Nepo Baby
***
It's fatoumspassion IMSAL
Another exclusive piece from the passionate writer of AYSAM, INTENSE LOVE, EHSAAS and SCARRED.
Free pages
Chapter 12
(Nepo Baby)
Tun daga ranar da Farouq yaga hoton Imsal a wayar ta komai ya canza,
Mummy ta fara lura da yadda yake treating ɗinta ya bambanta, da dacan kafin yaga Imsal, ba wai gaba ɗaya ya daina halinsa ba, arrogance ɗinsa yana nan, attitude ɗinsa ma duk yana nan.
Amman sosai yake raga mata akan sauran ma'aikatan sa baki ɗaya, Idan za’ayi meeting indai yaji sunan Barrister Aisha yana ciki, yana ƙoƙarin zuwa kan lokaci don ya fahimci idan akwai abinda tafi tsana atattare dashi be wuce late coming ba.
Idan tana bayani haka ze bada attention ɗinsa ba tareda danna waya ko any gadget ba yana sauraronta,
ba kamar da can da sometimes tana yi yana katse ta yana tafiya hutu, kuma duk tsaf Mummy ta lura dashi,
aranta jira kawai ta ranar da zezo ya faɗi abinda yake cikin zuciyar sa game da yarta ita kuma alokacin zata fara jan nata zaren.
Ko sati ba'ayiba ya kasa hakuri, ya kawo kansa har cikin office ɗinta dake building ɗin Nexora, duk sanda take da aiki dashi inta shigo anan take zama.
tana zaune ranar wata wednesday bata jima da shigowa ba tana ta aiki kan wasu files a laptop ɗinta taji ana knocking,
is so unlike him yayi knocking idan ze shigo guri straight yake turo ƙofa ya shiga ko inane kuwa, jin ana knocking bata kawo shi bane tace
“Come in.”
Turo ƙofatr yayi ya shigo cikin wata dark brown colour suit babu necktie as usual ya buɗe shirt ɗinsa ta ciki cikakken ƙirjinsa duk awaje gefen wiyansa tattoo ɗinsa na showing sosai,
hannayen suit din ya tattare sun dawo gwiwar hannu, ɗagowa tai tana kallonsa da alamar tambaya tana faɗin
“Mr Farouq?”
Kai tsaye yace mata
“I need file ɗin da muka tattauna akai earlier,”
Miƙewa tai tana faɗin
“yana cikin inner office bari na ɗauko.”
Wucewa tayi ta shige cikin inner office ɗinta don lalubo mishi file ɗin da yake bukata.
Tana ɓace wa daga sight ɗinsa, Idonsa ya koma kan wayarta, ba tare da ɓata lokaci ba ya ɗauka,
Ya samu guri ya zauna yadda kikasan tasa da hannunsa na hagu kasancewar sa lefty ya fara operating wayar, duk da cewa da password akai in few seconds yayi unlocking ɗinta,
Wani shegen smirk ne ya bayyana a saman fuskarsa yana faɗin
“Predictable…”
Gallery ya shiga in no time ya fara laluban hotunan Imsal aikuwa nan take ya shiga cin karo dasu,
Hotuna da dama, na gida, na school, da random moments videos, be dau tsawan lokaci ba kawai ya shiga turasu cikin tasa wayar da sauri.
daidai hotunan yana gama shiga wayarsa ya farajin takun heel ɗinta alamar ta fito tana bayansa,
ƙoƙarin ajje wayar ya keyi amman harta zagayo, suka haɗa ido, kallon tuhuma ta shiga yi masa ko a jikinsa ya ajje wayar saman table, itama ajje file ɗin data dakko tayi tana tambayarsa
“Me kake yi da wayata?”
Da wata iriyar strict voice dabe taɓa jinta da ita ba,
jingina yayi jikin kujera, anitse yace mata
“Relax.”
ƙanƙantar da idanuwanta tai looking damn serious tace
“Answer me, Farouq.”
