabin jiki *RUKAYYATU* (Aunty Ummi) Son so fisabilillah😍
BOOK 1
Page 16
Hannun Salmah da ke miƙa mata wayar ta bi da kallo, gabanta na ɗan faduwa, “Ya Anas da daddaren nan.” Ta furta a ranta kafin ta miƙa hannu jiki a sanyaye ta karɓi wayar ta kara a kunneta. Sallamarsa da nutsattsiyar muryarsa ya ratsa kunnuwanta, ta lumshe idanunta a hankali ta bude akan fuskar Salmah da ta ja ta yi mata tsaye a gaba, tana binta da wani irin kallo wanda ta rasa gane kansa. Itama ido ta zuba mata, tana nazarin yanayinta, sauyin da ta gani a tattare da ita yau a bayyane yake, wannan ba shine yanayin da take shiga ba a duk lokacin da ta haɗa ta da Anas domin su gaisa, farin ciki da annashuwarta basa ɓoyuwa murmushinta baya yankewa, har takan yi mamaki hakan wasu lokutan. Ta san fushin da take yi da ita akan Suraj bai isa ya janyo wannan sauyin ba. Muryar Ya Anas ce ta katse mata tunani, “Ayush!” ta ji ya kira sunanta da wani salo mai daɗi, “Na'am Yaya.” ta amsa a sanyaye tare da dauke idanunta daga kallon Salmah, “Ki na jina?” “Umnh! Ina wuni?” “ Lafiya kalau kyakkyawar ƙanwata.” Murmushi ne ya suɓuce mata ba tare da ta shirya ba, “kai Ya Anas ina kyan yake.” Ta yi maganar da wani salo wanda ya tilastawa Anas lumshe idanu, a hankali muryarsa cike da nishaɗi ya ce “Yana tare da ke My Ayusher.” Zaro ido ta yi kafin da sauri ta juyo ta kalli Salmah da har lokacin take tsaye a kanta, tasan sarai ta ji domin wayar a handsfree yake, suna haɗa idanu Salmah ta juya da sauri ta shige toilet, jingina bayanta ta yi da kofar toilet ɗin bayan ta mayar ta rufe, tare da sakin wahayen da take ta kokarin dannewa tun ɗazu, da tana da dama da ta hana, data dakatar sai dai bata da wannan ikon a halin yanzu, ta daɗe a haka tana tausar zuciyarta, sai da ta tabbatar sun kammala wayar kafin ta watsa ruwa ta fito bayan ta daura alwala.
A kwance ta tarar da Aysha wayar kife a kusa da ita, idanunta a lumshe ta juya mata baya, motsin fitowarta bai sa ta juyo ba duk da tana da tabbacin ba barci take yi ba.
Wayarta kawai ta dauka itama ta hau gadon ta kwanta bayan ta rage musu haske, WhatsApp ta shiga ta duba saƙo, ta kai mintuna biyar tana jujjuya sakon a zuciyarta kafin ta yi reply ta kashe wayar ta kwanta bayan ta yi addu'a.
Wannan daren ya zama mai tsauri ga Aysha, abubuwa biyu suka taru suka mata rubdugu, abinda ya faru ɗazu tsakaninta da Mr AA ya kasa barin kanta, ga kuma wata sabuwar da Ya Anas ya Kunno mata, fatanta ya fahimce ta, ya yi mata uzuri, sai dai tana matsanancin jin kunyar Ammie, Abie, dama shi kansa Anas ɗin.
Washegari ya kasance asabar babu aiki kuma babu makaranta, hakan yasa bayan sallar asuba da suka sake kwanciya ba su tashi ba sai kusan goma. Kallo ɗaya Salmah ta yi wa Aysha ta tabbatar tana cikin damuwa, ta san dama za a rina, wai an saci zanin mahaukaciya, ba za ta ce mata komai ba har sai ta nemi shawararta, za ta zuba mata idanu ta ga iya gudun ruwanta.
