HADUWAR DARE

Chapter 9&10

by @meenatyandoma

*HAƊUWAR DARE*

©️Meenat A. 'Yandoma

MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION

Page 9&10

...Ganin wutar dakin na faman fafarniya Shi ya Kara birkita Usmar da ke gefen gado. Ba Shiri ya kashe wayar yana rarraba Ido. Wutar dakin ce ta dawo lokaci Daya, ajiyar zuciya ya sauke ya na Mai Kara godewa Allah akan abinda ya faru. Motsi Zainab ta fara ga dukkan alamu ta farka. Bude Ido tayi ta mike tare da cakumar Usman "gata nan wallahi ita CE ina bude Ido na ga ta fita daga dakin nan" ta karasa maganar tana Shirin fashewa da kuka. "Wace ce ki nutsu mana" kokarin dakatar da ita ya ke yi ganin zata sauko daga saman gadon. Kanta tacusa tsakanin cinyoyinta tana kuka Mara sauti. Wani irin tausayi ta ba Shi har ga Allah Yana kaunar Zainab wata irin kauna da bata da misali. "Baby" ya Kira sunanta. Bata dago ba Amma ta tsayar da Kukan. "Ki kwantar da hankalinki kin samu accident a gida kin Jima a wurin nan a kwance yanxu ne aka samu kika farfado" "aljanu zasu kasheni bazan koma gidan can ba, Ka canza mini gida in ba haka ba wata ranar gawata zaka dawo Ka iske" "subhanallahi! wace irin magana ce wannan? Kin dai San Bana son zancen mutuwa KO kin manta tare zamu rayusannan mu mutu tare? Haba Zainab ki yi hakuri komai zai zo karshe in Shaa Allah " shuru tayi ta tsayar da Kukan tana ajiyar zuciya. Da kyar ya samu ta koma bacci, Shi dai ya kasa rintsawa tunaninsa daya Shi ne zuwan mahaifiyarsa gobe a Asibitin. Karar wayarsa ne ya katse masa tunanin da yake, number dazu ce  tsoro ya ke yi ya dauka sai da ya fita waye kafin ya dauka. A yanzu Kam muryar da bazai manta da ita ba wato ta Zulfaida ita ya ji. Sun Jima suba hira sai da dare ya Raba sosai ya koma cikin dakin. Shi ma don likita ya Sanar masa ga Shi nan zai duba jikin Zainab. Kamar an jefota haka ta fado cikin dakin, duk dakewa irin ta Maza sai da Usman ya tsorata. Sanye take da Kaya irin na nurse GA wata uwar allura a hannunta. Sai faman rarraba Ido take yi, kakkarfar mace baka Kirin ta tunkari Zainab dake kwance. "Baiwar Allah lafiya me like Shirin yi haka?" Ya karasa maganar tare da shiga tsakani. "Ka bani hanya likita ya turoni ayi Mata wannan allurar da gaugawa" cewar matar cikin wata irin murya tana zazzare ido. "Ke fita ki bar dakin nan ban yarda da ke ba, ki fita na ce" ya daka Mata uwar tsawa ya na mai nuna Mata hanya. Firgigit Zainab ta farka sakamakon hayaniyar da taji. Likitan ne ya shigo dakin ya na tambayar lafiya, "wannan matar ce ta shigo dakin kamar an jefota wai zata yi ma Zainab allura" "allura kuma? Likitan ya fada Yana kokarin kallon fuskar matar."wace ce wannan? Noo wannan ba nurse dinmu ba ce security kuna ina " wani irin tsalle ta yi ta fice da gudu kafin sunyi yunkurin kamata. Doctor da Usman tare suka take Mata Baya, Amma KO inuwarta Basu gani ba Mamaki sosai ya kama su, to wace ce wannan? Zainab kuka take cike da matsananciyar damuwa. Security din da Doctor ya tura me suka dawo suna haki. "Sir ba mu ga kowa ba KO inuwar ta bare kuma kurarta babu"  "Anya kuwa kun duba sosai? " "Kwarai kuwa sir mun duba sosai Amma babu ita. " Fashewa da kuka Zainab ta yi "Ka gani KO! a Asibitin ma ban tsira ba. Wannan aljanar Kasheni take so tayi Ka kiramin dangina wallahi a tsorace nake" rarrashinta ya Fara yi Doctor kuwa da mamaki ya ke kallonta. "Kamar maganar aljana na ji kuma yi KO, Kai kun bani dariya. Asibitin nan kafin mu bude ta sai da muka Kira shugaban masu ibada daga wata babbar church, don haka kada kiyi tunanin fatalwa KO aljana zata iya shigowa" shuru Usman ya yi saboda Shi ma Bai yarda aljana ba ce. Kawai dai abin da ya sakarwa ransa wata Mai Shirin haddasa fitina ce ta bullo. Daren ranar ba su runtsa ba da asuba ma hana Shi fita sallah tayi sai dai suka