ZAZA&ZAK

Chapter 06

by @fatoumspen

ZAZA
Yau ta sha gantali ta qoshi… Har fada sukayu Da wani me Gyaran Mota ya fasa mata baki har gefen bakin yadan Kumbura, Thou shima sai data tabbbatar tabar masa tabo don sai data cire masa hakorin gaba sannan ta kumbura masa goshi…. sam da kely ne suke zugata , Kuma zak samm baya son Take fada especially with men, sabuda karsu ce zasu rama ta wata hanyar men of their Area are not to be trusted, kowa mugun kansa neh….
Tafiya sukeyi suna cin gyada heading to gidan kallo sabuda sunce bazasu hau machine yakaisu ba gwara suke a qafa, Suna tafe suna cin gyada, ZAZA gaba daya hankalinta bai bata ta nemi waje tai sallah ba kawai ta gwammaci idan ta koma gida ta jero su duka…
A haka suna tafe suna cin abinsu har suka isa wurin dayake somehow well developed, ba laifi wajen Da kyan sa kuma kaman hade yake da Bar, shiyasa wurin ya zamana kaman wani wajen shakatawa ga mutanen dake area din, ticket suka siya sannan suka shiga ciki, sam da kely suka siya bitter , ita kuma ZAZA dama bata sha sabuda sarai tasan Zak ya hanata., kuma duk rashin jinta tasan baya mata da wasa ubanta yake ci… 8:00PM za’a fara buga wasa tsakanin Madrid da Barcelona, wurin duk y’a kacha me da hayaniya anata musun ball wasu ma har kaman sayi fada, sai da attendant din wurin ta musu magana sannan suka nutsu, harda zaza kuwa a cikin wanda suke musun ball din ..

