HADUWAR DARE

Chapter 11&12

by @meenatyandoma

*HAƊUWAR DARE*

©️Meenat A. 'Yandoma

MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION

Page 11&12
... Security ne suka shigo dakin da kyar da jibin goshi suka rasa fadan. Mama sai faman surfa ihu take tana debewa dangin Zainab albarka. "Ba dai kun nunamin tsafi da asiri shi ne abin da ku ka iya ba? Kun taba Ni da ɗana. Ku saurari zuwana sai da ɗaiɗaita rayuwarku ta yadda za ku ji kun tsani duniya me ma ya saka kuka hada iri da mu." Mama ta karasa maganar tana mai kamo hannun Auta. "Ai kin jima da makara, tunda har kika bari ya auri Zainab ina mai tabbatar miki da sai gani sai hange ke in takaice miki magana ta koma karama har abada ba za ki iya raba wannan auren ba" kaka ta fada.
"Hajiya don girman Allah kuyi hakuri. A asibiti muke cikin mutane ku duba ku ga yadda hankalin mutane duk ya dawo kanmu" Umma ta fada. "Ke ar! Mara buri kamar ba diyarki ba ce aka gama yi ma Zagin tafasar Zaliha amma har kike da bakin fadar haka?"
Alhaji Hadi ne ya shigo wurin a rikice ganin mutane sun cika dakin kamar wata kasuwa ce ke ci a wurin.
"Subhanallah! Lafiya me ya faru?" Ya karasa maganar yana tallafo habar Usman da ke hawayen bakin ciki. "Dole ka tambaya lafiya ai ba ku ma ga komai ba tunda da Ni za kuyi fada zaku tabbatar da ni din dai ce wadda ta haifi Usman. Kurwarsa da ku ka kama zan amso ta da karfin tsiya."
"Subhanallahi! Me kuke fadi haka tsafi kuma. Kinga don girman Allah in matsala ce kamata ya yi mu kebe sai a tattauna, amma yanzu cikin mutane kowa ya fito ya na jin abinda muke fada tamkar muna tonawa kanmu asiri ne" 
"Kunga bayin Allah! Ku fita daga dakin nan tunda dai ba zaku daina fadan nan ba" Security ya fada ya na mai nuna masu hanya. "To karamin mara kunya ba sai ka fada ba yanzu zamu fita mu bar maku asibiti ku" ta karasa maganar tare da fizgar hannun Auta suka fice. Bayan su Usman ya bi cikin kunar zuci sai dai ba shi ya cimma su ba sai a bakin titi. "Au! Biyomu Ka yi ka karasa wulakanta mu, ko ka bace mini da Gani ko in yi maka abin da baka taba yin zato ba" ta karasa maganar tana nunasa da yatsa.
Ba yadda ya iya ya na ji ya na gani a tasi suka hau. Ajiyar zuciya ya sauke zuciyarsa cunkushe da tunanin abin da zai je ya tarar idan ya iske ta gidan. 
Ƙarar wayarsa ya ji daidai lokacin da zai shiga asibitin. Ganin mai kiran ya saka shi sauke ajiyar zuciya bai san lokacin da murmushi ya suɓuce masa ba. Ya dauki mintuna sha biyar suna waya kafin koma cikin. Cunkuson mutanen kowa ya watse sai dangin Zainab da Ke ta faman kimanin wannan lamari. Musamman Umma, bata ji dadin abin da ya faru ba ko alama. Allah ya ga abin da ke cikin zuciyarta ta so a ce Zainab ta Samu kwanciyar hankali da fahimtar juna a tsakaninsu da dangin mijinta amma ina Hajiya ta karasa lalata komai. Ajiyar zuciya ta sauke sa'in da ta ji Hajiyar ta ci gaba da magana. "A da nayi tunanin Jikalliya ta bi mu gida har jikinta ya samu ya warware, amma yanzu na canza shawara gidan mijinta zata koma ko dan In nunawa matar can cewar bata isa ta shiga tsakanin mata da miji ba.” 
“Hajiya sai nake ganin abin da kika biye mata ku ka yi bai kamata ba. Kamata ya yi a ce anyi magana ta fahimta ba wai shiga rikici har mutane su san halin da muke ciki ba" 
"Hadi! Kayi min shuru har ka fini sanin abin da ke daidai. To na yanke da anyi sallama gidan mijinta zamu wuce da ita, kafin in kimtsa in koma gidan ta inga yadda zaman ke kasancewa." Shigowar likita ta saka ta yin shuru. Bayan ya gama dubata sauran magunguna ya rubuta tare da rubuta masu takardar sallama. Ba karamin dadi Hajiya ta ji ba koba komai yau zasu koma gida saboda ta tsani zaman asibitin nan. Ba don umma  ta so ba haka suka kwasa aka tafi mayar da Zainab Gidan miji, wadda ita a tsarin ta bata so komawa yanzu na. So tayi a barta har sai ta samu sauki sosai ta yadda za a nemar mata maganin ci gaba da zama a gidan can, saboda bata manta da azabar da ta sha ba. Lallabata kaka ke yi akan cewa zata dawo nan ba da jimawa ba ta rika taya ta zama na wani lokaci. Tun bayan fitarsu Usman ke cikin damuwa wadda ta kasa boyuwa a fuskarsa. "Usman lafiya kuwa?" 
Ajiyar zuciya ya sauke. "Lafiya da sauki Zainab. Ina tunanin irin haɗuwar da zanyi da mahaifiyata idan naje gida, zainab ina kaunar ki sosai haka ita ma mahaifiyata soyayyar da nake yi mata ta daban ce. Sabanin da kuke samu da ita ya na matukar yi mini ciwo. Banjin dadin abin da ya faru ba ko alama. Tsoro na Allah tsorona kada ta dauki mummunan matakin da zai gigita rayuwarmu"
Shuru ta yi domin tun kafin aurensu ta san bata cikin zuciyar mahaifiyarsa. Babu yadda za ta yi domin wanda ya rigaka kwana tasan sai ya rigaka tashi...