Jin ta kira shi Farouq kai tsaye yasa ya ɗan kalleta, kafin ya taɓe baki cikeda izza yace
“Akwai asset ɗina ne mai girma a ciki.”
Ya ƙarasa faɗa kanshi tsaye
tsayawa tai cak,
dan mamaki tana faɗin
“Excuse me?”
gyara zamansa ya ɗanyi yana faɗin
“Your daughter.”
Jin abinda yace Mummy ta saita nutsuwar ta tana dubanshi da kyau tana tambayar sa,
“Me kake nufi?”
Ɗage girarsa guda ɗaya yayi sama looking completely unbothered yace
“I want her.”
Zama Mummy tayi tana sauke numfashi pretending as if abinda ya faɗa be daketa tace
“Farouq…”
Kafin ta karasa faɗar me zata faɗa ya katse mata hanzarinta ta hanyar faɗin
“Imsal Umar”
Ya ɗaura da
“Seventeen, Kano, attending Imperial Highschool, SS2, Hafiza”
Da mamaki take kallonsa jin yadda yake zazzago bayanai akan yar ta,
Ya cigaba
“Quiet, Introverted, No public exposure, She have a very clean record.”
Ya ɗan ɗago daga saman kujerar yana crossing legs ɗinsa yace
“She’s exactly my type.”
Mummy shiru tayi na wasu sakanni tana processing yadda ya zama ahead of her,
Tace
“bibiyar min yarinya ka saka akayi kenan?” ta tambaya afusace
Anitse yace
“Of course.”
Kafin ya ɗanyi dariya yana kaɗa kansa,
Mummy basarwa tayi katta nuna zalamarta afili ya rainata tace
“Farouq… yarinya ce.”
“Not for long,” ya bata amsa hankalinsa kwance
tace
“Karatu take yi.”
“Zata gama,” ya sake bata amsa,
Girgiza kai tayi don so take seta jamasa rai tukunna don yasan darajar yarta tace mai
“No.”
Girarsa ɗaya ya sake ɗagewa wanda ta lura ɗabi'arsa ce yin hakan alamar tambaya, ganin be fahimci ma'anar no ɗin da tace ba yasa ta sake maimaita masa
“My answer is no.”
ɗan karkatar da kansa yayi yana mata kallon mamaki yace
“Because of my reputation?”
Kai tsaye tace masa
“eh.”
Kafin ta cigaba
“My daughter is not… your type of woman.”
Wani dangerous smile ne ya bayyana saman face ɗinsa yana fito da dimples ɗinsa da suke ƙarawa face ɗinsa wani irin kyau na musamman yace
“And what type am I?”
Haɗe rai Mummy tayi tana faɗin
“Not her kind.”
Gyara zamansa yayi looking very serious ba kamar ɗazun da yake magana cikin fara'a ba yace
“I have a deal for you.”
Kallon tuhuma ta kuma yimasa don tasan yaron mugun sheɗani ne,
Tace
“Farouq...”
Ɗaga hannunsa ɗaya yayi sama alamar dakatar da ita yana fadin
“Just listen.”
Shiru tai tana sauraransa kamar yadda ya buƙata ɗin
Yace
“na san me kike so?”
Kallonsa tai da alamar tambaya a idanuwanta
Ya cigaba
“Attorney General of the Federation.”
Kasa ɓoye shock ɗin data shiga tayi seda ya bayyana asaman fuskarta,
ganin haka yasa yayi wani miskilin murmushi yana faɗin
“I know how much you want it.”
Jin batace komai ba yasa yace
“I can make it happen kinsan da hakan shiyasa ma kika jure aiki a ƙarƙashina.”
Mummy kasa magana tai don gaba ɗaya ya shallake dukkan tinaninta wato duk abinda take ciki yana sane kar yake kallon ta,
Ahankali yace
“Trade by barter.”
Gyara zama tai tana sauraronsa
Yace
“Ki bani ita, ni kuma zan baki kujerar da kike buri tsawan rayuwar ki.”
