HADUWAR DARE

Chapter 7&8

by @meenatyandoma

***

*HAƊUWAR DARE*

©️Meenat A. 'Yandoma

MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION

Page 7&8
...Wayarta take ƙoƙarin lalubowa sai dai ji ta yi ta taɓa wani abu mai laushi a daidai lokacin da wutar dakin ta karasa daukewa. Walau wutar ta dawo lokaci daya, da sauri Zainab ta kalli inda wayarta take. Luƙeƙen ƙafan ga wanda ake kira da jankwataki ya bude katon bakinsa ta gani kwance saman wayarta. Ihu ta kwana ta daka uban tsalle tare da nufar kofa. Security din da ke bakin da gudu ya taso ya na fadar lafiya. “Maciji mai kama da kadangare a cikin falo” ta karasa maganar tana neman rirrike mai gadin. Kasancewar gudan akwai wutar nefa shigewa ya yi sai dai neman duniya ya yi amma babu kadangare kai ko bakar leda bai gani ba bare ya yi tunanin wani abin cutarwa ya shigo. 
“Hajiya! Mafarki ne kika yi, hakika babu komai a cikin gudan nan. Me ma zai fiddo kadangare da daren nan shi da in dare ya yi baya gani kwata-kwata”
“Baka ga komai ba? Me kake nufi” 
“Ina nufin babu kadangare a cikin gidan nan ya karasa maganar yana kokarin zama” 
“Wallahi karya kake. Baka isa ba sai ka shiga ka fito mini da kadangaren nan in ba haka ba yau sai Umar ya canza mana security din gidan nan” ganin zata kulla masa salalar tsiya komawa ya yi cikin falon ya barta tsaye a farfajiyar gidan. Tsikar jikinta ce ta tashi lokaci daya, in ba kunnenta bane kamar muryar almajiri ta jiyo a waje. “Almajiri kuma a wannan unguwar? Kai Aa kunnuwa na ne. Me zai kawo almajiri a irin wadannan unguwannin? “Ki taimaka min da ruwa” muryar ta daki dodom kunnenta. Samun kanta tayi cikin mabayyanin mamaki, kofar get din ta kama ta bude. Karamar yarinya ce ba zata haura shekara goma sha uku ba baka ce ta ban mamaki irin bakin da tunda Zainab take a ranar ta fara ganinsa. “Ki taimaka min da ruwa mai sanyi” muryar yarinyar ta daki dodom kunnuwanta. Duk da ta tsorata da ganinta karfin halin fara magana tayi. “Baiwar Allah daga ina a cikin daren nan haka? Ban gane ki ba ko sabbin zuwa unguwar nan ne, ga shi ko sunanki ban sani ba?”
“Za ki gane ni yanzu ba da jimawa ba. Ki fara bani ruwan” yarinyar ta fada tana kallon kwayar idon Zainab. Juyawa ta yi cikin gidan store din ta dake gefen dakin mai gadi ta shiga da nufin dauko ruwan. Ihu ta kwala jikinta na kyarma cike da tashin hankali. Yarinyar ta gani rike da kwalbar lemu. “Ya na ga kin firgita? Na zo na dauka ne domin na fahimci baki iya sauri na, ina matsayin bakuwarki kin kasa karrama ni. Ja da baya ta fara yi tana kokarin guduwa, sai dai ji tayi kamar an daure ilahirin jijiyoyinta ta kasa kwaikwayo motsi. Karo na farko da ta tuna da sunan Allah, ji tayi ilahirin jikinta kamar an warware mata kulli. Yunkurawa ta yi da rarrafe ta nufi kofar fita. Ji ta yi an fizgota da karfin tsiya anyi baya da ita. Saman iska ta ga yarinyar na shawagi kamar tsuntsuwa. Kara himma tayi ganin ta na ga da kofar fita. Wani abu mai kama da Kwalba ta ji saukarsa a goshinta. Daga nan sai ihunta security ya jiyo, kwance ya ganta cikin jini goshinta duk ya ɓaci da jini. Iyakar rikicewar ya rikice Number Usman ya kira amma ina ga shi dai ta shiga amma miss Call biyar ba a dauka ba. Gani ya yi idan ya bari ta ci gaba da zubar da jininta, komai zai iya faruwa. Kasancewar akwai key a hannunsa bai bata lokaci ba wurin sakata mota ya dauki hanyar asibiti...
