ZAZA&ZAK

Chapter 03

by @fatoumspen

FAROUQ 

tunda ya gama brake fast ya koma dakinsa car keys dinsa da laptop dinsa y’a dauka sabuda zaman gidan ya ishe sa , harabar gidan ya fito ya nufa inda ake ajiye motocin gidan, samun kansa yayi da kare musu kallo kaman me neman wani abu Ganin ba motar nimrah yaja doguwar ajiyar zuciya ya maza ya kauda tunanin dake neman ziyartar sa, motar ya shiga, me gadi ya bude masa gate yana masa adawo lafiya…. tafiya yakeyi bai sanma inda zaije ba Tunda Already ba lokacin zuwa judges bane yanzu sabuda 12 tayi already, wayarsa ya dauko yai dialing number Abokinsa Salman, Bugu 1 ya dauka bayan sun gama waya ya nufi wurin aikin salman sabuda likita ne….  Bai dauki lokaci dayawa ba ya isa Asibitin parking yayi ya shiga, ya nufi office din Dr salman din, Sama sama yake amsa gaisuwar ma’aikatan asibitin… bude office din dayaji anyi yasa ya dago kansa Y’a sauke su akan Farouq dayake shigowa, Fuskarsa a sake yace “ Welcome sir “ yana sara masa irin yanda ake sarawa sojoji… Waje farouq ya samu ya zauna akan wata Doguwar kujera dake office din … wani kallo salman y’a masa y’a jefa masa tambaya “ kai lafiyar ka kalau kuwa , ya zaka shigomin office ba sallama “ Dafe kansa Farouq yayi daga bisani ya juyo da idonsa yana kallan abokin nasa  a hankali ya bude baki yace  “sorry man Wlh ba a nitse nake ba “.. Dr salman tattare kayan dake gabansa yayi ya dawo kusa da abokin nasa Kare masa kallo yakeyi yana karantar yanayinsa, tambaya ya jefo masa kai tsaye “ Nimrah right?” Da Sauri Farouq ya kalli Dr salman kaman bazayyi magana ba kuma daga baya sai yace “ Salman I’m tired “ Salman yayi wani Dan murmushin gefen baki ya sake jefawa farouq wata maganr “ Marry her “ da sauri farouq ya tashi daga kishingiden dayake Yana kallan salman sosaii cikin mamakin kalaman nasa, Bai amsa masa ba kawai yadau car keys dinsa yabar office din ba tare da ya sake waiwayen Dr salma din ba… Dariya salman yayi sosaii yana cewa “ Abokina ya shiga hannun mata, ba boka ba tsafi yarinyar nan tana neman haukata farouq soja guda “ baya mamaki sabuda kaidin mata na dayawa…..

ZAZA &ZAK 

juye da debewa suke tayi, yawo sukeyi sosaii tsakankanin Areas din dake lagos…

Sun gama sauke duk mutane motar ya rage ba kowa , Keys din motar ZAK ya bawa ZAZA yace ta maida Motar tasha sannan ta koma gida shi Akwai inda zaije, karba tayi ta figi motar da gudu har sai da Zak ya tsorata yana mamkin irin rashin hankalin zaza…..

tafiya takeyi tana gudu abinta hankalinta kwance tanayi tana leqowa tana zagin duk wanda ya shiga gabanta, Waqa takeyi sosaii while driving…. dafff da zata shiga titin dazai sadata da anguwan su ba tsamani sai ga wata black land cruiser taji tinted, karo suka kusayi da sauri taja wani wawan birki tana dafe kirjinta don ta tsorata sosaii, Sai data nutsu sannan ta dago kanta taga yanda mutane ke kallansu wasu na zaginta, ranta ne ya baci ba second thought kawai ta bude motar ta sauko ta Gyara zaman P cap dinta Ta gyara kwalar rigarta, ta kamo gaban wandonta tana wani bouncing, ba tsoro bare shakka ta tafi gaban motar ta tsaya ta gaban motar tana kare mata kallo, ganin ba wanda ya kulata yasa ta karasa gaban motar………

