Chapter 04
by @fatoumspen
ZAZA&ZAK
F notes ✍️
Tunda taje hotel din ta shiga room din data kama…. jakarta ta ajiye sannan ta cire Abayan dake jikinta ya rage daga ita sai bra da Dan shot daya kama jikinta wayarta ta janyo tayi snapping picture ta turawa farouq ta WhatsApp, bayan ta tura masa ta shiga contacts tai dialing number mahaifiyarta… Ringing 2 Aka daga wayar sallama tayi maman tata ta amsa mata tana tambayarta ya take, itama ta amsa mata da Alhamdulillah, cikin kulawa mahaifiyarta ke qara jajjada lafiyar yar tata,..sun dan dau lokaci suna waya daga bisani Nimrah tace da maman nata tana buqatan kudi like 50M account dinta yadanyi qasa, ba musu mamanta ta amsa mata da tohm, bayan sun gama wayar in 10 seconds sai ga alert din 15M ya fado account dinta, murmushi tayi tana yiwa ummin nata Addu’a…
chat ta shiga yi da friends dinta tanayi tana scrolling a instagram… kiran sallah azahar ne ya tashe ta ta shiga bathroom tayi Alwala ta zura Abayar ta tai rolling mayafin ta tada sallah akan carpet din dake room din, bayan ta idar taji wayarta na vibrating dubawa tayi taga conference video call ne from her 2 best girls (Raihana, Nafee ) , dagawa tayi tana Sakar musu harara tace “ kufa kun fiya takura Wlh , mene na video call kuma “ raihana ce ta maida mata da hararar itama tace “ swear you don’t miss us “ Dariya Nimrah tayi tace “ When are you coming back raihana?” raihana ta amsa “ next week in sha Allah, awwww is someone trying to…..” katse su nafee tayi da cewa “ girls kun manta dani ne “ Dariya dukkansu sukayi suka amsa mata a tare “ yesss yar baqa “ Dariya sukayi dukkansu a tare suke shiga hirarsu ta qawaye, bayan sun gama ta duba WhatsApp taga Farouq yaga picture din amman bayyi reply ba , wayar ta ajiye ta shige cikin duvet din gadon ta qara gudun AC ba jimawa bacci y’a gaba da ita cikin mafarkin farouq kaman yanda ta saba.
Wait !! Guys what’s between Nimrah and farouq ? I’m not getting it , kaman wadda ta shanye sa ko yake tsoronta?
Su waye zaza da zak? basuda iyaye neh? Zaman kansu sukeyi ? meyasa sunayensu kaman ba na musulmai ba
What’s wrong with hajiya Suwaiba da Hajiya hadiza me yasa basa maraba da zuwan IMRAN???
ku buyoni mu cigaba da nitsawa cikin labari domin mu mata fahimtar wasu abubuwa da dama a cikin labarin nan
Thank you for your support and love I really appreciate you guys.
A short biography of Alhaji Muhammad muhammad Maitama
Muhammad Dan asalin garin Yola ne daga mahaifiyarsa har mahaifinsa yan Adamawa yola ne, mahaifiyarsu Me suna fatima zahra’u wacce ta kasance jika a gidan sarkin yola…Su 4 mahaifiyarsu ta haifa Ibrahim, Muhammad , Sunusi, Halimatu….. Alhj Muhammad maitama Babban soja ne kuma da yayi retire yayi governor a Garin Adamawa wanda yai silar tara arziqinsa, Ya so a yaransa wani ya gajesa ya zama soja Allah bayyi ba Tunda yaransa suka taso sukayi ilimi wanda a qasar waje ma sukayi karatunsu, Ya dora yaransa akan sanin kasuwanci sosaii wanda Allah ya taimakesu Kasuwancin ya musu Albarka suka tara nasu arziqin tunda qananan shekaru, Ibrahim ne ya kasance me sha’awar siyasa tuni ya fada harkar siyasa….. Muhammad kuma Babban Dan kasuwa ne sai Sunusi dayake da shaguna hade da malls a Garin kano, kaduna da kuma Abuja, Sai autarsu Halimatu wacce ta zama babbar likita bangaren mata Wato Gynecologist, kuma tana Auran dan uwan mahaifiyarta wanda mahaifinsa ne ke da sarautar a lokacin…
Ibrahim na Auran yar Deputy governor Maryam .. Yaransu 4 Mata 2 maza 2(Salim, maleek, Humaira, Suhaima)
Sai Muhammad dayake da mata 3
Hajiya iklima Danta guda 1 Wato farouq
Hajiya suwaiba yaranta ( Ahmad , kabir , usman, Amna)
Hajiya sadiya yaranta 6 ( zaitun,Fatima,sahila,Ashraf Affan).
IMRAN kuma zaku san ko waye a cikin labari
Sunusi kuma Bashida yara matarsa 1 kuma Dansa 1 Muhammad (Abba)
Sai Halimatu tanada yara 3 maza 2 sai mace 1 Autarta wacce sai data jima sannan ta haifeta don ta dauka ma ta daina haihuwan. ( Saifullah, sa’id,Nimrah).
Dukkanin yaransu suna karatu, Ba wanda baya karatu wasu ma sun kama aiki, wasu kuma suna business.
Farouq ne ya gaji kakansu da zama cikakken soja wanda yake daff da samun matsayin major … sai farouq wanda Allah ya dorawa Alhj Muhammad Muhammad maitama Qaunarsa, Yana qaunar imran sosaii har son da yake masa baya boyuwa, shima ya dorasa akan turbar zama babban soja wanda a yanzu yake da Matsayin Major….
hajiya halimatu tana mugun qaunar yarta tilo guda 1 Wato Nimrah kasancewarta Auta kuma mace 1 da Allah ya bata, Soyayyar da take mata bai hanata bata tarbiya ba da kuma dorata akan turbar Addini, sai dai wani lokacin Nimrah na taba rashin ji na yaran zamani….
lokacin da taje korea aka mata Surgery ba qaramin bacin rai halimatu ta kwasa ba tayi fada sosaii… yawan kasashe kam sosaii takeyi sai dai Ba’a barinta taje ita kadai sai dai ta tafi da one of her cousins ko a dauka mata special guard …..
soyayyar farouq ce tai mata farar daya tunda ta sanya idanunta akansa, sabuda kasancewar ta mara son jama’a kuma ba me zuminci ba karatunta ma duk a UK tayi, Sai data gama tass sannan ta dawo Nigeria a nan ne ta jarabtu da zazzafan son farouq wanda ya hada harda obsession shiyasa take mugun feelings dinsa… wayewa baisa ta bada mutuncin ta ba haka kuma bata sa ta bawa wani Da namiji jikinta ya taba ba, Chan ma hakan ba ra’ayinta bane kasancewarta me kyankyami sosaii shiyasa ma bata hada jikinta da wani namiji sai akan farouq. For the first time ta hada jikinta da nasa kuma she’s soo sure and comfortable with him!….
Ibrahim is presently a Deputy governor na garin Adamawa.
Alhj Muhammad maitama y’a rasu presently, Hajiya zahra’u ce a raye sai tsufa daya kamata.
Wannan kennan!! A short biography of maitama family!!
Cigaban labari ✍️……