Usman kuwa bayan sun gama sallah samun kansa ya yi da lalubo wayarsa, wayam bai ji taba. "Kash!" Ya furta a sa'in da ya tuna cewa ya barta a gida. "Zulfaida!" Ya fada a cikin zuciyarsa. "Bai kamata in koma gida ba. Tunda ko na koma babu amfani ba numberta ke gareni ba" ya fada a daidai lokacin da ya fito daga cikin masallacin. "Kayi sauri ka nufi gidansu " wata zuciyar tayi saurin umurtarshi. Bai bata lokaci ba sai ga shi a kofar gidansu, sai dai har yanzu gidansu akwai duhu sosai. Sabanin kowane gida ka kalla akwai hasken Nepa. Shawara ya ke ta yadda zai aika a fito masa da ita, gata dai ba irin unguwannin da ke da yara bane bare ya aika wani. Matsawa ya yi kofar gidan, ya sunkuyar da kansa kasa ya na tunanin ta yadda zai fito da ita. "Umar bani na ce zan kira ka ba" kamar daga sama ya ji muryarta ta daki dodon kunnuwansa. Sai da ya san firgita ganin Zulfaida tsaye a gabansa cikin shigar bakaken kaya.
"Yaushe kika fito ba tare da na sani ba" murmushi ta yi duk da cikin duhu suke sai da ya hango hasken haƙora ta. "Daka aika wani da yanzu wani zancen ake yi, gidanmu ba irin kowane gida bane shigarsa ba tare da izini ba zata iya aika mutum ga da-na-sa-ni. Ya akayi ka zo ba tare da izini na ba?" Shi ma din dariya ya yi. "Hukunci Indai naki ne a shirye nake na dauke shi. Ai da na san haka ne bazan nemi izinin kowa ba zan kutsa kai cikin gidan."
"Hmm! Mu ajiye wannan maganar a gefe! Tunda mun gaisa zan iya komawa ciki?" Ta karasa maganar tana kallonsu. "Haba dai daga fitowarki kamar dai kina korata, ni da ya kamata mu shiga daga ciki in gaida Hajiya in bata hakurin kade mata diya da nayi"
"Zaka shiga amma ba yanzu ba sai In ka dawo a wani daren"
"Dare kuma? Ni zanyita zuwa ne da dare?" Usman ya fada da mamaki a fuskarsa.
"Kwarai kuwa! Domin ni ba a gani na sai dare kaf jama'ar gidanmu da dare ake samun damar ganinsu." "To shi  kenan. Amma dai bazan bar kofar gidan nan ba sai kin bani wani abu da in na tafi zai rika tunanin da ke, In ba haka ba gobe da sanyin safiya zan dawo gidan nan" Zoben da ke sanye jikin dan yatsanta ta fiddo. "Ga zobe in Ka murza shi ma zaka iya gani na" murmushi Usman ya yi "kamar a Film sai In ga kin bayyana ko?" Ya karasa maganar cikin zolaya. "Kwarai kuwa! Yanzu dai sai da safe na maka alkawarin zan kiraka saboda ka samu numberta." Bata jira ya amsa mata ba ta shige gidan da sauri.