Wani irin mugun shiru ne ya ratsa office ɗin sanda ya gama maganar kawai tai ɗuf, tana tinanin yadda zata ɓullowa lamarin batasan sanda ta samu couraage ɗin kallonsa ba tana faɗin
“GET OUT.”
ɗan kallonta yayi ganin she's damn serious korarsa take daga ɗaya daga cikin offices ɗin dake cikin Company ɗinsa, ba tareda ya motsa ba yace
“Barrister...”
Katse sa tai saurin yi tana nuna mishi ƙofa tana fadin
“I Said OUT.”
Idonta cikeda fushi
Kafin tace
“Ba zan taɓa ba ka ‘yata ba, ita ɗin ba yar tsana bace da zaka sakata a bet ka mallaketa ko ka saka kuɗi ka siye ta”
Ta ƙarasa numfashinta na fita da sauri da sauri,
Girgiza ƙafa ya farayi yana faɗin
"Mummy calm down kibar fushi kada zuciyar ki tai miki ciwo"
Awani iskace,
Tace
"Nasan inada mafarkin zama Attorney General of federation kuma babban burina ne,
amma not at the expense of giving my daughter to you"
Miƙewa Farouq yayi yaɗan gyara cuff ɗinsa, ya kalleta na ɗan lokaci kafin yace
“You’ll think about it.”
Irin his very sure of himself ɗinnan,
Jujjuya kanta ta fara yi tana faɗin
“Never.”
Cikeda ƙarfin hali,
Tsugunnowa yayi yana kallon cikin idonta yace
“Everyone does… eventually.”
Ya juya ya fice a office ɗin yana rufo mata ƙofa.
Mummy yana fita ta dafe kanta tana jin tama kasa tinanin abinda zata aiwatar kawai ta ɗau waya ta shiga kiran Hajiya Nafisa tana laburta mata duk abinda ya faru,
itama Hajiya Nafisa supporting ɗin yadda ta koreshin tayi tace mata koda zasu bashi Imsal ba dai ta cikin sauƙi haka ba,
se sun tabbatar idan auren ta zeyi da gaske bawai lust bane kawai ya saka yake son abashi ita.
jinjina kai tayi bayan sun gama wayar hankalinta ya kwanta ta mike tana tattare files ɗinta ta fice tabar office ɗin baki ɗaya ta koma law firm ɗinsu.
kwana biyu da faruwar wannan abu, Mummy bata sake ji daga Farouq ba,
Abin ya bata mamaki, don tasan halinsa shi ba irin mutanen da ake ce musu“no” bane kuma no ɗin tayi aiki gurin hanasu mallakar abinda suke so.
Sai kuwa gashi arana ta uku tana office ɗinta nacan firm ɗinsu, secretary ɗinta ta shigo tana sanar mata cewa,
“First Lady is here to see you.”
Murmushi tai tana jinjina kai ganin haƙarta ta soma cimma ruwa anfara tafiya high,
gyara nutsuwar ta tai tana cemata
"Kice ta shigo"
Ko second biyu batai ba se gata ta shigo itada security dinta da take rike da handbag ɗinta ta chake aƙofar.
Ita ta ƙaraso cike da class don Hajiya Farida macece mai tsantsar waye wa,
ga aji da gayu kana kallonta tun daga ɗan kakkauran jikinta da kalar fatarta da dakakkiyar suturar da take jikinta zaka gane cewa arziƙi,hutu da mulki ya gama ratsa ta irin manyan matannan ne da ake ji dasu aƙasar ake kuma damawa dasu.
dasauri Mummy ta miƙe cikin nuna girmamawa har suka rungume juna tana bata air kiss, cike da faran faran take faɗin
“Assalamu alaikum SAN”
“Wa alaikumussalam Your excellency,"
Mummy ta amsa itama cike da da tata wayewar da fara'a, gurin zama ta bata, kafin itama ta zauna bayan ta tambayeta me za'a kawo mata,
girgiza kanta tai alamar babu komai kawai.
Gyaɗa kai Mummy tai tana bata attention ɗinta baki ɗaya,
Murmushi Hajiya Farida tayi tana tambayar ta
“Farouq ya zo ya same ki ko?”
