LULLUƁIN BIRI

26

by @halimahz

*Bayan wucewar awanni shida. Miyyetti Hospital, Room 05.*

Cikin vip room ɗin, Turaki ne jingine a jikin pillow ɗin da aka saka masa a bayansa, goshinsa ɗaure da bandage, an naɗe wurin da ya ji ciwo da shi.

Gefensa kuma wata farar tsohuwa ce kamar balarabiya a kan kujera, da siririn farin medical glass a idonta, ta yi jugum tana ta kallon jikan na ta. 
Lokacin da aka kawo Turaki da Zaytuna asibiti, lokacin ta kira wayar Baffa take sanar masa tana ta kiran wayoyin yaran bata samu, har ta Babarsu Hajiya Madina ma ta kira bata samu ba, shine Baffan ke faɗa mata halin da suke ciki na cewar suna asibiti, Zaytuna da Muhammad duk sun suma, kuma sama da rabin awa babu wanda ya farfaɗo a cikinsu.

A lokacin Granny ta kira ɗanta ta ce a yanzu ba da ɓata lokaci ba tana son zuwa nigeria, kuma a awa biyar da minti hamsin da biyar sai gata ta a asibitin cikin tashin hankali, sai dai ko lokacin da ta zo ɗin duk sun farka, Zaytuna ma har ta miƙe, shine dai ke kwance saboda ciwon da ke jikinsa.

Granny ta numfasa ta ce,"Ramla dai ta cuci kanta, don ba zan ce ta cuce mu ba. Ka san me? Do you know what I want from you Muhammad?"

Turaki ya haɗiye abu ya kalleta yana jiran cewarta. "Muhammad ka manta da Ramla, ka manta da ita da abin da ya shafeta, ka samawa kanka lafiya, ka samawa kanka kwanciyar hankalin da ka rasa tun ranar da tasa ƙafa ta tafi ta barku...".

Turaki ya katse ta da cewa,"Granny, do you know what you’re saying?"
Ta jijjiga masa kai ta ce,"I know Muhammad. You should forget Ramla, just like she has forgotten you."

Jinginar da kansa ya yi, ya sauke nauyayyan numfashi ya ce,"Granny hannunka baya ruɓewa ka ce zaka yanke ka jefar". 

Ta ce,"Idan ta kama a yanke sai a datse shi a huta da ciwo. Komai ai kamawa take".

Idonsa na kallon ƙasa ya ce, "Kar ki manta, duk lalacewar uwa—uwa ce. How can I possibly forget her? Kina nufin na manta da ita da duk abin da ya shafe ta? As in, how? Ki daina faɗar abin da ba zai yiwu ba Granny."

Yanayin yadda ya yi maganar ya ƙara bata tausayi sosai. Ya rumtse idonsa, zuciyarsa na tafarfasa, ya ce, "Even though I was six years old at the time, Granny I still see everything clearly in my mind. Ina kallon lokacin da ta sa ƙafa ta yi tafiyarta ta barmu ba tare da ta waiwayi kukan da nake yi ba. Ba ta dubi kukan Zaytuna da ke naɗe a cikin showel ba. Ta yi tafiyarta ta barmu, as if ba daga jikinta muka fito ba, as if ba ita ta kawo mu duniya ta hanyar aure na sunnah ba. What if the fire had burned us? What if we had died? Da Allah bai kawo Maama a lokacin ba fa?”

Duk girmansa, duk jarumtarsa, babu wani abu a duniya da ke hana hawaye sauka masa farat ɗaya idan ya tuna da wannan lokacin. Ba ya sanin lokacin da hawayen ke zubo masa a kan kuncinsa, sai dai kawai ya tsince su suna zuba.

Rumtse ido yayi sosai, a cikin kunnensa yana jin sautin kukan Zaytuna da ta dinga tsalawa a wancan ranar, yana jiyo na sa sautin kukan da ke fita da harufan sunan Mum. Yana jin komai kamar yanzu yake faruwa, tana fa kallon yadda wuta ke ci a ɗakin, amma ta tankaɗasa ya koma ciki ta rufe ƙofar ta barsa daga shi sai jaririyar da ke cikin gado kusa da inda wutar ke daɗa kamawa, ta yi tafiyarta ko tausayinsu bata ji ba, Me suka yi mata?

Har yanzu tambayar da yake ta so yayi mata kenan, ya ganta ya tsuguna a gabanta ya tambayeta zunubin da suka aikata mata, sannan sai ya roƙar musu yafiyarta, idan ta yafe musu sai ya bata labarin abin da yake ɓoyewa kowa a halin yanzu, kowa banda Bello da Zaytuna.

Amma kuma a ina zai ganta? Yaushe zata dawo gare su? Ta na raye ko kuwa ta bar duniyar?