Chapter 01
by @fatoumspen
Bismillahir rahmanir rahim
Chapter 01
F notes ✍️
ZAZA,ZAK&
LAGOS STATE iwaya lagos main land LGA, Da misalin Karfe 10:00AM Waje ne ciki da hayaniya very busy and crowded ba wanda zai ga wurin yace wai Safiya ce sabuda yanda wajen yake a hargitse, mutane iri iri, masu sana’a nayi masu Fada nayi masu abun hawa na fama da customers, masu shaye shaye nayin abunsu ba ko Darrr……… wata hayis ce cike da mutane, yanda ake hayaniya a wajen zaka san cewa fada akeyi a wajen sabuda yanda ya kachame da hayaniya yawancin yaren dake tashi a wurin pidgin English ne Wato broken English, sosaii mutane suka zagaye Bus din ana kallan ikon Allah…….. wata budurwa ce sanye da wani bujen wando black color sosaii wandon ya mata yawa banda belt data saka ta daure shi dan tsaff zai fado sabuda wandon babba ne , ga wata Red T shirt itama qatuwa a jikinta, Sai P cap baqa data saka a kanta ta maida gaban hulan zuwa baya irin yanda wizaye sukeyi, sosaii shigar maza ne a jikinta, Musamman wani cover takalmi dake qafarta wanda yaji jiki yaji duniya …… Hannunta saman wandonsa ta Damko belt din wandon nasa da iya qarfinta take jijigashi da Riqon gaske datayiwa belt din nasa, qarfaffan bayeraben data riqe ne ya fizge P Cap din datake kansa cikin masifa irin ta zafin yarabawa yace “ Keehhh!! I go wound you ooo no try me this early morning, I go slap you…..” bata bari ya qarasa maganr da yake yi ba ta wani daki kirjinta da dayan hannunta cikin Masifa itama ta fara magana dukda tsayin da gayen ya fita amman hakan baisa taji shakkarsa ba “ touch me if dem born you well , uwaka!!! If you no touch me , seee Oga cow boy you must pay me my money ooo , stop raising nose like buns wey see yeast finish , I no de fear you “ … wajen ne ya sake kachamewa wasu na qoqarin rabasu wasu suna zugata taci ubansa ta karbi kudinta, Fada akan kudin Bus ba baqon abu bane a wajen mutanen … wani dogon saurayi ne sanye da Riga da jeans ga wani kyalle daya daura akansa ga karan sigari daya soka a gefen kunnensa, wajen ya nufo cikin bacin rai yana zuwa ya kutsa cikin mutanen har ya qarasa inda budurwar ke riqe da wandon qato…. Hannunta ya fizge daga jikin wandon mutumin cikin bacin rai ya kalli qanwar tasa ya bude baki cikin harshen broken yace “ZAZA wetin happen ?” qugu ta kama cikin masifa da karaji ta fara masa bayani tana wani juya manyan idanunta“ Brother ZAK make una talk to this man ooo I no won wound pesin this early morning, tell him to give me my remaining balance “ Kallan mutumin yayi sai huci yakeyi kafin yayi magana mutumin ya Rigasa bude baki cikin daga murya yace “ n ko fe ba e ja( I don’t want to fight you) since when did you start picking customers from agege to iwaya for 500 Naira , na 300 I go pay oo” … Damkar wuyansa zak yayi Ya matso dafff dashi suna shaqar tsamin juna yace “ Oga na me you go follow talk not my sisa, make we talk man to man, you go pay 500 now now or I’ll call my boys to scatter your face “ … Jin za’a kira masa yara yasa yace “ is not because I’m scared of you that I’ll give this money na because I get place to go …Mtswwww Ole “ hannu yasa a aljihu ya ciro 500 ya wurgawa ZAZA, Hannu tasa ta dauka tasa A jakar dake zagaye a qugunta… Nan suka qara misayar yawu daga baya kuma kowa ya watse aka cigaba da sabgogi. ZAK ya tada Bis din ZAZA ta dafe motar irin yanda kwandasta sukeyi tana ihu da duk karfin muryarta tana kiran sunayen anguwanin da zasuje ko zasu samu wasu customers din………..