Mummy jan numfashi tayi kafin tace
“eh..... ya zo.”
Murmushi Hajiya Farida tai tana faɗin
“ya faɗamin.”
Ta ɗan gyara zamanta tana facing Mummy tace
“Nima na zo ne saboda shi.”
Shiru Mummy tayi alamar tana sauraranta
“Barrister Aisha…”
Hajiya Farida ta faɗa cikeda nutsuwa
Mummy tace
"Yes your excellency"
Tace
“Ban taɓa ganin ɗana ya kalli wata macen ba tun tasowar sa, balle har yaji yana sonta ya nemi aurenta"
Gyada kai Mummy tayi alamar tana sauraranta,
Hajiya Farida murmushi tai mai laushi tana faɗin
"Naga abinda ban taɓa gani ba awurin Farouq akwanaki biyunnan Barrister yaga yarinyar ki,
kuma yana sonta dagaske, his not here to flirt, aurenta yakeson yi dagaske"
Mummy jin anzo inda ta keso azo ɗin yasa taja ajiyar zuciya tana danne duk wani urge nason amincewa right away tace
“Imsal Yarinyace,
shekarar ta goma sha bakwai gaba ɗaya ko secondary school bata kammala ba...”
Hajiya Farida jinjina kai tai alamar ta fahimta kafin tace
“yace ze jirata Barrister,
shima ɗin ai har yanzun yaro ne his 27, yaushe yaushe yafara rayuwar inaga yafi kowa dacewa da ita,
sannan baze taɓa hanata karatu ba, zeyi supporting ɗinta akan kowana goal dinta inma karatunne ko wani abu daban,
ze bata kariya,kulawa da soyayya da duk wani abu da ya mace mai shekarunta zata buƙata"
Mummy shiru tai kafin tace
"Hajiya Farida bari na fito miki a mutum Farouq siyan ƴata ya keso yayi da kuɗi da power,
ni kuma ƴata tafi karfinsa da duk abinda ya mallaka,
ya gane burina nason kasancewa AGF shine yake son wai muyi trade by barter na bashi ita nima yasa baki Mr president ya bani abinda nakeso,"
Tana ƙarasa mata bayani ta koma baya ta jingina da kujerarta tana sauraron bayanin da Hajiya farida ta soma mata
Tace
"Kinsan shi yarone karami,
be taɓa soyayya ba besan yadda ake yinsa the right way ba,
amman duk abinda ze kalla yaji yana so abune me mugun daraja agurin sa da gurinmu barrister,
yarki tafi karfin asiyeta kamar yadda kika faɗa,
shiyasa nazo da ƙoƙon barata kiyafe masa mu ƙulla wannan alherin tsakanin families ɗinmu,
inaso ki yafe masa wautace yayi saboda besan meye rayuwa ba,"
Jinjina kai Mummy tai irin ta fahimta ɗinnan,
Tace
"shikenan na gane amman inada sharaɗi kuma darajar ki zeci your excellency,"
jinjina kai Hajiya Farida tayi tana faɗin
"Nagode sosai da girmamani da kikai kika saurareni Barrister you'll never regret this in sha Allah,
faɗi sharaɗin naki koma meye mun amince in sha Allah,"
Tace
"seta gama makaranta zama afara maganarsu,
sannan seta amince dashi don ba zanyi mata dole ba,"
Murmushin Hajiya Farida tai cikin gamsuwa take faɗin
"Thank you barrister mun amince,"
Tace
"Sannan Ma, kija mishi kunne yana sakawa ana stalking min yarinya,
ya janye mutanensa akan yarinya ta imba haka ba idan mahaifinta ya gane komai ze iya faruwa"
ɗan jim tai kafin tace
"Kn sha Allah ze janye Barrister,
ai kingama mana alfarma tunda kika amince dashi uwa ai itace jigon gida" murmushi tai jin yadda Hajiya Farida ta huran tata.