"Hakika ina kaunanki Zulfaida. A yadda na tsara rayuwata da Zainab kadai ta isheni, sai ga shi ƙaddara ta fado muni dole in kawo ki cikin gidana" ya karasa zancen zucin ya na mai zura Zoben a cikin yatsansa. Ya na tafiya ya na murmushi tamkar sabon kamu. Gabansa ne ya yanke ya fadi ganin kofar gidansa a bude. Turawan da zai yi sam babu Emanuel da sauri ya nufi falo. Wayarsa ce kadai ita ma Zainab bata nan. Five miss called daga Emanuel. A yanzu kam ya san koma meye babu lafiya. Toilet din ɗakinta ya Tura nan ma bata nan. Jiki na ciri ya dauko kira Emanuel, saka wayar ya yi a cikin aljihu ba tare da ya rufe gida ba ya nufi asibitin da suke. Bayan ya karasa kwance take goshinta ya sha bandeji sunyi mata allurar bacci. Daga ita sai Emanuel cikin dakin. "Lafiya me ya faru da ita?" Ya fada a daidai lokacin da ya zauna a gefen gadon. "Sir! Ina zaune a bakin aikina na ga Madam ta fito da gudu wai kadangare cikin falonku. Haka na shiga nayi bincike iyakar kokarina amma ko bakar leda ban gani ba, fitowa nayi na sanar mata sai dai kartajewa tayi akan ban duba sosai ba da idonta ta ga kadangare mai suffar maciji. Haka na sake komawa cikin fakon bakin kokarina na duba amma har yanzu dai babu, ina kokarin fitowa said ihunta na jiyo lokacin da na shiga store kwance take cikin jini ban san me ya faru ba"
"Subhanallah! Kana nufin babu wanda ya shigo bare kayi tunanin shi yayi mata haka? "
"Sir kai shaida ne wannan unguwar cike take da tsaro ko bera ba za a bari ya shigo ma mutum guda ba, sir ina cikin tashin hankalin halin da Madam take ciki"
Shuru Usman ya yi domin har ga Allah lamarinta ya fara ba shi tsoro.   Sallamar Emanuel ya yi ya koma gida ya rage dakin daga shi sai ita. Tunawa da yayi da masifar mahaifiyarsa ya saka shi lalubo numberta. 
Kwance take har bacci ya fara daukarta ringing din wayarta ya farkar da ita. Karamin tsoro taka ganin mai kiran, dauka ta yi ta kara ta a kunnenta. "Lafiya wannan uban kira da daren nan" shuru tayi na wani lokaci kafin ta ci gaba da magana. "Wallahi kayi karya, Ummin ce zata zo ta kwana da matarka ita ina iyayenta suke? To bude kunnuwansa da kyau ka jini. Ni ban haifa maku diya ba domin ta zo tayi jinyar matarka a asibiti. Ba dai ka ce ka ji ka gani ita kake so ba haka gata. Ƙitt! Ta kashe wayar. Ummi da ke gefenta ce ta taɓe baki "haka waccan munafukai matar tasa ce ya kira ki a kanta cikin daren nan"
"Ki bari kawai aura! Kin san da cewa yayi In bada ke kije asibiti ku kwana da ita suna asibiti. " Uwar ashar Ummi ta danna ta ɗora da fadar. "Mama ko zata mutu sai dai ta mutu idan sai na je" 
"Kwantar da hankalinki gobe zan masu dirar mikiya shi da ita ke har ma da damginta sai na yi abin da zai sakar masu diyarsu"
"Yawwa mamana! Shi ya sa nake kaunarki" kada kai suka suyi da nufin gobe da safe zasu yi ma asibitin dirar mikiya. 
Usman kuwa ya rasa me ke yi masa dadi, shawara ya yanke ya kira mahaifin Zainab ya sanar da su halin da ake ciki.
Ya na kashe wayar kira ya shigo masa da wata irin Number da Bai taba gani ba bare ya gane daga wace kasa ne. Sallamar da yayi ya kara wayar a kunne da, ɗif wutar dakin ta dauke. Ba shiri ya cire wayar daga kunnensa sakamakon wata hargowa da sautin ihu cikin mummunan amo da ya biyo...

Meenat A. 'Yandoma