A tare suka yi breakfast kamar ko yaushe, sai dai yau dining ɗin shiru babu mai cewa komai, tun bayan gaisuwar da su ka yi, dama Salmah ce mai surutun kuma yau kanta ya dau caji, Abie ne ya fara kammalawa, sai da ya goge hannu da bakinsa da tissue, sannan ya kalli Ammi ya ce “ Yaushe Anas ya ce zai dawo?” A zabure Aysha ta dago jin an ambaci Ya Anas, sai dai babu wanda ya kula da hakan sai Salmah. “Au kaima bai faɗa makan ba kenan?” cewar Ammi tana yar murmushi, “ Ya ƙi, amma ya bani tabbacin cikin watan nan zai dawo.” yar dariya Ammie ta yi ta ce, “ Shiryayye wai bazata zai yi mana.” Murmushi Abie ya yi, “ To Allah ya kawo shi lafiya.” duk suka amsa da Ammi, yunkurawa Abie ya yi zai miƙe, da sauri Salmah ta ce, “Abienah.” ya juyo ya zuba mata ido alamar yana saurarenta. “ Abie za mu je saloon ni da Aysha, yau babu school.” ɗan shiru ya yi yana nazari kafin ya ce, “ Okay ku shirya, Salman ya kai ku.“ Ya ciro card ya miƙa mata tare da fadin “ Na san shi a ke wa.” dariya suka saka, Salmah ta karba tare da faɗin “ Mun gode sosai Abie, Allah ya saka da alkhari ya kara buɗi, mu biya Shopping?” Murmushi ya yi kafin ya gyaɗa kai.
Daɗi sosai ya kama Salman, jin zai samu damar fita da mota yau, a zuciyarsa sai shiwa Salmah albarka ya ke yi, ta dade bata yi abinda ta faranta masa ba irin yau, don dama tun ɗazun yake jujjuya yadda zai samu aron motar Ammie su fita yau suna da wata ƴar taro na yan team ɗinsu.
“Yau kuma gulmar ce ta motsa?“ Ammie ta faɗa tana hararar Salmah, dariya duk saka saka saboda gane abinda take nufi, “ To Ammie ai ke ce baki sakar mana kuɗi kamar Abie.” Cewar Salmah tana dariya, “ Ya yi kyau ai, ni kujerar zama ce, ina nan za ku lallaɓo ku same ni.” “ Ayya ki yi hakuri farar uwa tauraruwar Abienah in Sha Allah ba za ta kai mu ga haka ba.” “ Ahaf! Ai kuma sai ki yi.” Ammie ta ƙarashe maganar tare da miƙewa ta ji bayan Abie da ya kama hanyar ɗakinsa yana dariyar surutu da iya kalmashe zance irin Salmah.
Daga haka cin abincin ya tashi, duk su ka yi ciki domin ƙimtsawa. Karfe goma sha daya da kwata, suka kammala shiryawa, kamar kullum, Salmah fuskar nan ɗau da makeup, yayinda Aysha ko hoda bata shafa ba, suka fito a tare cikin ankon atamfa, Salmah na mata mitar rashin son kwalliya. Zuba musu ido Salman dake tsaye a falo shima cikin shiri yana wulwula makullin motar Ammie da ke hannunsa ya yi, yana kallonsu tare da nazarin kowacce, ko daga yafa mayafinsu za ka hangi bambamcinsu a zahiri, Salmah yar gayu ce ta karshe mai son ado da kyale kyale, kana ganinta ka ga big girl, yayinda Aysha take mai tsananin natsuwa da kamewa, a suffa kuwa, Salmah dirarriyar macece full option, kana ganinta kaga matar manya kamar yadda take faɗa kullum, iya hips da mazaunanta ka kalla zaka shaida hakan, ba ƙiba gareta ba sai dai akwai ƙaya, shiyasa kullum Salman ke ganin tsaurin idon abokinsa, da tunanin inda zai kai wannan zuƙeƙiyar halittar. Yayinda Aysha ta ƙasance, mai jikin Fulani, siririya fara mai yalwar gashi, sai dai tana da sharp mai matukar ƙayatarwa da daukar hankali, cikin nan nata a shafe kamar bata cin abinci hakan ya baiwa ƙugunta damar nuna bajewarsa a bayyane daga sama kuma abubuwan basu da wani girma ɗas da su daidai jikinta. A fuska kuwa kowacce da kalar sanyayyar kyawunta mai tafiyar da imanin mai kallo.
A gurguje su ka yi wa Ammie sallama suka tafi, Salmah a baya Aysha a kusa da Salman, tuƙi yake yana amsa kiran abokansa yana shaida musu ya yi nasarar samun motar, ciki harda Suraj, shiru Aysha ta yi a gaba tana tunani, yayinda Salmah ke baya tana charting.