Mansir bayan y’a ajiye madam dinsa ya wuce barrack dauko Imran , Bayan ya dauko shi suka wuce hanyar gidan kallon da zasu, Imran har ya fara mita ganin irin Area din da suka zo…. dama sai da sukai magrib sannan suka fito … ko wannensu yaci riga da wando imran kam kaman don shi aka yisu… P cap y’a saka akansa sabuda baya son kallo hakan takura masa yakeyi, Even him sef knows he’s not 😂
Tun kan su shiga wurin imran ya fara qarewa wajen kallo.. a duk sanda zaiga wasu low lives sukan Tuno masa da wani bangare na rayuwarsa daya zame masa kaman wani ciwo da bazai iya warkewa dashi ba… Yana wannan tunanin mansir y’a tabasa tare da ce masa ya fito daga motar su shiga ciki, ba musu haka ya fito daga motar yana qara gyara zaman P Cap din dake kansa, tickets mansir ya siya musu, yana gaisawa da mutanen wajen su kuma suna sara masa sabuda Sanin wasu daga ciki dayayi, some are even his childhood friends don dai shi Allah ya masa daukaka….. Imran karewa wajen kallo yakeyi yana kallan mutanen ciki yanda yaga kowa yana sha’anin gabansa and how people are really happy with what they have and who they are …. saurin kauda tunaninsa yayi daga nan bangaren sabuda wani zafi da kirjinsa ya soma yiiii….. Ball aka fara gudanarwa  waje yayi tsitt ana kallo kowa attention
Dinsa nakai, Su imran ma haka don imran mayen ball ne sosaii ya so zama Footballer Allah ne bayyi ba….
Wasa yadau zafi ana gaff da cin kwallo daya wanda ake saka ran Madrid ne zasuci… Zaza sai harziqa takeyi kaman ita ke playing ball din , Ganin irin wasan da player din nasu keyi yasa ta daki cinya ta miqe tsaye cikin ihu tace “ BABA play ball naaaawwww!!! Which kind play ne dis noww “ tana magana tana kama ganan wandonta as usual… muryarta ce ta doki dodan kunnensa, without his acknowledgment ya samu kansa ya dago kai ya kalli Wace wannan dukda attention dinsa nakan ball din shima yana jin haushin kalan wasan da player dinsu keyi… Sauke idonsa yayi a bayanta sabuda player tana daga gabansu ne, bayanta kawai yake iya gani, a zuciyarsa yake cewa me namiji yakeyi da muryar mata kuma… don tunaninsa bai basa mace bace kwata kwata.. sam ne yaja ta ta koma ta zauna yana ce mata “ my guy calm down na”…… haka aka cigaba da buga wasa jikinta tsuma kawai keyi… imran dake zaune sai tsaki yakeyi , chan dai ta daki cinyar mansir yace “wtf kaga wani Dan iskan wasa da guy dinnan yakeyi “. Dariya Mansir yai yace “ Ai Naga alama wasan nan namu ne yau, bazakuci ba “  tsaki kawai imran yai don gaba daya attention dinsa nakan ball din….. within some seconds sai gashi Madrid sunci kwallo 1–1-0 .. ihu wajen yandauka, imran ya daka kafarsa a qasa yana cewa “ ehennn na now I dey watch football, sorry man amman as usual mu zamu lashe wasan nan”.   Tsaki mansir yai ganin anci team dinsu, har lokacin ZAZA takiyin Shuru sai maganganu takeyi… a haka har zo match din karshe anyi 2-2 .. za’a buga wasan karshe … kowa a tsume yake ana jiran aga suwaye zasuci, zaza kasan zama waje daya tayi kaman wata me jiran sakamako……
Dan wasansu ne ya buga ball bata sauka ko ina bai sai cikin raga…. zaza da imran a tare suka miqe suna ihun “ Goalll!!!!!!” 
Mansir baima damu da cinyesu da akai ba kawai he was just to happy seeing how excited his friend is, it’s been a while daya gansa cikin mood dinnan, his excitement was everywhere in his face he could no longer hide it …. he enjoyed every moment a gidan kallon nan da shida abokiyar ihunsa wacce ko fuskarta bai gani ba amman a ransa yana cewa Dan daudu da kallan ball…..lols…😂
imran really enjoyed the moment, basu bar wajen ba suka siya Champaign  a bar din wajen suka zauna suna sha…. zaza da maqogaronta ya bushe sabuda kwakwazo gashi ba damar ta sha bitter , kuma Wurin babu mineral daga Wines sai champagne sai bitters sai local wines … Hango su imran datayi a VIP suna shan champagne yasa taji wani abu na fuzgarta zuwa wajen don ta samu abinda zata zubawa bakinta, without a second thought ta nufi wajensu… Suna zaune suna sipping suna hirar su suka ga mutum a tsaye akansu… before imran y’a dago kansa ya tsinkayi muryarta tana cewa “ ehmm brozz sorry I badged , make una help me put something for my mouth, I’m super thirsty and I no won take the remaining things wey them sell for this place na only champagne I go take, because my broda forbid am for me to take anything Alcohol, and I don’t have money to buy this drink you dey take, make una help me biko “ tana hade hannayenta waje 2, tunda ta fara magana ya zuba mata ido yana son tunano inda ya taba ganin face dinta, shi kam mansir Dariya ma ta bashi, without saying anything to her kawai y’a miqa mata remaining champagne din dake Cikin kwalban, karba tayi da sauri ta fara kwankwada Sai data jiqa maqoshinta sannan ta dire musu, wani kallo imran y’a mata a ransa yana cewa me take nufi su sha ragowarta kennan ko meh? ….. shikam mansir kallon ikon Allah kawai yakeyi, kallanta takai ga Imran taga shima ita yake kallo hannu ta daga masa tare da cewa “ Oga yellow man Good day ooo I greet, this your friend is a good friend hold am tight “ Dariya  mansir yai yace mata “ Ahh telll home oo, but I thought say na Man U be before …” Dariya itama tayi tana kama gaban wandon ta tana gyara saman P cap dinta tace “ ahh broz na soo, na woman I be or you can marge am together make it man-woman “  mansir was enjoying the conversation he said “ Ahhh really Interesting but why can’t you take bitters or any alcoholic drink ?”  Qeya ta sosa tana sunkuyar dakai tace “ broz na muslim I be oo “ .. mamaki kwance a fuskarsu dukkansu suke kallanta, imran shi kam yama rasa me zaice ikon Allah kawai yake kallo, katse shurun tayi da tambayar Mansir «  black broz what time is now please I don’t have a phone with me RN , “ dauke idonsa yai daga kanta ya duba wristwatch din dake daure a hannunsa ya sake maida kallansa kanta sannan yace “ 9:30PM ma……”  bata bari ya qarasa ba ta wani dora hannu akai kaman zatai kuka tace “ I’m dead today!! brother zakk go kill me today , I don finish , eiiiiii “ Duk ta gigice bata sake bi takansu ba suka ga ta juya da gudu tayi wajen sam da kely dake zaune suna awkin shan bitter , tankado qeyarsu tayi suka bar wajen cikin sauri hankalinta gaba daya yayi kan zak…