ZAZA&ZAK

Chapter 07

by @fatoumspen

ZAZA & ZAK

F notes ✍️

 

Tunda zaza tabar wajen mansir ya juyo da hankalinsa wurin imran yace “ man kaga wani ikon Allah “ .. miqewa imran yayi yana gyara zaman wristwatch din hannunsa yace “ kaga don’t include me in your rubbish da kai da waccen yaron/yarinya or whatever, I have a lot to do tashi mu tafi “.  Tsaki mansir yai  yace “ kai Wlh you are so boring sometimes, is not your fault ma woman you need for your life tuni zaka daina wannan abun da kake “ wani kallo imran yaiwa Mansir sannan yace “ ni nace maka I’m in need of a woman ? don kai Dan iska ne shikkena kowa ma irinka ne”. Wata dariyar sheqiyanci Mansir yai yace “ swear say dis your manhood no need woman?, kaga nan babban Don iska is not you I saw the other day with your standing Dick, shi wannan kuma Aljanu ne kennan”  gaba imran yai kawai yana takaici da kuma kunyar abunda mansir y’a fada, shi kuwa Dariya mansir yake tun karfi harda qara ce masa “ my friend idan ka riqe mace zata ci ubanta Wlh …” qara sauri imran yayi jin batsar da mansir yakeyi…….