********************
Kasancewar daren jiya bai samu isasshen barci ba, domin kwana ya yi da damuwa da tunanin yarinyar da ko sunanta bai sani ba. Hakan yasa ya tashi yau asabar very weak. kamar yadda ya zamar masa a jiki, in dai ya kwana a gida ɗaya da mahaifinsa to da safe zai shiga su gaisa, yau ma hakan ta kasance, misalin karfe tara na safe, ya tarar da General Idris Kangiwa a falonsa yana zaune shi kaɗai yana karatun jarida daily trust, kallo ɗaya General ya yi masa ya fahimci a kwai damuwa tattare da ɗan nasa, jaridar da ke hannunsa ya ajiye tare da zare gilashin kara karfin gani da yake da sawa idan zai yi karatu saboda jikin girma, ya fuskancesa da kyau.
“ Ina kwana Abba.“ Ya furta cike da tsantsar ladabi bayan ya rusuna ya sunƙuyar da kai ƙasa alamar girmamawa irinta al'adar gaisuwar malam bahaushe. Yana ci gaba da ƙare masa kallo ya amsa da “Lafiya ƙalau Babana, yau an kwana a nan kenan.” “ E Abba na shigo around 11, ka kwanta lokacin, ya ƙarfin jiki.“ “ Alhmdlh, da sauƙi.“ “ Masha Allah, Allah ya ƙara maka lafiya.” “Ameen, Allah ya yi maka Albarka ya jiƙan Zainaba.“ lumshe idanu ya yi a hankali ya bude a fuskar Gen. Alamar amsawa,daga haka ya koma ya zauna a ƙasa yana fuskantar Mahaifinsa, a ƙa'ida idan suka yi irin wannan zaman, su kan yi hira su yi raha su tattauna abubuwa ma su mahimmanci, su ji damuwar juna, har zuwa lokacin da za su yi karin kumallo, daga nan kuma sai su yi sallama, wata ƙila kuma ba za su sake haduwa ba sai bayan wasu kwanaki domin shi AA ba zaunin waje guda ba ne. Sai dai koda bai kwana a ƙasar ba, ƙa'ida ce kullum safiyar duniya sai sun gaisa da mahaifinsa ta waya.
Shiru shirunsa da ya yi yawa yau, ya kara gaskata zargin Gen. Akansa domin duk da kasancewarsa mara surutu da hayaniya a gaban mahaifinsa ba haka yake ba, shine mutum na biyu bayan Mother da yake sakewa da shi su yi hira sosai har ya ji wani sirrinsa, shine mutumin da yake ganin rauninsa, shine mutumin da yake zama ya yi kuka a gabansa domin ya samu salamar zuciya idan wani damuwar ya ciyosa, yana da tarin abokai amma mahaifinsa shine amininsa.
Cikin hikima Gen. Ya fara jansa da hirar da yek da tabbacin zai rage masa damuwarsa, kafin ya jeho masa tambaya game da halin da yake ciki. Shiru ya ya yi kusan minti ɗaya, kafin ya sauke numfashi a sanyeye ya ce, “ Abba bibiyata su ke yi, Abba mai yasa ba za su barni ba, me na tsare musu.” shiru ya yi yana kallon Gen. Da ya lumshe ido tunda ya fara magana, ya ci gaba da cewa, “Abba, wannan karon sun zo da sabon salo, mace su ka sanya, da ita suke so su yaudare ni su kaini ƙasa.” Jin hakan ya sanya Gen. Bude idanunsa da suka rine nan take ya zuba masa alamar karin bayani, gane hakan yasa ya ci gaba da basa labarin haduwarsa da Aysha har karo biyu da yadda haduwar ta kay, kiransa da suna Babangida da nuna sanyayyarta a garesa har zuwa irin munanan kalaman da ta farfaɗa masa.