yi ta a cikin dakin. Gari na Fara haske sai ga su Kaka sun iso. Ganinsu ya saka Zainab rirrike kaka tana Mai fashewa da kuka. "subhanallahi! Usmanu me ya faru da ita na ga duk ta fita hayyacinta?" Shuru ya yi ya na sosai Kai. A abin da ya fahimta in ya yi wasa kakar nan tata tsaf zata girgide masa aure. "Kaka Kasheni su ke Shirin yi, ni na sani wallahi bibiyata suke yi." Kaf abin da ya faru ta kwashe ta Sanar da su. Salati da sallallami suka hau yi cikin tashin hankali. "Kasan wadannan abubuwan su na faruwa Amma baka taba fada mini ba, bare a nemar maku magani. Aiko ya Zama farillah Ka kawota gida har sai an yi Mata magani." cewar Kaka. "Hajiya ba haka ya kamata ba, yarinyar nan addu'a ce kwata-kwata na fuskanci bata yi Amma jikina na bani babu wasu aljanu da ke damunta" Umma ta fada. Mahaifinta ne ya karbe zancen "yawwa Nima abin da nake son fada Kenan. Sai kuma tsoro data sakawa rayuwarta, tsoro Abu ne Mai kyau a wani lokaci Amma a wani lokacin ba Shi da amfani. Daga inda ya yiwa mutum yawa komai zai iya faruwa. Amma don Allah Hajiya ki daina maganar zuwa wurin masu magani mafi yawancinsu mushurikai ne"  "Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun! Shi Kenan Hadi Ka fitar da ni daga cikin musulumci, yanzu ni ce kafira ?" Zabura Alhaji Hadi ya yi tare da zubewa a saman gwuiwowinsa "don girman Allah Hajiya kiyi hakuri kinga a cikin mutane muke Kada kitara mana jama'a." "Na Tara din ni zaka Kira da bokanya, ni da na tsuguna na haifeka Hadi?" Kasa magana ya yi Domin in da sabo ya Saba da halin Hajiya, in ya biye Mata kaf mutanen Asibitin zata iya Tara masu su. Hakuri ya bata ya fita daga waje. Sallamar da suka yi CE ta saka Su Kaka kallon kofar. Mahaifiyar Usman ce tare da kanwarsa. Yadda kasan sun ga kashi haka suke yamutsa fuska ba Wanda suka yi ma magana kallon Usman tayi. Da sauri ya hau gaidata. "Kayi min shuru da wani rawar jiki saboda an kwantar da matar gwal a Asibiti, abin da nake so in ji Shi ne ba dai ciki ba ne KO? Don in dai Shi ne sai dai idan da abinta ta zo, wata biyar kadai a ce an Fara laulayi. Don wallahi KO da bakar jaba suke tsafi sai kun rabu, in Banda kaddara daka dorawa kanka da rashin Jin maganata ina Kai ina wannan yarinyar" ta karasa maganar ta na Mai nuna Zainab da tayi mutuwar zaune tun farko Fara maganar. "Ki bar su Mama AI Shi idonsa ya rufe an kwaso budurwa+ an yaba masa ta ina zai gane cutarsa akayi" cewar auta. A fusace Kaka ta Fara magana. "Amma ke dai tsufa ya zo Miki da gardama. Daga fadowarki cikin daki sai ki hau aibata mana jika KO gaisuwa babu tsabar tsana da kiyayyar da kika yima yarinyar KO halin da take ciki Baki duba ba. To Bude kunnuwanki da kyau ki jini. Ko da a ce cikin gareta Kai a ma dauka ya zarta wata biyar, ke Bari ma in fito Miki a mutum ko yau Zainab ta haihu ki so ko kuma ki ki da dai na Danki ne. Saboda KO saurayi yarinyar nan bata kulawa sai Danki" Kaka ta karasa maganar a fusace. "ke tsohuwa ki gyara kalamanki kafin in saita Miki bakinki. Ke har kin isa uwata na fada kina fada. KO da ya ke in dai rashin tarbiyya ne tsotsarsa Ku Ka yi." Tatsss kake ji. Usman ya dauke Auta da lafiyayyan mari, ajiye hannunsa Kenan Mama ta daukesa da Mari dama da Hagu. "Shashasha Wanda Bai San inda ke yi masa ciwo ba. A gabana zaka daki yar uwarka akan waccan shegiyar matar taka?" Ta karasa maganar tana huci. Auta a fusace ta fizgo Zainab da ke saman gado ta rufeta da duka, ganin haka ya saka Kaka dauketa da Mari ta hau jibgarta. Mama kuwa ganin sun yi ma autarta taron dangi ihu ta rika yi tana neman dauki ita ma ta afka aka ci gaba da fadan da ita. Kafin kace me wuri ya koma filin dambe mutanen da ke kusa da dakunan kowa ya fito kallon wannan sabon tashin hankali da KO a tarihi ba su taba Jin anyi irinsa ba a cikin asibiti...

***