zaune yake a bayan motar yana danna system din dake kan cinyarsa, Dogayen yatsansa farare tasss dasu farcinan tsaff dasu Yake sarrafawa akan system din with full concentration, karar burkin da akaja a motar ne yasa ya dago manyan idanunsa ya dorasu akan driver dinsa dake sanye cikin uniform din sojoji, Daga bisani ya sauke idonsa akan ZAZA dake tsaye gaban motar su ta kama gaban wando, a wannan lokacin bazai iya tantance namiji ne ko mace, Driver din nasa ne ya juyo da sauri yace “ Sorry sir “  ya juya yana kokarin fita ranshi a bace, kafin ya bude motar Cikin dakakken voice dinsa na cikakken namiji ne zati yace “ Stay back !” dawowa driver din yayi da sauri yana cewa “ Yes sir “ …. daga nan ne suka ga ZAZA ta tazo saitin inda driver din nasa yake tana cika tana batsewa, kwankwasa glass din window din tayi tana cewa “ Oga Come down , with your car wey resemble boat “ sosaii Ran driver din ya baci ganin rashin kunyar da take neman yi musu, qara kwankwasa glass din tayi azafafe, Glass din ya sauke a hankali….. Baki ta bude zata Yanko masa magana idonta ya sauka akan sojan dayake cikin kakinsa fuskar nan a murtuke Gashi gabjeje a dai dai lokacin kuma wani tsadadden kamshi ya doki hancin ta ya shige har cikinta sabuda muguwar shaqar data masa.. wani yawu me kawri Ta hadiye sai zazzare ido takeyi, Wani tsawa Sojan ya daka mata “ Young lady or young man , are you mad !!!” … ba shiri tai kasa tana daga hannu sama cikin tashin hankali bata damu ba da a gefen titi take ba, kuma tasan ko zasu kashe ta babu me chetanta « sorry sir!!! Sorry sir! Mon sirrr!!! attention!!!!” Su kawai take jerowa hankali a tashe , ya bude baki zayyi magana kennan muryar boss din nasa ta daki kunnenta “ I don’t have enough time to waste here !” .. daga inda yake zaune y’a sara masa sannan yace “ I’m very sorry sir “ sannan y’a kalli zaza yace “ I’ve marked your face “ … yaja glass din .. ba shiri ta matsa don kar ya taka ta da mota…. a zabure ta koma wajen bus dinta tana ta zazzare ido Kirjinta na daukan 3-3…. Bus din ta shiga ta zauna tana murnar arziqin data awna yau , tada bus din tayi Tajata a hankali ba tareda da sakeyin gudu ba, har ta isa anguwansu bata gama dawowa dai dai ba , ganin Kely qawarta da kuma Sam Abokinta a tasha suna jiranta yasa ta mance da wani abu daya faru da ita dazu, Parking tayi ta sauka ta zura keys din a jakar dake waist dinta…….. ihu sukeyi suna hailing juna wanda ya kasance kaman shine gaisuwar da sukeyi tsakaninsu, tafawa takeyi dasu cikin raha… Sam ne yace “ My guys I get something for you ooo” kely da ZAZA suka matso kusa dashi suna kiran ne zaice musu .. Sam yace “ I get one place where we go go , na 5000 per each pesin u know we get match to watch today oo “ Ihu suka hauyi suna murna, kely tace “ k know my guys go win this play , Barcelona for lifeee “ wata dariyar sheqiyanci zaza tayi tana wani kama gaban wandonta tace “ You wey loose every game , Abeg na Madrid go win , me and you know this naaaa “ .. nan suka hau musun ball daga nan suka siya bread da coke suka ci, suka tafi gantalin su da suka saba suna tafe suna tsokanar jama’an wurin……..

ZAK

Tunda suka rabu yadau hanyar kasuwar agege machine ya hau ya qarasa kasuwar…. Alwala yayi ya samu wani waje yadan kebe ya gudanar da sallah azahar lokacin 2:30PM .. hankalinsa na kan zaza don yasa yau tunda ta samu sake ba lallai hankalinta ya bata taje tai sallah bah… yana idarwa yai Addu’a sannan y’a miqe ya shiga kasuwar…. manyan shagunan dake kasuwar yake bi yana dubawa idan da wanda za’a saukewa kaya ayi dashi, haka kuwa y’a samu aka dinga sauke kayan wani babban shago……..