Murmushin manya Gen ya yi, a ransa ya ce“ Lallai sun yi danganci, wannan abinda da suka yi tamkar sun yi wa kansu talala ne, lokaci ya yi da zan gano su wanene mutanen da ke bibiyata a duhu, ana daf da yin walƙiya.” a zahiri kuwa cewa ya yi, “ Ina bukatar sanin komai a kanta yar gidan wanene menene kamashonta a tafiyar, ka sanya ido sosai mata shu'umai ne, sannan ka zurfafafa bincike.” sun ci gaba da tattaunawar sirri na abubuwa masu mahimmanci da suka shafe su, kafin daga bisani su gangaro harkar siyasarsu, yadda zabe ke gabatowa da shirye shiryen da su ke yi mata. A haka Aunty Rukayya matar Gen. Ta shigo falon da sallama cikin ado na kece raini, sosai fara'ar fuskarta ta fadada lokacin da ta hango AA a falon, “ A'a ɗan gidan Mother yau an kwana mana nan kenan.” Da murmushi ya kalleta tare da faɗin, “ Eh Aunty ina kwana.” “ Lafiya kalau ya gajiya, ya kwana biyu, jiyan nan na ke cewa Gen idan ka yi aure dai nan za ka ajiye mana ɗiya, wata kila albarkacinta mu dinga ganinka.” Da sauri ya kalleta jin za ta jiƙo masa aiki, domin idan da yar tsamar da ke tsaninsa da Abba to maganar aure ne, kuma yasan da gangan ta yi hakan, domin ita da Mother suna mayaƙan Abba, sai dai abinda babu wanda ya sani, ita da tata manufar a kansa. Da ido ya yi mata alamar ta yi hakuri ta yi shiru, ta ko dauke kai alamar ta ƙi, ganin haka yasa ya yi zaraf ya mike, yana neman hanyar arcewa. “Oh don na yi maganar Aure shine ka miƙe, to Allah ya shiryeka, na yi shiru.” kallonta Gen. Ya yi ya ce“ Barshi ya fi ruwa gudu Rukayya, ni dai ki zama shaida zan fada a gabanki na yi masa mata.” a tare gabansu ya faɗi shida Aunty Rukkey, kasancewarta wayyayiyar mace, sai ta yi kokarin aro jarumta ta yafa, ta saka shewa tta yi guda tare da faɗin, “ Ma sha Allah, yaushe aka yi hakan.” “ Yau.“ ya bata Amsa yana sakin murmushin da shi kaɗai ya san manufarsa.
Da sauri AA ya isa gabansa, ya zuɓe a marairaice ya ce “Abba don.... Hannu ya ɗaga masa, “Na gama magana bana son jin wani ƙorafi, tashi mu je mu karya.” ya girgiza kai “ Na ƙo shi.” “ To je ka.” Gen ya faɗa cikin tsare gida. Miƙewa ya yi jiki ba kwari ya kama hanyar ficewa, “ Ka tsaya mana ko Tea ne ka sha.” Cewar Aunty Rukayya bayan ta raka shi da kallo. Dakatawa ya yi ba tare da ya juyo ba ya ce, “ No, Nagode Aunty, fura nake buƙata zan je wajen Mother yanzu.” yana gama fadin hakan ya ci gaba da tafiya. “ Ba ka ji ba.” Muryar Gen. Ya sake katse shi, wannan karon juyowa ya yi saboda girmamawa amma bai ce komai ba, “ ka da ka manta da, binciken yarinyar, ina son sanin komai a kwana bakwai ko ƙasa da haka.” “ In Sha Allah.” shine amsar da ya iya bayarwa kafin ya fice daga falon yana jin kansa na sarawa. Kai tsaye tamfatsetsen sashensa gari guda ya nufa, a gurguje ya shirya cikin shigarsa ta ɓadda kama, dauki karamar mota ya bi ta get ɗin baya ya dauƙi hanyar gidan Mother motor su Ussy babban yaronsa mafi kusanci, na biye da shi a baya ba tare da saninsa ba.
Ko da Aunty Rukayya ta yi serving ɗin Gen kasa zama ta yi, saboda damuwa da tashin hankalin da ke nuƙurƙusar ranta, asiri ta basa, ta tashi ta nufi ɗakinta, a nan ma tsaye ta yi tana kai kawo, tare da nake faifan tunanin da hikimarta, “kai ina ba zai taɓa yiwuwa ba, ya zama dole na samu biyan ɓukata, ba zan taɓa zuba ido na rasa farin ciki saboda farin cikin wasu ba, so so ne, amma son kai ya fi. Wayarta ta zabura ta dauka da sauri ta lalubo wani lamba da ta yi saving da Baby ta danna masa kira......