Miƙewa tayi tana kallon security ɗinta da sauri matar ta ƙaraso ta karbi handbag ɗinta ta buɗe tana murmushi tace
"barrister karfa kice cin hanci na baki wannan ganin cancantar ki yasa ni da kaina na miƙa sunanki gurin Mr president yace abaki wannan kafin kizama surukarsa officially"
karɓar takardar tayi tana dan murmushi kawai tana Allah Allah Hajiya Farida ta fita ta buɗe har waje ta rakata kafin ta dawo ta shiga buɗe takardar.
Official appointment ne as Special Adviser on Legal Affairs to the Presidency.
Wani babban mukami ne wanda yake very close to abinda take hari wato AGF, amman ne bekai shiba, but she's very happy saboda ko shidin batai tinanin samun sa nan kusa ba,
tai murmushi tana zama kan kujerarta tashiga jujjuyawa,
ta fahimci sarai abinda Farouq yayi ɗanɗanone ya bata na irin ikon da zata samu idan ta zama sirikarsa,
idan ta zama ɗaya daga cikinsu,
idan ta cika mishi burinsa na auren Imsal.
rufe ido tayi tana tinanin kanta da irin rayuwar da zata samarwa da ƴaƴanta idan ta samu wannan matsayi musamman Imsal wacca itace ladder ɗin da ta hau wannan abin yazo mata cikin sauƙi haka.
Hajiya Nafisa ta kirawo, a Abuja yammacin ranar tai mata suka shiga celebrating tun daga wannan lokaci Farouq yake wa imsal hidima ta hanyar mahaifiyarta ba tareda tasan yana yiba don haka kawai ze ɗau millions of dollars ya sama Mummy a account akan ta yiwa Imsal shopping dashi.
kuma bata ƙasa agwiwa haka zata je kano ta ɗibi yaran taita musu siyayya iri iri duk wani abu na yanmata da ta gani seta siya musu Musamman Imsal hatta da skincare ɗinta ya banbanta dana kowa cikin yayanta da kanta ta ɗauketa ta kaita gurin likitan fatarta a Abuja seda ya dubata yaga kalar mayukan da zasu mata ya mata recommending ɗinsu.
hatta wayoyin hannunsu duk cikin kuɗaɗen da Farouq ke saka matane wata rana randomly ze aiko shopping akawo har apartment din Mummy na Abuja abama.
Imsal haka zalika Hajiya farida itama bata ƙasa agwiwa kusan walk in closet ne guda da Imsal aɗakin da Mummy take shirya mata agidanta na Abuja tana zuba mata duk wasu kayayyakin da Farouq da matar ubanshi suke kawowa,
alkhairai take samu tako ina sanadin Farouq hatta da yawan ayyukanta sun ragu saboda kuɗin da take samu a aikin da zatai asati Farouq can send triple of it acikin wuni ɗaya.
Itada Hajiya Nafisa sungama tsara komai kan yadda zasu aurar da Imsal inta kammala secondary school,
ta cigaba da karatun agidan sa biki sukeso suyi wanda ba'a taɓa yinsa ba akaf faɗin Nigeria domin tasan Farouq Nepo baby ne besan ciwan kuɗi ba balle darajar su kashe su ya keyi ba tareda tinanin komai ba musamman lamarin da ya shafi Imsal bayaji baya gani wata irin makauniyar soyayya ya kema yarinya mara linzami.
*Present*
Yau ne ranar da su Imsal suka fara Waec, practical biology ne paper ɗinsu ta farko, hakan yasa ita kaɗai ta shirya bayan sungama wayarsu tareda Abdullah tanata narke mishi tana cemai ita tsoro take ji shikuma yace mata he trust her she'll ace it, haka dai da kyar aka gama wayar ƙarfe goma Malam garba ya ɗauke ta zuwa school ita Natasha yar art ce batayin subject ɗin.
She's nervous gaba ɗayan ta, don sanda taje already ɗalibai sun shiga tayi late amman ba'a fara raba paper ba ƙarasawa tai ta shiga exam hall, ta nemi sit number ɗinta ta zauna.