Wajajen 5:00PM suka Paka Bus din tasu a tashar da ake ajiye motoci , fitowa sukayi a tare suna hira cikin yaren hausa , ZAZA tana tafiya tana kama gaban wandonta kaman wata namiji sai wani karkacewa takeyi kaman Wata wizi kaman ba mace ba , kallanta Zak yayi yace “ wai ke ban hanaki kama gaban wandon nan ba , uban me kike kamawa “ … hannu ta daga masa sama alamun bada hakuri tace “ calm down boss I dey sorry “ .. tsaki yayi ya wuce gaba ta maza ta bishi a baya, suna tafe suna gaisawa da chafkewa da mutanen su , don ba qaramin sani aka musu ba a area din , yawancin mutanen area din sun san ZAZA da ZAK haka kuma yawancin mutane ke qaunarsu wasu kuma najin haushin su,wasu kuma ba ruwansu dasu……. , wani waje sukaje inda wata matashiyar mata dake siyarda abinci kanta sanye da wani Wig dayaji jiki ga rigar data saka ta matseta ga uban tumbi, Fuskar nan ta sha makeup, suna isa wajen matar ta hade rai ta kauda kai daga kallan su, ZAZA ce ta fashe da Dariya ta kama gaban wandon nata ta fara wani tsalle tana hailing matar “ Mama cimaka the best cook of this town, you no say your food sweet pass Five start hotel own, see mama your………” katse ta matar tayi tare da daga mata hannu cikin Dan hade fuska tace “ ZAZA don even start , me i no go give you any food today until you pay me my money , ahhh me I don talk finish, please make una shift don block my customers way” Zak ne ya karbe zancen da cewa “ ahh mama ciamaka calm down naa we go give you your money how much is it sef?” … gayara zamanta mama ciamaka tayi tana harar zak tace “ Na 10k , na transfer or cash ?” Wani zaro ido ZAZA tayi Cikin sauri tace “ chimooooo mama ciamaka 10k for wetin? for the rice wey no even cook well” hannu Zak yasa ya bige bakin ZAZA cikin masifa yace “ if I hear your mouth again I swear I go wound you “ .. riqe bakinta tayi tana ta qunquni… babu me tsawatar mata ta nutsu irin yayanta zak shi kadai take dagawa qafa shi kadai yake mata yanda yaso, bayan shi ba wanda ya isa ya takata ta kyalesa…. hannu yasa a jakar dake rataye a qugunsa ya lissafo 10k ya miqawa matar sannan ya qara dauko wata 4k yace ta basu Beans and roasted plantain sai pure water… zuba musu tayi tana sakin fuska sabuda an biyata kudinta, karba sukayi suka wuce gida , suna tafe suna gaisawa da jama’a….. Around 5:30PM suka shiga gidan nasu …
Gida ne irin gidan hayar nan me dakuna a jere , me dauke da mutane daban daban, compound din gidan kacha kacha sabuda tsabar ido kar wani ya gyara wani ya mora shiyasa gidan kacha kacha, yara ne gasu nan birjik sabuda Akwai ma’aurata a gidan kuma akwai masu zaman kansu…… Shige da fice kawai akeyi wasu na wanki wasu na girki, yawancin mutanen dake gidan Christian ne mutum 2 ne musulmai wanda sunada aure tare da iyalinsu suke zaune a gidan kuma yarabawa ne. ……. Tun shigar su gidan ta hade rai sabuda kar wani ya kawo mata wargi Don fada ba wani baqon abu bane wajenta yanzu zata zage su daku da mutum duk girman sa kuwa, shigowa cikin gidan sukai Zak shima bai kula kowa ba suna daff da bude dakin su wata mata sanye da hijjab wacce ake kira da mama Abdul ,wacce take daya daga cikin musulman gidan kuma matar Aure ce, Ganin Matar ta nufo zaza,, daure fuska tayi ta kauda kai, matar wajen su ta qaraso da fara’arta a fuska, bude baki tayi tace “ Assalamu alaikum ZAZA welcome back , I greet you oooo” zak kallan matar yayi ya kauda kai don shi ba Ruwan shi da sabgar mata, ZAZA ma kusan hakan take tafi gane rayuwar ta sometimes cikin maza ko kuma matan da suka kasance irin ta masu irin halinta, don a nata tunanin mata wanda suka amsa sunansu mata duk munafukai ne….
Hade rai zaza tayi tace “ hold your greeting ma wetin happen ? You owe me? “. Murmushi matar tayi tace “ no I just say make i greet my Neigbour “ .. ZAZA ta kauda kai daga kallanta tace “ Okay I hear you Thank you” daga nan suka shige Dakinsu suka barta tsaye, mutanen gidan ne suka fara mata Dariya wasu suna gulmarta, bata kulasu ba ta wuce dakinta ta rufe….. Daki ne babba wanda suka raba shi gida 2 tare da saka labule wanda ya zamana shi kadai ne ya raba musu dakin, palour ne a farko sai Daki dake bayan labulen, wasu kujeru ne guda 2 wanda sukaji jiki duk pachi jikin su sai wani carpet dayake a shimfide a palour din ga yan tarkacensu tukunya da gas Da dan abinda ba’a rasa ba , dakin kuma katifa ce a shimfide da bedsheet sai wata katifar a jingine, Kayan su kuma a cikin bakko sai abun wankansu dake gefe a ajiye da mai da turare guda 2 sai Dan mudubi da aka manna a bangon dakin, babu wasu tarkace sosaii a dakin amma a tsaftace yake tsaff tsaf…..