Machine suka hau sabuda su qara sauri don su samu su koma da wuri, gaba daya hankalinta nakan zak…. Sun sauka bata jira su sam ba tayi Gidan su cikin sauri, Tana zuwa kuwa ta tarar dashi a qofar gida yai folding hannunsa a kirji yana kallanta, bacin rai kwance a fuskarsa…. a hankali ta qaraso inda yake tsaye , bai kulata ba kawai y’a shige cikin gidan ta bishi a baya, har suka isa bakin dakin su, key din ta dauko a jakarta jikinta duk a sanyaye bude dakin tayi suka shiga, glove din dakin ta kunna, Zak bai ko kalli inda take ba kayan hannunsa y’a ajiye ya dau Jallabiya da soso da sabulu ya wuce toilet ruwa ya watsa ya daura Alwala ya sako Jallabiyan sa ya fito, Bayan ya fito still bai ko kalli inda take ba , sallah ya tayar ya gabatar da isha’i, yana idarwa yai Addu’oinsa….. Zaza duk a tsorace take ganin yaqi kulata gaba daya tasha jinin jikinta, Ga saloli da batai ba tasan yau me kwatarta a hannunsa sai ubangiji… Wani kallo ya watsa mata rai a bace yace “ tashi kije kiyi Alwala kizo kiyi sallalolin dake kanki “ ba musu ta miqe cikin azama toilet dinsu ta shiga ta daura alwala, Tana son yin wanka amman sanin ya hanata wanka da daddare.. alwala kawai tayi ta fito ta koma dakin nasu, Doguwan riga ta saka ta saka hijjab ta fara jero salloli, yana zaune yana kallanta yana nazarin ta har ta idar da rama sallolinta….. Sai zazzare ido takeyi, Miqewa tayi ta linke dadduma ta ajiye ta cire hijjab din shima ta ajiye…. A dake yace mata “ zo nan!” A hankali ta qaraso inda yake zaune ta zauna a qasa shi kuma yana zaune akan kujera, kare mata kallo yakeyi yana mamkinta sometimes yana mamkin chanzawar datayi tun zuwansu lagos , ajiyar zuciya yayi sannan ya fara mata magana” Fatima Zara!!” Tunda taji ya kirata da asalin zunanta yasa ya qara sunkuyar dakai tasan cewa tabbas yau asalin yayanta Zakariyya ne yazo… zak ya cigaba da magana “ Zara Kina son kisamin hawan jini neh?? dame na rage ki dashi? I’m I not providing enough? Bani kula dake yanda ya kamata? Kina tunanin inajin dadin irin rayuwar da mukeyi a matsayin mu na cikakkun musulmai! zara dame kikeso naji? Dake ko da irin rayuwar da muka tsinci kanmu? Zara I’m deeply hurt Wallahi “ … hawaye ne kawai suke zubawa idonta zuciyarta na mata radadi… shima daurewa yakeyi kar ya zama weak y’a cigaba da magana “ zara Kinsan hukuncin wanda yake tara sallah kuwa, ai inaga bama saina tuna miki ba , idan kika mutu kicewa Allah  meh? Wani excuse kike dashi naqin yin sallah? Don kinga bacin rana yana sawa wataran mu hada sallah baki ganin irin babban dalilin dake sawa Bamuyi? kin san a garin da muke kinsan irin mutanen da muke zama dasu, why are you trying to make things hard for me ? I’m I not a good brother…” muryarsa na tsinkewa… cikin kuka ta bude baki tace “ Yaya zakariyya!”  Dakatar da ita yayi “ ban gama magana ba “ … sunkuyar da kanta tayi “ zara ina jin takaici da haushin irin rayuwar da kika tsinci kanki abin namin ciwo , ya kikeso nayi? Kina ya mace amman ji irin rayuwar da kikeyi, age mates dinki a inda muka baro duk sunada aure da yara, Ko kaya da kika nasa ki dinga sawa sabuda kareki nakeyi daga sharrin kwadaituwar maza sabuda kyan sura da Allah yai miki, duk abinda kika ga inayi I’m just trying to protect you! Wallahil azim wallahi zara ba irin wannan rayuwar nakeso yar uwata tayi ba , Wallahi rayuwa me inganci nakeson gina miki , rayuwa me kyau nakeson gina miki ba irin wannan ba , Zara ba yarinya bace ke you are 23 for God’s sake !, ina jin ciwon yanda ban bawa rayuwanki meaning ba dukda nasan Allah ne keyin komai, amman yaci ace idan ma karatu ne nasa kinyi kema ki zamo abinda zaki alfahari dashi ko bayan raina ki tuna da gatan danai miki …”  jikinsa ta fada tana wani irin kuka ce cin rai, shehsekan kukanta ne kawai yake tashi, sosaiii maraicinsu ya taso mata a wannan lokacin, duk yanda yaso daurewa shima kasawa yai hawaye ke zuba a idonsa , patting back dinta yakeyi alamun rarrashi sannan y’a cigaba da cewa “ idan kina wasu abun nasan ba laifinki bane , laifi nane dana kasa baki ingattaciyar rayuwa!” Wani kukan ta sake fashe dashi, cikin rawar murya tace “ Wallahi… ya.ya ka bani.. komai kamin komai… I’m a bad sister,… duk kokarin da kakeyi akaina… na kasa samar maka..kwanciyan hankali…I’m sorry Yaya….” Kuka takeyi sosaii shi kuma yana patting back dinta sannan yace “ shhhhhh! Kukan ya isa haka kina so kanki yai ciwo neh? …. Inaga idan kikaga na fadi na mutu zaki fi nutsuwa ai ko Baby zaa dita “ Wani kukan ta sake fashewa dashi tana shesheka tace “ Yaya you will not die Wallahi na daina komai zan dinga sallah Wlh akan lokaci Wlh na da….ina.. fada … da kowa…” …. Shuru yai for some seconds sannan y’a dago ta daga jikinsa suna facing juna sannan yace “ zara I’ve made some decisions, daga yau bazaki qara bina Yawon Bus ba , na samu wanda zaike tayani, sannan no more roaming about a gari, na soke yawo sannan na soke zuwa kallan ball ke kadai idan kina so we’ll go together, sannan bazan iya rabaki da su kely ba but yawo dasu ko ina na soke shi!…. Dama I didint want you to be indoor Shiyasa nake barinki kina fita kuma nake barinki muje driving tare harna koya miki ma… Stay at home kafin na samu kudin da zan sakaki a a makaranta, karatu zaki cigaba gwara ki zama Architecture din da gaske tunda you have the talent .. you must change Zara “