LULLUƁIN BIRIFree

ArewaPen original

RomanceFreeOngoing

LULLUƁIN BIRI

  • 1views
  • 72chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

ongoing

No synopsis yet.

About the author

Sunana Halima.hz, ni marubuciya ce, kuma ƴar kasuwa mai siyar da nau'in sutturun sawa. Ina rubutu don in rayar da abubuwan da mutane ke ji. Ba na rubutu don nishaɗi kawai, ina rubutu don motsa tunani. Kowanne labarina yana ɗauke da murya...

More from @halimahz

Sample · 1

*1**APRIL 20th 2021.**American Hospital Dubai, 2:30pm.*_"Hey don't move, we are us navy seals...God! Damn it...we have a tango in the north wing every week. stop! stop! stop!...great team work guys, yeah we will mark you for the assist on this one."_Sautin da ke fitowa kenan daga cikin ƙatuwar plasma ɗin da ke manne a bangon ofishin, cikin wani american film me suna Steel Brigade. Dai-dai lokacin da sojojin su ka kama mutumin da ke sanye da mask, dai-dai lokacin Yusuf da ke juyi akan kujerarsa yasa tafukan hannunsa duka biyu ya shafo fuskarsa tare da fitar da iska daga bakinsa. "Ohh dammm it"."Ai na faɗa maka sai sun kama shi". Kalid wanda har yanzu bai ɗauke idonsa daga kallon tv ɗin ba ya faɗa a sa'ilin da duka haƙoran gabansa ke bayyana a waje alamar yayi farin ciki da abinda ya faru.Yusuf ya ƙara juyawa akan kujerarsa zuwa gefe guda sannan yay guntun tsaki yace,"Ko waye producer ɗin nan sam bai iya tsara film ba"."Hhh to ai hakan shine dai-dai, kai kana kallon sojojin nan kasan bana banza ba ne. Kuma gwara a kama shi tun a farko, wasan zai fi tafiya dai-dai"."Kuma wataƙila ya suɓuce masu ba"."Ta ya ya? Macece fa ai da kamar wuya ta iya ƙwacewa"."Wannan ai ba mace ba ce"."Bari su buɗe fuskar zaka gani, ai yanayin gudun kaɗai zaka fahimci macece, mace mai kamar maza kenan".Shirun Kalid ɗin ya haɗe da san da sautin maganar film ɗin ta ci gaba da tafiya, nan su kai shiru suna ci gaba da kallon._"Get the mask!!...there is no harmful in the air we already checked, expect for the thorpe's breath."_ Ɗaya cikin sojojin yay maganar a tsawace inda a take ya fizge mask ɗin daga fuskar mutumin, kuma lokaci ɗaya zaton Khalid ya bayyana, hakan kuma ya wanzar da dariya a fuskarsa, nan ya juyo ya kalli Yusuf da ke aikin jan gajeran tsaki babu ƙaƙƙautawa alamun ba hakan yaso ba.Lokacin da Yusuf ya buɗi baki zai yi magana lokacin ƙofar ofishin tayi ƙara, aka turota a hankali inda wata matashiyar budurwa ta bayyana hannunta riƙe da wasu takardu, jikinta kuma sanye da unifom na ma'aikatan jinya. Ta mayar da ƙofar ta rufe sannan ta ƙaraso cikin ofishin tana ƙarasawa gaban tebirin da Yusuf ke zaune kan kujera yana juyawa gefe zuwa gefe a hankali.Cike da girmamawa ta rissinar da kanta tare da aje fayel ɗin hannunta akan teburin tana tura su zuwa gaban Yusuf. "Ranka ya daɗe ga result ɗin da aka samu". Ta faɗa tana harɗe hannayenta zuwa baya."Ta farka ne?". Yusuf ɗin ya tambaya a sa'ilin da ya buɗe fayel ɗin yana dubawa."Ehh ranka ya daɗe ta farka wajen ƙarfe ɗaya da minti goma sha biyu, amma bata fi sakan huɗu ba ta koma, da alamu dai har yanzu da saura kamin ta dawo hayyacinta".Shiru ya biyo bayan maganarta, idon Yusuf ta cikin farin gilishin da ya manna na bin rubutun da ke cikin fayel ɗin, karantarsu yake da fahimta, wucewar daƙiƙa ɗaya, Biyu, Yusuf ya ɗago kansa akan...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters72
premium0

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play