Rufe kofarsu sukayi bayan sun shiga , takalmansu suka ajiye a kofan, Zama akan kujeran zaza tayi sabuda gajiyar datayi, shima zak zama yayi ya daga kansa sama tare da rufe idonsa kaman me tunani, chan ya tsinkayo muryar Zaza tana ce masa “ brother please make una bath you don spoil the air wey inside this room…..” bata gama rufe bakinta ba taji saukar P cap dinsa a fuskarta, miqewa tayi a zabure tana kama gaban wandonta tace “ ahhh ni karka jimin ciwo wlh Don na gayama gaskiya “ harararta yayi yace “ ke ai kamshi kikeyi, Qazama number 2 kuma kizo muyi sallah “ itama hararsa tayi tana shinshina jikinta taji ko da gaske warin takeyi, bata tanka masa ba ta daga labulen ta shige dakin, kayan jikinta ta cire ta ajiye sannan ta dauko wani zani ta daura ta dauko hijjab ta zura sannan tadau bokiti da sabulu da omo ta fito, shima miqewa yayi ya shiga dakin ya cire kayan sa ya zura jallabiya sannan ya Kwashe kayan nasu ya ajiye inda suke saka kayan wanki…. Tana fita ta daure fuska, wajen rijiyar taje ta bude ta debi ruwa ta cika bokitin, daya daga cikin bandakin gidan ta shiga wanda shine mallakin yan part din su domin bandakin biyu ne sai me gidan ya raba musu… ba laifi bandakin bai wani lalace ba dayawa, shiga tayi ta fara wankewa sannan tayi wanka ta daura Alwala ta zuro hijjab dinta ta dauko sabulu da sosan ta fito, rijiyar ta sake zuwa ta sake cika bokitin ta kai bandakin ta ajiye, dakin nasu ta koma tacewa zak takai masa ruwan wankan, fita yayi shima ya tafi watsa ruwan, kafin ya dawo har ta shirya cikin wando da riga as usual sai dai wannan ba jeans bane palazo ne me laushi da yar T shirt ta shan iska… hijjab ta zura ta shimfida musu dadduma tana jiransa ya dawo, ya dan dau lokaci gashi anata haramar Kiran magrib… shigowa yay da bokitin da kuma Soso da sabulun ya riga daya shiryo a bandakin yana shigowa turare kawai ya fesa ya saka hula tashi kafiya naci ya jasu sallah, qira’a ce me dadi ke tashi a palour din nasu, cikin nutsuwa yake karatun, haka suka jero sallah tun daga Azahar har zuwa magrib da aka gama kira domin akwai masallaci a wurin sabuda musulman dake Area din wanda ba wani yawa gare su ba yan kadan ne, kuma a hakan arnan wajen adawa sukeyi da masallacin shiyasa ba koda yaushe ma ake jin kiran sallah ba sabuda sun hana hakan sai dai in limamin ya basar ya kira kawai wanda shima kiran sallah da yakeyi Cikin tone din yarabawa don bayerabe ne shima ……. Suna idar da sallalolin dake kansu Zaza ta fara qoqarin fizge hijjab din jikinta don wani zafi ne yake addabarta dukda akwai fanka, hannunta dake kokarin cire hijjab din ya bige cikin hade fuska yace “ wai ke bazaki hankali bane , kullum sai na tuna miki”. Tsuke fuska tayi tana cewa “ what now ?” Harara ya aika mata tare da janyo adhkar hard copy ya dau 1 ya miqa mata daya, Tana bata fuska ta karba , sai da suka gama sannan suka ajiye, sai wani sosa ciki takeyi alamun yunwa ya dameta, ledan da suka siyo abincin suka janyo plate ta dauko suka juye sannan suka faraci bayan sun gama suka sha ruwa zaza tayi gyaysa tare da yin hamdala, wayar sa ya dauko daga cikin yar jakar yasa chaji, Itama jakarta ta dauko ta dauki keypad dinta tana ganin missed calls din qawarta Kelly, kiranta tayi bugu 2 ta dauka , ba sallama ba komai suka hau hailing din juna suna cewa juna my guy , Suna cikin wayar ne kelly take ce mata ta fito su hadu akwai sabga, Kai ta dago ta kalli zak dake kallanta dauke idonta tayi daga kallan sa tace ” my guy I go call you back” ta katse wayar ta ajiye, kallanta yai ya hade rai yace “ karki kuskura kicemin fita zakiyi “ sosa keya ta farayi cikin rashin gaskiya tace “ Brother see Wallahi I go come back soon, na kelly dey wait for me outside we get some things to do, biko no stop me please Abeg” tsareta yayi da idanu yana karantar ta daga bisani kuma yace “ I’m going out so ina kikeso mu ajiye mukullin idan na rigaki dawowa wa?” Miqewa tayi cikin jin dadin zai barta ta fita tace “ hold am I go wait for you outside zan jiraka idan na rigaka dawowa “.. da haka sukai shawara, tashi yai ya chanza kayansa zuwa Riga da wando ya dau yar jakarsa ya daura kyalle a kansa ya fita, Itama shiryawa tayi cikin Riga da wando da suka mata yawa sosaii, zak ne ya dasa mata wannan dokar na saka kaya da zasu rufe surarta sabuda gudun yan iska, shiyasa duk yawancin kayan nata manya ne sun mata yawa … tana gama shiri tadau p cap ta saka a gashinta dake cikin wata yar qaramar hula kuma a nannade yake, jakarta ta dauka ta rataya a qugunta sai wayarta data saka a charge tabar su suyi chaji tadau mukullin room din ta fito ta rufe itama tayi waje……..