Mama kuwa bata bari suka koma gida ba saboda zuciyarta a matukar fusace take. Da dukan kokarinta ita da auta suka nufi wurin boka.
Kamar yadda aka saba yau ma kafin su furta bukatarsu  bokan ya fara rattaba masu bayani. "Aikin ki akwai hadari, tabbas kamar yadda kika fada ɗanki zai kara aure. Amma fa babu nutsuwa bare alkhairi a cikin sha'anin shin kin amince?"
"Boka! Ina dai zai kara aure yarinyar can ita da dangi ta su tozarta duk hadari da wahalar dake ciki na amince."
Tuntsurewa ya yi da mahaukaciyar dariya. "Tabbas hankalin shi zai dawo kanki, ina mai kara maimaita miki akwai hadari za ki iya rasa wani abu mai matukar muhimmanci wanda ni kaina na kasa gane wane abu ne" 
"A'a Mama kada ki amince da aikin nan, idan kaikayi ya koma kan mashekiya fa, ni dai na tsorata kada a ce garin gyaran gira a tsone ido"
Uwar tsawar da Bokan ya daka ma Auta ce ta sakata hadiye sauran maganar da ke cikin ranta.
"kul na sake jin kin saka mana baki akan maganar da bada ake ake tattaunawa ba, zabi ya na wurin Uwarki ba ke ba"
"Tuba take boka yarinya ce bata san gaban wanda take ba. Ayi mata aikin gafara, sannan maganar hatsari ko wani abu makamancin hanka ban damu da shi ba domin ni kaina na rasa gane wace irin tsana nake yiwa sirikata ba, ko kasheta aka yi ina ji a zuciyata ba zan huce daga ɓacin ran da suka sakani ba"
A karo na biyu ya sake ke cewa da dariya. "Tabbas kin bata kinyi nisa amma tunda haka kika zaba mu zamu cika miki burinki. Ki kuka da kanki duk abin da ya biyo baya" ya karasa maganar tare da janyo wani katon kasko mai cike da ruwa. Wani kara ya dauko yana wasa da shi a kan ruwan tambar mai yin rubutu, ya dauki mintuna da dama kafin ya ɗago kansa ya kalli Mama. "Leko ki ganewa idonki"
Auta hada rawar jiki ta ke shirin lekawa.
Tsawa ya daka mata. 
"Da kinyi gigin lekawa makancewa za kiyi"
Dafe kirji tayi a tsorace jin abin da bokan ya fada.
Mama kuwa Cike da farin ciki ta leka cikin kasko. Zabura ta yi ta fiddo ido waje, zuciyarta na lugude tamkar zata faso kirjinka ta fado kasa sakamakon abin da ta gani...

Wannan littafin na kudi ne. Za ku biya 500 a wannan account din 8133562798 Opay AMINA ABUBAKAR.
Ko kuma ku turo katin MTN ta wannan Number ***

Saura Page Biyu mu karasa free pages.

Meenat A. 'Yandoma
***

***