Cikin awa biyu kusan kowana ɗalibi ya kammala jarrabawarsa,
ta musu daɗi sosai fiye ma da yadda sukai tsammani haka duk suka firfito wasu nata hayaniya wasu na farinciki ganin sun fara cikin sa'a.
Imsal ma cikin jin daɗi ta fito ta tsaya a gefen gate inda Malam Garba yake jiran su in suna ciki,
amman ba kowa alamar be zoba,
ɗan jim tayi ta koma gefe ta jingina da wani ƙarfe tana ta zuba ido tana jiransa har students suka fara raguwa sosai da yake ba ranar makaranta bace susu ka ɗaine masu jarrabawar sukazo,
ganin lokaci naja yasa ta ɗauki wayarta tana tinanin koya mantane ta danna kiransa, seda ta kusa tsinkewa ya ɗaga ahankali tai sallama
“Assalamu alaikum”
Kamma tace komai yace
“Ameen Wa Alaikumussalam Hajiya Imsal,” muryarsa cike da damuwa.
A hankali tace
“Antashi Baba yau fa da wuri muka gama, nace bari na tina maka ko ka manta?
Cikeda damuwa yake faɗin
“dan Allah Hajiya Imsal kiyi haƙuri wllh ban mantaba… babur ɗinne ya samu matsala, kinsan ƙarfen nasara yanzun hakama Ina gurin gyaransa”
Jin tayi shiru yace
“Bari na samo wani na aro, zan zo na ɗauke ki, kiyi haƙuri kinji yar albarka”
girgiza kai tayi kaɗan kamar tana gabansa tace
“A’a Baba, ka barshi kawai, zan samu napep ɗin haya na hau"
Ta faɗi hakane don tasan ze iya zuwa ya wahalar da kansa gurin ganin lallai lallai ya samo aron babur ɗin koda hakan kuwa ze zama damuwa agareshi,
Yace
“Amma Hajiya...”
Bata bari ya ƙarasa ba anitse tace mishi
“Ba komai zan iya, Nagode.”
Tana jin sautin murmushinsa ta wayar yace
"Toh ƴar albarka se kin dawo nagode sosai"
Tace
”Ameen"
tana kashe wayar.
Wata irin rana ake bugawa a garin sosai don lokacin zafi ya shigo ka'in da na'in hakanne yasa yau ko facemask ɗinta bata saka ba,
ta rataya ƙaramar handbag ɗinta da tazo da ita yau,
wacca exam card ɗinta ce, da inhaler da calculator, da kayan rubutunta da some naira notes ne aciki se ta mayar da wayar ma ciki ta fara tafiya ahankali cikin nutsuwa.
Tana fitowa daga school ɗin, wani daga cikin classmates ɗinta Mukhtar shima yana fitowa da motarsa ya shiga danna mata horn, juyawa tai ya zuge glass yana faɗin,
"Malama Imsal baki tafi ba"
da yake yaron yana da kirki suna ɗan gaisawa ta jinjina mishi kai
Yace
“Shigo mana, in sauke ki.”
Kallonsa tai tana girgiza mai kai tace
“A’a nagode.”
yace
“Come on, rana fa, Imsal karta koɗar mana da wannan jar fatar taki”
Jin abinda yace bama ta tsaya sake sauraronsa ba ta juya tana faɗin
“Zan samu napep.”
Ta cigaba da tafiya abinta, sanin halinta ba shigowar zatai ba yasa mukhtar jan motarsa kawai ya wuce.
Trekking ta fara, zuwa babban titi don street ɗin da makarantar su take area ce ta GRA public transport basu fiya yo gurin ba seka fita titi ko in kai sa'a.
A jikinta taji kamar ana binta, juyawa tai taga wata mota lexus tana tafiya slowly a bayanta,
da farko ta dauka kawai hunch ɗinta ne amman ganin motar taƙi sauri ta ƙi gaba duk inda tayi seta bita yasa ta fara jin tsoro ta shiga sauri kaɗan kaɗan,
horn motar ta fara mata ƙasa ƙasa,
Cikin tsoro ta riƙe jakarta ƙamƙam da niyar takewa ta fara gudu kawai wata napep ta fito daga wani layi da sauri ta shiga tare shi tana faɗin
"Malam tsaya, Please tsaya"
Tsaya wa yayi aiko tai daurin shigewa da gaggawa tana faɗin
"Goron Dutse"
Ja me napep yayi,
yana yin gaba,
se alokacin hankalinta ya kwanta ta jingina da ƙarfen tana daidaita numfashinta ahankali.
Seda sukai kusan tsakiyar hanya idonta ya sauka akan mirror ɗin gefen, har lokacin motar na biye dasu, anan ta ƙara tabbatar wa ita ake bi motar baƙiƙƙirin, gata da tint me shegen duhu karyar ka, ka gane waye aciki duk saka idonka.
Zuciyar ta ce ta fara bugawa da sauri,
ta riƙe gefen napep ɗin da ƙarfi, ta shiga jero addu'o'in neman tsari har suka iso ƙofar layinsu,
nuna masa inda zeyi tayi,
ya shigar da ita har ciki, har sannan motar na biye da ita adaidai kofar gidan Hajiya ya sauketa layin tsit ba kowa da yake tsakiyar rana ce duk ba jama'a sosai.
Buɗe purse ɗinta tai tsabar tsoro hannunta ya shiga rawa inhaler ɗinta ta faɗo ƙasa da pen ɗinta, bata bi takansu ba, tashiga laluben kuɗin data zira cikin ƙaramin zip wani irin ƙamshin turarene ya daki hancinta, kafin taji tsayuwar mutum kamar abayanta, tsayawa tai chak tana rarraba ido,
"ungo wannan"
Ya faɗa yana miƙa mishi 1k note, karɓa me napep din yayi yana ƙoƙarin bashi change, yace
"jeka kawai"
da sauri Imsal ta juya suka haɗa ido da wani saurayi matashi wanda baze fi age mate ɗin su Rayyan ba cikin wani white medicated shades, da wani sea blue yard mai laushi ajikinsa, harda hula akansa, he's very fair don da kaɗan zata iya finsa haske.
Tace
"ka barshi kawai gashi"
ta shiga lalube tana ciro kuɗin ta me napep har ya ƙara gaba.
Juyowa tai kanta aƙasa ta mika masa kuɗin tana faɗin
"nagode,"
murmushi taji ba tareda ya karɓi kuɗin ba yace
"aiba ke na bawa ba kyakkyawa"
ganin baze karɓa ba neman magana ya keyi yasa tai saurin ƙarasawa gaban gate ɗin gidan ta shiga bugawa,
tsugunnawa saurayin yayi ya daukar mata pen ɗinta da inhaler data yar yana bin bayanta yana ganin yadda take kakkare fuska da hannu ɗaya saboda ranar da take dukanta, yace
"your things beautiful,"
bata juyo ta kalleshi ba balle ta amsa ta cigaba da buga gidan duk a tsorace take kamar kice kurket ta saka gudu.
jingina yayi da jikin gate din ya kalli yadda ɗan hannun nata farare tas suke buga gate ɗin,
Ahankali yace
"Please listen to me kinji yar makaranta nasan your desperate ki shiga gida, amma not it seems universe ɗinma is in my favour gashi anƙi zuwa abuɗe miki kawai ki faɗamin sunanki kiban number ki sena dawo takanas tunda naga gidan,"
Shiru tai masa yadda kasan da gunki yake magana ahankali yace
"haba baiwar Allah,
don Allah kice wani abu mana,"
jin yace don Allah yasa ta waiwayo kanta aƙasa tana tsayawa da buga ƙofar tace
"dan Allah nima ka tafi Nagode,"
Murmushi yayi yana riƙe da inhaler ɗinta yace
"toh se kin karɓi abinki zan tafi sannan ki bani number wayarki"
hannunta ta buɗe tana miƙa masa alamar ya bata kayan ta memakon yasa mata seya tsaya yana bin fararen tafin hannun da kallo ita sam bata sani ba jira take kawai yasa mata kayanta ta cigaba da bugunta.
kawai sukaji ana danna musu horn da alamar motarsa tayi blocking wanda ze shiga gidan juyawa yayi yana kallon motar wacca da alama gidan zata shiga ya kalli Imsal yana faɗin
"kyakkyawa gidanku akazo bari na gyara parking ɗina ko,"
yana saka mata inhaler ɗinta saman hannunta,
da sauri ta cigaba da bugu jin horn ɗin yayi yawa yasa ta juya, batasan sanda ta damke inhaler ɗinta da pen din dake hannunta ba, tanajin kamar ta saki fitsari a wando tsabar shakka, idonta akan motar, wanda ya biyota ne ya janye tasa motar,
@360 ya ƙaraso da motar daf da ita kamar zema bugeta da ita amman yanayin daf da daf ya tsaya,
daidai Malam Haruna daya zagaya bayan gida tun ɗazun yana ƙarasowa,
ya zuge gate batasan sanda ta wuce gida da sauri ba, ƙafarta na hahharɗewa tanajin motarsa bayanta alamar shima shigowar yayi.
bata sake yunƙurin juyawa ba har ta ƙarasa main door na gidan tsabar ruɗewa batasan sanda ta fara kiciniyar buɗe kofar ba, jinta arufe yasa ta danna bell da sauri, Muryar Natasha ce taji tana faɗin
"waye?
waye ze fasa mana dodon kunnenmu, eh?da sauri Imsal tace
"its me Nats open the door,"
buɗewa Natasha ta shiga yi tana faɗin
"au dama kece ya Imsal ya...."
bata ƙarasa ba taga Imsal ta raɓa ta gefen ta tawuce ciki da sauri binta da kallo tai tana faɗin
"Lafiya,"
Ganin bata kula taba yasa ta juya zata rufe ƙofar hango Abdullah da yagama parking tai ya fito fuskar sa ahaɗe bubu rahma ko kaɗan yana tunkaro cikin gidan ta juya ta kalli bayan Imsal da tini tai gida ta dawo da kallonta gareshi da daf yake da ƙaraso wa tace
"hmmm tare suka dawo kenan,
Ya na ganshi afusace,
Meya haɗasu kuma?"
tsabar son ganin ƙwaf ƙwaf jatai ta tsaya har ya ƙaraso,
tace
"ya mu'allim ina wuni ashe tare kuke,"
ɗan juyawa yayi ya kalleta wani irin ja taga idonsa yayi sosai taji tsoro ta ɗan matsa baya tana kallon yadda jijiyoyin kansa suka tashi kana kallonsa kasan a fusace yake,
ba tareda ya amsa gaisuwar taba yace "where is she?"
Ciki ta nuna masa be ko sake kallonta ba taga yayi ciki, ta tsaya tana riƙe ƙugu tana faɗin
"toh fah aini nasan za'a rina wai zafi zanin mahaukaciya."
It's fatoumspassion IMSAL
Don't forget to
Like
Share
Vote
Comment.
SPECIAL ANNOUNCEMENT
Ina farin cikin sanar muku cewa zan fara posting sabon novel dina IMSAAL a ArewaPen da Wattpad 🤍
But don’t worry… WhatsApp readers are still my priority 🫶🏽
Nothing is changing here, this is still home ❤️
To celebrate this, I have something special for my real supporters
🎁 The FIRST 20 PEOPLE to:
✔ Follow me on ArewaPen
✔ Follow me on Wattpad
Will get FREE entry into my paid WhatsApp group 💫
🎁 HOW TO QUALIFY 🎁
After following me,
📌 Take a screenshot showing you’re following me on BOTH platforms
Then send it to me on WhatsApp 👇
📩 ***
⚠️ Include your username
⚠️ Only the first 20 valid people will be accepted
⚠️ No screenshot = no entry 👀
ArewaPen @fatoumspassion
Wattpad @fatoumspassion
Hurry… once the 20 slots are gone, that’s all 🔥